Showing 72001 words to 75000 words out of 270744 words

Chapter 25 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2932

kallo, dan bata san komai ba............. Ni kuwa nace ta ina zaku sani? Ku ba ƴan boko ba, mummynta tana wajen aiki, kai kuma daddynta baka gari, ai kunma yi sa'a da Allah ya haɗata da Rimsha, da yanzu wani labari ake yi, da Mr Emmanuel ya jima da buɗe maku aiki, idan da rabo sai dai ku kanta da ciki ba tare da kun san ya aka yi ba, Allah ya baku amanar ƴaƴa, amma kun sake su kun tafi neman duniya, kun barwa masu aiki ragamar kula da su, tamkar ba ku aka bawa amana ba, tamkar ƴan aiki aka bawa amanarsu, ga duniyar yanzu yanda amana ta yi ƙaranci, baku san su masu aikin ya halinsu yake ba, yanda lesbian ya yawaita a duniyar nan, ku dai kawai kun sakar masu komai ba tare da dogon tunani da kuma yin aiki da faɗar Manzon Allah manzon tsira ba, wayewanku dai bai amfaneku ba! Wlh idan baku tuba ba, sai Allah ya kamaku, dan duk wani ɗa a duniyar nan, sai Allah ya tambayi iyayensa ta yanda suka kula da shi, hakki ne da kuma amana ya basu, dan haka sai ku kara zage dantse, Allah ka bamu dacewa.

Daddyn yana karɓar Anayar, Mark ya yi saurin shigewa cikin motar, shi ma zuciyarsa tana yi mashi zafi da kuna, Alex ya so ya rakasu, Lion ne ya hana shi, haka motocinsu ya tashi ya bar gidan, suka nufi airport, sai dai kafin su bar gidan, sai da Lion ya ja kunnan gataman a kan kada ya bari wani ya shiga gidan ko kuma wani ya fita ba tare da ya basu izini ba. A gabaɗaya sojoji goma sha biyu da suke gidan, sojoji uku Lion ya barsu a kan su cigaba da kula da family, ya tafi da guda tara.

Da yake motocin suna sharara uban gudu sosai, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa airport ɗin, an gama shirya masu komai, dama tun jiya Lion ya shirya wasu abubuwa da zai buƙata, dan haka suna zuwa kawai suka ɗauki hanya, ba ɓata lokacin jirginsu ya ɗaga zuwa Enugu state........... TO FATAN MU DAI ALLAH YA TSARE HANYA, YA KUMA KAREKU DAGA SHARRIN QUEEN!!.

A gida kuma, komawa cikin gida gabaɗaya family suka yi. A palon sama suka zauna, rarrashin Rimsha da Anaya suka hau yi, da kyar suka samu suka yi masu shiru, ita Rimsha ta tada kai da laps ɗin gwaggo, barcin wahala da kewar mijinta ya ɗauketa, ita kuma Anaya ta tada kai da laps ɗin Brr Naurat, sai tunanin Mark nata take yi, tana bin jama'ar palon da kallo, ita dama Jehan already tana barin wajen bedroom nasu ta koma, saman bed ta haye, haka ita ma ta murji kuka tamkar babu gobe, daga haka barci ya yi awon gaba da ita cike da tunanin mijinta kuma abokin diramarta, yau ina zata sanya ranta? Ya tafi ya barta, yau babu tsokana, yau babu rigima, Allah sarki, dukkansu gwanin ban tausayi.

Bayan ƴan kuka sun yi shiru ne Brr Naurat ta sami damar nuna masu Abba Alex, cike da murna suka rungumi ɗan uwansu, duk da cewa daddyn Rimsha da daddyn Anaya suna kama sosai da Brr Naurat, amma Alex ya fisu kama da Turawa sosai, shi ba zaka taɓa cewa Dr Salman bane ma mahaifinsa, saboda shi da su Trump wato kakan Mark ya yi kama, da su yake muguwar kama, duk cikin ƴaƴan Brr babu mai wani irin launin idanu irin na ƴan uwanta, sai shi Alex ɗin, shi kaɗai ne mai blue eyes irin nasu Trump, sai kuma a cikin jikokinta, kanwar Anaya Zaira, idanunta ash color ne, sune kawai masu wani launin idanu ta ɓangaren Brr.

Daddyn Anaya ne ya katse masu hiran da cewa "Daughter a ina kika san wannan mutumi da kika rike yanzu kina kuka?". Tana daga kwance, babu kunya ko ɗigo a idanunta, cikin tsantsar shagwaɓa ta fara magana. "Daddy Mark ne fa, kuma shi nake so, kuma shi ma yana sona, kullum ma yana yawan ce mani na gaya maka yana son kawo maka ziyara".

Cikin nuna ko in kula, bai ɗauki zafi ko kaɗan ba, dan wayayyun mutane na wuce misali, sun kwankwaɗi boko, dan haka sai ya ce "To kin san shi ne? Su waye iyayensa? Kuma a ina yake?".

Turo baki ta yi tana faɗin "Daddy dukka wannan shi zaka tambaya mana, ni ban san kowa nasa ba bayan mijin Rimsha da yake ogansa, shikenan".

Salatin mummynta ta sanya tana faɗin "Yanzu daughter baki san iyayensa ba, baki san halinsa ba, kawai ke ƴar soyayya sai kika fara son shi ko? Wai ni yaushe ma kika girma ne? Yau ga ikon Allah, ko secondary school fa yanzu kika fara, amma kike zancen son wani?".

Kuka ta saka masu tana faɗin "Daddy baka ga mummy ba, yanzu zaki fara ko mummy? To ai shi yana da kirki, kuma ai kinga idan bashi da kirki ba zai zauna a gidan nan ba, ni mummy dan Allah ki bari mana, ke komai mutun ya yi sai kin yi complain, sai ki rinƙa cewa mutun yarinya, kullum ba'a kara girma a wajenki, kullum sai naci marking sosai a school, amma sai kice bana ƙoƙari, daddy ne kawai yake cewa ina ƙoƙari, shiyasa fa yanzu zan dai'na nuna maki papers ɗina, daddy da Yah Feroz kawai zan rinƙa nunawa". Ta kai karshen maganar tare da mikewa daga kwanciyar da ta yi, tana turo baki ta sa kai zata wuce izuwa ɗakinsu Rimsha.

Daddyn nata ne ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Zo nan abinki my daughter, rabu da mummy, ni nasan yana da kirki sosai, yanzu dai zo ki gaya mani a ina yake aiki dan na binciko wanene shi?".

Ba musu ta nufi daddyn nata, a jikinsa ta kwanta tana tura baki tana faɗin "Daddy kai'na yana yi mani ciwo, ni ba zan iya jure Mark ya je wannan waje ba".

Dafa kan nata ya yi tare da fara ce mata sorry, Zaira ƴar auta tana zaune shiru kusa da daddyn Jelly, baiwar Allah sam bata da rigima, tamkar ba ƴar auta bace ita, Anayar da take babba ta fita yawan rigima da shagwaɓa.

Brr Naurat ce ta katse masu zancen da cewa "Mark dai jika ne ga babban yayanmu, haka jika yake a wajena kamar yanda kuke jikokina, so bana tunanin mutumin banza ne, tunda har yana tare da su Saif, to a gaskiya shi ɗin ba mutumin banza bane, a gabaɗaya su Saif babu na banza a cikinsu, kuma sai hali yazo ɗaya ake abota, dan haka ina kyautata mashi zato, kuma ina farinciki da Allah yasa jinin babban yayana zai auri nawa jinin, duk da sun gujeni, sun koreni a cikinsu, to ga shi Allah zai sake haɗa ni zumunci da su ta kan jikokinmu kuma, mu zamu aurawa Mark Anaya in har tana son shi yana sonta, shikenan sai ya karɓi musulci ayi masu aure".

Kusan a tare dayawa daga cikin jama'ar palon suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, daddyn Anayar ya ji daɗi sosai, ita kuwa Anaya cool murmushi ta saki tana faɗin "Good ƴar tsohuwa that's why i like you, ashe gwara da baki mutu bama, ga shi kin yi amfani".

Ita dai mummyn Rimsha baiwar Allah, duk kunya ya rufeta, kunyar Brr Naurat ma take ji sosai, ga su Abban Imran dukka surakananta ne, hakan yasa duk ta takure waje guda,. A duk cikin palo ita da aunty matar Abbi ne kawai suka san menene kunya, sune kawai masu kunya, ita ma Ammien su Imran ba kunya ke gareta ba, kowa yasan kabilar igbo dai ba kunya ce da su ba. Duk Anaya ta san mummyn Rimsha ta ji wani irin kunya, ta kuma ga laifin mummyn Anayar sosai, dan kome Anaya zata yi a yanzu, to laifin mummynta ne, saboda Anaya yarinya ce, kuruciya na a kanta sosai, tun farko ya kamata mummyn nata ta koya mata kunya, kamun kai, kamala, da dai sauransu, amma ji yanda Anaya take magana abu sam babu tsari, iyayenta ne a cike a cikin palon nan, amma ita babu ruwanta, tamkar da sa'aninta ko kannanta or kawayenta take hira, abin sam bai yi wa mummyn Rimsha daɗi ba, bayan ita da Aunty kowa a cikin palon babu wanda ya ga aibin abin da Anayar ta yi, shi ma daddyn Rimshar bai ga aibin hakan ba, dan a cewarsa, ai yarinta ce kawai tasa Anayar yin hakan, idan ta girma zata dai'na........Babban magana girma kuma na nawa?.

Haka suka cigaba da zuba hirarsu har zuwa rana ta ɗago, Anayar ma tuni ta yi barci a kwance a saman laps na daddynta, sai sauke nauyayyar ajiyar zuciya suke yi a cikin barci, sun sha kuka sun ƙoshi, ita ma Jehan barci ne ya ɗauketa, ta ci kuka kamar ba gobe.

After 2 days.

A cikin wannan kwana biyu da suka wuce, abubuwa da dama sun faru, bari mu fara da ɓangaren su Lion, sun isa Enugu state lafiya, kamar yanda Ammie ta basu address ɗin gidansu, haka suka yi amfani da shi, sai dai ko da suka je, gidan babu kowa, gate ɗin gidan ma a rufe yake ruf, da alama an ɗauki lokaci babu mutane a cikin gidan.

Zubawa gidan idanu sosai Lion ya yi, kai daga ganin gidan kasan ba iya kuɗin nema ne kawai ya gina shi ba, wannan uban kuɗi da aka narka wajen gina gidan, ai dole sai da kuɗin TSAFI, dama already Ammien ta gaya masu Queen bata zama a gidan, bata nan a cikin gidan, kuma gidan babu kowa, dan haka ko sun je, wahala za su sha, shi kuma Lion abin da kuka sani ne, a duk lokacin da ake magana, to yana nutsuwa ne ya saurari maganar da kyau, dan tattare zancen mai maganar a cikin ƙwaƙwalwarsa yake yi, saboda samun mafita, yana aiki ne da kaifin basirarsa sosai da sosai, a lokacin da Ammien take bada labarin Daular Mutuwa, a lokacin ya nutsu sosai yana jinta, a maganarta ta ce a baya tana shiga har cikin Daular Mutuwar, which means da akwai hanyar da zai sadaka da Daular Mutuwa daga ta cikin gidan kenan, kuma dama ai da kamar wuya ace babu wata hanya daga cikin gidan Queen da zai sadaka da Daular, tun da ita ce shugaban Daular, to dole akwai hanyoyi ma ba hanya ɗaya ba ta cikin gidanta, hakan tasa ya ce da Ammien ta bashi address na gidan Queen ɗin, kun ji masu hikima da basira, ita kuma Ammien sam bata kawo cewa da haka zai yi amfani ba, dan ita bata taɓa shiga Daular Mutuwa daga ta cikin gidansu ba, ta waje take shiga, Queen ta ɓoye masu hanyar cikin gidan, hanyar sirrice wanda babu wanda ta yarda ya sani, sai ita kaɗanta.

Duk sojojin sun tsaya suna jiran su ji me Lion ɗin zai ce, basu ankara ba sai ganinsa suka yi ya yi bismilah ya kama gate ɗin gidan ya haye, dan ba mutane a cikin gidan.

Wani abin da basu sani ba shi ne, tun da suka baro garin Kaduna a kan idanun Queen suke tafiya, har suka iso Enugu, duk motsinsu tana ganinsu, ta barsu ne kawai su iso, dan a cewarta a cikin satin nan, suna da liyafa a gidan nata, dodan tsafinsu na bukatar jini sosai, akwai wasu sabbin ma'aikata da suka karu, dama idan baku manta ba, duk waɗan da suka jima a Daular Mutuwa, in dai Queen ta kasa kashe su, to tana mayar da su mutanenta ne, sai ta juyar da su izuwa irinsu barbushi, to akwai wasu mutane guda biyu ciki har da Mustapha da wani, a satin nan za'ayi liyafar mayar da su mukarraban Queen, wato su zama magicians suma. BABBAR MAGANA, shi ne yasa Queen ɗin ta bar su Lion ɗin su iso kawai ta bawa dodan tsafinsu su, asha jininsu a ji daɗin yin liyafa da kyau, har shiga cikin gidanta da suka yi a yanzu, duk tana kallonsu, dariya ma suke bata.

Su kuwa bayan sun dira a cikin gidan, kai tsaye kofar da zata sadasu da babbar palon gidan Lion ya nema, babu tsoro ko ɗarɗar a tattare da shi, kai tsaye ya shige cikin gidan, kamar gidansa ne, yana shiga har da kunna wutar palon, dan ya gani ko suna aiki, sai dai a ganin sojojinsa ne suke ganin ya kunna wutar ne dan yaga ko suna aiki, shi kuma akwai dalilin da ya sanya ya kunna wutar, kunsan baya abu haka kawai, sai da dalili.

Yana kunna wutar ya nufi wata ɗaki da take fuskantar kugu maso gabas, tsohowar ɗaki ce sosai, dan da alama a kaf cikin gidan, ɗakin ce kawai ba'a buɗe kofarta, saboda kofar ta kama sosai. Har lokacin idanun Queen na'a kansu, ta kuma cire duk wasu matakan tsaro na koforin dake gidanta wanda zai sadasu da cikin Daular Mutuwar, ma'ana ta buɗe masu hanya kenan, jira kawai take yi su shigo. Su kuma bayin Allah, sam basu sani ba, babu wanda ya kawo wa ransa cewa Queen ɗin tana kallonsa, ɗan gara Lion ɗin ma, shi dama yasan matsafan nan babu abin da ba za su iya yi ba.

Yana isa wajen kofar, babu tsoro bai yi wata wata ba ya kai hannu ya murɗa handle ɗin kofar, nan take kofar ta buɗu, ganin ta buɗe ne yasa ya gane cewa lallai akwai wata a kasa, dan wannan kofa ta jima a rufe, bai kamata ace daga ya ɗan taɓata ta buɗe ba, dole da akwai wata a kasa, ga shi kuma gidan babu mutane ma, tun daga nan ya fara zargin wani abin a ransa, sai dai bai nunawa sojojinsa da alamar matsala ba, saboda kada ya sare masu gwiwa, ita kuma Queen bata taɓa tunanin cire makullan kofofin da ta yi zai iya sanya Lion ya fara zargi ba, bata kawo haka a ranta ba ,dan bata san kaifin basirarsa da kwakwalwarsa ba, sai dai hakika ta jinjinawa jarumtarsa, musamman yanda ya shigo mata gida kai tsaye, ya kuma nufi wannan kofa babu ko tsoro a ransa, yana acting tamkar shi ya gina mata gidan..........

(ni kuwa na ce in dai lion ne fin haka ma zai yi, shi gida nawa ma ya shiga ya nuna masu izza tamkar shi ya gina masu gidan? ya kuma aikata abin da zai aikata ya fito lafiya lou, ya shiga gidan Abba tamkar gidansa, ya je ya ɗauki Akila, ya kuma ɗaura mata aure da Aseef, sannan ya taka kafarsa har kasar Russia, ya je ya ɗauko Brr Naurat, su ma ya shiga gidansu tamkar shi ya gina masu, har ma da ɗaure gabadaya ƴan gidan ya yi, haka kuma ya fito kasar Russia lafiya lou, saboda tsantsar karfin hali da nuna isa, haka ya shiga gidansu Rimsha kamar gidansa, ya ɗaukota ya fito, ai shi Lion dama dai'dai yake da kowa, ko ya kuka ce READERS? Yanzu kuma ga shi a gidan Queen of Daular Mutuwa, kamar gidansa ya shige😂 Queen taga iko da nuna isa😂)

Cikin ɗakin suka shiga, gabaɗaya cikin ɗakin babu komai, wayam yake, sai lallausan carpet na alfarma dake sumfuɗe a cikinta. Zuba masu shegun idanunta Queen ɗin ta yi ta cikin ruwan tsafinta dake kwance a tsakiyar faɗarta kamar pool, sai kallonsu take yi, tana son ganin gudun ruwansu. Areef dai yana goye da uban jaka a bayansa, sai Allah yasan me ya lodo a cikinta!.

Sai bin ɗakin da kallo sojojin suke yi. Wani irin sihirtatcen kamshi ne ya fara tashi a cikin ɗakin, shi dai Lion har cikin ransa bai yarda da wannan kamshi ba, dan haka sai ya ce da sojojinsa su sanya face mask a face nasu dan kada su shaki kamshin.

Bai kai ga rufe baki ba, nan take sojojin nasa suka fara zubewa kasa kamar gawarwaki, dama wannan kamshi wani tuggune da Queen ɗin ta haɗa masu, ta ha kance kawai zata ɗaukesu izuwa cikin Daular Mutuwar.

Lion kafin ya yi wani yunkuri shima sai ya ji gabaɗaya jijiyoyin jikinsa sun tsaya, nan take ya ji tamkar an sare mashi ƙafafuwansa, dole shi ma ya zube kasa, dan already dukkansu sun shaki wannan kamshin turaren.

Areef yana ƙoƙarin yin kan Lion ɗin, shima sai ji ya yi tamkar an raba kafafunsa da jikinsa ne, nan take ya zube kasa, duk suka zama kamar gawarwaki, ga dai idanuwansu a buɗe, amma sam jikinsu babu karfi, babu mai iya motsa ko da ɗan yatsansa.

Haka suka cigaba da shaƙar wannan daddaɗar hamshin duk wasu gaɓɓai na jikinsu suna mutuwa, har idanunsu ma ya rufe ruf, kamar babu rai a tattare da su.

An ɗauki tsawon lokaci suna a haka, har sai da yamma ta yi, rana ta faɗi, sannan ne Queen ɗin ta fara ɗaukar mataki a kansu. Wasu zaratan mazaje jarumai masu ji da lafiya da karfi Queen ɗin ta aiko, zu ashirin cif, haka ta aikosu aka kwashi su Lion ɗin gabaɗaya, ɗakin dai babu wata kofa bayan wanda su Lion suka bi suka shigo, daga ta sama waɗan nan zaratan maza suka ɓullo, haka kuma da suka ɗauki su Lion ɗin, suka bi da su ta saman suka fita, ɓacewa suke yi ɓat........ KAI QUEEN SHEGIYA CE, TA WUCI TUNANIN MAI TUNANI TUNKARARTA SAI AN SHIRYA.

Kai tsaye sai cikin Daular Mutuwar aka wuce da su Lion, basu san ta hanyar da aka bi da su ba, dan Daular Mutuwa fa a yanzu bata da hanyar shiga sam sam. BABBAR MAGANA TASHIN HANKALI DA BA'A SAKA MASHI DATE, SU LION ZA SU FITO KUWA?.

A takaice dai a wani killatatcen waje Queen tasa suka kulle su Lion ɗin, waje ne mai cike da abubuwan ban tsoro da juya kwakwale, ashe ita Rimsha a cikin kaso ɗari ko kaso ɗaya na bala'in da kuma ɓangarorin dake a cikin Daular Mutuwar bata gani ba, akwai abubuwa da dama sosai. Gabaɗaya su Lion ɗin an kasasu ɗakuna daban daban, ba'a haɗasu waje guda ba, da alama Queen ta fi tsanar Lion a cikin tawagar, shi wani waje na daban mai cike da tsaro na bala'i ta kai shi, babu wani abin da idanu zai iya gani a wajen, saboda tsananin duhu dake a cikin ɗakin, ta sanya sarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login