Showing 210001 words to 213000 words out of 270744 words
Date: 28/5/2024
E41
Dr William kuma ya riko shi sai faman tambayarsa yake yi, sun mance da zancen cewa faɗa ma suke yi shi da gwaggon, sun rungumi ɗan nasu suna tambayarsa me yake faruwa?.
Wucewa gwaggo ta yi tana tambayarsa ina Jehan ɗin! A ina ne bedroom ɗin nasa?.
Da sauri ya bi bayanta dan ya je ya nuna mata, duk a birkice yake bawan Allah. Rufa masu baya Dr William ɗin ma ya yi.
Kamar yadda ya barota haka suka shigo suka sameta, ko motsi bata yi, tana a sume. Saman bed ɗin gwaggon ta haye ba tare da ta sake ɗaga idanuwa ta kalli in da suke ba.
Ganin hakan yasa Dr William ɗin ya fahimci abin da ya faru, ƙoƙarin taimakawa gwaggo ya fara yi, dakatar da su ta yi tare da ce masu daga shi har Areef ɗin su fita su bata waje dan Allah, sannan Areef ya kawo mata A box ya kuma nuna nata word room nasu, dan ta je ta ɗauki abubuwan da zata ɓukata.
Jikinsa har kerma yake yi bawan Allah, duk a tsorace yake ya wuce ya nufi wajen da yake ajiye A box ɗin nasa, da yake dukkansu suka da A box ɗin a cikin bedroom ɗin nasu, sai ya ɗauko da sauri ya kawo mata.
Karɓa ta yi tare da kara gaya masu su fita su bata waje ta yi aikinta. Ba musu Dr William ya ja hannun Areef ɗin dan shi bashi da burin da ya wuce yaga gwaggo a cikin farinciki, baya son ɓata mata rai, shiyasa ya ja Areef ɗin dan su fita wajen kamar yadda ta buƙata.
Da farko Areef ɗin ya kafe yaki fita, sai da gwaggo ta yi mashi kalamai masu taushi tare da gaya mashi in dai yana ɗakin ita ba zata iya duba Jehan ba, so idan yana son a ceci ran matarsa sai dai ya fita. Jin hakan ne yasa ya yarda ya bi daddyn nasa suka fice waje.
Bedroom na daddyn nasa suka wuce, sai kerma jikinsa yake yi, duk jarumta irin tasa yau ya nemeta ya rasa, wani irin tsoro ne ya shige shi.
A saman bed nasa daddyn ya zaunar da shi yana mai tausarsa tare da kara mashi kwarin gwiwa.
Murya a raunace ya ce "Daddy ba zata mutu ba ko?".
Zama a gefensa daddyn ya yi tare da ɗan rungumo shi yana faɗin "In Sha Allah ba zata mutu ba, babu abin da zai sameta, mommarku ƙwararriyar likita ce, zata yi mata magani, cikin ƙanƙanin lokaci zata sami sauki, be strong my son".
Sake jikinsa ya yi ya kwatar da kansa a saman laps na daddyn nasa yana faɗin. "Daddy she's bleeding and kuma bata motsi, please daddy help me kada ta mutu, i really love her more than your expectations". Ya yi maganar da wata iriyar raunataciyar murya.
"My son calm down, babu abin da zai faru ka ji ko? Bari na kawo maka ruwa ka sha, sai ka kwanta a saman bed nawa ka huta kaɗan kafin mommarku ta gama aikinta ka ji?".
Shiru ya yi ya kasa magana, saboda bai san me zai sake cewa daddyn nasa ba. Ruwa mai sanyi a fridge daddyn ya ɗauko mashi tare da dawowa ya kawo mashi. Tsabar yana cikin damuwa bai san time ɗin da ya ɓalle robar ruwan nan ya fara sha ba, sai da ya shanyeta tas ne ya lura da ma ruwa yake sha ashe.
Karɓar robar dad ya yi tare da ce mashi to ya kwanta ya huta, wayo daddyn yake so ya yi mashi, yana so ne ya saka shi yin barci, idan ba haka ba ciwon kai zata kama shi, saboda da alama abin ta taɓa shi sosai, yasan cewa idan ya ce kai tsaye ya kwanta ya yi barci, ba zai taɓa yarda ya kwanta ɗin ba, amma da yake babba kam babba ne, kuma wanda ya haifeka ko bai taɓa zama a class ba to zai iya juyaka ta sigar da baka yi tunani ba koman iliminka kuwa, koda ka kai matsayin professor or Dr, bare kuma shi Dr William da karatun ma da ya yi sam babu wanda ya yi ko rabinsa a cikinsu, da shi da gwaggo ai sun yi karatu bana wasa ba, idan baku manta ba duk soyayyar da suka yi a tsakaninsu, basu taɓa yarda soyayyar ta shafi karatunsu ba, shi ne ribar da suka fara cinmawa kenan, dan haka sai ya lallaɓa shi har ya yarda ya kwanta ba tare ma da yasan ya kwanta ɗin ba, zama a kusa da shi daddyn ya yi yana mai cigaba da lallaɓa shi har sai da burinsa ya cika barci ɓarawo ta ɗauki ɗan nasa.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya nufi waje, dan ya je ya duba gwaggo da kuma jikin Jehan ɗin, tun da Allah ya taimakesu barci ya ɗauki Areef ɗin, kuma da alamar gajiya sosai a jikinsa, so barcin nasa zata yi nauyi sosai.
A ɓangaren Lion da sir Arvin kuwa, ko da sir Arvin ya lura da canzawar ɗan uwan nasa, sai ya yi ƙoƙarin tambayarsa me yake faruwa ya gansa a cikin damuwa har haka?.
Sam Lion bai ɓoye mashi komai, ya gaya mashi abin da yake faruwa a tsakaninsa da Rimshar, daga karshe ya rufe mashi da cewa "I can't sleep without her, am in to much of missing her".
Matsowa sir Arvin ɗin ya yi tare da dafa kafaɗunsa, cikin nutsuwa ya fara magana. "Ba tana sonka sosai ba?".
Jinjina mashi kai ya yi alamar yeah tana son shi sosai.
"To in dai tana sonka sosai me ka zauna jira? Go and carry her, duk fushin da take yi da kai na tabbata sai dai idan bata haɗa jiki da kai or baka ɗaukota zuwa nan ba, kuna dawowa cikin bedroom nan shikenan, ka mantar da ita cewa tana yin wani abin wai shi fushi da kai, are you not a man? Ai ba ma sai na gaya maka ba, yakamata kasan abin da zaka yi mata".
Nisawa ya yi kafin ya ce "I know that idan na ɗaukota ko kuma na tsaya na yi magana da ita na second biyar kawai zata dai'na yin fushin, dole ma ta sauko ta hakura, tana da zuciya mai kyau, but the problem here is, wannan abin da ta zana a jikinta, i don't want to see it at all, yana sanyani ciwon kai mai tsanani, and then kuma yana sanya zuciyata tashi, ba dan haka ba, zan yi abin da ka ce".
Shiru sir Arvin ɗin ya ɗan yi kafin ya ɗaura da cewa. "Ka danne zuciyarka, ka kawar da tunanin abin a ranka, and then kuma ai abin ba wani abin kyama bane ba, is just a flowers ne fa kawai, please Saif kada ka cutar mana da kanka, kawai ka je ka ɗauko ta, ka kalli flowers ɗin da ta yi ɗin a matsayin masoyiyarka da tafi kowa sonka ta yi maka kwalliya, idan ka gan shi ta wannan sigar to tabbas zaka ji kana son flowers ɗin sosai, ka kallah a matsayin kai ta yi wa kwalliya, kuma soyayya ce tasa ta yi maka hakan, you will love it more than your expectations".
Shiru ya yi tamkar ba zai sake tankawa ba, sai kuma ya miƙe tsaye tare da sumbatar sir Arvin ɗin a kumatu yana faɗa mashi yana zuwa bari ya je wajenta. Da ɗan guntun murmushi sir Arvin ɗin ya bishi da shi yana mai jin tsananin kaunar ƴan uwan nasa har cikin ransa.
Yana fita part na gwaggo ya koma. Babu kowa a cikin bedroom ɗin na gwaggon, kai tsaye sai ya nufi ɗaya daga cikin bedroom da yake a part ɗin wanda yake zaton zai samesu a ciki.
Ya kuwa yi sa'a Akila da Aafia suna a cikin bedroom ɗin, Rimshar bata nan.
Karo na farko a rayuwarsa tun da ya girma ya yi wayo da ya fara magana da wata mace bayan Rimsha da gwaggo, Aafia ya tambaya ina Rimsha, dan Akila kam har yanzu tana ƙudundune a cikin bargo, da alama zazzaɓi ne yake damunta.
Sosai Aafia ta tsorata da ganinsa, tun da take bata taɓa ganinsa ba sai yau, wani irin razana ta yi saboda kwarjininsa, ga shi yana sanye ne da kayan barci ya kuma saki dark black curly hairnsa nan har baya, sai ta kalli kamar aljani ne ba mutun ba, saboda azababben kyansa, ga idanuwansa sun kara kyalli, saboda dare.
Bakinta har kerma yake yi wajen bashi amsar Rimsha tana ɗakin mummynta. Bai sake bi ta kansu ba, ya juya ya fito daga part ɗin mai gabaɗaya.
Part ɗin daddyn Rimshar ya shiga, bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa. Iya daddyn Rimsha ne kaɗai a cikin parlourn, mum da ita Rimshar suna cikin bedroom, yanzu suka kammala cin abincin a tare, shi ne mum da Rimshar suka shiga ciki, ita mum ta wuce bedroom nata, ita kuma Rimsha ta shiga ɗayar bedroom ɗin, dan ta yi wanka ta shirya ta kwanta a cikin bedroom ɗin, ta ce wa mum ɗinta yau a nan zata kwana, da mum ta ce ta je wajen mijinta, sai ta ce ai baya son ƙunshi ya ce sai ƙunshin ta goge, idan ba haka ba zai yi amai, shi ne yasa mum ɗin ta barta a part ɗin nasu ta kwana.
A cikin tsakiyar parlourn ya shigo yana mai kara yin sallama, da mamaki daddyn Rimshar yake kallonsa, kasancewar shi ne babba kuma yasan halin Lion ɗin, izuwa yanzu ya fahimci wanene shi, ya fahimci ba wai son shi ne Lion ɗin baya yi ba, kawai shi yanayinsa ne a haka, amma yana tsananin sonsa, a duk cikin ƴan uwan gwaggo ma yafi son shi, hakan tasa ya ce "Saif lafiya kuwa?".
Zubawa uncle ɗin nasa idanu na ƴan sakanni ya yi kafin ya ce "Uncle am looking for my wife".
Haƙiƙa daddyn ya yi mamakin na jin cewa Rimsha yake nema, saboda ta ce masu wai shi ne ya ce ta tafi sai ƙunshinta ya goge zasu sake haɗuwa, to ya aka yi yanzu kuma yake nemanta? Kenan karya ta yi masu ne ko yaya?.
Sexy voice ɗin Lion ɗin ne ya katse mashi tunanin da yake yi da cewa. "Uncle where's she? And what are thinking?".
Nisawa daddyn ya yi kafin ya ɗan yi murmushi kaɗan, sannan ya ce mashi. "Am thinking about you and Rimsha, she's inside that bedroom".
Kamar zai sake tambayar daddy tunaninsa shi da Rimsha kuma a kan me yake yi? Sai kuma ya fasa ya nufi bedroom ɗin kawai. Da kallo daddyn ya bishi har ya karisa shiga cikin bedroom ɗin.
(Asamu wata fisabilillah ta koyawa TRIPLETS kunya 🤌 sam su basu da shi, bama iya TRIPLETS kawai ba, gabaɗaya familyn Dr William zaku taimaka ku koyawa kunya my readers 🤌 dan turawan nan sai a hankali, yanzu dai babu ruwansa ya shige cikin bedroom ɗin abinsa, dan ma dai dukkansu daga su har su daddyn Rimsha jirgi ɗaya ce ta kwaso su, akwai mix na jinin a jikinsu, shiyasa basu damuwa)
Yana shiga cikin bedroom ɗin ita kuma ta fito daga wanka kenan, ɗaure take da towel a kirjinta, iya rabin santala santalan cinyoyinta towel ɗin ya tsaya mata, ta saki kyakkyawar gashin kan nan nata, sai ƙoƙarin goge gashin nata da ƙaramin kyakkyawar towel da yake a hannunta take yi.
Sam bata ji shigowarsa ba, kuma bata lura da shi a bakin kofar bedroom ɗin ba, sai dai kuma kamshin perfume nasa da ya bulbule ko'ina a cikin ɗakin ne yasa ta fahimci lallai ya shigo ko kuma yana kusa da bedroom ɗin, ta ɗaura wannan ƙaramin towel ɗin a saman kanta ya yin da ta dukar da kai tana goge gashin nata, kasa ɗago kai ta yi ta kalli hanyar shigowa ko kuma ta karewa cikin bedroom ɗin kallo, saboda tana tsoron haɗa idanu da shi, tabbas tasan ya shigo ko yana kusa.
Sak ta tsaya a tsakiyar ɗakin ta kasa iya cigaba da nufar gaban mirror da take nufin zuwa, ta kuma kasa iya cire wannan ɗan towel ɗin daga kanta ta ɗago ta kalle shi, tsoro ne duk ya kamata.
Shi kuma yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman Lion chest nasa yana kare mata kallo cike da sonta da kuma tsantsar kaunarta, sir Arvin ya yi gaskiya da ya ce mashi idan ya kalli ƙunshin nata a matsayin shi ta yi wa kwalliya zai ji abin ya burgesa, karo na farko a rayuwarsa da hakan ta faru, sai ya ga ƙunshin ya yi mata kyau sosai, bare ma ƴan yatsun hannun nan nata da suka ji jan ƙunshin suka yi jajir har wani maroon maroon suka yi, sai abin ya yi matuƙar tafiya da imaninsa.
Ganin ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ga shi kuma tana fama da ciwon kafa tana aikin ɗingisata, sai ya ce bari ya rage mata wahalar tsayuwar nan da ta yi. A hankali ya tako zuwa in da take. Hannu ya kai ya cire ɗan towel ɗin daga kanta kafin ya ɗauketa cak. Sai a saman mirror chair ya sauketa. Hannunsa dukka biyu ya sanya yana ƙoƙarin tattaro mata gashin kan nata domin ya tara waje guda ta samu ta buɗe idanu su kalli juna.
Sai dai ko da ya tara mata gashin nata, sai ta datse idanuwanta gam taki yarda ta buɗesu.
"Meeshana". Ya ambaci sunanta kasa kasa cikin wata iriyar murya mai sanyin gaske. Har cikin ranta ta ji wannan zazzaƙar sexy voice ɗin nasa, hakan yasa ta saka mashi kuka idanu a rufe tana faɗin "Ni Yah Saif me ya kawoka gidanmu? Ni ka tafi bana son ganinka, me kazo yi?". Duk zakin sexy voice nasa da kuma kewarsa ne ya ruɗata ta ce ya tafi masu daga gida, wai gidansu, idan ka bibiya ma bata san ta faɗi hakan ba, so mugun wasa.
Rage tsawonsa ya yi ta yadda ya ɗan kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, a kunne ya raɗa mata. "Kewarki ne ya kawoni gidanku rigimammiya kawai, kuma ba zan tafi ba sai tare da matata, ko ki bini mu tafi, ko kuma nima na kwana a nan, wai Meesha yanzu kin dai'na jin tausayi nane? Kin dai'na so nane?".
Kai ta gyara mashi alamar yeah ta dai'na son shi. "Okey to buɗe idanunki ki kalli cikin nawa idanun ki gaya mani kin dai'na sona, idan kika yi hakan zan tafi".
Kuka ta sake saka mashi tana faɗin "Ni wlh ba wani buɗe idon da zan yi, a haka ya isa, ni kawai ka tafi".
Nisawa ya yi tare da manna mata sumbata a wuya, ga ruwan dake sauka daga gashin kanta yana jika mashi face nasa, kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana. "Meesha meyasa kike son ki wahalar dani ne? Kin san me nake ji kuwa? Kin san adadin son da nake yi maki kuwa?".
Turo ɗan baki ta yi tana faɗin "Yah Saif baka sona, idan da kana sona ba zaka tafi ka barni ba, kuma baka kirani a waya ba, sannan kuma......."
Bai bari ta karisa maganar ba ya kai hannunsa ɗaya ya rufe mata ɗan bakin nata, a kunne ya raɗa mata. "Wlh i really love you more than anything in my life my Meesha, kawai aiki ne ta sha gaban tunanina ta yadda bani da zaɓin da ya wuce na yi maki abin da nayi maki, please kada ki horani da fushinki a gareni, ba zan iya jurewa ba kin ji ko? Am so so sorry na rashin kiranki da ban yi ba".
Juyowa gare shi ta yi tare da fara kai mashi dukan wasa a kirji tana faɗin. "Ni babu ruwana da kai, kawai ka tafi part naka, ni na dawo wajen daddy na kenan".
Riko hannayen nata da take kai mashi dukan ya yi yana faɗin "Da gaske kin dawo wajen uncle?".
Kai ta gyaɗa mashi alamar e da gaske tare da cewa. "Kuma ba zan sake zuwa in da kake ba, sannan daddyna abin da nake so shi yake so, shi ma zai ce ba zan bika ba".
"Okey bari mu gani da ni da ke waye uncle ɗin yafi so". Ya kai karshen maganar tare da sake hannayen nata ya juya izuwa parlour.
Still har lokacin daddyn nata yana zaune a saman table ɗin yana shan green tea mai zafi, mum ma ta fito cikin shigar kayan barci, bata san cewa Lion ɗin yana part ɗin nasu ba, shi kuma daddy ya manta bai sanar da ita ba, Allah ma yasa tana zaune a kusa da daddyn ne, iya wuyarta zuwa face nata zaka gani, da a tsaye take ne sai ta ji kunyar Lion ɗin sosai, shi dai kunsan ba dai ya ji kunyarta ba, sai dai ya barta da jin kunyar ita, to Allah ma yasa a zaune take suna hira da mijin nata ita ma, sai abin bai bata kunya sosai ba, amma dai bata so hakan ba sam sam, dan da ta gan shi ya fito daga bedroom ɗin da Rimshar take a cikima sai da gabanta ya faɗi.
Daga ɗan nesa da su ta kusa da bedroom ɗin da Rimshar take ya tsaya. Kallon shi daddyn Rimshar ya yi kafin ya tambaye shi lafiya?.
"Uncle Meesha ta ce ba zata bini ba, wai ta dawo wajenka kenan". Ya faɗa yana kallon daddyn a cikin ido.
"Ta isa ta ce ba zata bika ba, tun wuri ta fito kafin nazo". Ya bashi amsa tare da miƙewa ya nufi in da yake. "Ina take nema?".
Dama da gangan Lion ɗin ya yi mata hakan, da gangan ya haɗata da daddyn nata, da biyu ya yi hakan. Cikin bedroom ɗin suka koma a tare, tana zaune a wajen da Lion ɗin ya barta sai aikin kumbure kumburen kumatu take yi.
"Rimsha yau kece kike cewa bazaki bi mijinki ba? Ke da nake yabo kullum ɗin? To tun wuri ki tashi ku tafi, da safe ma zamu haɗu da kene, me kika ce mana ɗazun? Ba kin ce shi ya ce baya son ganin lallen da yake hannunki ba, dan haka ki dawo nan da zama ba?". Ya yi maganar cikin harshen Hausa, dan kada