Showing 201001 words to 204000 words out of 270744 words
airport ɗin, so kowa zai so ya san daga ina jet ɗin ta fito? Su waye kuma a cikinta? Dan haka manya manyan mutane masu faɗa a ji, sojoji da kuma ƴan'sanda sun cika airport ɗin tab, ga kuma ƴan jaridu kala kala makil a cikinta.
Sai dai su gwaggo basu fito daga cikin jet ɗin ba har sai da motocin su Lion suka danno hancinsu a cikin airport ɗin, sannan ne Areef ya yi umarnin da a boɗe masu jet ɗin su fita.
Sojoji biyun nan ne suka fara fitowa, sannan Alex ya rufa masu baya, sai Dr Salman and Brr Naurat da suka biyo bayansu suna shawagi kamar wasu taurari, kun san hasken Brr Naurat ba irin nasu bace, ta fi su Aseef haske sosai da sosai, duk da suke Turawa dukkansu, amma ta fisu haske, tayi fari over har haske ya so ya yi mata yawa, shiyasa gwaggo take sajewa da Turawar ai, saboda hasken Brr Naurat ke gareta, dama ita gwaggo ai Baturiya ce ba bakar fata ba, duba da yanayin yanda take ga ta girman kasar Russia.
Gwaggo da ƴan matanta tare da Areef sune a karshen fitowa, mummyn Rimsha ma ta rigasu fita, sun bar su Adiva a cikin jet ɗin, daga baya za'a ɗaukesu.
Gabaɗaya wajen motocinsu Lion ɗin suka nufa, ƴan jaridu da shegen gulma duk da basu san su waye bane, sai ɗaukarsu a hoto suke yi, saboda sun gansu daga cikin jet ɗin Lion suka fito.
Wani irin birki gwaggo ta ja a dai'dai tsakiyar airport ɗin lokacin da idanuwanta suka sauka a kan Lion da sir Arvin da suke tsaye a jikin motar Lion ɗin suna ɗan tattaunawa. Sam sam bata san da zancen sir Arvin ɗin ba, sun ruɗar mata da ƙwaƙwalwa, ta kalli Lion ta sake kallon sir Arvin, ga shi sun yi shigar kaya iri guda, Lion yasa nasa shi kuma sir Arvin ya sanya kayan Areef, so kayan iri ɗaya ne sak, dama haka kayan TRIPLETS suke, abin da ɗaya yake da shi sauran ma suna da shi, so sun fito tamkar mutun ɗaya ne, mai iya rabe su sai Rimsha da Pinky, dan Rimsha idan Lion goma masu kama ɗaya za'a kawo mata, to ba shakka zata fitar da nata Lion ɗin daga cikinsu........... Haƙiƙa ta yi wa masoyinta farin sani🤌😂
Sam gwaggo bata san time ɗin da ta saki hannun Rimsha ba, dama ta rike hannunta ɗin ne saboda ɗingisa kafa da Rimshar take yi, shi ne yasa ta rike hannunta dan ta taimaka mata, amma ganin sir Arvin da Lion yasa ta saki hannun nata tana binsu da kallo, ta kasa iya cigaba da tafiya.
Ganin hakan yasa Lion da sir Arvin ɗin suka nufota a tare, a lokacin kuma tuni su Brr Naurat sun shiga cikin motocin da suke jiransu, shi kansa Areef kasa cigaba da tafiya ya yi, duk wanda yasan cewa TRIPLETS mutun uku ne ba huɗu ba, sai da ya dakata da tafiya a lokacin, Rimsha ma ta sha ruwan mamaki sosai, amma Akila da Jehan basu wani sha mamaki ba, wucewa ma suka yi izuwa cikin motocin, dan su dama can ba wani sanin Lion suka yi ba, bare su sha mamaki dan an sami mai kama da shi, dama basu gama sanin su waye TRIPLETS ɗin ba.
Tga ma dai tsayawa ya yi yana kallon ikon God.
A tare suka iso wajen gwaggon, welcome suka yi mata, sir Arvin ya riga Lion rungumeta, dan Lion ɗin ya gaya mashi ita ce mommansu, kuma shi ma ya ga hakan a face nata, saboda tana kama da Aseef idan ka ganta a fisge, kuma ita gwaggo na gaya maku farar baturiya ce, bata da banbanci da su.
Shi kuma Lion a ɗan gefe guda ya tsaya yana karewa Rimsha kallo, ƙunshin jikinta kawai yake kallo, sam baya so, amma a yanzu dai bashi da zaɓin da ta wuce ya kawar da kallonsa daga kan ƙunshin nan, shi ne zamansa lafiya, dan haushinsa ake ji..........😂
Sam gwaggo bata san wanenen ya rungumeta ba, bata san sir Arvin ne ko Lion ba, ita dai ta shiga ruɗani, kanta ya kulle, sai kawai ta rungume shi ita ma.
Areef ne ya matso kusa da su yana tambayar Lion wanene wanda ya rungumi mommansun nan.
Harararsa Lion ɗin ya yi kafin ya ce "Saif ne mana".
Siririn dariya Areef ɗin ya yi yana faɗin "Sai dai biyunin Saif, wai kai Lion kana tunanin ko mutuwa nayi na dawo ba zai iya tsamoka daga cikin dubu irinka bane? To idan ma haka kake tunani ka makara, ni dai nasan TRIPLETS nawa TRIPLETS nawa ne babu in da zasu je su ɓuya mani ban iya gane su ba, yanzu dai gaya mani wanene ya rungumi momma? Dan brain nawa tana dab ta tarwatsewa, irin wannan kama haka".
Kin kara tanka mashi Lion ɗin ya yi, saboda bai son buɗe baki a cikin taron wannan uban jama'a haka.
Ko'ina hasken ɗaukar hoto ne kawai yake tashi a airport ɗin, daga masu cameras har masu wayoyi, abin ya girgiza jama'a, sun rasa wannan baki da gidan The General of the Army's yake yi na menene? Suna son jin su wanenen suke ta zuwa gidan, jiya wasu sun je, yau kuma ga wasu, anya lafiya kuwa? Babban abin da yafi damun jama'a ma shi ne, yadda yau suka ga Lion a cikin bakaken fata, shi da kowa ya sani a baya sam baya son bakaken fata, dan ma dai Allah yasa yawancin familyn gwaggon turawan ne ita ma, saboda kal kal suke kamar ka taɓa jini ya zuba, musamman daddyn Rimsha da Azharuddin Bature, so mix nasu da bakaken fata dai kaɗan ne, iya gefen Dr Salman ne, wanda kuma mutun biyu ne kawai daga cikin ƴaƴan nasa suka fito chocolate colors irinsa, sauran duk brr Naurat suka yo, shi kam Alex ma ai ba'a magana, harta blue eyes ke gare shi, sak su yake.
Waɗan da basu ganin abu su yi shiru har sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan su waye ne su gwaggo?.
Kasa hakuri gwaggon ta yi har sai da ta tambaya ya aka yi suka zama su biyu masu kama ɗaya? Ta manta da cewa jariranta biyu ne masu blue eyes kuma kamanninsu ɗaya sak, sannan Lion bai sanar da ita abin da ya je yi a kasar China ba, ya dai ce mata ya je yin wani aiki, so bata san da zancen komai a kan su Cherish ba.
Kasa kasa Lion ya ce mata "Idan mun je gida kun huta zuwa gobe zan gaya maki".
Jinjina mashi kai ta yi, sai da ya yi magana ta iya gane shi ne Lion, dan haka sai ta dawo da kallonta a kan sir Arvin, ko ba'a gaya mata komai ba ta ji a jikinta cewa ɗanta ne shi ma, sai dai ta rasa ya akayi ya zama ɗanta, ita dai tasan TRIPLETS ta haifa, kuma duk suna tare da ita, gaskiya kanta ya kulle a wannan gaɓar, bata san cewa tun time da ya faɗo duniya aka ɗauke ɗayan ba, tun time da bata a cikin hayyacinta aka rabasu, so lokacin da ta dawo cikin hayyacinta sai ta kalli su uku ne, anrigada an ɗauki ɗayan, dan haka bata san da shi ba baiwar Allah.
"Let's go momma". Lion ya faɗa har lokacin idanunsa suna a kan Rimsha, ta ɗaure fuska sosai, ita a dole da gaske fushi take yi dashi, taki yarda su haɗa ido kuma. (Rimsha want to kill me with laugh🤌😂)
Hannun gwaggon sir Arvin ya riko tare da wucewa gaba yana faɗin "Let's go momma". Gaba suka yi, Rimsha ta rufa masu baya tana ɗingisa kafa. Zuba mata idanu Lion ɗin ya yi yana kallon yadda take ɗingisa kafafun nata tana aikin wani turo baki, alamar tana jin zafi. Sai da ta ɗan yi tafiya kaɗan, sannan ya bi bayanta, ya tako izuwa in da take, bai yi mata magana ba ta baya ya sa hannu ya sunkuceta sai saman shoulder ɗinsa.
Habawa nan take jama'a suka fara yi masu hotuna na musamman, kowa sai tambayar kansa yake yi wacece ita? Yau Lion da ɗaukar mace, macen ma kuma gata bakar fata, sai dai kyakkyawar gaske ce, kuma a baynar nasi ya ɗauki kayarsa, ko a jikinsa? Lallai kam.
Kuka ta sa mashi tana faɗin "Ni Yah Saif ka sauke ni........"
Wani irin harara daya dalla mata ne yasa ta kasa iya cigaba da yi mashi magana, nan take ta haɗiye kukan nata cif, saboda tsoronsa, kuma ita ma dama bata son ta yi ja in ja da shi a cikin mutane, koda kuwa a cikin family ne bare kuma mutanen garin, hakan ma yasa ta yi shiru sai sun isa gida.
Tun da ya ɗauketa har ya kaita cikin motarsa karewa face nata kallo yake yi, ya yi tsananin kewarta sosai, ga shi ta sha gyara ta sha kyau over.
Tun da ya ɗauketa kuma jama'a suka aikin kashe masu hotona babu kakkautawa.
Sir Arvin cikin motar da yazo suka wuce da gwaggo, shi kuma Lion cikin motarsa ya wuce da Meesha, Areef da Jehan suna nasu motar, Akila ta yi mamakin rashin ganin Aseef a wajen, bata san cewa bai ma san sun iso ba, Lion ya ɓoye mashi, dan kada Dr William ya ga dukkansu basu nan ya damu, shi ne yasa ya bar mashi Aseef ɗin.
Sai da suka shiga cikin motocinsu, sannan ne Areef yasa bodyguards na Lion da su fito da Maryam da Adiva, su kuma fito dasu copper.
Haka kuwa aka yi, suka fito da su. Daga nan motocin suka tashi izuwa gida. Kan kace me labari ya baza gari, wasu su ce Lion ya yi aure ya auri bakar fata, wasu kuma su ce budurwarsa ce, wasu ma cewa suke yi yarinyarsa ce, dan sun ganta ƴar karama, basu san wannan under 15 years ɗin ita take cazawa His Excellence Lion ɗin nasu kai ba, wasu kuma su ce sai dai ko idan ya fara neman mata, dan su basu taɓa jin yana da aure ba, ko da sunan wasa ma basu taɓa jin yana da alaƙa da wata mace ba, a iya saninsu ma shi mutun ne da ya tsani mata a rayuwarsa, so dan haka wannan yarinya da ya ɗauka a airport karuwarsa ce, haka gidan wasu jaridun suka rubuta, abin ku da siyasa, tuni magana ta bazu har kunnan His Excellence. Yanzu wasan zai fara kenan....🔥
Kuma da idanunsa Lion ɗin ya ga jaridar da aka buga wai The General of the Army's ya ɗauko karuwarsa daga airport, ga shi kuma yadda aka ɗauki hoton nasu da aka sanya a jaridar, sun fita sosai, ya tsareta da idanu tamkar zai cinyeta, shi da kowa yasan mawuyacin abu ne ya ɗaga ido ya kalli abu na second biyu ma a rayuwarsa, amma ita ya tsareta da idanu sosai, ai dole dama ace wani abu a kan hakan, dan irin wannan kallo haka ya wuce na ƴan uwantaka ko kanwa ma, kallon tsantsar madarar soyayya ce tare da kewa ya rinƙa zuba mata.
Ganin wannan labari da aka buga a jaridar a wayarsa yasa ya kashe wayar ma gabaɗaya, yazama mashi dole ya fito ya gayawa duniya wacece Rimsha, ko yana so ko baya so, idan ba haka ba wannan magana ta karuwarsa ce ita zata iya sa ya kashe mutane dayawa, dan Rimsha ta fi karfin su dangantata da karuwarsa, zuciyarsa ba zata ɗauki hakan ba, bugu da kari hakan zai taɓa mashi siyasarsa sosai, so yana da kyau ya yi wani abin a kai koda ba yau ba ba gobe ba.
Ita kuwa Rimshar sai aikin turo baki take yi ta kawar da kai gefe guda, ita a dole bata son su haɗa idanu, sam bai kulata ba, dan baya son hayanayi a yanzu, wannan kalma ta karuwarsa ce da aka dangantata da shi ta tsaya mashi a rai, ta ɓata mashi rai, dan haka shi ma bai sake bi ta kanta ba har suka isa gida.
Sun isa gida lafiya, ita dai gwaggo bin sir Arvin kawai take yi, saboda tana jin a jikinta ɗan tane, amma duk ta ƙosa ta ji gaskiyar wanene shi?.
Ana kashe motocin a parking space na gidan suka fara fitowa, nan suka zama cikakkun ƴan kauye, dan gidan Lion fa ko mai mulki idan ya zo sai ya zama ɗan kauye, saboda ya tsaru ne iya tsaru, Daula ce guda.
Lion dai bai bi ta kansu ba, yana fitowa ya wuce cikin gida, ɗaukarta ya yi cak suka nufi parlourn, sai kalle kalle take yi, taga abin da ya sha gaban tunaninta.
A saman sofa mai zaman mutun uku ya zaunar da ita, sannan ya haura sama ya kira su Dr William.
Lokacin da ya sauko kasa su gwaggo duk sun shigo cikin parlourn. Koda gwaggo ta ga Dr William bata nuna kamar ma ta san shi ba, sai ta ɗauke kanta kawai, ta cigaba da kallon su Pinky da Handsome.
Shi kuwa Dr William yana ganinta ya furta A'isha, dan ko mutuwa zai yi ya dawo ba zai manta da face nata ba. Sam bata ɗaga idanu ta kalle shi ba, saboda bata san menene yake faruwa ba.
Cikin sanyin murya Lion ɗin ya ce da daddyn Rimsha "Uncle ka kai Dr Salman and brr Naurat ɗaya daga cikin part dake a hawa na uku, su Areef kowa already yasan part nasa, kai kuma Uncle sai ka ɗauki part ɗaya a hawa na biyu, daddy da momma ma part nasu yana hawan da kake......" Kasa karisa maganar ya yi saboda wani irin kallo da gwaggon ta wurga mashi, dan kawai ya ce daddy da momma part nasu na hawa na biyu, tasan da ita yake yi, kenan ita da Dr William? Tab akwai ƙura, sam bata ma san time da ta harare shi ɗin ba, sai da ta ga ya dakata da maganar da yake yi ne ta fahimci ashe ta harare shi ne........... (Gwaggo duniya😂)
Ganin ta banka mashi wannan harara yasa ya ja bakinsa ya yi shiru tare da wucewa yana faɗin "Momma ki zaɓi duk part ɗin da ya yi maki, ku je ku yi wanka ku huta, yamma ta yi yanzu, sai mun haɗu a dinner". Ya kai karshen maganar tare da wucewa sama abinsa, ba zai iya da masifar gwaggo ba, irin wannan harara da ta wurga mashi tasa bai san time da ya dakata da magana ba, to tun wuri gara ya kama kansa kada ya sami rabon mari. (Tab waye yaga an mari His Excellence Lion?😂 Akwai show🔥😂)
Ganin yadda ya ja bakinsa ya yi shiru ba ƙaramin dariya ya bawa gwaggon ba, dariya ta ɗan yi kafin ta wuce ta haura saman ita ma.
Ambatar sunan Dr William ɗin ya fara yi, ko kallon in da yake bata yi ba, ta haye sama dan ta duba ɗakin da ya yi mata ta zauna a ciki, shi kuma daddyn Rimsha ya yi wa su brr Naurat jagora dan cika umarnin Lion.
Jehan ta bi bayan mijinta, Aafia ta bi bayan gwaggo, parlourn ya rage saura Dr William da ya yi mutuwar tsaye yana mamakin menene yasa gwaggo taki kula shi? Ko dai bata san gaskiyar abin da ya faru bane? Sai kuma Handsome da shi dama bashi da kowa, sai kuma sir Arvin da bai wuce saman ba, Rimsha ma ta miƙe tana ɗingisa kafa ta bi bayan gwaggon.
Aseef kuwa ya tsaya ne yana karewa ƙunshin dake a hannun Akila kallo, akwai ƙura, dan wlh ya tsani ƙunshin nan, dole ta goge shi idan tana son zaman lafiya. (Da alama Aseef ya manta ita ƴar aljannace bata laifi🤌😂😂)
Tausar Dr William ɗin sir Arvin ya yi, ya sanar da shi cewa a yanzu gwaggo ba zata saurare shi ba har sai ta ji gaskiyar abin da ya faru, idan ta ji gaskiya zata saurare shi, ya yi hakuri dan Allah. Da kyar dai ya samu ya shawo kansa ya yarda ya wuce part nasa, zuciyarsa cike da tunanin gwaggon..............
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*
Date: 27/5/2024
E40
Juyawa sir Arvin ɗin ya yi da nufin ya haura sama shi ma, sai yaga Aseef a tsaye ya zubawa Akila idanu yana kare mata kallo, ita kuma ta yi kasa da kai tana wasa da ƴan yatsun hannunta da suka ji ƙunshi suka yi jajir da su.
"Aseef lafiya kuwa? What are doing here? Kowa ya wuce bedroom nasa dan ya je ya huta kai kuma ka tsayar da ita a nan! Shin ita bata gaji bane?".
Tsabar bakinciki kamar ba zai amsawa sir Arvin ɗin ba, amma sai ya daure ya buɗe baki cike da tsananin ɓacin rai zai fara magana. Bai kai ga fara maganar ba wani irin amai mai karfin gaske ta kwace mashi, kafin ma ya yi yunkurin motsawa daga in da yake har ya wanke ko'ina a arear wajen da amai ɗin, ga shi ya kasa dukawa kasa bare aman ta ɗan yi mashi