Showing 54001 words to 57000 words out of 270744 words
gaskiya ba zan kyaleta ba!".
Sake Rimshar Lion ɗin ya yi yana mai dawo da kallonsa a kan Areef dake kare mashi kallo shi ma. "Me kake zuwa yi a wajen Josephine time da kake zuwa wajenta?". Shi ne tambayar da Lion ɗin ya wurga mashi.
Miƙewa daga jikinsa Rimshar ta yi, sannan ta nufi kofar fita. Hannunta Areef ɗin ya riko yana tsokanarta "Sister yau kin mance da ni ko? Wato ma fita zaki yi kamar baki ganni ba ko?".
Katse shi Lion ɗin ya yi da cewa "Saketa ta wuce, sannan ka juyo ka bani amsa ta".
Kasa sakin nata Areef ɗin ya yi, dan shi ya ji ne ma kamar bai san wacece Josephine ɗin ba, baya son a kawo mashi maganarta, dan haka sai ya ce "Wai kai Lion ka bari mu gaisa da ita mana".
Sosai Aseef ya yi mamakin abin da Areef ɗin ya yi, shi dai a iya saninsa ya san cewa Areef ɗin yana yawan tsawatar mashi a kan kada ya kuskura ya rinƙa rungumar Rimsha, or ya kamata hannunta a gaban Lion, idan ba haka ba, to za su yi babu daɗi da Lion ɗin, dan wannan uban kishin nasa, to ya aka yi yau shi kuma Areef ɗin da kansa ya rike mata hannu, kuma har Lion ɗin ya ce ya saketa, amma yaki, anya kuwa babu wata alamar tambaya a nan?.
Shi kuwa Lion ɗin sam bai ɗauki zafi ba, saboda ya lura, yanzu koma ta halin ƙaƙa, so ake a kai shi ƙasa, so ake a rinƙa fusata shi, yana ɗaukar zafi, har ta kai ta kawo zuciyar ta kasa ɗauka, ta buga ya mutu kowa ya huta, tun da ya fahimci haka kuwa, to ba shakka zai yi taka tsantsan wajen ganin ya danni zuciyarsa ba zai ɗauki zafi ba!! Wannan shi ne yaki sunkuru, Lion dai yana faɗa da aljani, shi baya ganinsu, amma su kuma suna ganin duk wani motsinsa.
Hannun Rimshar ya riko tare da jawota ta dawo jikinsa, cikin sanyin murya ya ce da Areef ɗin "Now amsa me".
Ita dai Rimsha yau tana ganin abin mamaki, ta lura yau gabaɗaya TRIPLETS ɗin a tsai tsaye suke magana da junansu, kamar ba lafiya ba, magana suke yi kai tsaye kawai.
"Saif ni ba wani abin da nake zuwa yi gidanta face gaisuwa, shi kawai nake zuwa yi".
Aseef ne ya amsa da cewa "Ba wani gaisuwa, akwai dai abin da yake kaika, Allah gara ma ka rabu da matar nan, duk da cewa ta taimakawa Momma a baya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana wani yamutse fuska.
"Anywhere zamu koma Washington gobe idan Allah ya kai mu, kuma gabaɗayanmu zamu tafi, saboda mun gama abin da ya kawo mu Naija, so idan mun bar Naija, mun barta kenan har abada!". Cewar Lion.
Da sauri Rimsha ta ɗago kai tana kallonsa, da mamaki fal a face nata ta ce "Noorish to ita kuma gwaggo fa?".
Shiru ya yi bai amsa mata ba. Areef ne ya amsa mata da cewa "Da Momma da ke da my baby, Heartbeat, dukka zamu tafi da ku mana, ai ku kun sallami Naija kenan".
Zaro dara daran idanuwan nan nata ta yi, a tsorace ta ce "To daddyna da mummyna fa?".
Aseef ne ya amsa mata da "A nan zaki barsu mana".
Sam bata san time ɗin da ta furta, "Na shiga uku na! Wlh ni ba zan je ko'ina ba, sai dai ku tafi ku barni". Bata san time ɗin da ta furta hakan ba, sai da ta ga irin kallon da Lion ya wurga mata ne, nan ne ta fara tunanin wai shin me ta faɗa nema?.
Gwaggo ne ta katsesu ta hanyar shigowa cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Ita ma tun da ta shigo Lion ya tsareta da idanu yana kare mata kallo, wani irin tausayinta ma yake ji a yanzu, an cuceta ba kaɗan ba.
Da sauri Rimsha ta bar jikinsa, ta nufi gwaggon tana dariya. Rungume juna suka yi, a tare suka kariso cikin ɗakin. A gefen gado kusa da Lion ta zauna, ita kuma Rimsha ta zauna a gefenta tare da kwanto da kanta a saman kafaɗunta.
"Saif kuzo muje palo, akwai maganganu da zamu tattauna da su Abban Imran and Brr". Cewar gwaggon kenan.
Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Ki shirya gobe zamu koma ƙasarmu".
Har tana haɗe word wajen cewa "Wace ƙasa kuma?!". Shiru ya yi bai bata amsa ba. Areef ne ya amsa mata da kasar da ake nufi, wato Usa.
"A'a ni zan zauna a cikin ƴan uwana, ku dai ku koma, duk time ɗin da kuka sami lokaci, sai ku kawo mani ziyara".
Miƙewa Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, ya nufi waje abinsa, dan ya san babu abin da zai hana su tafi da ita, ta gama zantukanta dukka, Nigeria kam sai ta barta..........Babbar magana.
Miƙewa suka yi dukkansu suka rufa mashi baya. A palo suka isko su Abba gabaɗaya, sai hira suke yi, amma ga dukkan alamu, suna cikin matsananciyar damuwa.
Saman sofa Lion ya zauna yana kallon baban Muneer dake a tsakiyar palon, Areef ya ɗaure shi da igiya kamar ba lafiya ba, ga bakinsa a kumbure suntum. Da kallo ɗaya ya yi wa baban Muneer ɗin ya fahimci koma me wannan dai ba mai laifi bane, amma sai bai tambayi meyayi suka ɗaure shi haka ba, ya zuba idanu kawai yana kallonsu, dan shi ciwo ma kansa take masa.
Tun ɗazun Akila sai jin sautin Muryar Ablah kanwar Haroon take yi ana kiranta, tun ana kiranta daga nesa har ta ji an matso kusa, sai ta ji kamar a harabar gidan ma ake kiranta.
Mikewa ta yi tare da gaya masu tana zuwa, tana fita daga palon shikenan ɓat ta ɓace tamkar wata aljanna, an ɗauketa. To fah.
Su kuma jama'ar cikin palon, Brr Naurat ce ta yi gyaran murya tare da fara yin magana cikin dattaku da nutsuwa. Nasiha ce mai ratsa jiki ta yi wa Ummin Dr Nawid, sannan ta ce mata ko sun ɓuyo mata yanzu, gaba dole zata sani, to gara su gaya mata kawai, ta yi hakuri Allah ya yi wa Dr Nawid rasuwa.
Yadda suka yi tunanin Ummin zata ɗauki abin, sai ya zamana ba haka ta ɗauka ba, sai ma wani irin murmushi wadda da ka ganta, kasan dole aka ƙaƙalota, shi ta saki kafin ta ce "Dama ni bani na bawa kai Nawid ba, Allah ne ya bani shi, kuma duk yanda nake son shi, na san Allah ya fini son shi, ni ba zan taɓa butulcewa Ubangijina wajen yin kuka ko makamancin hakan dan ya karɓi rayuwar Nawid ba, na yi imani ya fi kowa sanin zuciyata, kuma a hakan ya ɗauki ran Nawid, ina farinciki da hakan, kuma ina kara godiya ga Allah, duk wanda bashi da yaro, ina rokan mashi Allah da ya bashi masu albarka, ni kuma ina rokan Allah daya kara mani hakuri, ina farinciki cewa ɗana ya rasu a ranar jumma'a, yanzu kawai ku kai ni naga gawarsa, zan yi mashi addu'a". Baiwar Allah, kowa yasan maganar nan ma da take yi, da kyar take fita, karfin imani ne kawai, da kuma yarda da ƙaddara, ta yarda da Allah shi ne mai yi, tana tawassuli da sunayensa tsarkaka, Allahu Akbar, a gaskiya samun uwa irinta a wannan zamani, zai yi matuƙar wahala, Imran da yake iya matsayin aboki a wajen Dr Nawid ma, sai da ya shiga tsakanin tashin hankali na wuce misali, bare kuma uwar da ta haifesa, kuma shi ne kawai ɗanta, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya kara mata hakuri, a gaskiya ta nuna jarumta da karfin imani.
Sosai suka tausaya mata, kowa sai addu'a yake yi mata, ita kuma Aafia, sai da suka samu aka yi mata alluran barci, sannan ne suka sami zaman lafiya, in ba haka ba, sai buge buge take yi masu.
Brr Naurat ɗin ce ta sake shigo da maganar case ɗin daddyn Jelly bayan ta sanar da Ummi ai an rigada an kai Dr Nawid makwancinsa, sai dai su je makabartan Ummin ta ziyarce shi a can kawai.
Tambayar baban Muneer Brr Naurat ta yi, a kan shi ya ɗauki Ayla ko ba shi ba? Idan shi ne, ya dubi girman Allah ya dawo da ita, dan tana da karamin ciki wlh. Girgiza masu kai ya rinƙa yi a kan shi wlh ba shi bane, amma bakinsa bata iya yin magana, dan ya kumbura sosai.
Rimsha ce ta katse su da cewa "Nashiga uku, Ayla ta sake ɓata?! Allah dai yasa ba Daular Mutuwa suka mayar da ita ba, shikenan wlh kasheta za su yi, dama Duna ya gaya mana in dai muka kuskura muka bari muka dawo wannan gida, to wlh babu mai iya fitar da mu, wayyo mummyna!!". Ta kai karshen maganar tare da mikewa da sauri ta faɗa jikin daddynta tana sakin wani irin kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro.
Tabbas an shafewa Rimsha tunanin Daular Mutuwa a cikin ƙwaƙwalwarta, yanzu ba ita ce ta yi maganar ba, Malika ce ta yi maganar, dan ita ta san Ayla tana can, bata da wata hanya da zata bi ta gaya masu Ayla tana can, dole sai ta hanyar shiga jikin Rimshar, saboda ita ce kaɗai ta taɓa zuwa Daular Mutuwar bayan Aylar, kuma tana son su san cewa head of the familynsu gabaɗaya wato Dr Salman yana can, shi ne yasa ta bi masu ta wannan hanyar ta shiga jikin Rimshar kawai.
Kowa na cikin palon mamakin jin sunan Daular Mutuwa yake yi, nan take Imran da Areef suka tuna da labarin da ta taɓa basu a baya, tabbas sun tuna da zancen, dan haka sai suka fara bawa jama'ar palon labarin irin ukubar da su Rimshar suka sha a wajen, shi ma daddyn Jellyn, sai a lokacin ya tuna da cewa tabbas Ayla ta taɓa gaya mashi zancen Daular Mutuwar nan, sosai abin ya dawo masu cikin kwakwalensu. Ganin hakan yasa Malikar ta fita daga jikin Rimshar, tun da sun tuna komai, sai ta kyalesu ta koma gefe kawai tana kallonsu.
Jin sunan Daular Mutuwa yasa Hjy Umaiya ta yi wani irin firgita sosai, a tsananin razane ta fara tambayar ina Akila, Akil, da kuma Imran?.
Da mamaki suke tambayarta lafiya, bata iya bawa kowa amsa ba, ita dai kawai tambaya take yi ina yaranta. Imran ɗin ne ya ce "Ammie gamu nan ai, lafiya meyake faruwa?".
Banda girgiza kai babu wani abin da take yi.
"Kai ina Akila? Ya ban ganta a nan ba?". Cewar Akil.
Nan fa suka fara waige waige. Shi dai Lion binsu da idanu kawai yake yi, ya rasa meyasa gwaggo ta ce sai dai yazo anyi magana da shi, suna ta surutu suna kara mashi ciwon kai a banza.
Wasa wasa suka fara neman Akila, shiru babu ita babu labarinta, nan fa Hjy Umaiya ta birkice masu, ta yi masu karamar hauka, faɗi take yi wlh Queen ta dawo mata da ƴarta, idan ba haka ba, to a wannan karon za su yi kare jini biri jini!!.
Zuba mata idanu kawai suka yi suna kallon ikon Allah. Brr Naurat ce ta tambayi Abban Imran wai matar nan tasa lafiyarta kuwa?.
Shiru shi ma ya yi ya kasa yin magana, dan kuwa bai san me zai ce ba.
Gwaggo ce ta miƙe ta riko Ammien tana tambayarta lafiya? Wacece kuma Queen?.
Cikin kuka ta basu amsa da mahaifiyarta ce, kuma ita ce shugabar wannan Daular Mutuwar da Rimsha ta ambata a yanzu.
Daga Imran har Areef sai da suka zaro idanu tamkar idanun nasu zai faɗi kasa, irin wannan bala'i na cikin Daular Mutuwar dukka Ammie ta ce uwarta ce shugabansu? Lallai kuwa, akwai cakwakiya.
Ita kuwa Rimsha miƙewa zaune ta yi tana karewa Ammien kallo, sai a yanzu komai yake dawo mata sabo, sai a yanzu take kallon tsananin kama na Ammien da kuma Duna, hakan na nufi duna ɗa ne ga Queen? Ko kuma ɗan uwanta ne? Dan sun yi kama sosai......WATA SABUWAR CAKWAKIYA KENAN, ME KUMA YA HAƊA AMMIEN DA DAULAR MUTUWA?.
"Abba menene ya haɗa Ammienmu da Daular Mutuwa?". Cewar Imran, da yake shi yasan labarin Daular a wajen Rimsha.
Zubawa Abban idanu kowa ya yi yana jiran amsa daga gare shi.
"Imran nima ban san me zan ce maku ba, amma ita Ammien taku ce kawai zata iya yi maku bayani".
Juyo da kallonsu a kanta suka yi, yau suna ganin tashin hankali, labarin yau kuma ya juya ta kansu Imran.......... TRIPLETS GIDAN SURPRISE, YAU KUMA LABARIN MU YA JUYA TA KAN SU IMRAN, SHIN AKWAI WANDA YA TAƁA TUNANIN QUEEN MAHAIFIYAR AMMIENSU IMRAN CE? TO YAU MA DAI SABUWAR BABIN CAZA KWAKWALWA MUKA BUƊE😂 KU DAI KU KASANCE DA PRINCESS TEEMA KAWAI, NI CE KAƊAI ZAN WARWARE MAKU WANNAN CAKWAKIYA!.
Cikin kuka da tashin hankali ta fara magana kamar haka. "Hakika kamar yanda na gaya maku cewa Queen mahaifiya ta ce, to ba shakka hakan ce, mun kasance kabilar igbo mazauna garin Enugu, kuma mun kasance kiristoci ne, karatu ya kai ni Kaduna state, a nan na haɗu da Abbanku, dama already tun kafin na tafi karatu, na san da gidan Daular Mutuwa, kakana ne ya kirkireta, kowa ya san kabilarmu da tsafi kamar baza'a mutu ba, to muma muna ɗaya daga ciki, Mahaifiyarmu, wato Queen, ita kaɗai kakana ya haifa, Shiyasa da ya mutu, sai ta gaji karagar mulkinsa a Daular Mutuwa, ni da kai'na ina zuwa har cikin Daular, kuma a lokacin babu wani abu na tsafi wanda ban iya ba, duk wata tsubbace tsubbace na iya nima, da ni da kanwata, sai kuma wani ɗan uwan mamana, mune na kusa da ita a Daular, a takaice dai na san komai, Allah da ikonsa, da Allah ya so ni da rahama, sai ya jarrabeni da son karatu, ita kuma kanwata, tana tare da Queen a cikin Daular, a gabana za'a yi tsafi da mace, a gabana ake komai na abubuwan subbace subbace da siddabaru, ko a jikina, dan lokacin zuciyar kafurci ne ke gareni, manyan mutane ne suke zuwa cikin Daular dan a biya masu bukatunsu, da akwai manyan manyan gidan matsafa da suka dogara da Daular, akwai abubuwa da dama wanda ni a yanzu na mance da shi ma gabaɗaya, kuɗi kuwa, habawa ai idan munaso ma mukam, zamu iya yin gadon kuɗi ku kwanta, muna da arziki na wuce misali, mu da mumuke bawa wasu ma, manyan mutane daga kasashen dake makwabtaka damu, suna zuwa neman arziki da abin duniya a wajenmu, wasu su kawo ƴaƴan ƴan uwansu mu yi masu kuɗi da su, wasu kuma ƴaƴan cikinsu, abubuwa dai da dama, mun shahara a duniyar tsafi. To a takaice dai sai Allah ya ƙaddara na tafi Kaduna state karatu, a can na haɗu da Abban Imran, wasa wasa muka fara soyayya, ina son shi sosai kasancewarsa Bature, kun san turawa da mugu mugun shiga rai ga farinjini, ga kyau na wuce misali. Daga karshe dai na musulta, saboda da shi, da ya kasance Allah yana sona da rahma, sai Allah ya saka mani kaunar addinin sosai, na yi karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai, ina jin alokacin da akwai abin da ya ɗaukewa Queen hankali, shi ne yasa bata lura da abin da nake yi ba, idan ba haka ba, wlh duk wani motsinmu tana gani a cikin madubin tsafinta, amma ga mamakina har na musulta, na kuma yi karatun addini, kuma bata gane ba. To a takaice dai, lokaci da muka yi hutu, sai Abban ya ce zai bini muje gidanmu ya gaida iyayena, daga nan ayi maganar aurenmu, da yake ni wlh na mance da ya gidanmu ma suke, sai na yarda mashi kawai, na ce muje, ba tare da sanin iyayensa ba, muka kama hanyar Enugu, a ranar naga bala'in da ban taɓa gani ba, dan da muka je gida, Queen ta ce wlh dani da Abban duk kashemu zata yi, to dama na gaya maku already nima a lokacin na iya tsafe tsafen nasu dukka, hakan tasa na yi fito na fito da mahaifiyata, dan na kare Abba kada su kashe shi, duk da na musulta, hakan bai hana ni na haɗa kayan tsafina dan muyi faɗa da ita ba, domin a lokacin a cewata, tsafin ne kawai zai kwacemu daga hannunta, mun sha azaba ta yanda sai da muka koma yin karatun Alkur'ani mai girma, sannan muka iya kuɓuta daga hannunta, a nan ne na kara yarda cewa tsafin ma dukka shirmen banza ne, tun da ga shi ya kasa kuɓutar da mu daga hannunta, karatun Alkur'ani mai girma ne ya kuɓutar da mu, tun daga lokacin sai na kara nesanta kaina da tsaface tsafacen, ita kuma Queen ta sha alwashin da ni da duk waɗan da suka tallafa mani, sai taga bayanmu, ni kuwa na ce mata idan ta fasa bata cika Queen of Daular Mutuwa ba, abin ya yi tsananin kona mata rai, dama kun san yanda kabilar igbo suke da tsananin zafi idan aka ce yau ga nasu ya musulunta, to haka nima dangina suka ɗauki wannan zafin, akwai wani ɗan uwanmu da dama shi zan aura, to da ya ji abin da ya faru, sai ya ce shi ma ba zai kyale Abba da gabaɗaya familynsa ba. In takaice maku dai haka muka baro garin Enugu babu daɗi, da kyar ma muka iya kaiwa airport muka dawo Kaduna, babban abin da ya kara sakawa naji ina son addini musulunci sosai, shi ne yanda iyayen Abba suka karɓeni, basu ji kyamata ba, dan na kasance Kristen kuma ƴa ga magicians, sam ba su guje ni ba, mahaifinsa Dr Salman yana da kirki sosai, ita kuma matarsa Amarya tana da bakar zuciya, sai dai ni ba zata iya cutar da ni ba, saboda already a dafe nake, jinin Queen ce ni, ta dalilina ma asirin da ta yi wa Dr Salman ɗin ya karye, dan wannan a jininmu yake, mune gidan asiri, mune asiri da kanta, duk girman asiri in dai ina wajen, to ba zai yi tasiri ba, ni ban san me Queen ta yi mana a jininmu tun muna yara ba, to haka gabaɗaya su Imran suka taso, ba'a iya cutar da su, saboda jina ne su,