Showing 93001 words to 96000 words out of 270744 words

Chapter 32 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4636

kuma sam bai ji kyamar jinin dake jikin Ayla ɗin ba, ya ɗauketa cak, ya goyata a bayansa, da kyar ta iya ruke wuyarsa, saboda tsananin azabar da take ji. Haka ya riko hannun Heartbeat tasa, sannan ya ce da Dr Salman ma ruke ɗayar hannun Heartbeat, komai zai faru kada su yarda su sake hannun juna.

To suka amsa mashi da shi. Da ɗan ɗaga murya ya ce duk su rufe idanunsu, dan yasan halin AKILA sarai, yanzu idan taga ta in da zasu faɗa, to haukace masu zata yi, ga shi ba damar ya goyata, saboda Ayla tafita bugatar taimako a halin yanzu.

Suna rufe idanunsu, ya jasu da karfi, gabaɗaya suka tafi suka faɗa ta in da Areef ya faɗa. Suna faɗawa bai fi da minti biyu ba, gabaɗaya ginin dake wajen ya ruguje ruguzum.

Suna faɗawa basu sauka a ko'ina ba sai a ainahin cikin fadar Queen da suka kwashe tsawon kwanaki suna ne ma, ashe su suna a sama da fadar ne ma, fadar tata tana a cikin kasa.

Suna dira a tsakiyar fadar, cikin hanzari ya sauke Ayla dan su dubata, su ceci rayuwarta, bai ma lura da cewa a fadar Queen suke ba. Sai bayan ya sauke Ayla ɗin ne ya ɗago kansa da nufin ya ce da Akila ta bashi ɗankwalin kanta.

Yana ɗago idanu suka yi ido huɗu da Lion da yake zaune a saman kujerar mulkin Queen ɗin. A dubu ɗari ya ɗago kan nasa da kyau, dan ya kalli shin abin da yake gani gaskiya ce.

Ba shakka Lion ɗin ne yake zaune kamar yanda ya gani tun farko, gabaɗaya jikinsa duk jini, da alama ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba, ya jingina kansa da jikin head na sofar, sai sauke numfashi yake yi a hankali hankali, yana wani irin nishi, alamar ya gaji over, daga hannunsa, kirjinsa, fuskarsa wajen kumatu, dukka jini ne ya ɓata shi, babu riga a jikinsa, ainahin kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa na cikakkun jaruman maza a bayyane, sai binsu da blue eyes nasa kawai yake yi abinsa.

A dubu Aseef ɗin ya miƙe tsaye yana kallonsa da kyau, a hankali ya fara bin cikin fadar da kallo. Can ya hango ƴar Queen ɗin a ɗaure da sarka, Lion ya yi mata ɗaurin goro, ita kuma Queen ɗin tana kwance flat a tsakiyar fadar, tamkar gawa, ko motsawa bata yi, da alama rai ya yi halinsa ne, ga kuma hannunta ɗaya babu shi, da alama Lion ya sare mata hannu ɗaya ne, alamu sun nuna ba karamar faɗa suka gwabza a tsakaninsu ba, dan kuwa sun ruguje komai na cikin fadar, babu abin da ya rage mai amfani a cikin fadar.

A hanzarce ya nufi Lion ɗin, tsabar a galabaice Lion ɗin yake ya kasa tambayarsa meya kawo shi nan? Ya aka yi kuma ya zo? Ya sha mamakin ganinsa sosai, sai dai ba zai iya yin wani magana ba.

Bai kai ga karisawa wajen Lion ɗin ba, sai ga Areef ya fito daga wata ɗaki dake a cikin fadar, hannunsa na ruke da wasu kyallaye farare guda biyu. Wajen Lion ɗin ya kariso yana faɗin "Saif bari na ɗaure maka hannun nan naka dake zubar da jini da wannan tsummar, sai na ɗaukeka mu fita daga wajen nan, idan ba haka ba, duk zamu mutu, kasan dai gabaɗaya gidan nan rugujewa zai yi ko? Tun da dama mafiya yawan ɓangarorin gidan ba ginasu aka yi ba, da tsafi aka yi su, to yanzu mai tsafin ma ta mutu, kaga suma dole ne su mutu, dan haka ka yi sauri muje". Ya kai karshen maganar yana karisowa kusa da Lion ɗin sosai.

Ɗaga mashi hannu Lion ɗin ya yi, alamar baya da bukatar a ɗaure mashi hannun nasa, ya bar mashi abinsa. Bai yi ja in ja da shi ba, sai ya bar mashi, dan yasan ba zai ce a bar mashi hannunsa jininsa na zuba haka kawai a banza ba.

Da kyar Lion ɗin ya yunkura ya miƙe, wani irin jiri yake kallo, yau tsawon kwanaki bai ci komai ba, sai gwabza yaki yake yi da mukarraban Queen har ya iso gareta, shi ne yasa ya galabaita sosai, kuma ko da ya iso gareta, ba ƙaramin yaki suka yi da ita ba, ta wahala shi ma ya wahala kafin ya samu ya kasheta.

Na san zaku so jin ya akayi hakan ta faru, to ku saurara. Shi Lion already ko da ya shaki kamshin turaren da Queen ɗin ta shaka masu a gidanta, to shi bai suma ba, saboda askar na safe da ya yi, askar na safe idan ka nutsu ka yi shi, Ubangiji ya yi alkawarin Mala'iku ne zasu kula da kai, babu abin cutarwa da zai sameka har izuwa maraice, idan ka yi na maraice, to Mala'ikun zasu sake kulawa da kai har izuwa gobe da asuba, wannan faɗar Allah da manzonsa ne, kuma ya yi karatun Alkur'ani mai girma sosai kafin ya baro gida, sannan ya yi adduo'i ba kaɗan ba, dan yanda yaga Rimsha ta rikice, sai ya ɗauki abin serious, shi kuma Areef da yake bai san ya Daular Mutuwa take ba, tun da Rimsha ba matarsa bace, bai san halinta ba, sai bai ɗauki abin serious ba, bai yi wani addu'a ba, shi dai ya saɓi jaka kawai, ya lodi kaya kamar wanda zai je honey moon da matarsa, to a takaice dai shi Lion ko da ya shaki kamshin turaren, bata yi mashi komai ba, ya kwanta ne shiru kawai tamkar ya suma, dan yana son shigowa cikin Daular Mutuwar ta kowace hali, a tunanin Queen, ita ce ta yi wasa da kwakwalwarsu, ta kuma kafa masu tarko, ta yi nasara suka faɗa, bata san cewa ita ta faɗa tarkon ba, ba ita ta kamasu kamar yadda take tunani ba, Lion ne ya kamata a cikin tarkon nata da ta kafa masu da kanta, wasa da tunaninta sosai ya buga, bata taɓa tunanin hakan zai faru ba.

Lokacin da ta rufe shi a ɗakin duhu, ta kuma daure shi, duk yana jinsu, yana a cikin hayyacinsa, ya yi masu abin da zaki yake yi idan zai farauci abinci ne, kwanciyar ɗaukar rai ya yi masu, abin da basu taɓa zata ba. Waɗan nan sarkokin da suka ɗaure shi dai, already kun san sarkokin tsafi ne, dan haka yana karanta masu Alqur'ani mai girma, duk suka ruguje, suka zama gari, sai dai ya sha bakar wahala sosai kafin ya fita daga cikin ɗakin duhun.

Yana fita kuma bai nemi kowa ba, sai ita Queen ɗin, sam bai nemi ina su Areef suke ba, dan yasan idan ya kamata to tamkar ya gano dukkan in da ƴan uwansa suke ne, saɓanin shi Areef da ya tashi sai ya fara neman Lion ɗin, da yake kowa da irin kaifin kwakwalwarsa da tunaninsa, kuma babba kam ko da minti ɗaya ya fika, to ko yaya babba ne, ya fika, shi ne yasa Lion ɗin ya fisu hangen nesa, dan ya fisu a komai.

Yasha bakar wahala sosai a wajen neman Queen ɗin, ya yi faɗa da mukarrabanta sosai. Tsawon kwanaki yana nemanta, a hanyarsa na neman nata ne ya kashe su barbushi, ya yi nasarar kashesu ne da taimakon Allah.

Haka ya yi ta fama har ya gano in da shegiyar fadar tata take.

Time da ya shigo fadar, babu kowa a ciki sai ita da ƴarta, duk ta tura mukarrabanta domin su kamo mata su Areef, bata san shi ma Lion ɗin ya fito ba, da taimakon sunan Allah ya ɓacewa idanuwan tsafinta, hakan tasa bata ga fitowarsa ba.

Tana ganinsa ta miƙe, da tsafinta ta yi ƙoƙarin damko wuyarsa ta janyo shi, dan ta hallaka shi.

Already kafin ya shigo cikin fadar tata da bismillah ɗauke a bakinsa ya shigo, dan haka sai ta kasa kama shi ɗin, ta yi ta faman gwadawa, amma ina takasa. Shi kuma yana tsaye gam, kamar wani jarumin sadaukin yaki.

Ganin ta kasa saka hannunta a jikinsa ne yasa ta fara ƙoƙarin tura mashi kayan tsafe tsafenta, dan su illatar da shi, to a nan ne aka samu wannan fashe fashen kaya da suka rinƙa yi a cikin fadar, sai da ta fasa komai nata da kanta.

Da ƴarta ta ga haka, sai ta yi ƙoƙarin tayata yakin, shi kuma Lion ya ɗauko wani wuka dake a wajen ajiye wukakensu, wuka ce mai tsananin kaifin gaske, ya yi amfani da ita ya sarewa Queen ɗin hannunta na dama ba tare da ta ankara ba, ya cire mata hannun tun daga sama wajen shoulder ta.

Yana datse hannun nata ya kai hannunsa ya cire zobben dake a jikin babbar yatsarta, wannan zobbe ba komai bane face karfin tsafinta, shi ne karfinta da komai nata, idan babu shi, to ita ba koman komai bace, already dama yasan da irin wannan zobbe, duk wasu cikakkun matsafa suna amfani da wannan zobbe, duk matsafan da basu da shi, to da sauransu, har yanzu basu kai shegu ba, akwai wata kungiyar matsafa da ya taɓa tarwatsawa a New York, suma haka ya datsewa shugabansu hannu, ya ɗauki wannan zobbe ya jefata a cikin wuta, daga nan alkadarin tsafin ta karye.

To ita ma Queen haka ya yi mata, yana cire zobben ya zura a aljihunsa, da ta ga haka, sai ta fara ƙoƙarin yin faɗar hannu da shi da hannu ɗaya, ga bakar azaba tana ji a hannun nata, amma saboda karfin hali, sai bata karaya ba, ta fara faɗa da shi, dan ta kwaci zobben.

Bugu ɗaya ya yi mata a bayan kunne ta wajen wuyarta, daga haka bai kara na biyu ba rai ya yi halinsa, dama kunsan ta tsufa, ta kai shekaru 45 zuwa 50 a duniya, to bugu ɗaya mai lafiya Lion ya yi mata, shikenan ta ce ga duniyarku. Already dama shi Lion kun sani, zaratan maza ma ya suka kare da shi? Da duka ɗaya yake kai mutun in da zai yi danasani har ƙarshen rayuwarsa, bare kuma ita Queen da take mace, macen ma tsohuwa, ai dukansa ɗaya ma ya yi mata yawa.

Ita kuma ƴarta Lion ɗin ya kamata ya ɗaureta, a cewarsa, bai yi tunanin irin hukuncin da yakamata ya yi mata bama tukun nan.

Yana kashe Queen ɗin kuma wasu zaratan maza suka shigo cikin fadar, matasan igbo ne, kyawawa da su majiya karfi, su goma sha biyu cif.
Ganin abin da yake faruwa ne yasa suka fara ƙoƙarin kashe Lion ɗin, to da sune ya yi faɗar nan da suka ji mashi ciwo, jikinsa duk jini, sun ji mashi ciwon ne kuma ta hanyar dogayen faratunan yatsun hannunsu da suke da shi, kun san soft skin nasa kuma, tana da laushi tamkar fatar jariri, ya ji hutu ya ƙoshi, to shi ne idan suka yagushe shi sai wajen ta yi jini, hakan yasa suka sami kalaba ta ji mashi ciwo sosai a jiki. A garin dukansu kuma ya yanke da wuka sosai a hannu, shi ne wajen da Areef ya ce zai ɗaure mashi yaki yarda. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru, abin da yasa gine ginen wajen kuma suke ruguzowa da kansu, saboda already da tsafi aka yi su, to kuma tsafin dake a cikin gidan a halin yanzu ya karye, komai ya lalace, dole gidan ta ruguje.......... To kun ji yadda aka yi, har kullum PRINCESS TEEMA ce taku ta amana mai abin ban mamaki🤙.

STORY.

Cikin wata iriyar kasalalliyar murya, can kasa kasa Lion ɗin ya ce "Areef ka ɗauko Mark mu tafi, ya sami karaya a kafa, he can't walk by himself".

Zaro idanu sosai Areef ɗin ya yi yana faɗin "Lion what are you saying? Mark fa ka ce?".

Jinjina mashi kai kawai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, saboda idan ma ba dan yana da taurin zuciya ba, Allah ko mikewa ba zai iya yi ba, dan tsananin yunwa, kuma dama already kun san shi baya da jumuriyar yunwa sosai, Areef ya fishi jure yunwa, amma shi da Aseef, sam basu shiri da zancen yunwa sam sam, sai dai kuma, basu cin abinci dayawa, idan sun ci kaɗan Alhamdulillah sun ƙoshi.

"I think Mark he already dead?". Ya faɗa fuskarsa ɗauke da mamaki ƙarara a bayyane.

Ko sannu Lion ɗin bai sake ce masu ba.

"Where is he?". Cewar Areef ɗin. Da kyar Lion ɗin ya iya nuna mashi wata hanya da take a cikin fadar.

Da sauri ya nufi hanyar, shi kuma Lion ɗin ya fara takowa a hankali yana nufo su Aseef.

Ganin yanda yake tafiya da kyar da kyar ne yasa Aseef ɗin ya kariso wajensa da sauri. Yana zuwa ya taimaka mashi suka karisa wajen da su Dr Salman suke tsaye.

Ayla baiwar Allah azaba tasa ta sume, har lokacin kuma jini take zubarwa. Kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mata ya kawar da kansa gefe guda, wani iri yake ji a cikin zuciyarsa, ga tunanin Meeshansa, ga bakincikin da yake ciki na cewar Aseef ba ɗan uwansu bane, ga bakin cikin abin da su Josephine suka yi masu na cin amanar mahaifinsu, sannan suka ci amanarsu suma, abubuwa sun taru sun yi mashi yawa a cikin zuciyarsa, ba dan yana da dakiya da juriya ba, da ya jima da faɗuwa kasa, da makiya sun yi galaba a kansa, sai dai ya rigasu ya ce Allah, dan haka Allah yake dafa mashi a koda yaushe, hakan tasa a kullum sai dai ya kara tsayuwa da kafafunsa gam, ba dai ya je kasa ba.

Areef ne ya fito daga wannan ƴar siririyar hanyar ɗauke da Mark ɗin a saman kafaɗarsa, baya ko motsi, da alama a sume yake.

A kusa da Dr Salman ya kwantar da Mark ɗin yana faɗin "Ina sauran sojojin kuma?". "The already dead, remain 2". Lion ɗin ya bashi amsa a takaice tare da wucewa ya nufi kofar fita daga fadar, dan fadar dab take da ta ruguje.

Sake ɗaukar Mark ɗin Areef ɗin ya yi, shi kuma Aseef ya ɗauki Ayla dake sume gwanin ban tausayi, duk sun jigata na kin karawa, duk wanda ya gansu a wannan hali, babu shakka sai ya tausaya masu, yau Lion da kansa da kyar yake tafiya, ko daga nan kun san bala'in Daular Mutuwa ta wuce tunanin mai tunani.

Sun ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kafin su kai wata kofa dake fuskantar gabas. A tab bakin kofar Lion ya tsaya ba tare da ya buɗeta ba. Sai kuma ya duƙa kasa a wajen, a hankali ya buɗe wata kofar kasa dake a wajen, sannan ya miƙe tsaye. In a cool voice ya ce masu su zo su shiga, nan ne kawai kofar da ta rage ta fita a gidan, duk saura sun ruguje, su yi sauri dan in da suke ɗin ma, dab yake da rugujewa, abu kaɗan ya rage.

Da sauri suka karisa wajen, ɗaya bayan ɗaya suka shi ga. Lion ɗin ne ya sake ce da Areef ya koma ya ɗauko sojoji biyu da suka saura da ransu.

A tare suka koma da Aseef, bayan Aseef ɗin ya sauke Ayla a cikin wannan hanyar kenan.

Da sauri suka ɗauko su. Suna fita daga cikin fadar ginin ta ruguzo a kan ƴar Queen ɗin da ita kanta Queen ɗin.

Daga in da suke suna jiyo sautin ihun ƴar Queen ɗin, amma babu wanda ma ya ji cewa tamkar mutunce take ihun neman taimako, ga shi ba halin ta gudu, dan Lion ya ɗaureta, haka gini ya ruguzo a kanta, da haka ta mutu. Sai dai fa sun sha ruwan mamakin jin ihun mutane sosai a lokacin da ginin yake rugujewa, hakan na nufin da akwai sauran mutane a cikin gidan, Allah sarkin ginin nata rugujewa a kansu, dan kofofin ɗakunan duk a rufe suke, ba halin su gudu, sai dai wasu daga cikinsu, sun samu sun iya buɗe kofar sun gudu, sun nufi sauran ɓangarori na cikin gidan, fatan mu dai Allah yasa su sami hanyar fita, suma su tsira, ko ina Mustapha da Kausar?.

Bayan sun shiga cikin wannan hanyar dukkansu, Lion ne na karshe da ya shiga, sai da ya tabbatar dukkansu sun shiga, bayan ya shiga, sai ya janyo kofar ya rufe.

Bayan ya Rufe ne ya tsaya ya tsare Aseef da dara daran idanuwan nan nasa. Ƴan kame kame Aseef ɗin ya fara yi, dan wlh idanun Lion mugun rikita mutun suke yi, musamman idan ya tsareka da su ba tare da ya yi magana ba, duk sai ka ji ka tsargu, ko da kuwa baka yi laifi ba, sai yasa ka rasa nutsuwarka, haka shi ma Aseef ɗin ya yi, duk sai ya rasa nutsuwarsa, ya kama ƴan kame kame kamar wani tsohon munafuki.

Ko sannu Lion ɗin bai ce mashi ba, ya sa kai ya nufi wajen da Ayla take kwance, ɗan duƙawa ya yi a kusa da ita, a hankali ya kai hannunsa ya saɓeta a saman kafaɗarsa, sannan ya ruke hannun Dr Salman da hannunsa ɗaya, bai ce da kowa komai ba ya kama hanyar fita.

Ganin haka yasa Aseef ya ɗauki soja guda ɗaya, shi kuma Areef ya ɗauki Mark, suka bar soja ɗaya a wajen. Kasancewar tafiyar Lion yana da sauri, hakan yasa ya yi masu nisa sosai. Can saman wani dutse ya kwantar da Aylar, sannan ya juyo ya dawo dan ya ɗauki sojansa ɗayan da yake a bakin kofar shiga hanyar. Duk sojojin suna a sume, kuma babu ruwan da za'a zuba masu su farfaɗo. Duk da ciwon da yake jikinsa, da wahalar da yasha, hakan bai sa ya ji cewa zai iya barin wannan sojan nasa a wajen ba, saboda amana da kuma sanin darajar rai irin nasa. Har cikin ransa yana jin zafin jikinsa, amma haka ya ciza laɓɓansa gam ya saɓi sojan nan a saman shoulder ɗinsa.

A hanya bai kai ga karisawa wajen da ya kwantar da Aylar ba, ya ci karo da Areef, karɓa mashi sojan Areef ɗin ya yi, ba musu ya miƙa mashi sojan suka cigaba da tafiya.

A takaice a haka sai da suka yi tafiyar kwana ɗaya da wuni ɗaya cur a cikin wannan hanyar, ba dan Allah ba, da ba zasu taɓa kai labari ba, sun sha wahalar da ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar ko makamancin irin hakan ta faru da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login