Showing 204001 words to 207000 words out of 270744 words

Chapter 69 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2987

sauki, a tsaye yake kwararata.

A dubu ɗari sir Arvin ɗin ya yi kansa yana yi mashi sannu, ita ma Akilar da sauri ta matso kusa da shi tana yi mashi sannu.

Tamkar kara injiza aman ta yi da ta matso kusa da shi, kara yawaita aman ya yi sosai, bata san cewa shi ƙunshin ne baya son gani ba, shi ne dalilin aman nasa, ga shi ta sake matsowa kusa da shi, ai dole aman ta karu, kuma babu halin yin magana bare ya ce mata ta tashi a kusa da shi, shi kuma sir Arvin bai san menene dalilin yin aman nasa ba, bare ya ce da Akilar ta matsa daga kusa da shi.

A wani irin dubu ɗari Lion da Areef suka sauko kasan, saboda aman da suka ji, kuma ko ba'a faɗa masu ba sun san Aseef ɗin ne, saboda yana aman ne tare da wani irin tari mai sanya bawa fita daga cikin hayyacinsa.

Sam aman yaki tsayawa, yi yake yi tamkar zai amayar da ƴaƴan hanjinsa, ga wani wahalallen tari da yake yi tamkar maƙoshinsa zai ɓalle.

Rirrike shi suka yi suka tsugunnar da shi kasa, daga Lion har Areef ɗin basu lura da Akilar a wajen ba, da sun ganta zasu gane dalilin yin aman, dan shi kansa Lion ɗin tun daga airport daya ga ƙunshin Rimsha yake jin zuciyarsa tana tashi, daurewa kawai ya yi dan babu yadda zai yi, amma shi kaɗai yasan me yaji dayaga ƙunshin, shiyasa ma bai kaita bedroom nasa ba, ya barta a parlourn, dan zata iya saka shi amai over.

Shi dama Areef bai zafafa a kan tsanar ƙunshin ba, tabbas dukka TRIPLETS suna da kyankyani over, amma na Lion da Aseef sune suka zafafa over, shi ma Areef ɗin da farko ya zafafa, amma yanayin aikinsa yasa ya saba da wasu abubuwa, hakan tasa kyankyanin nasa ta ragu ba kamar nasu ba, so shi zai iya zama da mace idan ta yi ƙunshi, abin hannunta ne kawai ba zai iya ci ba idan ta bashi, amma dan zama waje guda, lafiya lou zasu zauna saɓanin Lion da Aseef da ko gani suka yi sai sun yi ta amai kamar su mutu.

Da sauri su gwaggo ma dukka suka sauko kasa, dan Aseef kamar zai mutu haka yake tari, kuma da sauti mai karfin tarin take fita, hakan ne ya bawa family da suke kusa damar jin abin da yake faruwa, ga aman taki tsayawa.

Ganin abin da yake faruwa yasa gwaggo, daddyn Rimsha and Dr William har suna rige rigen karisowa wajen nasu.

Sai dai kuma shi kansa Dr William ɗin yana zuwa ya yi ido biyu da ƙunshin hannun Akilar, kan kace me shi ma ya fara sharara nasa aman, hakan na nufin abin nasu ma na gado ne.

Sai a lokacin kuma Lion ya lura da Akilar, dafe kansa ya yi tare da sanya hannusa dukka biyu ya ɗauki Aseef ɗin cak dan su bar wajen, idan ba haka ba suna iya rasa shi ma mai gabaɗaya, dan irin wannan tari da yake yi ai zai iya kashe mutu har lahira.

Duk Aseef ɗin ya bata mashi jiki da amai, amma sam bai damu ba, ya wuce da shi kai tsaye cikin part nasa, kai tsaye toilet ya wuce da shi, bai sauke shi a ko'ina ba sai a cikin jacuzzi mai cike tab da ruwan wanka da ya haɗa, dama wanka zai yi ya jiyo tarin Aseef ɗin.

Sai a lokacin kuma aman ta tsaya sak, hannu bibbiyu Aseef ɗin ya dafe saitin kirjinsa da shi, saboda wani irin azababben ciwo da yake yi mashi, duk kuma wannan tari ita ce sila, ita ta ja mashi wannan ciwon kirjin.

Zuba mashi idanu kawai Lion ɗin ya yi yana kallonsa, shi ma dai aman nan yake ji ba kaɗan ba, bare ma da ya sake ganin ƙunshin Akila, sai abin ta kara tada mashi da zuciya, gara mashi ƙunshin Rimsha ma, saboda nata ja ne yafi yawa a jiki, na Akila kuma a iya yatsu kawai aka sanya mata ja, sauran dukka bakin kirin ne, hakan yasa nata ya fi basu kyama.

A parlour kuwa, tamkar gwaggo bazata kula su ba, sai kuma ta ce da Akilar. "Akila zo mu tafi, ƙunshin hannun nan naki ne basu so, haka Dr William yake tun bai kai haka ba, ina ga shi ne yasa autana ma yake amai, sun yi gado kenan, Areef sai ku san yadda zaku yi da shi ya dai'na yin aman ai".

Guntun murmushi sir Arvin ya yi, gwaggo duniya, har cikin ranta take jin ciwon wannan aman da Dr William yake yi, amma taki bayyana hakan, sai dai ta fake da su Areef su san yadda zasu dakatar da aman, dan tana tsoron kada mijin nata ya mutu..............(Kai ana duniyanci a TRIPLETS, soyayya ba karya bace😂)

Tana kai karshen maganarta ta ja hannun Akilar suka nufi sama, sai dai zuciyarta a cike yake tab da damuwa, shap ta manta da cewa Dr William baya son ƙunshi, kuma bata kawo a ranta cewa a cikin ƴaƴan nasa akwai wanda ya gaje shi ba, shiyasa ma ta bari su Rimshar suka yi lallen, to yanzu meyakamata ta yi kenan? Ta tambayi kanta.

Tamkar mummyn Rimsha ta shiga cikin tunaninta sai ta ce mata "Aunty Aisha meyakamata ayi kenan? Tun da ya zama Aseef baya son wannan lalle, to ba shakka dukkansu haka suke! Ga shi kuma dukka yaran sun yi ƙunshin".

Gwaggon tana zama a bakin bed a cikin bedroom nata ta amsa mata da "Gaskiya kam kuma ba'a kyauta masu ba, ni wlh na mance da cewa mahaifinsu baya so ne, kuma tunanin na tambayesu ko na tambayi matan nasu sam bai zo mani ba".

Zama ita ma mummyn Rimshar ta yi a saman bedside drawer tana faɗin "Amma kuma dakamar wuya ace matan nasu basu san basu so ba".

Ɗago idanu gwaggon ta yi ta sauke su a kan Rimsha dake kwance a saman bed ɗin, ta basu baya, jin abin da suke faɗa yasa ta rufe idanuwa kamar mai yin barci, dan kada mummynta ta tambayeta ta san Lion na son ƙunshi ko bata sani ba, idan ta ce ta sani wlh mum ba zata kyaleta ba, idan ta yi wasa ma sai ta sha lafiyayyen mari, shi ne yasa ta yi kamar ta yi barcin karya dan kada a tuhumeta.

Ambatar sunanta gwaggon ta yi, shiru bata amsa ba, saboda ta yi barcin karya.

"Rimsha fa barci ya ɗauketa, ke Akila kin san da cewa Auta baya son lalle ko baki sani ba?". Cewar gwaggon.

Shiru ta ɗan yi kamar mai tunani wani abin, sai can kuma ta ce "Kamar dai na sani ne Kamar kuma ban sani ba, na manta, amma dai a tsakanin Jehan da Rimsha akwai wadda ta taɓa ce mani mijinta baya son ƙunshi ya hanata yi". Ta kai karshen maganar tana ɗan sunkuyar da kanta kasa.

Mummyn Rimsha ce ta ce "Au kinma taɓa ji kenan? Akila shin kun san me kuke yi kuwa? Yanzu dai kinga halin da kika jefa shi a ciki, ba tare kuma da ya yi maki laifin komai ba, kin ɗauki alhakinsa, kinsan kalar tsinuwar Mala'iku da zaki samu kuwa? Ace ma baki san yana so ko baya so ba, meyasa da zaki je yin lallen baki tambaye shi yana so ko baya so ba? Kin san da cewa komai zaki yi a yanzu sai idan yana so ko baki sani ba? Ki sani fa in dai mijinki bai yi maki laifin komai ba kika azabtar da shi, wlh babu in da zaki je sai Allah ya kamaki, koda ma ace ya yi maki wani laifin bai kamata ki rama da sharri ba, ki kyale shi ai Allah yana ganinku, kada ki yarda kiyi abu da gangan dan ki kuntatawa wani ma bare mijinki, kowa ya biki da sharri ki bishi da alkhairi, sai kiga Allah ya kareki daga wannan sharri da yake nufarki da shi, duk lokacin da kika yi abu da gangan dan ki cutar da wani, ki sani Mala'ikun Allah ta'ala suna tsine maki albarka, tsinuwar mutun ɗan adam ma kawai idan aka barki da shi ya zaki kare bare kuma tsinuwar Mala'iku? Common bakin mutane yana lalata mutun bare shinuwa bare kuma na Mala'iku, tun wuri na gaya maku ku shiga hankalinku ku san menene miji a gareku, ba abin wasa bane shi ɗin, yana da kyau ku kula sosai".

Da yake Rimsha da gangan ta yi ƙunshin nata, sai ta ji kamar da ita mum take yi, duk sai ta damu sosai, jikinta duk sai ya yi sanin, yanzu ace ita ma Lion idan ya ganta zai yi ta zuba amai kamar yadda Aseef ya yi ai ba kamar cutar da shi ta yi ba, meya yi mata da zata cutar da shi haka? Koda ma ace ya yi mata wani laifin meyasa zata cutar da shi ta abin da tasan baya so? Meyasa ba zata tsaya a iya fushin da ta yi da shi ɗin kawai ba? Meya yi mata har haka da ya cancanci hukuncin cutarwa daga gareta?. Sosai ta rinƙa tunani tare da danasanin yin wannan ƙunshi da ta yi, sai dai kuma bata jan ye fushin da take yi da shi ɗin ba, ta ce dai fushi kam ba zata fasa ba tun da ya nuna baya sonta...

Ƙasa da kai sosai Akilar ta yi tana sauraron nasihar ta mum, ya ratsata sosai da sosai, duk sai ta ji babu daɗi, ta ji ta matuƙar damu sosai.

Ita kuwa mum sosai ta yi masu nasiha mai ratsa jiki, sannan ta miƙe ta nufi nata part ɗin wanda yake a kusa dana gwaggon.

Tana shiga ta isko daddyn Rimsha yana tsaye a wajen mirror.

"Kin tafi wajen ƴaƴanki kin manta da ni ko? Kefa ko kewata ma baki yi ba ko?". Ya faɗa yana juyo da kallonsa a kanta.

A gefen bed ta zauna tana mai bashi hakuri. Toilet ya nufa yana faɗa mata ba zai hakura ba, bari ya fito wanka zai ɗauki mataki...........🙄🙃

A ɓangaren Aseef kuwa, ya ci bakar wahala kafin ya samu ya dawo dai'dai, har wani firgicewa fuskarsa ta yi, bawan Allah ba laifinsa bane, a jininsu abin yake, gado aka ce ba karambani ba.

Shi ma dai Dr William ya ci bakar wahala kafin ya samu ya dawo dai'dai, bedroom nasa Areef ya wuce da shi, suka bar masu aiki da aikin gyaran parlourn, kowa ya wuce part nasa, dan su yi wanka su huta zuwa dare.

After some hours.

Lion da sir Arvin zaune suke a saman bed ɗin na Lion da yake a cikin bedroom nasa, ita kuma Pinky tana a tare da Dr William, daga shi sai sir Arvin suka saba a gidan, sai kuma Lion tana ɗan yarda da shi, albarkacin kamar da yake yi da sir Arvin yasa take yarda da shi idan zai ɗauketa ko ya bata abu, tana yarda.

Sai hira suka yi gwanin ban sha'awa, da yake dukkansu ba sarakan yawan magana bane, sai ya zamana hiran nasu sama sama suke yinsa.

Areef ne ya shigo cikin bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama, kayan barci masu bala'in kyau irin na jikinsu Lion ɗin ne a jikinsa, sai dai nasa ash color ne, Lion da sir Arvin kuma nasu white colors ne, da alama shi ma sir Arvin sarkin son farin abu ne, dan ko kayan Lion zai sanya farare kal kal yake ɗaukowa, son farin abin nan a jininsu yake. (Nima a jinina yake, fav color na kenan a duniya🥱 kusan komai idan zan saya in dai akwai fari, to shi zan ɗauka, kuma kun shaida😂)

Saman bed ɗin ya haye yana faɗin "Our Lion what's wrong with you? And meyasa baku fito mun je dining room dan yin dinner ba?". Ya yi maganar yana mai karewa Lion ɗin kallo, nazari face nasa yake yi, da yake shi ya san ɗan uwan nasa fiye da sir Arvin, shiyasa yana shigowa ya fahimci akwai abin da yake damunsa, dan damuwar ta fito karara a saman face nasa, shi kuma sir Arvin sam bai gane ba, saboda dama bai san halinsu ba, da saura tukun nan.

"Areef Meesha fushi take yi da ni fa, taki zuwa in da nake, kuma she knew that i hate this thing that she did on her legs and hands, amma ta je ta yi har da wuyarta, because of tana fushi da ni". Ya faɗa yana mai ɗauko wayarsa dake a saman bedside drawer.

Da yake shi Areef yasan menene matsalar da take a tsakaninsa da Rimshar, sai ya ce "Ok yanzu dai muje muyi dinner, daga baya zamu yi maganar Rimshar, dama shiyasa nace maka idan ka sauka a kasar China ka kirata a waya, saboda mata sai ana lallaɓasu".

"Yau kowa a bedroom nasa zai yi dinner, saboda rashin jituwa da yake a tsakanin momma da dad, bana son mu haɗu a dining room ba tare da na gayawa mum abin da yake faruwa ba, idan ba haka ba za'a samu matsala, dan dad ba zai ganta ya yi shiru ba, ita kuma ba zata saurare shi ba, so the solution kawai kowa ya yi dinner a bedroom nasa, zuwa gobe da safe ko anjima zan sameta na gaya mata abin da yake faruwa". Cewar Lion kenan.

Baki ɗauke da sallama Aseef ya shigo cikin ɗakin, duk ya yi wani iri da shi bawan Allah, wannan aman da ya rinƙa yi ta galabaitar da shi sosai, har ya ɗan yi rama, sai dara daran idanuwan nan nasa kamar ball.

A saman bed ɗin shi ma ya haye yana faɗin "Ni Areef ka matsa bari na yi barci".

Fuska a ɗauke da mamaki sir Arvin ya ce "What? Ina ƴar aljannarka take da zaka zo nan kace zaka yi barci? Ina ka barota?".

Areef ne ya capki zancen da cewa "Shi ne nima abin da zan tambaya kenan, ina ka baro Heartbeat da zaka zo nan ka ce mana bari ka kwanta, Heartbeat taka da kake ta kukan ta dawo ne fa! Ko ka manta ne?". Ya kai karshen maganar yana dariya, dan yasan me matsalar, da gangan ya yi mashi wannan tambayar.

Shi dai Lion ko a jikinsa, ƙoƙarin mikewa ma yake yi ya je wajen gwaggo, dan ya kalli Meesharsa, yana kewarta sosai, yana son ganin face nata ko zai sami saukin abin da yake ji.

"Ni Areef ku rabu dani, su fa mata idan ka biye masu wlh sai ka mutu bama kasan ka mutu ɗin ba, sai ka ji ka kabari zaka gane".

Dariya kamar Areef zai mutu, shi dai yana burin daman yaga Aseef da Akila sun yi faɗa kamar yanda Lion da Rimsha suka yi a yanzu, dama sun ishesa, ji yake kamar duk ya shakesu, bini bini suna manne da matan nasu, to yau dai Allah ya kamasu dukkansu, matan nasu yau ji da sabon iskanci suke yi, ita kam Rimsha ai sai dua'i, wai fushi ma take da Lion, ita kuwa Akila ƙunshi, dole Aseef ya daka yaji sai ƙunshin nan ta goge............😂

Damko Areef ɗin Lion ya yi tare da haɗe hannayensa dukka biyu, dan Areef yana kule su har wuya, suna fama da zafi zai kara masu wani ta hanyar yi masu dariya, a maimaƙon ya tayasu shawo kan matsalarsu, amma saboda neman tsokana sai ya kama dariya, yau kam ba zasu barshi ba.

Da sauri Aseef ya sauka kasa daga saman bed ɗin ya je ya ɗauko igiya dan tsabar mugunta, so yake yi Lion ya ɗaure Areef ɗin, ɗaurin goro su jibge shi, saboda Areef ɗin yana kara masu zafi a kan zafi na abin da suke ji, idan ba iskanci ba yazo ya tasasu a gaba yana masu tambayoyi, idan sun gaya mashi ga yadda aka yi, sai ya zauna ya yi ta dariya har yana shakewa tare da yin tari tsabar mugunta, wlh dole yau su yi maganinsa. (Rifat yau Allah ya kama Areef ɗinki, kuma ba mai kwatarsa😂 dama tara mashi suke yi tun tuni, sai yau dubunsa ya cika)

Karɓar igiyar Lion ɗin ya yi tare da fara ƙoƙarin ɗaure hannayen Areef ɗin. Da sauri sir Arvin ya ce "A'a meyayi maku zaku ci zalinsa?."

Kin kula shi Lion ɗin ya yi, Aseef sai faman dukan Areef ɗin da pillow yake yi yana faɗin "Kai ma Allah yau ba zaka je wajen matarka ba, a nan zamu zauna kamar masu takaba a tare".

"Wannan ne kuma baku isa ba" Cewar sir Arvin, ya yi maganar tare da kai hannunsa zai kwaci igiyar da Lion ɗin yake ƙoƙarin ɗaure hannayen Areef ɗin da shi. Da sauri Aseef ya yi ƙoƙarin hana shi, amma ina tuni ya kwace igiyar yana faɗin "Areef jeka wajen matarka hai, shi Saif waye ya ce ya yi wa tasa Queen ɗin laifi? Kai kuma Aseef me kayi mata nema da har ta yi fushi da kai ɗin ma?".

Har lokacin Areef bai dai'na dariya ba ya ce "Lion fa sai da nace mashi idan ya je kasar China ya kirata a waya ya rarrasheta, dan shi ya yi mata laifi, ya ɗauka mata wasa ne, to ai ga shi yanzu zai karɓi ga shi a zuciyarsa". Ya kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariya.

A kule Lion ɗin ya haɗesu daga Areef ɗin har sir Arvin ɗin ya murɗe masu hannu ɗai ɗai ta baya, sai da sir Arvin ya furta wash da karfi.

Aseef kuma tsabar mugunta har da sake ɗauko wata igiyar dan Lion ya ɗauresu. Ƙoƙarin kwace kansu suka farayi, da Aseef ya ga haka sai ya matso ya fara taya Lion ɗin dannesu da kyau, kamar wasu ƴaƴan mage, abin dariya gwanin ban sha'awa.

Shigowar Tga da Mark cikin ɗakin ne yasa Lion ɗin ya sake su, dan idan baku manta ba baya wasa da TRIPLETS nasa a idanun kowa, dan baya son ra'ini, so baya son su Mark suga ashe yana wasa da ƴan uwan nasa har haka, shi ne yasa ya sakesu tare da miƙewa ya ɗauki wayarsa ya nufi waje.

Mark bawan Allah har yanzu yana ɗan ɗingisa kafa, bai gama samun sauki ba, sai dai ya kara wani irin azababben kyau, ya ɗan yi ƙiba kaɗan, ga shi kuma ya tara gashin kansa saboda jinyar da yake yi, sai ta kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login