Showing 144001 words to 147000 words out of 270744 words
a wajen bai motsa ba, cikin girmamawa ya sanar da shi babu kowa a cikin ɗakin. Jinjinawa Donal ɗin kai kawai ya yi, alamar ya ji ya tafi to. Da sauri ya juya ya bar wajen.
Shiru Lion ɗin ya yi yana tunani, tabbas in dai babu kowa a wajen, to ba shakka Areef ne ya yanke masu hukunci. Kamar yanda ya yi hasashen kuwa hakan ce, Areef ne yasa aka kashe mutumin, dan dayaga Lion ɗin ya shiga busy, sai ya bibiyi case ɗin kawai ya yanke masu hukunci, su kuma malaman makarantarsu Rimsha ya sanya sojojin dake gidan suka basu horo mai tsanani, sannan ya sallamesu. Time da ya sallamesu ko takawa da kafafunsu basu iya yi, da rarrafe suka bar gidan, shi ma Areef oga ne wajen iya bada punishment idan ka shiga hannunsa.
Ya ɗan ɗauki lokaci a tsaye a harabar gidan kafin ya wuce izuwa garden, dan ya kwanta ya ɗan huta, tun da wannan abin ya faru, bashi da wajen zama sai wannan garden ɗin, ita ma ba dan daɗi yake zama a cikinta ba, kawai dan bashi da yadda zai yi ne, garden ɗin yanzu duhu take yi mashi, Rimsha ita ce dama fitilar dake haske duk in da yake, so yanzu bata nan, ko'ina duhu yake yi mashi, sai dai ya runtse idanuwansa ya zauna a waje kawai, amma ba dan daɗi ba.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa, A'A Salahuddeen ya turo yayyunsa dan a tambaya mashi auren Hanan, dan shi da gaske yana sonta, sai dai baya zuwa wajenta, a waya kawai suke yin hira, saboda yana jin zafin su haɗa idanu da maman Ayla, kun san kuma tana gidan Abbin, so ita kanta Aylar baya son haɗa idanu da ita, yanzu kunyar mutanen gidan ma yake ji, saboda abin da mahaifinsa ya yi, da farko ma kamar zai hakura da neman auren Hanan ɗin, sai da Imran ya karfafa mashi gwiwa, sannan ya turo yayyunsa.
Abbi ne ya yi masu jagora izuwa garin Katsina, dan su nemi auren Hanan ɗin daga hannun mahaifinta, shi kuma daddyn Jelly ya ce ba zai sami zuwa ba, saboda rashin lafiyar Ayla, almost wajen 3 months a yanzu kenan da kwanciya ciwon nata, amma bata warke garau ba, sai kuka abu kaɗan, duk ta zama wata birkitaciya baiwar Allah, so daddyn baya son ya matsa ko nan da can daga kusa da ita, duk da cewa mamarta tana kusa, amma ya fi son ya zauna ya kula da ita. Yau ɗaukarta ma ya yi suka tafi gidan Azharuddin Bature, saboda gidan babu kowa, Abbi da su Aunty sun tafi Katsina, maman Aylar ma ta bisu, dan su yi wa Hanan ɗin kara, Aunty ta ce tana son zuwa taga iyayen Hanan ɗin, shi ne Abbi ya ce to su je a tare, sun baro Aafia sai Hjy Hadiza da ba zama a gidan take yi ba, yanzu ma bata gidan, su Abbi suna fita ita ma ta fita, yanzu yawon bin malamai take yi, duk dan ta shawo kan Abbin, sai wahal take yi buƙata ta gagara biya, a matsayinta na uwa ta kasa zama ta yi jinyar Aafiar, sai gantali take yi a kan namijin da bai san ta yi ba, dan shi Abbi yanzu idan ba Aunty ba, baya ganin kowa a gabansa.
Shi kuwa Irfan ya koma school abinsa, dama bai kammala master nasa ba, shi ma Akil sun koma Madina shi da Umaishansa, cikinta ya girma sosai har ya shiga watannin haihuwa, a yanzu kula na musamman Akil yake bata. Saura Imran da Jelly ne kawai a tare da Hjy Umaiya, shi ma Imran ɗin zai koma U.s, dama a can yafiye yawan zama, soyayyar jelly take dawo da shi Naija dama, so yanzu yana so ne ya ɗauketa su koma can mai gabaɗaya, ya zama Naija sai dai su kawo ziyara, Ammie ce ta dakatar da su yasa bai tafi ba, ta ce bata yarda ba, ya zauna a nan tare da su, Akil ya tafi shi ma yana son ya tafi ya barsu da kewa, sai rarrashinta yake yi yana neman shawo kanta dan ta yarda, so har yanzu dai bata amsa mashi da to ba, amsar kawai yake jira jirginsu ya ɗaga.
❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷
Su Abbi sun dira garin Katsina lafiya, kai tsaye gidansu baban Sadiq suka nufa, sam Abbi bai manta hanyar ba, motoci biyu suka yi dama, na familyn A'A Salahuddeen ɗaya, na Abbi, Aunty, Hanan ɗin, sai mana Ayla, su kuma mota ɗaya, .
A kofar gidan daga can ɗan nesa suka yi parking na motocin nasu, sannan suka fito suka nufi gidan. A kofar gida suka tsaya, Hanan ta ce bari ta shiga ta duba baban nata, su Aunty su zo su karisa ciki tun da mata ne.
Ba musu suka bita izuwa ciki, su Abbin kuwa suka gyara tsayuwa a wajen, sai kallon kaskanci ƴan uwan A'A ɗin suke yi wa gidansu Hanan ɗin, basu yi zaton a irin wannan lakar gidan za su wanko kafa su zo nemawa A'A mata ba, su duk a zatonsu a gidan Abbin matar take, sun ɗauka ƴarsa cema, dama idan baku manta ba gabaɗaya familyn A'A akwaisu da jiji da kai da alfahari, hakan yasa suka fara surutai a kan su fa a gaskiya sun fi karfin su nemi aure a irin wannan gidan.
Sai hakuri Abbi yake basu, kin yarda suka yi, suka ce wlh A'A ba zai kawo masu wannan gayyar tsiya, gayyar talauci gidansu ba, dan haka ya nemi mata ƴar gidan mutunci, ƴar gidan mutane ba muna mutane ba. Surutai dai marasa daɗin ji suke ta jefar Hanan baiwar Allah da shi, sun ki tsayawa kuma baban Sadiq ɗin ma ya fito, sun ce sun fi karfin haɗa idanu da shi ma, sai da Abbi ya kira A'A a waya, suka haɗu suka rinƙa basu hakuri, sannan suka yarda zasu haɗu da baban Sadiq ɗin, amma su daga yau sun zame hannunsu a kan batun auren A'A, sun yarda zasu tambaya mashi auren, amma ya sani idan ya aureta kada ma ya ce zai kawo masu ita gidansu, su je can gidansa ya zauna da ita, basu bukatar ganin ƴar matsiyata a cikinsu, haka ba dan ya so ba ya ce ya yarda da sharaɗinsu, sannan ne suka ce to baban Sadiq ɗin ya fito su yi komai a wuce wajen.
Ko da baban Sadiq ɗin ya leƙo ya ga manyan mutane masu ji da Naira, sai ya yi maza ya koma ya ɗauko tabarmar amarya mai kyau, kunsan shi da son abin duniya dama, tuni ya fara yi masu mubaya'a tare da zubar da girma da mutunci, abin ma har sai da ya bawa Abbi kunya, sai da ya yi danasanin rakosu da ya yi, dama tun farko basu ɗauki Hanan ɗin da daraja ba, ga shi babanta ya zo ya kara zubar mata da mutunci, duk sai Abbin ya ji wani iri, ya ji dama ya zo shi kaɗai ya gayawa baban ga abin da ake ci, daga nan ya sanar da shi zai yi mata miji ya bashi izini, idan ya bashi izinin sai ya aurar da ita cikin mutunci kawai, idan ya so bayan auren sai Hanan ɗin ta kawo A'A ɗin ya gaida baban nata, amma yanzu komai ya riga na kwaɓe, sai dai Allah ya ceceta kawai daga hannun familyn A'A, dan zata wahala, zata sha kyara, gori da kuma walaƙanci tare da cin mutunci, marainiyar Allah, sai dai daɗin abin ma dai A'A ba mazauni Nigeria bane ba, bai cika zama a cikin ƴan uwan nasa ba, so zai ɗauketa ne su tafi, shi ne sauki da zata samu, ba dan haka ba tana a tsaka mai wuya.
A ɓangaren su Hanan ɗin kuwa, hannu bibbiyu maman Sadiq mace mai kirki da mutunci ta tarbesu, da yake yanzu ɗakinta Sadiq ya gyara mata shi, sai ya zamana fes gwanin birgewa, dama ita ba mace mai kazanta bace, tana da tsabta sosai, dan haka ko'ina fes a cikin ɗakinta, ga ɗan lafiyayyiyar bed nata mai matuƙar kyau da Sadiq ya saya mata, ta shimfiɗe shi da bed sheet mai kyau dai'dai talakawa, sai kamshin turaren wuta ƴar icce ɗakin nata yake.
A saman tabarma suka zauna, cikin mutunci ta kawo masu ruwa a randar tulunta mai sanyi. Karɓa suka yi a mutunce suka sha, sannan suka fara gaggaisawa dan sanin juna. Hanan ce ta gabatarwa da Maman Sadiq ɗin su waye su, tare da yi masu karin bayani. Kara faɗaɗa murmushinta Maman Sadiq ɗin ta yi tana mai kara yi masu sannu da hanya tare da zuba masu ruwan godiya a kan ruke Hanan ɗin da suka yi.
A can waje kuwa, baban Sadiq yana jin cewa neman auren Hanan suka zo yi, tun bai san su waye su ba ya ce ai ya basu ita duniya da lahira, ko bata so dole ayi auren, dan haka kada su damu. Ji Abbi ya yi tamkar ya kifa mashi mari, wannan wani irin uba ne? Abin ya yi matuƙar kona ran Abbi sosai da sosai. Shi wato baban Sadiq idan dai ya ga ƴar maiƙo maiƙon kuɗi duk sai hankalinsa ya tashi, duk sai ya ruɗe ya fita a hayyacinsa ya rasa tunaninsa, abin takaice, ya Allah ka rabamu da mataciyar zuciya.
A can gida Kaduna kuwa, da misalin karfe 8 na dare, su Abbi basu kai ga isowa gida ba, suna a kan hanyar dawowa. Aafia ita kaɗai ce a gidan, baiwar Allah a yanzu saura ƴan kwanaki ta kammala iddarta, amma bata sani ba, Abbi ya bar Hjy Hadiza a gidan ne dan ta kula da ita, bai san suna fita ita ma ta yi nata ficewar ba, dama kun san daddyn Jelly da Aylarsa basu nan, so basu dawo ba har yanzu, shi ma Irfan baya nan, so ya rage saura ita kaɗai a gidan.
Fitowa palo ta yi ta zauna a saman sofa, daga ita sai ƴar doguwar riga mara nauyi a jikinta, kanta na sanye da turban cap white color, ta yi wata iriyar ramar da idan ka kalleta sai ka tsorata, sai ka zubar mata da kwallah, dama kun san ita bata da ƙiba sosai, bata kai su Umaisha ba, so ta kara figewa kamar figaggiyar kaza kwaila, abin dai gwanin ban tausayi, ta yi duhu sosai, sai wannan dara daran idanuwan nasu na gado zaka gani a face nata, hancinta ya gara tsawo sosai, saboda ramar, ba laifi tana samun sauki, duk abin da mutun yake yi tana sane, ta koma normal kamar da, sai dai magana ce da bata buɗe baki ta yi, amma tana jin komai, da alama a yanzu babu wata cuta a tattare da ita face jimamin mutuwar Dr Nawid, shi ne yasa bata magana sam sam.
Ta yi shiru ta zubawa Tv idanu kamar mai kallon Film, a zahiri ba kallon take yi ba, ta lula duniyar tunani ne kawai. Sallama ta ji daga bakin kofar shigowa, a hanzarce ta kai kallonta a wajen. Abbo ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
A razane ta miƙe tsaye, dan kuwa ba zata taɓa mantawa da fuskarsa ba, a lokacin da Dr Nawid ya zo mutuwa, tabbas fuskantar Abbon ya bayyana a saman face nasa, shi ne ya kara jefata cikin tashin hankali da ya juyar mata da ƙwaƙwalwa, saboda yanda da ga fuskar Dr Nawid ɗin ya canza a lokacin, kun san dama ita already bata san Abbo ba, time da aka yi aurenta da Dr Nawid Abbo baya gidan, idan baku manta ba ya tafi wajen tsafinsu, so baya nan, ita a Man na school nasu wanda ya kashe Amal ta san Abbo, bata san ainahin face nasa ba, farkon ganinta da face nasa dai ranar da Dr Nawid zai mutu, kuma bata manta da shi ba!!.
"Aafia lafiya kika razana kika mike haka?". Ya faɗa cikin nuna kulawa, tamkar bai san me ta razananwa ɗin ba.
Baya ta ɗan ja kaɗan tana girgiza mashi kai tare da fara ruwan hawaye. "Aafia lafiya kike kuwa? Meyake faruwa? Kullum ina zuwa dubaki bana samun damar ganinki sai yau, kullum idan nazo sai na samu kina barci a ɗaki".
Ya yi maganar yana nufota. Baya baya ta fara ja tana girgiza mashi kai ta kasa yin magana.
Nufota ya cigaba da yi yana ta wasu surutai da bata gane me yake faɗa ba. Har suka kewayo ta wajen kujerar dake kusa da kofar fita, hakan ne ya bata damar ta zunduma ihu tare da juyawa a guje ta fita daga cikin palon, da gudu ya bi bayanta.
Mai gadi yana zaune a saman chair nasa bai ankara ba sai ganin Aafiar ya yi ta buɗe gate ta yi waje a guje. Kafin ya mike ya zo ya bi bayanta dan ya ga ko lafiya, sai ganin Abbo ya yi ya zo ya wucesa fiw kamar wani fanka ya yi wajen shi ma, ai a dubu ɗari mai gadin ma ya nufi waje, dan a tunaninsa irin wannan fitowa da suka yi da gudu kamar wasu iskar fanka to ba lafiya ba cikin gidan yake, gara mashi shi ma ya gudu waje, koma me zata faru a ciki ya tsaya daga ta waje yana kallah. (Wayyo cikina, jama'a mai gadin nan zai kasheni da dariya, a'a yana da gaskiya fa😂 gara mashi ya tsaya ta waje, yaga sai fitowa suke yi kamar iskar fanka, tamkar waɗan da ake gefowa daga sama, kunga kuwa dole ya yi ta kansa shi ma😂)
Kasancewar unguwar ta manyan mutane ne, babu kofa a wajen, duk suna cikin gidajensu, kuma Aafiar tun da ta yi wannan ihun sau ɗaya bata sake yin wani ba, dama kun san ba magana take yi ba, yanzu ma Allah ne kawai ya ƙaddara ta iya zunduma wannan ihu ta farkon, daga shi kuma bata sake yin wani ba, tana ta ƙoƙarin ta yi ihu dan a kawo mata ɗauki, amma tamkar an shake mata wuya, ta kasa iya buɗe bakin nata, haka ta cigaba da gudu da iya karfinta na karshe, dan ta ceci kanta daga sharrinsa. Shi ma Abbon da gudu ya biyo bayanta, ga shi dare ne ba rana ba.
Tana haurowa ainahin babban titin fita daga unguwar tasu wata dankareriyar mota ta kwasheta, saboda ta shigo kan titin ne babu excuse, a guje kamar mahaukaciya. Shi kuwa Abbo buƙata ta biya, dama shi burinsa kawai ya kamata, ko tana raye ko tana mace, koma yaya dai ya kamata kawai. Dan haka ko kaɗan bai damu dan mota ta bugeta ba, sai ma wani daɗi da ya ji, ya nufi in da take kwance cikin jini malale a gefen hanyar dan ya ɗauketa...............
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 8/5/2024
E27
Da kyar mai motar ya iya taka birki, saboda yanda kan motar ta so ta kwace mashi.
Bai tsaya dai'dai ta nutsuwarsa ba ya fito a hanzarce, dan ya duba ko tana raye ko ta mutu.
Dai'dai lokacin shi kuma Abbo ya karisa wajenta da nufin ya ɗauketa.
"Hi guy, where will you take her to?". Ya yi maganar cikin ƙwararriyar harshen turancinsa, kuma ya yi maganar yana nufosu, sanye yake da wandon jeans baka mai shegen kyau, sai army's T-shirt daga ta sama, kafafunsa na sanye cikin wasu kyawawan tsadaddun Booth mai matuƙar kyau, launin black color, ya saki gashi har bayan wuya, sai kamshi yake zubawa.
"She is my daughter, i want to take her to hospital". Ya bashi masa shi ma cikin harshen turanci ba tare kuma da ya ɗago ya kalli wanene bane, shi dai burinsa kawai ya ɗauketa su bar wajen.
Jin hakan yasa Tga ɗin ya juya ya nufi wajen motarsa ba tare da ya sake yi masu magana ba, dama idan baku manta ba shi baya son bakaken fata, yanzu ma abin da yasa ya fito dan yaga wanene ya buge ne, saboda a matsayinsa a soja bai kamata ya taka dokar kowace kasa ba, hakan ce ma kawai tasa ya fito, to tun da ya ji mahaifinta yana wajen, sai ya koma cikin motarsa da nufin ya bar wajen kawai.
Kunna motar ya yi tare da ɗan yin reverse, dan ya samu damar wucewa. Kamar wanda aka yi wa allura, sai wani tunani ya faɗo mashi a cikin ransa, idan har da gaske wannan mutumin mahaifin yarinyar nan ne meyasa baya kuka da ya ga an bugeta? Meyasa bai nuna damuwa da tashin hankali ba? Ko dai su mutanen Nigeria haka suke basu damu da ƴaƴan su ba ne?. Waɗan nan sune tunani da tambayoyin da suka faɗo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa kamar wadda aka yi wa allura.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce yes maybe mutanen Nigeria haka suke, basu damuwa da ƴaƴan su ne. Tuna hakan yasa ya ja motarsa ya bar wajen.
Shi kuwa Abbo hannu ya kai da nufin ya ɗauketa, sai ya ji a yanda yake ɗin nan fa ba zai iya ɗaukarta ba, dole sai ya canza zuwa