Showing 96001 words to 99000 words out of 270744 words
shi ba.
Da yake hanyar yana da faɗi, kuma yana da reshuna, ma'ana hanyar ta rabu kashi kashi. Kun tuna hanyar da su Rimsha suka bi suka fita? To ɗaya ne daga cikin reshen wannan hanyar, ta kasu ne kashi kashi, to suma haka suka cigaba da tafiya a cikin wannan dutse, har Allah yasa suka fita.
A wajen fita ma ba karamar gwagwarmaya suka sha ba, dan an rasa wanda zai iya jijjige masu kofar ya buɗeta su fita, duk sun galabaita fiye da tunanin mai tunani, shi kansa Aseef ɗan dirama, yanzu ya yi laushi, bare Heartbeat nasa da Dr Salman, ai ba'a magana bayin Allah.
Daga karshe dai Lion ɗin ne ya daure ya cije ya buge masu kofar tare da taimakon Aseef, shi kam AREEF ya zama tamkar Aseef a baya yau, ya yi laushi over, ga bala'i yunwa.
Suna buge kofar wani irin hasken rana ne ya haske masu idanu, dukkansu sai da suka datse idanuwansu, kafin daga baya su sake buɗewa a hankali.
Lion ne ya fara sako kafafunsa waje, dan shi ne babba, shi ne yakamata ya fara fita, dan yaga ya yanayin hanyar take. Kungurmin dajin nan ne da su Rimsha suka fita ta wajen, sai dai su Rimsha ta baya suka fito, su kuma ta gaba suka fito, dama kunsan hanyar tana da reshuna.
Ganin wannan dajin ne yasa ya ce su fito kawai su tafi, zasu cinma gari a gaba ai. Wahalar dai su fita gari ne, suna fita gari koma ina ne komai zai saukaka masu, dan su ko'ina suka je, to dole masu ruke da mulkin garin su tarbesu hannu bibbiyu, dan ko a kasar America da kanta moryiyinsu tana da matuƙar kaifi fiye da tunanin mai tunani, ga shi kuma su taurari ne na faɗin Washington DC da kewayenta, ta ko'ina ana ji da su fiye da tunanin mai tunani, so wahalar ta dai a yanzu su fita gari ne.
Cigaba da tafiya suka yi ta yamma maso arewa, bama su iya gane gabas ba bare yamma, su dai in da ya fi yi masu, in da suke ganin zai fi masu sauki, nan suka bi.
Da yake rani ya shigo, damuna ta tafi, sai ya zamana ƴaƴan itatuwan dake a dajin sun fara ƙarewa, haka dai suka cigaba da tafiya.
Sun yi tafiya mai nisa sosai daga in da suka fito, sannan ne Lion ya zauna a kasar wata bishiyar mangoro mai matukar girma, kusan kamar bishiyar kuka. Abin mamaki a kasar wannan bishiyar su Rimsha suka fara zama time da suka fito, dan hanyar da su Lion ɗin suka biyo, ya zo ya haɗu da hanyar da su Rimsha suka biyo, dan idan baku manta ba, ta yamma su Lion ɗin suka juya suka bi, hankan ce ta mayar da su ta wancan hanyar.
Dukkansu zama suka zo suka yi a kusa da Lion ɗin, sauke Mark Areef ya yi, sannan ya shiga cikin dajin, dan ya nemo ruwa, su samu su yayyafawa sojojin nan su faffaɗo, idan suka farfaɗo, komai zai zo masu da sauki, zasu rage wahala ta ɗaukarsu.
Jingina kansa da jikin itacen Lion ɗin ya yi, a hankali ya lumshe idanuwansa, wani barcin wahala ce ta ɗan ɗaukesa a wajen, ita ma Akila kwanciya ta yi a kasar, tare da tada kai da laps na Heartbeat nata, tana kwanciya sai barci, shi ma Dr Salman kwanciya ya yi, ya yi barci bawan Allah, ita Ayla, dama already a sume take.
Kafin Areef ya dawo, duk sun yi barci, ya ɗebo ruwa a cikin wata gora da ya gani a wajen, sai a lokacin ya tuna da jakarsa da ya barota a fadar Queen, har ruwa da akwai a cikin jakar. Ajiye ruwan ya yi, sannan ya zauna dan ya mike kafafunsa ya ɗan huta, shi ma ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
After some hours.
Can cikin barci Lion ya ji motsi a kusa da su, duk da ya san suna da yawa a wajen, amma wannan ba motsin mutun bane, mutsin wata dabba ce, kunsan shi dama already bashi da nauyin barci, dan haka sai ya farka. A hankali ya buɗe idanuwansa. Wata zabgegiyar kunama ce a kusa da Aseef dake jingine da jikin itacen yana barci shi ma, ga Heartbeat ta yi barci a saman cinyarsa, shi Lion already dama ya saba da irin wajen nan, wanda ya fi haka haɗari ma sun zauna a ciki kafin ya taka matsayin da yake a kai yanzu, ai dama soja bai kamata ya ji tsoro ko kuma ace waje irin wannan ta zamar mashi bakuwar waje ba, musamman ma sojoji irinsu na Usa.
Dan haka sai ya kai hannunsa ya kama kunamar, tana ƙoƙarin kai mashi harbi, ya yi maza ya damki karin nata, da karfi ya tsige daga jikinta ya gefar gefe guda. Yana gefarwa sai ya ji wani motsi daga ɗan nesa da su, alamar tafiyar mutane ne. Lumshe idanuwansa ya yi yana mamaki mutane kuma a wannan dajin?.
Bai buɗe idanu ba har sai da ya ji isowar mutanen kansu. A hankali ya waro idanuwansa a kansu. Mutanene sun kai su 10, kaɗan ne daga cikin mutanen da su Areef suka taimaka a cikin Daular Mutuwar, su ne waɗan da Aseef ya buɗewa kofa suka fita.
Sannu suka yi wa Lion ɗin cikin harshen yarabanci. Mayar da idanuwansa ya yi ya lumshe, a cewarsa basu ishe shi kallo ba, ba zai ɓata idanuwansa wajen ganinsu ba.
Wata daga cikinsu ne ta yi magana cikin harshen turanci, a in da ta ce "Laaa kuga abin mamaki, ga shi yana zaune a wajen, ga kuma zanen face nasa a jikin itacen da yake zaune ɗin! Ko dai shi ne ya zana? Amma kuma kamar zanen ya jima!".
Jin sun ambaci sunan zane ne yasa ya waro idanuwansa, dan shi dai yasan Meeshansa ce kawai ta iya zana shi, kuma ba shakka ya ga tulin zanensa da ta yi a cikin Daular Mutuwar, a hanyarsa ta zuwa neman Queen, a lokacin ya ci karo da wani ɗaki, yana shiga ya tatda zanen face nasa da yawa a ciki, duk tabi jikin bango ta zana, wannan ɗakin kuma ba ko'ina bane face ɗakin da Rimshar ta zauna, idan baku manta ba dama ta yi zanensa sosai a wajen.
A hankali ya juyar da kallonsa izuwa kan in da matar take nunawa, dan ya kalli zanen da idanunsa. Bai yi mamaki ba, kuma da kallo ɗaya ya yi wa zanen ya gane tabbas zanen Rimsha ce, saboda zanenta baya ɓuya mashi, tana barin alama guda ɗaya a jikin zanenta idan ta yi, wannan alama kuma ba komai bane face a duk in da ta zana face nasa, to sai ta zana mashi lips nata a saman kumatunsa, alamar ta yi kissing na zanen, so a dukka zanensa da ta yi a rayuwarta, da akwai wannan alamar ta kiss ɗin.
Mai da idanuwansa ya yi ya lumshe yana tunani yanzu duk irin wannan wahala ta wannan hanya haka Meeshansa ta biyo? Yanzu haka ta keta wannan kungurmin daji haka? A gaskiya Queen ta cuce shi dayawa, ta wahalar mashi da pleasurensa, dole Rimsha ta ce ba zata dawo Daular Mutuwa ba, ashe azaba ta sha na kin karawa baiwar Allah, ya zama dole idan ya koma gida ya kula da ita sosai.......
Yana tsaka da tunanin ne mutanen suka katse mashi tunanin da cewa sun zo su taimaka masu ne, da akwai abinci da ruwan sha a masaukinsu, su zo suje sai su ci.................Lallai rashin sani yafi dare duhu, basu san wanenen Lion ba, da sam bama za su zo in da yake ba bare suce ya zo ya ci abincinsu da suka girka da ita ce duk hayaki, abincin ma a dajin suka samo shi, sai Allah ne yasan menene ma, sai kuma su da suka girka, to shi Lion da ma bai iya cin abincin Nigeria ba! Ai ko sau ɗaya bai taɓa gwada cin abincin Naija ba, bai iya ba, baya ma son kamshinta, ina da tabbacin ko yunwa zata kashe shi ba ci zai yi ba, komai haɗin da za'ayi wa abincin Naija da wuya ya iya ɗanɗanawa, abinci mai rai da lafiya wadda ta amsa sunanta abinci ma kenan, ina ga kuma wannan abincin nasu na ƴan gudun hijira? Ai ko kallo ma ba zai yi ba bare ci, zai ce datti ce, kuma kun san shi da bala'in kyankyani, ai idan ya gani da ido ma, ya rinƙa sheka masu amai kenan har sai abin da hali ya yi kuma.
Ko kallon in da suke bai sake yi ba, tamkar ma babu shi a wajen, da suka ga bai amsa ba, sai suka yi tunanin bai ji su bane, sai suka sake yi mashi magana. Wani irin tsawa ya daka masu na su tashi su bashi waje, dan sun ishe shi. Bayin Allah har wani firgita suka yi, su da suka zo taimako, dama sun ga cewa Areef da Aseef sun taimaka masu ne, shi ne suma suna ganin a yanzu sun sami dama, bari suma su taimaka masu, basu san waɗan nan ba'ayi masu goninta ba, ai TRIPLETS barsu kawai a yanda ka gansu, dan sun wuce tunaninka, sai kana tunanin yau zaka gansu a fari, sai ka gansu a ja, haka suke, baka gane ina suka dosa, sam su ba'a yi masu goninta, kuma ba'a burgesu, idan ba yanzu ma da suka sami mata bane abin ya ragu, da a baya ne ai ba'a ma magana.
Tsawar nan da ya daka masu ne yasa su Areef suka farka daga barcin da suke yi. Kallon sama da kasa Areef ya watsawa mutanen, a lokacin kuma already sun juya zasu koma wajensu.
Miƙewa ya yi ya ɗauko robar ruwan da ya ajiye, a gaban sojojin ya dawo ya tsugunna, a hannunsa ya tarbo ruwan tare da fara yayyafa masu a face nasu.
Kusan a tare bayin Allah suka farka, ganin sun farka ne yasa ya ajiye ragowar ruwan, ya koma kusa da Ayla dake kwance bata ko motsi.
Shiru ya ɗan yi yana tunanin, shin ya dubata ne? Ko dai ya barta kawai sai sun isa gida? Dan ko ya ce zai dubata ma, sam babu kayan aiki, babu komai a tattare da su, ga shi kuma cikin jikinta ne ya fita, aiki take bukata na musamman. Daurewa dai ya yi ya kyaleta ba dan ya so ba, bawan Allah yana da tausayi sosai.
Mikewa Lion ya yi ya nufi cikin dajin, dan ya duba ya wajen yake, bayan ya karɓi Jacket ɗin dake jikin Aseef. Shi kuma Areef ya fara ƙoƙarin tattare kansu, dan su tafi, ya yayyafawa Mark ma ruwa, bayan ya farfaɗo, sai ya saɓesa a saman kafaɗarsa, kasancewar ya sami karaya a kafar tasa, da haka suka mike suka fara tafiya, Lion kuma ya shige cikin daji, Areef ya ce su je Lion ɗin zai samesu a gaba ai, ya san halinsa sarai, ga sauri a wajen tafiya, zai yi saurin cin masu.
Haka suka cigaba da tafiya, Lion bai sake haɗuwa da su ba har sai da rana ta kusa faɗuwa, a can gaba da nisa sosai ya cin masu, ya wanke jikin dake jikinsa, ya wanke face nasa sosai, ya yi salloli dake a kansa da sauran abubuwa, ya saki dark black cuirly hair nan nasa, ga shin ma yanzu ta kara tsawo sosai, ya jima bai rage tsawonta ba.
Ya sha ruwan mamaki yanda ya rinƙa ganin zanen face nasa a wannan daji, abin ya yi matuƙar burge shi, wani irin azababben kaunar Meeshantasa ya kara ji a ransa, burinsa kawai ya je gida ya ganta, yana tsananin kewarta, ji yake yi kamar a kan kaya yake da bata nan a kusa da shi, baiwar Allah, duk ta bi ta zane face nasa abinta, ba shi kaɗai ya yi mamaki ba, har da sauran abokan tafiyar tasa, kowa ya yi matuƙar mamaki na ganin zanensa a jikin itatuwan dake a dajin, ga zanen ya fito ɓaro ɓaro gwanin birgewa, kamar ka kira shi ya amsa, sai dai babu wanda ya yi gigin yi mashi magana a kan zanen, ko Areef bai yi mashi maganar ba, dan bai ga fuska ba, ya bari sai sun je gida, idan suka huta zai yi mashi tsiya a kan zanukan, sojojinsa sai kallon zanen suke yi suna satar kallonsa, Meesha ta ja mashi, Allah ma yasa sojojin kwara biyu ne kawai suka gani, sai Mark wanda already ya san komai.
A haka suka kwashe kwanaki suna tafiya a cikin wannan dajin, banda ƴaƴan itatuwa babu wani abin da suke ci. Da kyar suka iya kaiwa cikin wani ɗan ƙaramin kauye dake kusa da dajin.
Tun da suka sako kafafuwansu a cikin wannan kauye, kowa dake cikin kauyen ya zuba masu idanu, sai kallonsu suke yi tamkar sun ga bakin halittu daga wata duniya ta daban, su kuwa ko kallon mutanen kauyen basu yi ba, suka cigaba da tafiya a galabaice.
Duk cikinsu babu mai ko raina biyar, haka suka cigaba da tafiya har suka fito cikin babban gari. Kai tsaye shagon sai da wayoyi Lion ya fara nufa, dan already dama basu zo da wayoyinsu ba, sun barosu kashe a gida. Sai ya ce su Areef ɗin zauna su jirasa, kada su bisa wahalar zata yi yawa, bari shi ya je, daga baya zai zo ya ɗaukesu.
Abin hawa ya tara, wato mai mashi, ya hau ya ce da mai mashin ɗin ya kai shi katafaren shop na sai da wayoyi, su kuma suka zauna a wajen wani babban masallacin suna jiransa.
Sun yi tafiya mai nisa kafin su kai challenge, wani kasuwar waya ce a cikin Ilorin state ɗin.
A tare da mai mashin ɗin suka shiga cikin wani katafaren shagon sai da wayoyi. Kun san yarabawa da shegen son kyawawan kuma fararen mutane, sai kallon shi suke yi kamar zasu cinye shi, haushi tamkar ya kwakwale masu idanu yake ji, dan ya tsani kallon nan da suke yi mashi. Amma ba yadda zai yi, dole ya yi abin da yake a gabansa kawai.
Yana zuwa ya zaɓi irin wayar da yake da bukata, sannan ya tambayi mai shagon suna karɓar transfer? E guy ɗin ya amsa mashi, da yake katafaren shago ne, akwai yaran gida dayawa a ciki, idan ka zo sayan abu, to za'a sami ɗaya daga cikin yaran shagon ya kula da kai, ainahin Managernsu kuma yana zaune a ciki, gabansa da tarin computers.
Tambayarsa Lion ɗin ya yi a kan zai tura masu 2 million Naira, sai su ɗauki kuɗin wayarsu, su bashi sauran kuɗin, sun yarda za su karɓar?. Kasancewar babban shop ne, akwai kuɗi sosai a ciki, sai Manager ya ce ba damuwa ya tura kuɗin. Kum san eƴamurai da bala'in son kuɗi, da kuma daraja costumers, sun iya business over, to shagon na eƴamuri ne bana yarabawa ba, shiyasa suka yarda cikin aminci.
Shi ma Lion ɗin cikin mutunci ya ce da guy ɗin da ya yi attending ɗin nasa, ya ɗan ara mashi wayarsa na minti biyar bari ya yi kira. Kun sansu akwai daraja costumers, dan haka ba musu guy ɗin ya ara mashi wayar.
Karɓa ya yi, number Imran ya saka ya kira, dan ya haddace number a kansa, sama da shekarun 8 suna a tare da Imran ɗin, kunga kuwa dole ya haddace numbersa, bare ma shi da yake da kaifin kwakwalwa sosai, duk wata number da take a wayarsa idan ka tambayesa zai zayyano maka ita.
Bugu ɗaya Imran ɗin ya ɗauka, a tsananin kasale ya ce da Imran ɗin zai turo mashi wata account number ya saka mashi 2m a ciki yanzu.
Jin muryarsa yasa Imran ɗin bai san time ɗin da ya miƙe tsaye zubur ba, a hanzarce ya fara tambayarsa suna lafiya? A ina suke yanzu? Kuma yaushe za su dawo?. Cikin ƙaguwa ya rinƙa jefo mashi tambayoyi.
Kasancewar a galabaice over yake, sai kawai ya katse kiran, dan ba zai iya biyewa Imran ɗin ya tsaya amsa mashi tambayoyin ba.
Yana katse kiran ya ce da guy ɗin ya bashi account number shop ɗin nasu. A hanzarce ya kira mashi, ya yi typing ya turawa Imran ɗin.
Ko minti biyu ba'ayi ba sai ga kuɗin Imran ɗin ya turo. A takaice haka suka gama ya biyasu kuɗin wayar ya karɓi saura chanjinsa, daga nan ya tambayi mai mashin ɗin ina hotel nasu mai tsananin kyau take.
Mai mashin da kuɗi yake so, sai ya ce su je ya kai shi, ba ɓata lokaci suka nufi hotel ɗin.
Katafaren hotel ne mai matukar kyau da kawatuwa, sai da suka tsaya a hanya ya sayi kayan sakawa a wani katafaren super market, sannan suka karisa hotel ɗin. Duk rana ɗaya ra'ina dubu ɗari biyu za su biya kowani ɗaki ɗaya. Ɗaki biyar ya kama masu, 1 million a rana kenan, Imran ya sake kira da number ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen, sannan ya saka shi ya tura masu kuɗin ɗakunan.
Daga nan ya karɓi keyas dan ya shiga ciki, mai mashin ɗin zai tafi, sai ya ce a'a ya jira shi bari ya zo zasu koma wajen da su Areef suke a tare, daga nan sai ya sallame shi. Okey mai mashin ɗin ya amsa mashi. Sama wajen ɗakunan da ya kama ya nufa, ɗaki ɗaya ya zaɓa ya buɗe ya shiga.
Ɗaki ne aljannar duniya, tamkar ɗakinsa na gidan nasa na Kaduna, haka ɗakin take, sai tashin kamshi air freshener mai daɗi take yi, komai very clear. Wayar da ya saya ya sanya a charji kasancewar da akwai wutar nepa, yana so ya yi charjinta dan ya saka sim card ya kira his excellence a turo masu jirgi su bar garin nan.
A hanzarce ya yi wanka, sannan ya shirya sosai cikin ƴan mintocin da basu fi 30 ba, ya fito suka tafi da mai mashin ɗin, dan ya je ya taho da su Areef. A hanya sai da ya tsaya ya saya masu ruwar roba mai bala'in sanyi da yawa, dan yasan suna jin kishin ruwa. Ganin yanda yake pacaka da kuɗi ba karamin mamaki ya bawa mai mashin ɗin ba, kasancewar shi ba wani sanin kan kuɗin Naija ya yi ba, ida zai sayi abu, ɗibar kuɗin kawai yake yi ya basu, ko sun bashi canji kuma