Showing 252001 words to 255000 words out of 270744 words
rabasu, dama kuma ko Dr William bai yi mashi abin da ya yi mashi a wancan ranar ba, dole a lokacin zai mutu, dan sai kwana ta kare ake mutuwa.
Amma kuma gaskiya in dai haka ne Roshan bai yi masu adalci ba, dan kuwa shi ne nan ya bada Jacob a matsayin magajinsa a kungiyar tsafi, da haka da haka har ya bada ƴaƴansa guda huɗun dukka, ka haifi ƴan huɗu gwanin birgewa, sannan dan tabbatar tsinuwar Allah a kanka ka rasa a me yaran zasu kajeka sai a karagar mulki ta tsafi, kuma sai ka rabar da su dukka? Abin kam ba'a magana, ga can wasu suna neman haihuwa ido rufe, haihuwa abin da ba'a sayarsa da kuɗi, hmmmmm.
"Dad wannan abin fa tsafi ne ya taɓasu, shi ne ya daskarar masu da jini, Mark mu je ka kai'ni gidan Shaikh Sultan". Cewar Lion, ya kai karshen maganar tare da wucewa gaba.
Binsa da kallo kawai suka yi, dan sun san bafa zasu iya dakatar da shi ba, domin Lion ai yama yi kokarin da ya tsaya a iya haka, TRIPLETS nasa sun wuce tunanin mai tunani a cikin zuciyarsa, zai yi fin ninki ba ninkin haka a kansu.
Suna fita gidan shi da Mark tare da shirga shirgar motoci masu numfashi da suka take masu baya, basu zame ko'ina ba sai wajen Sheikh Sultan, suna fita daga gidan kuma ruwan sama tamkar da baƙin kwarya ta fara zuba.
Rimsha na zaune kusa da baby's ɗin Jehan tana aikin kallonsu, sai ta ji kamar alamar saukar ruwan sama, kai ta ɗago tana kallon sama, kamar zata iya ganin saman daga cikin ɗaki.
Shiru ta kasa kunne tana son ta gane wai da gaske ruwa ake yi ne ko kunnenta na jiyo mata karya ne. Ta jima a haka, amma bata iya ganewa ba, dan idan mutun yana daga ta cikin gidan nasu, ko karan ruwan sama ba zai ji ba, sai dai ɗan alama alama.
Hakan yasa ta miƙe da sauri dan ta fito waje ta duba, amma kafin ta tafi, sai da ta bi yaran dukka ta rinƙa manna masu kiss a goshi kamar zata cinye masu goshi, har uwar baby's ɗin ma bata bari ba, sai da ta bita ta sumbata, sannan ta diro kasa daga saman bed ɗin, su gwaggo suna ta aikin bule ɗakin da air freshener masu daɗin kamshi bayan sun kammala tsabtace ko'ina tsab.
Waje ta nufa da sauri. A hanzarce ta sauko kasa, ita sam bata yarda ta bi ta elevator, stair case take bi abinta, da wasu ƴan kafafunta na under 15 years ɗin nan.
Waje harabar gidan ta fito, sai dai ta kasa iya buɗe kofar parlourn nasu har sai da Aseef ya zo wucewa ne ya buɗe mata.
Wani irin siririn murmushi tare da tsantsar farinciki ne ya bayyanar mata a saman face nata, sosai ta ji daɗin ganin wannan ruwan saman.
Babu wani tunani bare ƙoƙarin yanke hukunci kawai ta afka cikin ruwan abinta, bata damu da cewa ya yanayin gidan yake ba, bata san cewa akwai manya manya Cameras da suke harabar gidan ba, domin gidan da president yake a ciki ai ya zama dole a bashi tsaro fiye da kowani gida a duniya.
Duk abin da take yi ana kallonta, sai magana take yi wa ruwan sama, tana wani irin tsantsar farinciki.
"Rimsha wato ba zaki girma ba ko?". Wata zazzaƙar murya ce ta yi mata magana ta bayanta.
Ba tare da ta juya ba ta ce.
"Malika kema ba zaki canza hali bako? Sai mutun yana tsaka da jin daɗi kike zuwa ne?". Ta kai karshen maganar tare da juyowa.
Ido huɗu suka yi da Malikar, sakarwa da juna murmushi suka yi kafin Malikar ta ce. "Ni yanzu ai ba wajenki nazo ba, wajen mummy nazo, munji cewa bata da lafiya, shi ne aka turoni na dubata".
Mamaki ne ya bayyana a saman fuskar Rimshar.
"Mummy kuma? Waye ya ce maki mummy bata da lafiya? Waye ya ce maki mummy ma tana nan? Mummy bata nan, kuma a ina ma kika san Mummyn?".
Nisawa Malikar ta yi kafin ta bata amsa da cewa. "Tun kafin na sanki na san mummy mana, tun kafin a haifeku muke tare da ita, amma ita bata sanni ba".
Guntun murmushi Rimshar ta yi kafin ta ce. "Amma gaskiya kekam Malika kin iya maganar banza, wani wai tun kafin a haifemu kike tare da mun, kalleki fa, tsawona ɗaya dake, amma shi ne kike cewa tun kafun a haifeni kike tare da mummy? Hala lokacin kina jaririya ne? Dan wlh ni dai nasan ko kin fini shekaru to da shekara ɗaya ne, amma kike zancen manya, Allah Malika kin iya tsara magana kamar wata babba".
Da yake Malikar tasan cewa Rimshar yarinya ce, sai bata ɗauki zafi a kan maganganun Rimshar da ta gaya mata ba.
"Amma kema Rimsha kin iya maganar banza fa, wuce nikam ki fita daga cikin ruwan nan kada mura ya kamaki ki kara mana zafi a kan zafi, kuma ga can motocinsu Saif suna kan hanyar dawowa, idan baki fita ba, kin san sauran, sai ya fasa ɗan bakin nan naki".
"Nifa Malika ba zan fita daga cikin ruwan nan ba har sai an ɗauke, kawai jeki abinki, Yah Saif kuma ba zai yi mun komai ba, sai dai ya ɗaure fuska ya ce kada na kara".
Girgiza kai Malikar ta yi tana faɗin. "Amma ai kin ce mashi kin yi alkawari ba zaki sake shiga cikin ruwan ba, ko kin manta ne?".
Kara faɗaɗa murmushin dake a saman face nata ta yi kafin ta ce. "Wannan alkawarin tsoro ne, barazana aka mun na yi shi, dan haka ba zan dai'na ba, ke dai kawai ki tafi abinki".
Ganin motocin su Lion ya danno kai cikin gidan ne yasa Malikar ta ɓace daga kan idanun Rimshar, sai dai bata tafi ba, tana wajen, dan tana jin daɗin ganin diramar Lion da Rimshar.
Ita kuwa Rimshar bata ma san sun shigo cikin gidan ba, dan harabar gidan gari ne guda, parking space yana ta gefe can, bazaka san mutane sun shigo gidan ba idan kana ta gefen shiga ainahin cikin gidan, dan haka da taga Malika ta tafi, sai kawai ta cigaba da sharholiyar tana juyi kamar wata mai tafiyar maciji.
Tana tsaka da juyawa tana rera wakar. Da kai ne zan yi, amma a maimaƙon ta ce da kai ne zan yi wuff, sai dai ta ce da Noorish na zan yi wuff, abin gwanin ban dariya, har yanzu akwai yarinta sosai a kanta.
Bata ankara ba sai ji ta yi ta bugi mutun wanda ko bata ɗago ta kalle shi ba tasan wanene, daga yanayin tsayuwar Lion chest nasa da take kyam har izuwa kamshin perfume nasa, hakan ne yasa ta gane wanene.
A dubu ɗari ta yi baya baya zata faɗi.
In da dai ya saba riƙota idan zata faɗi, wato wuyar rigarta, a yanzu ma nan ya riƙo tare da ɗan daidaita mata tsayuwarta yana kallon face nata.
"Ban hanaki shiga cikin ruwa ba?!" Ya yi maganar tamkar mai jin barci, da alama akwai gajiya sosai a tattare da shi.
Tsuru tsuru ta yi da idanu tana tunanin me yakamata ta ce mashi, dama idan baku manta ba, time da ya hanata shiga ruwan, a cikin zuciyarta ta ce ba zata dai'na ba, ga shi kuwa bata dai'na ɗin ba.
Malika dake laɓe tana kallonsu me zata yi banda dariya, barema da ta ga Rimshar ta yi tsuru tsuru da idanu, abin ba ƙaramin dariya ya bata ba, kamar ba yanzu Rimshar ta gama cika mata baki a kan Lion ɗin ba zai yi mata komai ba.
"Ba dake nake magana ba ne?". Ya sake jefo mata wata tambayar.
Ɗan satar kallon hanyar guduwa izuwa cikin gida ta yi, dan ta samu ta gudu, sai dai kuma ai jikinta akwai ruwa over, tana guduwa zata zame ta faɗi kasa, ya zata yi kenan?. Ta tambayi kanta da kanta.
Kallon gefen ido ya wurgawa Mark dake tsaye a gefensa. Tun bai yi magana ba Mark ɗin ya miƙa mishi jakar Sheikh Sultan ɗin dake a rike a hannunsa tare da sa kai ya wuce abinsa, dama saboda jakar ya tsaya bai wuce ba. Shi kuwa Al Shaikh yana cikin mota ba zai iya fita a cikin ruwan nan ba. Binsu kawai da idanu yake yi babu ko kyaftawa.
Ganin bata da mafita ne yasa ta fara ƙoƙarin magana tana in ina.
"Kayi hakuri na manta ne, kuma na tuba ba zan sake ba ka ji?!". Tana magana kamar da gaske, alhalin karya take yi, gobe ma taga ruwa sake shiga zata yi.
(Wlh Rimsha ƴar dirama ce😂)
Sarai ya sani ba wani mantawa da ta yi, iya shege ne kawai, yasan halinta, ba kasafai ta cika mance abu ba, musamman ma da ya kasance maganarsa ce, ba zata taɓa mancewa ba. Dan haka sai ya kara ɗaure fuska sosai na wuce misali, dan ma ta san yanzu ba da wasa yake yi ba, a kan wannan shiga ruwan zai iya zaneta sosai wlh.
Yana ƙoƙarin yin magana tamkar daga sama ya ji an ambaci sunansa daga bakin kofar shiga parlourn. Ko bai ɗago ba yasan wacece, dan muryarta ita kaɗai ce ba ta biyunta a zuciyarsa.
Kin ɗagowa ya yi su haɗa idanu, sai ma ya yi kamar bai ji ba, dan so yake yi ya hukunta Rimsha.
"Saif ka kyaleta ka zo". Cewar gwaggon dake tsaye a kofar parlourn.
Ita gwaggo tasan amanar da yake a tsakanin Rimsha da ruwan sama, tun suna Dubai haka take, komai sanyin da ake yi sai ta shiga ruwa idan aka yi, yanzu ku duba mani uban sanyin da yake a U.s ɗin nan, amma hakan bai hanata shiga cikin ruwan sama mai uban sanyi ba.
Jin abin da gwaggon ta ce ne yasa ya kama hannun Rimshar kawai suka nufi cikin gida.
Sam ba haka Malika ta so ba, ta so ya bata mari ko guda ɗaya ne, dan Rimsha bata ji, basu son tana shiga cikin ruwan sanyin nan, amma sam bata ji.
A parlourn ƙasa ya saki hannunta tare da wucewa sama, a lokacin shi kuma Mark ya shigar da Sheikh Sultan, dan ya yi mashi amfani da lema ne suka shige ciki.
Shaikh Sultan dattijon arziki dattijon kirki, yana ganin su Areef ya fahimci tsafi ce ta ɗan taɓasu, dan haka sai ya fara aikin zuba masu adduo'i babu kama hannun yaro.
A kusa da su Lion, sir Safwan, and Aseef suka zauna, shi kuma Dr William sai ya fara aikin cirewa uncle Herry bullet ɗin da yake jikinsa.
Gwaggo kuma ta gama aikin Jehan ta zo ta fara aikin duba daddyn Rimsha, dan kafafunsa suna ciwo sosai.
Izuwa yanzu gabaɗaya gidan sun san da cewa su daddyn Rimsha sun dawo, dan haka kan kace me sun cika word room ɗin nan tab.
Ita kuma Hjy Rimsha uwar rigima, da farko da Lion ya barta a parlourn ƙasa ya haura sama, ta so ne ta koma wajen ta ɗan kara shiga cikin ruwan saman, saboda tsabar rashin jin magana, shiyasa Malika ta so Lion ɗin ya bata koda mari ɗaya ne, kila zata rinƙa jin magana.
Amma kuma da ta sami labarin su mummynta sun dawo, ai kuwa da gudu ta haura sama, a gaggauce ta canza kayan jikinta, ta fasa wanka a ruwan saman.
Bayan ta gama canza kayan ne tana ƙoƙarin fitowa waje daga bedroom ɗin nasu, shi kuma Lion yana sako kai, karo suka ɗan yi.
Baya kaɗan ta koma tana faɗin. "Noorish wai su mumnyna sun dawo?".
Hannu ya kai ya tura kofar bedroom ɗin. Yana turata kuma ta rufe kanta, bai ce da ita komai ba ya wuce ya nufi toilet ya barta tsaye a wajen.
Bata damu ba ta nufi hanyar fita, sai dai kuma kofar a rufe, bata iya buɗe kofofin gidan ba, dan dayawansu ma da fingerprint suke aiki, wasu da card, hakan yasa bata iya buɗe kofar ba.
Tamkar zata yi kuka ta koma saman bed ta kwanta tana jiransa ya zo ya buɗe mata ta fita.
Shi kuwa samun tabbacin su Areef zasu iya tashi ko yanzu daga bakin Sheikh Sultan ne ma yasa ya dawo cikin bedroom nasa dan ya yi wanka, Sheikh Sultan ya ce kowani lokaci tsafin zai iya sakinsu, yana sake su kuma zasu koma normal kamar babu abin da ya taɓa taɓasu.
Bayan ya yi wanka, cikin pajamas ya shirya, sannan ya sanar da cewa kada wanda ya dame shi a yau, dan yana da abin yi nasa na kansa.
A saman bed ya iskota, sai latsa mashi waya take yi tana jiransa ya zo ya buɗe mata kofa ta fita.
Kwanciya ya yi tare da kurawa Tv idanu yana kallon kyawawan baby's ɗin Areef, sai ɗaga hannayensu sama suke yi, ga Jehan ɗin kuma sai zuba barci take yi, su gwaggo sun gasa mata jikinta da ruwa mai zafi, sannan suka yi mata alluran barci, dan ta huta.
Ganin yana ta kallon yaran ne yasa Rimshar ta ce. "Noorish mu kuma sai yaushe zamu haifi namu?".
Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya dawo da kallonsa a kanta.
"Ai ina ganin ma yanzu zaki karɓi naki baby's ɗin, ba dai kin shirya ba?". Ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya.
"Wlh Noorish na shirya, ko yanzu ka bani".
"To zo ki karɓa". Ya faɗa tare da jawota jikinsa.
"Noorish iya baby's fa kawai zaka bani, irin na Jehan ko Akila nake so".
Kasa kasa ya ce mata. "Fin haka ma zan baki, mu our baby's special ne". Ya kai karshen maganar tare da haɗe fuskokinsu, cikin salo ya fara aiwatar da abin da yake da niyya.
"Noorish baby fa kawai zaka bani". Ta faɗa a ɗan tsorace.
Katseta ya yi ta hanyar zuwa mata tongue nasa a cikin ɗan bakin nata, hakan yasa ta yi shirun dole ta fara karɓar sako.
Ai yau ma ba shi ya kyaleta ba har sai da ya fanshe kewarta na tsawon watannin nan da ya yi, sannan ya rabu da ita.
Ban da kuka hawaye bibbiyu babu abin da take yi mashi, ta ji a jikinta ne ba karya.
Rarrashi ya hauyi babu kama hannun yaro, sam taki kula shi.
Ganin haka sai ya ce ta yi shiru bari ya je ya yi mata wanka sai suje wajen mummynta.
Jin hakan yasa ta danne ta yi shiru, tana jin raɗaɗin zafi kam, amma a haka ta danne, dan tana son ganin mummynta.
Sumbatar lips nata ya yi yana faɗin. "I really love you my Meesha".
Turo bakin nan ta yi, kamar zata sa kuka ta ce. "Love you too". Ta yi maganar kamar wadda aka saka dole.
Kamar zai sake yin magana, sai kuma ya fasa tare da miƙewa ya ɗauketa sai cikin toilet.
Wanka ya yi mata kamar yadda ya faɗa, sannan ya naɗota a towel ya dawo da ita saman bed, ya koma cikin toilet, dan ya yi nasa wankar, taki yarda su yi a tare ne, har wa yau kunyar yin wanka tare da shi take yi, shiyasa yake fara yi mata kafin ya yi nasa.
Kafin ya fito daga wanka har ta shirya cikin wata abayar, ta haye saman bed ta kwanta, ta yi shiru tana jin raɗaɗin da gabanta yake yi mata.
Har ya fito ya gama shiryawa bata sani ba, ta afka duniyar tunani.
Bayan ya kammala ne ya dawo wajen bed ɗin.
"Let's go". Ya faɗa yana ɗaure dark black curly hairnsa a bayan wuyarsa.
Make mashi kafaɗa ta yi, ta ce sai dai ya ɗauketa cak, dan ita bazata iya tafiya da kafafunta ba.
Bashi da zaɓin da ya wuce ya yi hakan, dan shi ne nan ya ja mata ai. Dan haka sai ya ɗauketa cak suka nufi wajen.
Sai shafa kyakkyawar bakin gashin sajensa take yi tana sumbatar wuyarsa.
Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Zaki fara ko? Ki cigaba, ai ban yi nisa da bedroom ba, sai na juya na mayar dake ciki, dama ni ban ƙoshi ba, kawai ragwantarki yasa na barki".
Ganin sun ɗan yi nisa da part ɗin nasu ne yasa ta ce.
"Allah Noorish ni ba raguwa bace ba".
Cak ya tsaya da tafiyar yana tambayarta. "Are you sure?".
Ganin ya tsaya ne, kuma tasan tsab zai iya juyawa da ita su koma ciki ya bata ajikinta ne yasa ta yi sauri girgiza kai tana faɗin.
"Am not sure, wlh yanzu ma wajen ciwo yake yi mu"
Ta kai karshen maganar kuma tare da saƙalo wuyarsa ta ɓuye fuskarta a wajen wuyar tasa.
Cigaba da tafiya ya yi ba tare da ya sake ce mata komai ba, ƴar rigima kawai.
Bai direta a ko'ina ba sai a cikin room ɗin, a lokacin kuma Allah da ikonsa mum ta farfaɗo, ta kuma dawo normal kamar yadda Sheikh Sultan ya faɗa, shi kuma Areef bai dawo normal ba, yes ya farfaɗo, amma kuma bai dawo dai'dai ba, dan lokaci da ya farfaɗo ya farfaɗo ne da karfi tare da fara yunkurin barin cikin ɗakin, su Uncle T ne suka danne shi, sai fisge fisge yake yi.
Da kyar suka samu suka dannesa ya nutsu Sheikh Sultan ya cigaba da yi mashi addu'a, daga haka barci ta ɗaukesa bawan Allah.
Mummy kuwa, ta dawo dai'dai sai hira da su gwaggo ma take yi, dama tsafin ne ya taɓata, a wajen faɗar tasu ne ma aka samu akasi su Anderson suna ƙoƙarin jefar daddyn Rimsha da abin tsafin, sai ya taɓata ita, shi ne ya kandarar mata da jiki kamar ta mutu.
Amma da yake babu abin da yafi karfin Allah, ayar Allah ba wasa ba, sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji ta dawo dai'dai normal abinta.
Shi kuwa Areef sai washegari suka samu ya dawo dai'dai. Yana dawowa dai'dai kuma Jehan ya fara nema, a nan ne Lion ya gaya mashi tana nan lafiya kuma ta haifa mashi ƴan huɗu jiya, ita ma tun jiyar take ta faman barci kamar me, ta gaji ne over, shiyasa take ta zuba barci kamar ba gobe baiwar Allah.
Mummyn Rimsha baki har kunne, ta ji daɗin samun jikoki QUADRUPLE, sai uban murmushi take yi abinta.
Cikin zumuɗi Areef ɗin ya ce zai je ya kalli Jehan ɗin. Hana shi Lion da sir Safwan suka yi, suna son ya ɗan huta, Lion ya ce da gwaggo a kawo mashi baby's ɗin nan ya kallesu, sai zuwa dare idan ya kara hutawa, sai ya je ya kalli maman babyn.
Haka kuwa