Showing 99001 words to 102000 words out of 270744 words

Chapter 34 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2974

baya karɓa, ko kallon canjin ma baya yi, hakan ce ta yi mugu mugun bawa mai mashin ɗin mamaki, duk da ya gan shi Bature jajir da shi, amma dole ya sha mamaki, dan akwai Turawa mazauna Nigeria sosai, so a tunaninsa irinsu ne, bai san Lion kam wannan karon ce zuwansa Naija ta farko ba, sai kuma ya haɗu da jarabawa, in ba haka ba ai before bai ma san Naija ba, bare kuma ya san ya take ko ya kuɗinta yake da sauransu! Shi ne yasa yake kashe kuɗin tamkar bai san ta yaya ake nemosu ba.

Kai tsaye wajensu Aseef ɗin mai mashin ɗin ya mayar da shi, shi kansa mai mashin ɗin sai satar kallonsa ta cikin mirror gaban mashin ɗin yake yi, saboda ba karya Lion fa duk wanda ya gan shi, in ma mace ko na miji, to sai ya saki baki ya yi ta kallon shi babu gajiyawa, saboda tsananin kyan da Allah ya yi mashi! Ga uban farinjini da kwarjini, bugu da kari ga waɗan nan dara daran idanuwan nasa masu rikitar da mutun idan ya kallesu.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E17


Date: 27/4/2024





Kamar yanda ya baro su Areef ɗin, haka ya dawo ya samesu. Ruwan ya fara basu, a hanzarce suka karɓa, Areef shi kaɗai sai da ya shanye roba biyu na ruwan, sannan ya kama mayar da numfashi, shi ma Aseef roba biyu ya sha, Akila rabin roba, Dr Salman ya shanye sauran rabin nata, sojojin Lion guda biyun nan kowannansu sai da ya sha roba ɗaya da rabi rabi, shi ma Mark roba biyu ya sha.

Daga haka Lion ya ce su tashi su karisa hotel ɗin, daga nan su yi wanka su huta kafin ya kira His excellence. Ya kai karshen maganarsa tare da juyawa ya hau bayan mashin ɗin da suka zo, sanna ya ce da mai mashin ɗin ya tara masu taxi su hau, ba musu ya tara masu taxi guda biyu, da yake a bakin babban hanya suke, sai aka yi saurin samun taxi ɗin. Rayuwa kenan, ba ta yanda bata juyawa mutun, wai yau TRIPLETS ne da shiga taxi? Idan ba ƙaddara ba, babu abin da zai kawo su Naija ma da kanta bare har wata Ilorin state, amma da yake kana naka Allah na nashi, sai ga su har ma Daular Mutuwa ba iya Naija kawai ba.

Haka suka shiga taxi ɗin, Mark da sojojin nan taxi ɗaya, Areef da Akila da Ayla suka shiga ɗayar taxi ɗin a gidan baya, Aseef kuma ya shiga gidan gaba na taxi ɗin su Areef, Dr Salman ya shiga gidan gaba na taxi ɗin su Mark, haka suka kama hanya.

Gaba mai mashin ɗin Lion ya yi, masu taxi ɗin suka rufa mashi baya, bayan su Areef ɗin sun gama shiga kenan, har lokacin Areef ne yake ruke da Ayla baiwar Allah, ko motsawa bata yi ba har izuwa yanzu, ba dan zuciyarta na bugawa ba, to da sai ma su ce rai ya yi halinsa.

Suna isa hotel ɗin Lion ya ɗebo makudan kuɗaɗe da a kallah za su kai 200k, ya bawa mai mashin ɗin nasa, shi fa bai san nawa ya bawa mai mashin ɗin ba, dan ko da ya bashi ma sai da ya tambaye shi ya isa haka? Ya biya shi hakkinsa ko dai sai ya kara mashi?. Bawan Allah bai san kan kuɗin Naija ba, mai mashin ɗin da yake yana da tsoron Allah, sai ya ce "Sir this money is too much, is pass my, I think this money pass 200k, my own money is only 5k, so I will going to carry my own and return the remaining change to you". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin cire 5k nasa.

A takaice Lion ɗin ya ce mashi kada ya damu, ya tafi kawai, dan shi bai ma san 5k a kuɗin Nigeria ya take ba, da ma dai dollars ce, ya santa a ido, ya santa a baki dukka.

Kun san yarabawa da iya zuba godiya, ai kuwa wannan mai mashin ɗin yana jin Lion ya ce ya bashi kuɗin, a dubu ɗari ya diro kasa daga saman bashin ɗin nasa, cikin hanzari ya zube gwiwowinsa a kasa a gaban Lion ɗin, nan take ya fara zuba ruwan godiya, adduo'i, tare da zallar ruwan albarka da fatan alkhairi.

Ko sannu Lion ɗin bai sake ce mashi ba, ya wuce ya je ya bawa masu taxi ma makudan kuɗaɗe da a kallah za su kai 100k ke. Haka suma suka fito daga cikin taxi ɗin tare da zube gwiwowinsu a kasa, suka hau engine zuba godiya.

Sam bai kula su ba, bai ma bi ta kansu ba ya sa kai ya wuce cikin hotel ɗin, Areef ya ɗauko Mark ya rufa mashi baya, shi kuma Aseef yana ɗauke da Ayla, haka suka shige ciki, suka bar masu taxi zube a saman gwiwowinsu suna zuba godiya.

Suna shiga Lion ya wuce bedroom nasa abinsa. Da Ayla da Akila bedroom ɗaya, Aseef da Areef bedroom ɗaya, Dr Salman shi kaɗai, su kuma sojoji da Mark nasu ɗaya. Haka suka kasa ɗakunan nasu, amma fa sun sha gwagwarmaya wajen diramar Aseef, dan ya ce babu mai raba shi da Heartbeat nasa, a tare za su kwana, Areef kuma saboda mugunta, saboda shi matarsa bata kusa, sai ya kafe a kan lallai Akila da Ayla za'a barta, dan ciwon ƴa mace ta ƴa macece, dan haka Akila zata kuka da Ayla. Kuka sosai Aseef ɗin ya rinƙa zuba masu, amma suka ki kula shi. Daga karshe dai sai ya hakura ya wuce bedroom nasu shi da Areef ɗin.

Lion yana shiga cikin bedroom nasa, wanka ya sake yi, saboda tsananin zafi da rana da ake narkawa. Bayan ya shirya cikin ɗaya daga cikin kayan da ya saya, sai ya ɗebi baya kala biyu ya kaiwa su Aseef ɗakinsu, sannan ya wuce ya fita daga hotel ɗin.

Su kuwa, wanka suka yi, kowa ya tsabtace jikinsa, suka sanya kayan da Lion ɗin ya kawo masu. Suna gama shiri sai ga masu karɓar order abinci sun shigo. Kasancewar su sun saba cin abincin Naija, sun ci shi a wajen Rimsha, sai suka bada order fried rice, and pepper chickens, sai ruwa da Maltina.

Mai karɓar order ya amsa da okey sannan ya fita, yana fita ya faɗa ɗakinsu Mark, bayin Allah su basu taɓa cin abincin Naija ba, amma a yau basu da zaɓin da ya wuce dole su ci, kada yuwa ta illatar da su, haka suka bada order pepper cikin, dan suka ganin kamar shi ne zai fi masu.

A ɓangaren Akila kuwa, order jolof rice and chips ta bada. Haka mai karɓar order ya tattara kan order tasu ya koma abinsa.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya kawo masu duk abin da suka saka order. Dukkansu babu daɗi bakunasu, amma haka suka daure suka tsakuri abincin, dan kada yunwa ta kayar da su.

After some minutes, Areef ne ya fito daga bedroom nasu, ɗakinsu Akila ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, da yake shi ya fisu tausayi, Ayla tana a cikin ransa, yana ta tunanin halin da take a ciki, ya kasa samun sukuni, burinsa kawai ya zo ya dubata, ya kuma sa Lion ya nemo likitar da zai bata taimakon gaggawa da zai taimaki rayuwarta kada ta mutu kafin su karisa gida.

Kamar yanda ya kwantar da ita, haka ya shigo ya sameta. Yana shigowa bai kai ga karisawa cikin bedroom ɗin ba, Aseef ya shigo shima bakinsa ɗauke da sallama, hannunsa ruke da wata jibgegiyar leda da Lion ya sayowa su Akilar kayan sakawa a ciki.

A bakin bed ɗin dukkansu biyu suka zauna, Areef ya kai hannu ya taɓa Ayla, dan ya ji har yanzu akwai sauran rai a jikinta ne. Shi kuma Aseef ya miƙawa Akila ledar kayan yana faɗin "Yanzu Lion ya dawo ya kawo maku, ya ce ku shirya da wuri, helicopter zata zo ta ɗauke mu zuwa gida". Ya kai karshen maganar tare da miƙa mata ledar.

Karɓa ta yi tare da fara buɗe kayan, Abays ne a ciki, sai takalma. "Heartbeat zaki iya yi wa matar uncle wanka idan na kai maki ita cikin toilet?". Cewar Areef.

Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e zata iya, dan tun ɗazun take yi wa Ayalar kuka, Allah sarki, ba shakka Akila tana da tsananin tausayi kamar Areef ɗin, halinsu kusan ɗaya, dukkansu, kuma babu in da suka baro daddyn Rimsha a kamannin hali, kunga shi ma duk abin da ƴan uwansa suka yi mashi a duniyar nan bai sa ya ji cewa ba zai iya taimaka masu ba, to haka Areef da Akilar ma suke, shi Aseef yana da zuciya gaskiya, idan ka yi mashi abu ya taɓa mashi zuciya, to yana wahala ya mance da wannan abin, kuma shi ruwa biyu ne, wani lokaci yana da zafi sosai, wani lokaci kuma yana da sanyi, kun tuna time da suke Washington? Har su Uncle T bai kyale ba, to haka yake, idan ka yi mashi laifi, to ba zai yafe ba sai ya rama, ko kuma ya fita harkarka, ya zubaka a kwandon shara, shi kuma Lion ai ba wata zancen fita harka, hukunci zai baka mai kyau, daga nan kuma shikenan komai zai wuce, bashi da riko kamar Aseef.

Ɗaukar Aylar Areef ɗin ya yi ya kaita cikin toilet ɗin, already Akila ta haɗa ruwa mai zafi a cikin jacuzzi, yana zuwa ya sanyata a cikin jacuzzin, sannan ya fito ya fice daga ɗakinma gabaɗaya.

Yana fita wajen Lion ya nufa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga bedroom ɗin, Lion ɗin yana zaune a bakin bed nasa yana aikin latsa waya.

Kusa da shi ya zo ya zauna yana faɗin "Ka yi magana da su momma ne?". Bai amsa ba, kuma bai ɗago ba, ya cigaba da abin da yake yi na tsawon lokaci, kafin nan ya ɗago kansa tare da kai kallonsa a kan Areef ɗin. "Where is your phone?". Yana gida ya bashi amsa.

Shiru ya ɗan sake shi kafin ya ce "A wajen waye wayar take? Momma or your wife?". Girgiza kai ya yi yana faɗin "In my room, kuma switch off nata ma na yi".

Okey ya amsa mashi da shi, sannan ya mayar da hankalinsa a kan wayar tasa, tun ɗazun number Rimsha yake kira, amma taki ɗauka, hasalima wayar tana a cikin bedroom nasa, ita kuma tana tare da Brr Naurat, dan taki yarda kowa a gidan ya taɓata sai Brr Naurat, ƙwaƙwalwarta sai kara birkice masu yake yi, abu kamar wasa yana neman ya zama babbar case, sam yanzu ta dai'na magana ma, idan ka tambayeta abu, sai dai ta zuba maka idanu kawai taka kallonka, Allah mai iko yau harta daddynta da mummynta bata sansu ba, abin ya yi mugun ɗaga masu hankali ba kaɗan ba, sun shiga damuwa na wuce misali, dan ma Brr Naurat tana kwanta masu da hankali ne, da abin sai ya fi haka, a takaice dai Rimsha bata leƙawa ko palo, ko da yaushe tana kwance a saman bed ɗin Brr Naurat, wanka ma Brr Naurat ɗin ce take yi mata, yanzu ta zama tamkar jaririya, wanka ma bata iya ba, in short ba wani abin da Rimsha ta iya a yanzu, common abinci Brr Naurat ce take bata a baki, duk taurin zuciya irin ta Jehan, sai da ta zubarwa da kanwar tata kwallah ba kaɗan ba, ta sha kuka sosai, saboda Rimsha dai ita kaɗai ke gareta, ita ce kawai kanwarta, duk wannan dirama da suke yi suna tsananin kaunar junansu na wuce misali, kawai Jehan ɗin ce dama da shegen iya tsare gida yasa Rimshar bata kusantar ta sosai, amma suna kaunar juna over.

Lion ya kira wayarta har ya gaji ya hakura. Hakika yana son yin magana da ita, saboda a jikinsa yana jin cewa bata da lafiya, ba lafiya take ba, dan duk lokacin da ya tuna sunanta, sai zuciyarsa ta harba, abin ya ɗan ɗaga mashi hankali, hakance ma tasa ya ce da His excellence ya sanya a turo masu jirgin helicopter kawai su koma gida da wuri, sannan da akwai abubuwansu da suka bari a airport na Enugu state, dan haka his excellence yasa ya mayar masu da shi gida. Burinsa kawai ya koma gida, da gwaggo da Rimsha sun tsaya mashi a cikin tunaninsa fiye da tunanin mai tunani.

A ɓangaren su Akila kuwa, Areef yana fita daga toilet ɗin Aylar ta farfaɗo, saboda ruwa da aka sanyata a ciki. Tana farfaɗowa ta fara zuba kuka babu kakkautawa, rarrashinta Akilar ta rinƙa yi, amma taki ta yi shiru, hakan tasa Akilar ta kyaleta ta yi mata wankar kawai, bayan ta gama ta tallafa mata ta fito, sannan ta ɗaura mata towel daga kirjinta, da kyar Aylar take iya jan kafarta har suka fito izuwa cikin bedroom ɗin. Ko da suka fito basu sami Aseef a ɗakin ba, ya fice abinsa. A bakin bed ta zaunar da Aylar, ta ciro kayan da Lion ya saya masu, tare da tallafa mata ta sanya a jikinta, sannan ita ma ta wuce toilet ɗin dan ta je ta yi nata wankar. Baiwar Allah Ayla, har kumbura face nata ya yi, ta yi wani iri da ita, gwanin ban tausayi.

A takaice dai sai misalin karfe 3 na yamma, sannan jirgin helicopter ya iso, basu ɓata lokaci ba wajen tafiya, Ayla dai sai ruwan hawaye take yi, cikinta tsananin ciwo yake yi mata, baiwar Allah bata taɓa jin azaba irin haka ba, dan cikin nata ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba, shiyasa ma ta kasa daurewa har take kuka. Areef bawan Allah shi ya yi ta fama da ita, ya yi ta rarrashinta har suka dira a cikin Kaduna.

Already su Imran suna airport suna jiransu. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka nufi gida, dan akwai majinyata sosai a tattare da su, shi kansa Lion ɗin kamata ya yi ace yana kwance a gadon asibiti, amma saboda dakiya da taurin zuciya tare da karfin imani, yasa ya dake, ya ki yarda ma kowa ya duba shi, ya ce sai ya dawo gida kawai.

Gabaɗaya family suna tsaye a harabar gidan suna jiran isowarsu, Rimsha, Jehan, Anaya, su ne kawai basu a cikinsu, suna ɗaki suna barci, Jehan da Anaya sun ci kuka sun ƙoshi ne har barci ya yi awon gaba da su, ita kuma Rimsha already kun san matsalar da take a ciki, an yi mata ruƙiya ma, amma shiru, farko sun ɗauka aljanu ne suka shafeta, sai da aka yi ta yin ruƙiya aka ji shirune yasa suka fahimci ba aljanu bane, wata matsala ce dai ta daban, dan haka sai suka kyaleta sai Lion ɗin ya dawo, dan sun san halinsa, kada su kira malami ko a kaita wajen magani ya dawo ya sauke masu kwandon aradu a kansu, dan ba ƙaramin aikinsa bane ya ce uban waye ya ce a taɓa mashi matarsa? Waye ya ce wani ko wata ya zo ya dubata? To gudun kwandon bala'insa ne yasa suka bar mashi kayarsa, ya zo ya san yanda zai yi da ita.

Suna dira a gida, Lion ne farkon da ya fara fita daga cikin motar, tun motar bata gama tsayawa a parking space bama ya fice abinsa. Sam bai bi ta kan kowa dake tsaye a wajen ba, cikin gida ya wuce abinsa, kai tsaye bedroom nasa ya wuce. Yana shiga ya nufi toilet, wanka ya yi a gurguje, sannan ya fito ya shirya cikin three cuter sky blue da singlet, singlet ɗin fara ce tas, tamkar yanzu ya cirota daga ledarta, abin da ya sanya ya saka singlet ɗin kuma, saboda ciwukan dake a kirjinsa.

A box ya ɗauko tare da zama a gefen bed nasa, dan hannunsa in da wuka ta yankar nan ba ƙaramar ciwo take yi mashi ba, hannun ta kumbura, kun san wuka da akwai dafi a jikinta, hakance tasa hannun ta kumbura sosai.

Family kuwa, cikin tsananin murna suka fara rungumar juna, kowa baki ya ki rufuwa, saboda tsantsar farinciki. Areef yana ɗauke da Ayla a saman kafaɗarsa, bai wani tsaya a wajensu ba, sai ya wuce izuwa cikin gida kawai, dan ya kwantar da ita, ta huta.

Gabaɗaya family sun sha matukar mamakin ganin Aseef a tare da su, sai dai kuma sun kasa iya tambayarsa ya aka yi hakan? Ga tambayar a cikin ransu, amma ta kasa fitowa fili, abin ya ɗaure masu kai, amma haka suka hakura suka daure.

Sai rungumar Dr Salman suke yi tamkar za su mayar da shi cikinsu, Brr Naurat har da ruwan hawaye, sai tsiya su Imran suke yi mata.

Shi ma Dr Salman ɗin ya sha kuka ba kaɗan ba, dan bai taɓa tunanin familynsa suna a raye ba, ya yi zaton komai ya kare ya lalace masu, ashe dai sunanan, sun zama taurari zakarun gwajin dafi ma a cikin al'umma, wannan abin ya yi mugun sanya shi farinciki wanda baki ba zai iya furtata ba. Haƙiƙa farincikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login