Showing 198001 words to 201000 words out of 270744 words

Chapter 67 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2992

zo ya zauna yana faɗin "Saif lafiya? Who are they?". Ya yi maganar idanuwansa na'a kan sir Arvin mai kama da Lion ɗin, sai kallonsa yake yi da mamaki cike fal a face nasa.

Nisawa Lion ɗin ya yi kafin ya ce "I can't talk to much uncle, but Arvin ka basu labarin abin da yake faruwa from A to Z, mu bamu bukatar jin yadda kuka yi rayuwa, just tell them who are you people's and what's going on here". Ya kai karshen maganar yana duba sakon da ta shigo wayarsa a yanzu.

"Kazo yanzun nan". Shi ne sakon da aka rubuta mashi tare da address. Wani siririn tsaki ya ja tare da duba time kafin ya kashe wayar mai gabaɗaya ya ajiyeta a gefensa, saboda ya lura su His Excellence ba zasu taɓa rabuwa da shi ba, shi kuma ba zai taɓa yarda ya haɗa hanya da su ba, saboda ya tsanesu fiye da tunanin mai tunani, duk da suke kakanninsa, sam baya son ganinsu, shi da ace Jacob Roshan yana raye ma, ai da da kansa zai kashe ɗan banza, kawai ya tashi ya ɗauki yara ya sadaukarwa da matsafa wai sune magadan kujerar tsafin nasa, tsabar iskanci ba zai sanyasu su gaje shi a abin arziki ba sai a na tsiya, ya cutar da rayuwarsu a banza da wofi, yanzu ga uncle Herry dai bama su san a in da yake ba, ya mutu ko yana raye Allah masani, ji yake yi kamar ya je ya tono kabarin Jacob ɗin ya gana mashi azaba ta musamman kafin ya mayar da shi (Wlh Lion zai kashe ni da dariya 😂 shekaru talatin da uku da mutuwarsa idan ka tono kabarin me zaka gani banda farin kashi? Kawai hakuri zaku yi kakanku dai ya cuceku a banza)

Nauyayyar ajiyar zuciya sir Arvin ya sauke kafin ya fara basu labarin duk abin da yake faruwa dallah dallah. Mamaki iya mamakin Dr Cherish sun sha, sai dai kuma daddyn Rimsha da yake yana da zuciya mai kyau sosai, sai ya ce. "Allah sarki ai da bata kashe kanta ba, yanzu dai wuta zata tafi kai tsaye, da ta bari ko musulta ne sai ta yi, ai Aunty A'isha tana da tawakkali, zata yafe mata duk da nasan zata surfa masifa ba kaɗan ba, amma tabbas zata yafe mata"

"Uncle kana nufin mommarmu mafaɗaciya ce?". Cewar Aseef.

Guntun murmushi daddyn Rimsha ya yi tare da faɗin "Bazaka san hakan ba sai ranar da ka yi wa Akila ba dai'dai ba, ai ina ga duk cikin yaran babanmu ba wanda ya kaita iya faɗa da surfa ruwan bala'i, ga zuciyar bala'i da rashin tsoro, kai faɗe ma ɓatawa, wani lokaci ka yi wa Akila zalinci ka ga ikon god, mantawa zata yi da kai autanta ne, saboda ba'a zalinci a gabanta, baka ga Jehan bace? Ai Jehan goyonta ne, shiyasa take a haka, Aunty Aisha karshe ce".

Shiru Aseef ɗin ya ɗan yi kafin ya ce "Wayyo i really love my momma, ai gara ta zama haka, idan ba haka ba mutanen duniya sai su rinƙa ɓata mata rai, amma idan tana da faɗa kowa zai ji tsoronta".

Shi dai Lion abin da kuka sani ne, binsu da ido kawai yake yi, sai hira suke yi. Handsome bawan Allah ya yi shiru, akace uwa da ɗa sai Allah, tunanin Dr Cherish kawai yake yi ɗan tahalikin nan, duk da ya ji abin da ta yi bata kyauta ba, amma kuma uwarsa ce, yana kaunarta over sama da kowa, dole ya shiga damuwa sosai na rashinta, babban abin tausayin ma shi ne, idan aka yi sa'a Dr William ya dawo cikin hayyacinsa to fa ba shakka bai san su ba, zai ce bai sansu ba, dan shi rayuwar da suka yi a China duk sun yi ta ne cikin shi baya a cikin hayyacinsa.

Gyaran murya sir Arvin ya yi tare da fara magana a nutse. "Now where is our real mom? I want to see her, i want to see this strong woman that give birth to QUADRUPLE, Lions and Kings! I want to see her more than your expectations, an cutar da ita ba karya, kuma ta sha wahala ba karya".

Kallon Aseef Lion ya yi kafin ya ce "Ka basu labari a kan momma".

Cike da mamaki tare da al'ajabin abin da Dr Cherish ta aikata ya fara magana a nutse, labari ya ɗauko masu tun kan soyayyarta da Dr William har kawancenta da Cherish ɗin, komarta Nigeria da duk abubuwan da suka faru, daga karshe ya rufe masu da mommar tasu tana hanyar zuwa ai.

Shiru sir Arvin ya yi yana mai kara jinjinawa mahaifiyar tasu, ba shakka ta cika jarumar uwa, gaskiya duk ita aka fi cuta a cikin wannan al'amari.

A wannan rana dai haka suka wuni cikin farinciki, Sir Arvin yaki yarda ya rabu da Lion da kuma Aseef, sun sake komawa TRIPLETS tun da Areef baya nan, duk ya ƙosa su Areef su iso ya ga cikon ɗayansu, yau a bedroom na Lion suka wuni, shi kuma Handsome a tare da daddyn Rimsha ya zauna, sai tunanin Dr Cherish yake yi, ita kam Pinky abin da kuka sani ne, tana manne da Sir Arvin, dan shi ta sani, da shi ta saba, ta saba da shi sama da mummynta, shiyasa ko'ina suna a tare.

Da daddare ma sir Arvin ya ce shi a bedroom na Lion zai kwana, dama shi Aseef ai already sun saba in dai kwana a bedroom na Lion ne, sai su zo su haye mashi bed nasa shi da Areef, su haye su kwanta, su bar nasu part ɗin, to yau shi ma Sir Arvin ya ce babu in da zai je, Lion ya ce mashi da akwai almost parts empty da babu kowa wajen guda uku a wannan hawa da suke, ya ɗauki ɗaya, ya ce sai wani lokaci zai ɗauki ɗayan, yanzu dai a nan zai kwana tare da su.

Aseef kuwa ya ce mashi "Ai bed ɗin tana ɗaukarmu mu dukka TRIPLETS dama, dan haka ga toilet ka yi wanka ya sanya kayan barcin Lion kazo mu kwanta, ni bari na kira matata".

Ɗan zaro dara daran blue eyes nasa sir Arvin ɗin ya yi tare da faɗin "Wow kana da mata?".

Jinjina mashi kai Aseef ɗin ya yi tare da fito da hoton Heartbeat ɗin tasa yana nuna masa.

Karɓar wayar ya yi yana kallonta. "She's so beautiful, amma bata sanya maka ciwon kai ko?".

Lion ne ya amsa mashi da cewa "Ƴar aljanna ce in ji Aseef ɗin, ƴar aljanna kuma ai kaga ba zata sanya mashi ciwon kai ba".

Kallon Lion ɗin da kyau sir Arvin ɗin ya yi kafin ya ce "Okey we can see ai, ni dai nasan mata koya kake dasu sai sun sanyaka ciwon kai, haka Dr Cherish da daddy, kullum cikin sanya shi ciwon kai take yi, ya yi ta faman shan magani, kuma wai a haka tana son shi".

Karɓar wayarsa Aseef ɗin ya yi yana faɗin "No my heartbeat dai daban take da kowace mace, wai baka ji Lion ya ce maka ƴar aljanna bace? Ai ƴar aljannarce da gaske, bata laifi, kuma bata son ɓacin ra'ina, ni ku bar damuna bari na kirata mu sha love ɗin mu".

Jinjina mashi kai kawai sir Arvin ɗin ya yi, dama shi Lion baya kula shi in dai a kan Heartbeat ce, dan fa shi Aseef bai yarda Heartbeat zata yi mashi laifi a duniya ba, ƴar aljannarsa ce.

Nufar toilet sir Arvin ɗin ya yi, ita dai Pinky tana zaune kusa da Lion saman bed, ta yi shiru abinta, wannan ita ce Queen amount the Kings, ita kaɗai ce mace a cikinsu, gata ƴar karama, zata sha gata kam, daga wajen Lion sai wajen sir Arvin abinta.

Har sir Arvin ya je zai shiga toilet ɗin, sai kuma ya dakata tare da juyowa, a kan Lion ya sauke idanuwansa, while shima Lion ɗin shi yake kallo. "Kai fa? Kana da mata?". Sir Arvin ɗin ya tambaya.

Jinjina mashi kai ya yi, calmly ya ce "I have a Queen amount the Queens, one in million".

Duk da sir Arvin baya dariya, a wannan gaɓar sai da ya ɗan yi siririn murmushi kaɗan, sannan ya ce "Oh ashe ba laifin Aseef bane, kai ma hakance, ƴar aljana wadda bata laifi kai ma ke gareka ba?".

Shiru Lion ɗin ya yi bai amsa mashi ba.

"Will you show me her pic's?". Cewar sir Arvin ɗin.

Girgiza mashi kai Lion ɗin ya yi. "No". Ya faɗa tare da kwanciya da kyau a saman bed ɗin.

Kamar zai tambaye shi meyasa ba zai nuna mashi ita ba, sai kuma ya fasa ya wuce cikin toilet ɗin kawai, sai dai zuciyarsa cike tab da mamakin ya aka yi matar Aseef take bakar fata? A haka ma bai san Akilar fara ce tas a Nigeria ba, in da Rimsha ya gani ne sai ya ce mata baka kai tsaye, saboda ita ce chocolate color, su Akila da Jehan ai fararen tattabaru ne, amma da yake shi mai jan kunne ne sai yake masu kallon bakaken fata.

A takaice dai a tare suka kwana a saman bed guda su ukun, Pinky dai tana manne da Sir Arvin, taki rabuwa da shi, a saman kirjinsa ta kwanta, kuma Lion bai rabasu ba, dan ya lura sun yi muguwar sabo fiye da tunanin mutun, so ba zai so a rabasu a kaita wani bedroom ɗin ba, sai dai da suka yi barci shi ya tashi ya bar masu bedroom ɗin, ya koma part ɗin Areef ya yi kwanciyarsa kayansa.

Washegari da safe suka rinƙa damunsa da tambayar meyasa ya gudu ya barsu da suka yi barci?. Shiru ya yi masu bai amsa masu ba, haka suka gama takura mashi da tambayar, da dai suka ga ba zai amsa masu ba, sai suka kama kansu suka nufi dining room, dan su yi breakfast.

Dr William kuwa tun wannan suma da ya yi jiya, har yau bai farfaɗo ba, kuma Lion ya hana a zuba mashi ruwa, ya ce su kyale shi na ɗan lokaci, dan da alama kullin da Dr Cherish ta yi mashi ne yake son kwancewa, shi ne ma yasa ya shiga doguwar suma bawan Allah.

Sai da suka yi breakfast a tare cikin farinciki, kowa yana farinciki amma banda Handsome, yana cikin damuwa bawan Allah. Yau Lion ma a tare da su ya yi breakfast, duk da baya karyawa da wuri, yau saboda su ya karya da wuri.

Bayan sun kammala ne suka ɗugunzuma izuwa bedroom na Dr William da yake kwance, yana kwance kamar yadda Lion ɗin ya kwantar da shi jiya, sai dai ko da suka shiga sai suka tarar da ya fara motsi, a hankali yake motsawa yana sambatu kasa kasa, basu iya jin me yake faɗa, saboda kasa kasa sosai yake magana.

Sai da suka matso kusa da shi ne suka fara jiyo abin da yake faɗa kasa kasa. Ba komai yake faɗa ba kuma face sunan gwaggo. A'ish, A'ish, yake ta kira.
Tsawon shekaru talatin da uku zuwa da huɗu kenan yau, tun kafin a haifi TRIPLETS ya rabu da gwaggo, amma yau sai ga shi anwayi gari bayan tsawon waɗan nan shekaru dukka ya farfaɗo da ambatar sunanta, Allah Akbar. Da alama ya dawo cikin hayyacinsa ne.

Sosai sambatun nasa yake kara yawaita, zuba mashi idanuwa suka yi suna kallonsa, Lion da daddyn Rimsha ne suka yi karfin halin fara tofa mashi adduo'i, dan kada ya tashi a birkice, suna tofa mashi adduo'in ne dan Allah ya taimakesu ya tashi a cikin nutsuwarsa.

Sir Arvin kuwa tuni idanuwansa suka ciko da kwallah tab, hakika ya ji tausayin daddyn nasu da kuma mommar tasu, tsawon waɗan nan shekaru masu uban yawa haka! Shin gwaggon ma zata yarda da shi kuwa? Idan fa aka karyawa mutun zuciya a karon farko, mawuyacin abu ne ya sake yarda da koma me! Allah sarki Dr William, rayuwarsa da akwai ciwo ainun.

Sun jima a haka kafin nan su samu ya farfaɗo mai gabaɗaya, ko da ya farfaɗo kuma da sunan gwaggo a bakinsa ya farka, ya tashi ne da tambayar ina take? Sai dai sun yi sa'a ya farfaɗo cikin hayyacinsa, ya farfaɗo a cikin nutsuwarsa, wannan adduo'i da suka rinƙa yi mashi ta taimaka mashi sosai. Sai dai fa kamar yadda Dr William ya dawo normal sanadiyyar mutuwar Cherish, haka suma su Anderson suka sami damar gane cewa ba Dr William na gaskiya bane a hannunsu, saboda Cherish ta mutu komai ya karye, gaskiya ta bayyana, akwai kura ba kaɗan ba, kada ku manta shi Sir Arvin ba musulmi bane ba, zasu iya ganinsa a duk in da yake tun da shi ne nasu, shi ne aka basu, shi suka ɗauka Cherish ta ra'ina masu wayo, ta kwace shi, tab ga rai'inin wayon da ta yi masu, hakan zai kara bakanta masu rai, akwai badakala!!.

Dr William yana ɗaura idanuwansa a kan su Lion ɗin ya dakata daga ambatar sunan gwaggo da yake yi, zaro idanuwansa ya yi yana kallonsu da mamaki, ga shi Lion da sir Arvin ya fara sauke idanuwansa a kansu, su ne masu kama da shi kuma. Cike da mamaki ya kai hannu ya shafi face nasa, dan ya ji wai nasa face ɗin tana nan ne ko dai ita ce aka cire aka sanyawa waɗan nan masu kama da shi ɗin?

Tambayar kansa yake yi su waye su? Sam bai san cewa yaransa bane, bai ma kawo a ransa cewa yanzu shakaru 32 sun wuce ba, shi dai yasan tabbas gwaggo tana da ciki, kuma cikin nata bai wuce wata 3 ba a lokacin da ya sani, to suwaye waɗan nan masu kama da shi ɗin kuma?.

Tambayar da yake ta faman jefawa kansa cikin ruɗani kenan, ya shiga ruɗani, ya kalli Lion ya kalli sir Arvin....... Allah sarki Dr William bawan Allah.

Ganin haka yasa daddyn Rimsha da yake ya fisu girma, ya kuma fisu sanin yakamata, sai ya ce masu bari ya bawa daddyn nan nasu labarin abin da ya faru, idan ba haka ba ƙwaƙwalwarsa tana a cikin ruɗani over, dan haka kowa ya zauna za'a sake dawo da labari daga farko.

Dukkansu babu wanda ya musawa daddyn Rimshar, waje suka samu suka zauna. Cikin nutsuwa daddyn Rimsha ya fara yi wa Dr William bayanin komai, tun daga farko har karshe izuwa yau yanzu da suke zaune, tashin hankali. Dr William ya yi shekaru 32 zuwa da uku bai san in da kansa take ba! Bai ma san wanene shi ba, anyi ta wasa da kwakwalwarsa tamkar yadda ake buga ball, bawan Allah, Allah ne kaɗai zai saka mashi wannan cuta da suka yi mashi, amma hakika ancuce shi ba kaɗan ba!!.

Ɗago idanuwansa ya yi ya sauke a kan yaran nasa, yanzu su dukka biyar ɗin nan ƴaƴansa ne bai sani ba, iya cikin su QUADRUPLE kawai ya sani, bayansu bai san komai ba, suma QUADRUPLE ɗin bai san su huɗun bane a cikin gwaggon, saboda a lokacin cikin nata karami ne, so ya ɗauka ma yaro ɗaya ne.

Suma kallon shi suke yi, alama ya yi masu da hannu a kan su zo gare shi, dukkansu suka miƙe amma banda Lion, dan shi da aka sake bada wannan labari ma an sake ɓata mashi rai ne, ji yake yi meyasa suka yi sakaci har Cherish ta kashe kanta? Ai da hukunci mai tsauri zata fuskanta, sannan wlh ba zai bar su His Excellence ba, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, dan haka ya kasa tashi ya karisa wajen Dr William ɗin ma, ya zauna yana ta binsu da idanu kawai.

Rungume juna suka yi da Dr William ɗin, a gefensa suka zazzauna, sai shafa fuskokinsu yake yi kamar ance za'a kwace mashi su, sam bai nuna cewa baya son ko ɗaya daga cikinsu ba, harta ƴaƴan Cherish ɗin ma, dan idan baku manta ba ai ya musulunta kafin su juyar mashi da kwakwalwa, so yana da ilimin addini ai, yasan laifin wani baya shafan wani, dan haka sai ya haɗasu ya rungume, yana shafa fuskokinsu yana kallon Lion da yake zaune yana binsu da kallo.

Alama ya yi mashi da hannu a kan yazo mana shi ma. Nisawa ya yi tare da miƙewa a hankali, yana isa wajen bed ɗin Aseef ya tashi ya bashi waje, kusa da Dr William ɗin ya zauna tare da ɗan sunkuyar da kansa kasa kaɗa, bawan Allah ƙoƙarin dannar zuciyarsa kawai yake yi, dan yazo har wuya, gaskiya an cucesu da yawa, jikinsa har tsuma yake yi a kan su His Excellence, barema wannan tsinanne Anderson ɗin, ji yake yi tamkar ya yi mashi gashin kazar Hausa, kun san kazar Hausa ce sai ta ji wuta sosai take gasuwa, to haka Lion yake ji zai yi wa Anderson idan ya kama shi............. Lallai Anderson zai gasu ba karya😂

A takaice yau dai sun yi wunin farinciki, duk bayan ƴan mintina sai Dr William ya tambayi Lion yasu gwaggo, sai dai Lion ɗin ya ce mashi suna hanya, sun kusa sauka, duk ya damu yana son ganinta bawan Allah, shin zata yarda ta karɓe shi kuwa?.

Sai can rana ta yi sanyi jirgin su gwaggo ya sauka a cikin Washington, sam Lion yaki sanar da Dr William cewa sun sauka lafiya, yana son kawai suzo gida su haɗu, baya son su tada mashi da tarzoma a airport, dan yasan wlh gwaggo ba zata karɓi Dr William a cikin sauki ba, ko da ta ji meyafaru, shi kuma Dr William ba zai iya ganinta ya daure har sai sun dawo gida ba tare da ya yi mata magana ba, so zasu iya tada masu da rigima a cikin airport ɗin, shiyasa sai ya boye mashi, suka barshi a gida suka tafi airport shi da sir Arvin da kuma daddyn Rimsha, shi ma Aseef yana wajen daddynsa ai, bai ma san su gwaggon sun iso ba, Pinky ma tana wajen Dr William, saboda ita ta saba da shi a rayuwar da suka yi a kasar China, dan haka sai ta sake jiki ta manne mashi.

Kafin su Lion su isa airport ma airport ɗin ta cika makil da jama'a, saboda kowa ya ji labarin jet ɗin Lion ta sauka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login