Showing 81001 words to 84000 words out of 270744 words

Chapter 28 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2984

kuma da izinin Allah sanadiyar wannan marainiyar Allah Maryam, in dai suka cutar da ita duk da whalar da ta sha, wlh Allah ba zai barsu ba, zai yi mata sakayya cikin gaggawa.

Ƙoƙarin kunna wayoyin ta fara yi, sai dai dukka sun ki kawowa, dan haka sai ta nufi waje da su, bedroom nasu ta nufa, chaji ta je ta sanya wayar tare da zama a gefen bed ta buga uban tagumi tana tunanin mafita. A haka Jelly ta shigo cikin ɗakin ta sameta, kusa da ita ta zauna tana faɗin "Aunty Jehan ina kwana?".

A lallai Ammie ta gyara Jelly, har da su Aunty Jehan, duniya sabuwa, wato rashin mahaifiya babbar musifa ce kuma babbar barazace ga tarbiya da kuma rayuwar yaro gabaɗaya, yanzu dai daga ɗan zamanta da Ammie har ta koyi wasu abubuwa masu amfani, ta nutsu sosai, Allah Ubangiji ka karawa mahaifanmu daraja, ka kara masu lafiya, ka kuma kara masu nisan kwana, waɗan da suka rigamu gidan gaskiya, Allah ka jikansu da Rahman.

"Lafiya lou Jalila fatan kun zo lafiya?". Ta bata amsa tare da mikewa ta nufi waje, dan ta je wajen daddynta, yau ta tuna da rayuwarta ta baya gabaɗaya, tana son ta je ta gayawa daddynta labarin su Sadiq ɗin Katsina, bata san cewa mum ta riga da ta gaya mashi ba, ya kuma ce idan su Lion suka dawo, komai ya dai'dai ta, zai taka kafarsa har izuwa Katsinar da kansa, zai je ya gaishe su, ya kuma yi masu godiya.

A garden ta isko daddynta, daddyn Anaya Abba da kuma Abbi, sai gwaggo da Brr Naurat da daddyn Jelly, suna tattaunawa a kan abin da ya wuce a baya, Brr Naurat ne ta ce daddyn Rimsha ya basu labarin yanda ya yi bayan ya baro gida, da kuma yanda ya yi rayuwa, yanda ya haɗu da mummyn Rimsha da dai sauransu, to bai kai ga fara basu labarin ba Jehan ɗin ta shigo baki ɗauke da sallama, a tare suka amsa mata, sosai Brr Naurat ta zuba mata idanu, tana tsananin Kaunar Jehan ɗin, saboda kamanceceniya da daddynta da take yi. Kuma a duk cikin surukanta Brr Naurat ɗin ta fi kaunar mummyn Rimsha da kuma Aunty matar Abbi, saboda sun fi girmamata, sunfi ɗaukarta da daraja, musammanma mummyn Rimsha, ta ɗauki Brr Naurat ɗin tamkar mahaifiyarta, hakan yasa ita ma tafi kaunarta sosai ita da ƴaƴanta Rimsha da Jehan, dama kuma kunsan already shi daddyn Rimsha shi ne shalelen Brr.

A duniya kowa yana son na gari, kowa yana son mutumin kirki, mai kyautata masa, ya Ubangiji kasa mu zama na kirki a koma wani irin hali muke ciki.

Kusa da daddyn nata ta zo ta zauna tana faɗin "Daddy yau fa na tuna da rayuwarmu ta baya ne, ina son naje Katsina wajen maman Sadiq, wlh tana da kirki over daddy, ta taimakemu sosai, ina son nima na taimaka mata, ina son ka bani kuɗi dayawa in kai mata".

Da yake daddyn nata yana zaune kusa da Brr Naurat ne, sai Brr ɗin ta kai hannu tana shafa kanta, a nutsu ta ce "Haka ake so Jehan, idan mutun ya yi maka alkhairi kada ka taɓa mantawa da shi, Allah ya yi maki albarka".

A tare suka amsa da Amin, sannan daddyn nata ya ce "To shikenan my baby, jeki cikin gida muna tattaunawa ne a yanzu, idan Allah ya dawo mana da su Areef lafiya, mun huta, komai ya lafa, zamu je Katsina ɗin ni da ke".

Okey ta amsa mashi da shi, sannan ta miƙe ta bar wajen, cikin bedroom nata ta koma, a in da ta ɗauki wayar Rimsha ta zauna a bakin bed kusa da Jellyn tana mai cigaba da kiran number Areef tamkar yanda ta saba a koda yaushe, sai dai kash a koda yaushe number tasa a rufe take, babu network sam sam.

Su kuwa su Brr Naurat, daddyn Rimsha ne ya fara basu labarin yanda ya yi rayuwa bayan barowarsa gida, cikin nutsuwa ya fara magana kamar haka.............

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E14



Date: 24/4/2024





Su kuwa su Brr Naurat, daddyn Rimsha ne ya fara basu labarin yanda ya yi rayuwa bayan barowarsa gida, cikin nutsuwa ya fara magana kamar haka.

"A lokacin da na fita gida, hotel na fara kamawa, ina shiga ɗakin nawa, na zauna na ci kuka na son ra'ina, a wannan rana na kwana ban yi barci ba, sai dai kuma na kudurci niyar duk wuya duk daɗi ba zan koma gida ba, ba zan sake waiwayar kowa ba, na kudurta a zuciyata zan yi rayuwata ni kaɗai'na, zan kuma tsaya tsayin daka na nemi ilimi, zan shiga siyasa, daga karshe kuma ina rokon Allah da ya bani iko da dama na samu na taimaki ƴan uwana a duk in da za su kasance, yin wannan tunani yasa ya sami karfin gwiwa, dan haka sai na tashi na yi wanka, na daura towel ɗin hotel ɗin na ɗan kwanta na huta, sai dai tunanin mummy da cikinta ya hanani sukunin, haka dai a daure ina yi mata addu'a. A washegarin ranar na nemi gida na saya, kuɗin da Mommy ta bani suna da mugun yawa sosai, da su na cigaba da yin rayuwata, na koma makaranta, na kuma fara sana'a, ko kaɗan bana tunanin komawa gida, a duk abubuwan nan da na saya kuma ko rabin kuɗin da mum ta bani ban taɓa ba, saboda kuɗin dollars ne, idan na canza kaɗan suna da yawa a kuɗin Nigeria, haka na cigaba da rayuwata ni kaɗai tsawon lokaci, ina zuwa makaranta, kuma ina juya kuɗina, akwai lokacin da ta kama dole na je gida, haka na shirya na je gidan, sai dai ban bari kunsan naje ba, takardun makarantata na je na ɗauka, a lokacin na sami mum tana zaune a garden, na tsaya tsawon lokaci ina laɓe ina ganinta, sai dai ita bata ganni ba, daga karshe na ɗauki abin da zan ɗauka na fita gidan, haka na kammala karatuna ni kaɗai na, ina kuma bibiyar ƴan uwana, ranar da aka ce daddy ya rasu, har gida nazo dan na tabbatar, amma babu wanda ya ganni, komai da yake wakana a gida ina sane da shi, har auren yaya babba duk ina sane da komai, kuma na tura mashi da gudumawata, sai dai bai san cewa ni ne na bashi ba, auren yaya Deen duk ina sane da su, har haihuwar Imran da matar yaya babba ta yi, duk ina sane, kafin haihuwar Imran ma korin Aunty Aisha da babban yaya ya yi daga gidansa duk ina sane, shi ne na je na ɗauketa, amma fa kafin na yi rayuwa da Aunty Aisha, na ruke Maik tukun nan, lokacin da naje gida dan tabbatar da mutuwar daddy, a lokacin na samu labarin cewa har da mum suka rasu, maganganun mutane ya kasu kashi biyu ne a lokacin, wasu sun ce ban da ita, wasu kuma sun ce har da ita, to ni dai da ban ganta a gidan ba, sai na ɗauko Maik muka dawo da shi gidana, ya yi rayuwa mai ɗan tsawo a wajena, ina ganin su baban yaya suka rinƙa nemansa, amma naki bayyana masu yana wajena, sai da ya ɗauki tsawon lokaci a wajena, sai tafiya ta kamani zuwa Dubai a kan harkar kasuwancina, bani da zaɓi dole na mayar da Maik gidan yaya babba, haka na shirya na ɗauke shi zuwa gidan, na bawa mai gadi shi, sannan na juya na koma, sam ban so rabuwa da Maik ba, na so na rene shi ne ya taso a hannuna, amma ba hali, da na tafi Dubai na ɗauki tsawon shekaru uku a can, a lokacin ne kuma Allah ya kara bunkasa mani arzikina, komai na taɓa kuɗi, har mamaki nake yi, abubuwa suka kara haɓaka, lokacin da Aunty Aisha ta baro gidan yaya babba ta suma a kan hanya, a lokacin ina Dubai, amma na sami labari ta hanyar security dana sanya yana yi mani gadin gidajen ƴan uwan nawa, dan ya gaya mani me yake faruwa, ina daga can nasa aka kai mani ita asibiti, satin ta ɗaya a asibiti na diro Nigeria, ni na cigaba da kula da ita na tsawon shekara ɗaya, bayan ta sami lafiya, sai na ɗauketa muka je har Washington, dan ta bani labarin abin da ya faru da ita, da muka je bamu sami waɗan da muke nema ba, sai na wuce da ita Dubai, a nan muka cigaba da rayuwarmu, ina sane da duk irin nemana da ƴan uwana suke yi, amma ko kaɗan ban ji cewa zan koma cikinsu ba, mun yi rayuwa mai tsawo a Dubai da Aunty Aisha, rabon auren Maryam ya dawo damu Nigeria, kafin mu dawo na sa an shifiɗa mana shinfiɗaɗɗen gini na alfarma, gini na gani na faɗa, muna dawowa na cewa Aunty Aisha zan je Niger in duba yanayin yanda ƙasar take, dan ina son buɗe company a can, a lokacin ina da wani aboki ɗan Niger ɗin, shi ne yake yawan bani labarin kasarsu, a makaranta muka haɗu, shi ne nace to bari naje ziyara na duba mu gani, ashe rabon auren Maryam ne ya kai ni, a hanyata muka haɗu da Shitu wanda ya kasance ɗan uwane ga ita Maryam ɗin, in takaice maku labari da na je ƙasar Niger, na so mu sauka a hotel, amma abokina ya nuna baya son hakan, ya nuna ba zai ji daɗi ba idan har ban sauka a gidansu ba, dan yana bawa ƴan uwansa labarina, iyayensa duk suna son ganina, yin hakan yasa na ce mashi to shikenan mu je gidan nasu, haka kuwa aka yi, lokacin kankanin na yi sabo da Shitu, muka zama kamar ƴan uwa, yana da kirki sosai, har muka karɓi number juna. Saukata a gidansu abokina naga karamci, suna da karamci sosai, mutanen Niger adilan mutane ne masu kirki sosai da sosai, suna da karamci over, haka suka karramani, suka mutuntani, a tare da abokina muka kwana, washegari da safe, bayan na yi wanka na shirya zamu je yawace gari da motar abokin nawa, muka shiga wajen mahaifiyarsa dan mu gaisheta, a nan na fara ganin Maryam, tana zaune kusa da mahaifiyar abokin nawa, da alama aikota aka yi, tana sanye da hijabinta har kasa, duk da cewa hijabin da kuma kayan jikinta duk a koɗe suke, amma ta yi shiga ta mutunci wanda duk wani ɗa namiji mai hankali zai sota, kuma zai yi sha'awar ta zama matarsa. Muna shigowa ta ɗaga mana gaisuwa cikin sanyin murya tana sunkuyar da kai kasa, kyakkyawar gaske ce sosai da sosai, sai dai alama akwai wahala sosai a tattare da ita, dan duk fatar jikinta a koɗe. A gaban idanunmu maman abokina ta bata sakon da ta zo karɓa a leda, ta tashi ta tafi abinta, mu kuma muka gaisa da maman abokin nawa, sannan ta zuba mana adduo'i tare da fatan alkhairi, daga nan muka fito, muna shiga cikin mota abokina ya kai mani duka yana faɗin malam ya naga sai kallon Maryam kake yi? Dariya na yi ina cewa kai kuma sarkin sa ido ba, dan Allah ƴar wacece? Ko kanwarka ce?. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen gaya mani cewa ita marainiya ce, kuma ga in da take rayuwa, ya bani labarin komai da irin wahalar da take sha a hannun ƴan uwan mahaifiyarta da sauransu, na ji babu daɗi sosai, kuma na tausaya mata sosai, dan haka sai nace to muje gidansu, ko da muka je sai muka tarar da Shitu a gidan, shi ma ashe ya je dubata ne, ɗan uwanta ne ta gefen mahaifinta daga Nigeria kenan, na ji daɗi sosai na ganinsa, a lokacin yarinya ce sosai, dan ba zata wuci irin 13 to 14 years ba, hakan ce ta bani kwarin gwiwar naji cewa ina son na aureta, dan na tsamota daga wahalar da take ciki, kuma bata wuce shiga school ba, in takaice maku labari zuwana Niger dai shi ne silar aurena da Maryam, Aunty Aisha da kuma abokan arziki sune suka tsaya mani akan komai, da yake a lokacin ba wani ɗaukar Maryam ɗin da muhimmanci ƴan uwan nata suka yi ba, saboda rashin iyayenta, sai suka bani aurenta ba tare da bincike ko bin diddigin wanene ni ba, na auri Maryam, bayan ganina da ita na farko da wata biyar dai'dai, sannan na dawo da ita Nigeria, na kuma kaita har garin Maiduguri wajen ƴan uwan mahaifinta, dan naji labarin komai a kansa daga bakin Shitu, daga nan muka sake komawa Dubai da zama, ban yi zaman Nigeria sosai ba, mun yi rayuwa cikin tsananin farinciki, na sanya Maryam a makaranta, ta yi karatu sosai, dan tana da kaifin kwakwalwa da basira, kuma nima ina kara koya mata karatu sosai, Aunty Aisha ma tana kara mata wani duk da cewa ita ma tana zuwa ismaliya sosai a lokacin, aurena da Maryam ya ɗauki tsawon lokaci kafin mu sami haihuwa, cikin mu na farko yaron bai zo da rai ba, mun ji tsananin rashin daɗi, amma mun fawwalawa Allah komai, haka muka cigaba da rayuwar farinciki, cikinmu na biyu yana da wata bakwai ta haife shi, shima ɗa namiji ne, ya zo da rai, an saka shi a kwalba kasancewar bakwaini ne, kwanansa uku a duniya ya koma ga mahaliccinmu, munji babu daɗi, saboda mun ɗauki son duniyar nan mun ɗaura mashi, amma ba yadda zamu yi tun da haka Allah ya ƙaddaro mana, a cikin Maryam na uku ma yana da wata uku cikin ya zube, daga nan na fara shiga damuwa sosai a kan hakan, na ce sai dai muje asibiti, ko da muka je ma babu wata matsala, kawai dai Allah ne bai kawo mai tsayuwa ba, haka Aunty Aisha ta rinƙa kwantar mani da hankali, da har na fara tunanin shikenan ni ba zan sami magaji ba, a lokacin fa Hassan na ma ya yi aure, ɗansa Feroz har yana gudu ko'ina, ya girma, ga su Imran ɗin yaya babba duk sun girma, amma ni kuma shiru, abin kullum da shi nake kwana da shi nake tashi, ita ma Maryam tana cikin tsananin damuwa a kan hakan, sai dai bata bari na gane ba, kullum sai ta yi kuka, bata san ina sane da komai ba, damuwar da take shiga ne ma yake kara tsananta mani tawa damuwar, haka na cigaba da ƙoƙarin faranta mata rai ko dan maraicinta, in takaice maku sai da muka sami ciki har sau biyar dukka basu zama, wasu ta haifesu da rai su koma, wasu babu rai, a ciki na shidda ne muka haifi ƴan biyu dukka maza, kuma dukka Allah ya barɓi abinsa, shi na farkon, wato Hassan ɗin satinsa ɗaya a duniya ya rasu, na biyun kuma sai da ya yi wata biyar a tare da mu, sannan Allah ya karɓi abinsa, ni nasan mumini baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, amma wlh wannan jarabawa ta ƴaƴa ya yi matuƙar girgiza mu, badan Aunty Aisha da take tare da mu ba, wlh da mun tabbaka babban kuskure, dan har cewa muka yi zamu sami wata mata mu biyata maƙudan kuɗaɗe, sai a sanya mata kwan haihuwata ta haifa mana yara ko uku ne, Aunty Aisha ce ta tsawatar mana sosai a kan hakan, a lokacin dai na bi umarninta ne kawai matsayinta na babba a kai'na, kuma ko ba komai Aunty Aisha ta nuna mana so da kauna nida Hassan fiye da tunanin kowa a lokacin da muke ƙasar Russia, amma banda haka wlh da a lokacin sam ba zan ɗauki maganarta ba, haka dai muka jure, ina ji ina gani dukka ƴan uwana daga mai yara uku sai mai yara biyu, shi babban yaya har matarsa ta haifi Imran, Akil, da kuma Akila, shi kuma yaya Deen, matarsa ta haifi Irfan, Aafia, and Umaisha har ma matar ta bar gidan a lokacin, ta bar Umaisha tana karama, Hassan matarsa ta haifi Feroz tana da cikin na biya, autanmu Maik dana rena da hannuna ma matarsa tana da ciki a lokaci, abin fa ba ƙaramin ɗaga mani hankali ya yi ba, Maryam da kanta ta ce na kara yin wani auren ko zamu sami ƴaƴan, naki yarda da zancenta, saboda bana son nayi mata kishiya, bana son kowa yazo ya takura mata, ina so ne ta yi rayuwar farinciki, ita kaɗai a cikin gidana, saboda mace ce ta gari, macece ƴar albarka, ta bani farincikin da ban taɓa tunani ba, tana da hankali da nutsuwa, ina tausayawa maraicinta, yanzu kuma ga rashin haihuwa, mun binne yara almost 7, amma shiru, a ƴan tsakanin nan muka sake samun ciki, a lokacin cikin matar Maik bai wani girma sosai ba, dan bai wuce 3 months ba, ita ma matar Hassan haka nata cikin bai fi wata uku ba, shiyasa ƴaƴan namu suka kasance shekarunsu ɗaya, sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login