Showing 141001 words to 144000 words out of 270744 words
ta zubawa juna kukan shagwaɓa kamar ba gobe, kuma haka zasu rarrashi juna, da yake sun saba ma abin ya zamto masu jiki.
"Gwaggo ina son muje shopping, za'a saya mani kaya da kuma waya, mafiya yawan kayan da nake sanyawa a gidan nan fa kayan Rimsha ce, to ni gaskiya na gaji da saka kayanta". Tana magana tana haɗe gerar sama da kasa.
"Dama basu yi maku lefe bako?". Cewar gwaggon. "Menene kuma lefe?". Ta tambaya tana bin wayar gwaggon dake ringing da kallo.
"Lefe kayan da maza suke sayawa mata kafin aure mana". Ta bata amsa tare da jawo wayar tata dan ta ga wanenen yake kiranta?.
"Mu babu wani lefe da suka yi mana, kawai ni gwaggo ki kira daddy a waya muje shopping hai, ina ruwana da wani lefe? Mu ba muna da kuɗin sayan kayan ba? Dole sai su ne zasu saya mana?". Ta kai karshen maganar tana turo baki tare da ɗaure fuska.
Duk abin da ta faɗa Areef ɗin yana jinta, saboda shi ne ya kira gwaggon a wayar, kuma already ta yi picking call ɗin, ga shi da English suke magana, so ya ji komai. Jehan sarkin iyayi da nuna isa, wato ita lefenma bata ce Areef ya yi mata ba, daddynta yana da kuɗi, dan haka su sun wuce ayi masu lefe. (Ni ko nace ba shakka duk wannan izzar da isar tata tana taka bakin gate na farko na gidan Lion na Washington zata zama ƴar kauye, dan gidansa ginine da babu kwatankwacinsa a Nigeria, maƙudan dukiya aka narka na kin karawa, Daula ce guda, idan kana cikinta sai ka yi tunanin ba'a duniya kake ba, Allah ka yi mana arziki mai albarka mai amfani da zamu taimaki Al'ummar musulmi Al'ummar manzon rahma manzon tsira.)
"Good morning momma". Ya faɗa cikin sanyin murya, duk da lokaci time na agogo namu da nasu daban daban, amma ratar bata da yawa sosai, kuma ya san safiya ce yanzu a Nigeria, shiyasa kawai ya ce mata good morning.
"Morning how are you and my auta?". Nisawa ya yi kafin ya amsa mata da "Autanki yana can yana aikin barci da ya saba, Momma please help me give my baby this phone, jiya taki yin magana da ni, fushi take yi da ni, dan banzo ba".
Kallonta gwaggon ta yi da mamaki a saman face nata, wato Jehan ta cika ƴar duniya, sai tazo ta nuna masu tamkar bata damu da Areef ɗin ba, tamkar bata son shi, ashe ma saboda bai zo ba har da yin fushi da shi ta ɓata rai, kai Jehan ba'a iya mata, kuma baka gane mata sam sam, ta sanya bawan Allah a cikin tunani, kuma sarai ita ma abin yana damunta, kawai dakiya ce, ita ma jiya ta ji a jikinta na rashin wayar da basu yi da daddare ba, ta dake ne ta nuna kamar ba komai, dan ma kada a ra'inata. (Allah mai iko, Jehan duniya, ta iya dakewa ta shanye abu kamar Lion, sai ta yi kamar bata san komai ba, alhalin tana azabtuwa daga ta cikin zuciyarta 😂)
Miƙa mata wayar gwaggon ta yi tana faɗin "Karɓi za'ayi magana dake". Harara ta wurga wa wayar tana faɗin "No need".
Nisawa ya yi kafin ya ce "Please my baby, ya isa haka wahalar da ni ɗin kin ji, i can't agree irin wannan avoiding nawan da kike yi, ina shan wahala sosai fa, wai baki jin tausayi nane?".
Wani irin sanyi ta ji a ranta na jin muryarsa, har da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, amma saboda taurin kai sai ta ce ita fa ta gama magana kenan ba zata karɓi waya ta yi magana da shi ba.
Gwaggo baiwar Allah tana ganin rayuwa wajen ƴaƴan nan nata da matansu, kowa da kalar tasa rashin kunyar. Katse kiran gwaggon ta yi tare da fara yi wa Jehan ɗin nasiha a kan ba'a yiwa miji haka, ta sani Allah zai kamata, tun jiya ta sanya mijinta cikin damuwa, ya kwana cikin ɓacin rai, sannan yau da safe ma ta tashi ta kara mashi wani? Bata da hankali ne? To wlh ta bi duniya a hannu.
Hararar gwaggon ta yi kafin ta ce "Kawai dan ke baki jawa Dr William aji ba shi ne ni zaki hanani jan ajina? Dake da mummy duk naji tarihinku ai, ba wani jan aji da kuka yi, ita mummy tana gani daddyna kyakkywa ta ce shikenan zata bishi ita kam, kema Dr William yana ɗan zuba maki kallon soyayya da waɗan nan blue eyes ɗin nasa kawai kika ruɗe, ba wani jan aji kike biye mashi, to ni wlh a'a, sai na ja ajina dan ma kada ya renani, dole ya kalleni da daraja, sai na wahalar da shi". Ta kai karshen maganar zata mike ta fice daga ɗakin, ko kunya bata ji ba, a gaban mahaifiyarsa take cewa sai ta wahalar da shi, duk wahalar da take bashi a yanzu bai isheta ba, ikirarin kara mashi wani ma take yi.
Rikota gwaggon ta yi tana salati, wai shin ya zasu yi da Jehan ne sukam? Yarinya ta ra'ina mutane? Wai jan aji take yi, lallai ma yarinyar nan.
Duk abin da ta faɗa a kunnuwar mummynta ta faɗa, dan mum ɗin ta shigo gaishe da gwaggo kenan ta ji suna maganar, shi ne ta tsaya a bakin kofa tana sauraronsu. Jin abin da Jehan ɗin ta faɗa ne yasa mum ɗin ta juya ta fasa shiga ɗakin, dan tasan mutun ɗaya ne a yanzu zai saita mata Jehan ɗin nan, tun farko gwaggon ce ta shagwaɓa ta, ta ɓatata, ta kuma sangarta, dan haka yazu basu isa su ce zasu tankwarata ba, Areef dai shi ne zai gyara mata zama ya dawo da ita a kan hanya tun da tana son shi, dan haka sai mum ɗin ta koma bedroom nata dan ta kira daddynsu ya haɗa ta Areef ɗin a waya tun da suna a tare, zata gaya mashi yadda zai yi mata magain Jehan ɗin ne, dan idan ba haka suka yi ba, Jehan fa ba zata gane me ake nufi da miji ba, already gwaggon ta ɓata komai.
(Gaskiya akwai cakwakiya kam, dole Areef ya saitata a kan hanya, idan ba haka ba zasu sha wahala.)
Sai misalin karfe 9:30 Lion da Tga suka dawo cikin gidan. Tga na yin parking a parking space babu ɓata lokaci Lion ɗin ya fito hannunsa na ruke da ledoji manya manya, Tga ɗin yaso ya karɓa mashi kayan, amma ya ce ya bar mashi abinsa, a haka suka nufi cikin gida.
Kai tsaye bedroom nasa ya nufa, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, gwaggo na bedroom nata, a saman bedside drawer ya ɗaura ledojin tare da zagayowa ya dawo ta ɗayar ɓangaren gadon, kusa da Rimshar kenan. Zama ya zo ya yi tare da zubawa face nata idanu yana kallon yadda ta kara uban haske kamar ba lafiya ba.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 7/5/2024
E26
A haka Gwaggon ta shigo ta same shi, magunguna da alluran ta fara ɗauka dan ta yi aikinta, tun bata yi mashi magana ba ya tashi ya fice daga ɗakin, dan yasan zata ce mashi ya fita ne, so is better for him da ya fita ɗin ma.
Yana fita garden ya koma, dan ya zauna ya huta. Saman sofa mai zaman mutun uku ya kwanta tare da miƙe dogayen kyawawan fararen kafafunsa, a hankali ya lumshe dara daran idanuwansa, sai tariyo mashi komai ƙwaƙwalwarsa take yi mashi, wani irin yanayi yake jinsa a ciki, da haka barci ta ɗan sace shi, dama kunsan ita barci ba'a cin bashinta, idan ma kaci sai ka biya, so gara ma kawai lokacin yinta ka yi ta sai ya fimaka.
After 15 days. (Bayan kwanaki shabiyar)
A tsawon kwanakin nan gabaɗaya ko motsawa Rimsha bata yi ba, sai dai duk da tana sume tana samun sauki dai'dai gwargwado, a yanzu jikin nata ya koma normal, temperature jikinta ya dai'dai ta, wannan uban haske da ta yi ma a yanzu ta ɗan koma normal colornta, duk da ba gabaɗaya ba. Shi ma Lion a yanzu hankalinsa ya ɗan kwanta, sai dai fa har ƴar rama ya yi, kyakkywar jajir ɗin skin nasa ta ɗan yi duhu, saboda ana zuba rana a Naija ba karya, damuna ta jima da tafiya, yanzu shirye shiryen azumi suke yi, saura watanni biyu a kama azumin, so fatarsa ta ɗan yi duhu, ya rame saboda ciwon na Rimsha, ga shi har tsawon waɗan nan kwanaki 15 ɗin bata ko motsa ba, a halin yanzu mummynta tasan me yake faruwa, sai dai bata ɗaga hankalinta ba, dan tasan already dama da akwai wannan rana a rayuwar ƴaƴan nata, Aseef yana wajen Sheikh Sultan, kullum suna manne da waya suna aikin da suka saba shi da Akila, kamar wasu chewing gum basu rabuwa.
Har wa yau abubuwa sai kara zafafa suke yi har suna tafasa a Washington, shi kuma Lion da ya tada tarzomar, hankalinsa a kwance yana Naija abinsa, ya baro su Areef da shan aiki, daddyn Rimsha ma yana can Washington ɗin already kun sani, takardan ɗan kasa Lion ya sanya ayi mashi, da kuma sauran abubuwa da suka shafi kasar, sam Lion yaki yarda ya haɗa hanya ko da ta waya ce da su His Excellence, sun buga sun raya, amma ina ya ce bashi da lokacinsu a yanzu, lokacin zama ya yi magana da su ta wuce, a yanzu primary election sai kara matsowa take yi, saura ƴan kwanaki, kun san yanayi na juyawa, haka shi ma watannin namu suke juyawa, so a yanzu kasar U.s tana shirye shiryen yin primary election ne, kuma Lion sai kara samun goyan bayan al'umma yake yi, shi kaɗai yasan kudurinsa idan ya ci wannan zaɓen, shi kaɗai yasan me yake shirya masu.
A waɗan nan kwanaki sha biyar ɗin dukka Jehan tana ta fama da rashin lafiya, ba komai ne ya haddasa mata hakan ba kuma face shareta da Areef ya yi, sai dai babu wanda yasan da dalilin rashin lafiyar tata, saboda dakiya irin nata, ta jure ta ɓoye abin a cikin zuciyarta, shi kuma Areef ɗin ya shareta ne bisa umarnin mummynta, ita ta gaya mashi ya jure ya daure ya shareta ko da na wata guda ne, dan idan ba haka ya yi ba, tabbas zaman aurensu zai bashi wahala, Jehan ba zata san mahimmancinsa ba, ba zata ɗauke shi da daraja ba duk da tana son shi, so yana da kyau ya fara koya mata hankali tun yanzu, a cewar mummyn nata kenan.
Ita kuwa Gwaggon duk hankalinta a tashe, ga Rimsha kwance kamar gawa tsawon kwanaki, ga Jehan ba lafiya, zazzaɓi mai zafi ne kamar zata mutu, ita gwaggo baiwar Allah bata san cewa ciwon Jehan Areef ne musabbabi ba, da ta sani ai da tuni ta sanya shi ya kira Jehan ɗin, dan kun dai san Jehan ta gidan ta ne, so yana da kyau ku fahimci duk abin da Jehan take yi ba fa laifinta bane, horon gwaggonce ita, komai ta yi dai'dai ne a wajen gwaggon nata, bata laifi, so kunga kuwa ai dole a samu matsala, idan baku manta ba tun farko, tun suna Abuja ita Rimsha ta fi shakuwa ne da mummynta, shiyasa ma tafi Jehan samun ilimin addini sosai, ita kuma Jehan tana manne ne da gwaggo, shiyasa ta fi Rimsha ilimin boko sosai, to idan baku manta ba tun ainahi suna da banbanci, dan gwaggo dai kowa yasan ƴar bokoce ta gasken gaske ma kuwa, kunga kuwa dole Jehan ta so boko sama da ilimin addini, dan ma dai an yi sa'a ita ma gwaggon akwai ilimin addinin ne, sai dai na bokon yafi yawa.
A takaice dai gwaggo bata san menene yake damun Jehan ba, sai faman tambayarta take yi menene matsalar, domin kuwa da ta yi mata test, results ɗin ya nuna mata cewa wannan zazzaɓi fa ba daga kwayar cuta Jehan ɗin ta same shi ba, zazzaɓi ne na damuwa da pressure ya yi mata yawa, anyi mata tambayar duniyar nan taki gaya masu menene yake damunta, dan a cewarta idan ta ce tana kewar mijinta ne ai ta zubar da mutuncinta. (E lallai baki dawo kan hanya ba Jehan, da sauranki.)
Mummynta kuwa ta san komai sarai, ta kyaleta ne sai ta yi laushi, sai ta buɗe baki da kanta ta ce da Areef ya yi hakuri ta tuba bazata kara ba, sai ta yi hankali ta koyi sanin darajar mutane. A koda yaushe idan gwaggon tana hira da Areef ɗin, idan ta tambayesa ya yi magana da Jehan ya ji ya jikinta yake kuwa? Sai dai ya ce mata e sun yi magana ta wayar Rimsha ko wayar Lion, yaki gayawa gwaggon gaskiyar basu magana, saboda mum ta ce mashi in dai ya sake ya bari gwaggo ta sani, to wlh daga shi har ita kanta mum ɗin gwaggo ba kyalesu zata yi ba, dan a kan Jehan fa ita bata ji bata gani, duk wanda zai taɓa mata Jehan zasu yi dirama daga nan har kotun bangon duniya, dan haka ya kiyaye kada ya yarda ya sake ya bari gwaggon ta san cewa basu waya kuma sanadiyyar hakance ta kwantar da Jehan ɗin rashin lafiya, shi dai ya san yadda zai yi kawai.
To shiyasa sam yaki yarda gwaggon tasan halin da ake ciki, amma fa shi ma yana azabtuwa matuƙa, yana ji a jikinsa, dan har zazzaɓi na kwana biyu sai da ya yi, kun san su dama basu iya so ba, idan suka fara son mutun, to wlh har ga Allah da gabaɗaya zuciyarsu suke son shi, babu wasa a ciki, hakan cema tasa su basu yin mata biyu, Baturen mutun mace ɗaya yake aura, dan su sunce ba zasu iya raba zuciyarsu gida biyu su bawa mata biyu ba, ɗaya ta ishesu, to wannan ɗayar gabaɗaya zuciyar tasu suke ɗauka su miƙa mata, shiyasa idan mace ta yi breaking heart nasu a soyayya har kashe kansu suna yi, ko kuma zuciyar ta buga su mutu, dan ba zasu iya jura ba. To dai shi ma Areef sai da ya yi zazzaɓi, gabaɗaya a daddafe yake yin duk wasu ayyuka na Lion, dan ma dai mumnyn Jehan ɗin ce ta ce ya yi hakan, da wlh ko kwatantawa ba zai taɓa iya yi ba, ba zai iya fitowa ya ce wa mum ɗin ba zai iya bane, kun san shi daban yake a cikin TRIPLETS, da Lion ne ko Aseef wlh ba mum ba ko uban mum ne ɓaro ɓaro zasu ce mata ba zasu yi ba, amma da yake shi Areef zuciyarsa daban da tasu, sai ya hakura ya daure ya bi abin da ta ce, dan ya ɗauki mum ɗin tamkar uwa tun da uwa ce ga matarsa farincikinsa, kuma mata ce ga uncle nasa da ya fi kauna, dole ya jure ya yi mata biyayya, banda haka wlh komai wahalar da shi da Jehan zata yi zai iya jurewa ya biye mata, dan yana sonta da gabaɗaya zuciyarsa.
A ɓangaren Aseef kuwa, har wa yau dai yana a wajen Sheikh Sultan abinsa, sai kwarara mashi ruwan adduo'i ake yi, saukar Alqur'ani mai girma babu kama hannun yaro, kullum yana hira da Heartbeat nasa sosai bawan Allah, suna faranta ran juna.
Har wa yau Akila da Jehan basu san menene ya faru da Rimsha ba, su dai an ce masu bata da lafiya ne kawai, so sun ɗauka zazzaɓi ne ita ma, da yake kuma Lion yana gari, sai basu nemi ganinta ba, dan suna tsoron shiga bedroom nasa, kuma already kunga a cikin bedroom na mijin nata take jinya, a in da ya yi dis virgin ɗin nata a wajen ake jinyarta baiwar Allah.
❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷
Lion ne tsaye a harabar gidan nasu, sanye yake da wando three cuter da riga mai karamar hannu, ƴar ramar da face nasa ta yi ta fito ɓaro ɓaro, ya ɗan rage tsawon gashin kansa, ya kuma ɗaureta a bayan wuya, face nasa ta yi fayau da ita kamar wanda ya tashi daga zazzaɓi, sai tashin daddaɗar kamshi perfume nasa yake yi, ya harɗe hannayensa a saman Lion chest nasa, duniya duk ta yi mashi wani iri.
Donal ne ya kariso wajen da yake a tsaye ɗin, sara mashi ya ɗaga hannu ya yi cikin girmamawa kafin ya ce "Sir Alex said you're call me".
Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci da a kallah zasu kai uku zuwa biyar kafin calmly ya fara magana "There's some cases da suke a hannun Mark before ya koma U.s, akwai wani mutumi da ɗauko shi daga Abuja da na bashi a kan ya horar mani da shi before na buƙace shi, to ina bukatar mutumin a yanzu".
Wani irin kamewa Donal ɗin ya yi tare da kara ɗaga hannu ya sara mashi, sannan ya wuce izuwa ɗakin da Mark yake kulle mutane.
Jim kaɗan ya dawo, Lion ɗin yana tsaye