Showing 153001 words to 156000 words out of 270744 words

Chapter 52 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2955

shi sosai, a daddafe yake iya barci, dan ma dai sai sun yi hira da ita a waya har zuwa asuba ne, shi ne yake samun nutsuwa kaɗan.

Shi kuma oga Lion, a yanzu ya kai point ɗin da dede da rana ɗaya ba zai iya raba makwanci da ita ba, yin hakan zai azabar da shi matuƙa, ya riga ya leƙa duniyar sama jannati, ya ɗanɗani zuma mai azababben daɗi, so ba zai iya jurar rashinta ba, shi ne yasa shi ma abin ya taɓa shi sosai, bugu da kari kuma ga shi ba waya suke yi da ita ba, bare ta ɗan ɗebe mashi kewa, tana sume bata san in da kanta yake ba, shi kuma da yake cikin hayyacinsa ɗin, da shi da sumammen babu wani banbanci sosai, saboda baya iya yin komai face tunaninta, ba shi da aikin da ya wuce kallon hotunanta da videos nata da ta rinƙa ɗauka a wayarsa time da ya tafi Daular Mutuwa, kun san dama ya tafi ya bar wayar a gida, so kafin ta fara rashin lafiya ta yi ta hotuna da videos da wayar, a yanzu sune suke rage mashi kewarta, kun fa san su Turawa na faɗa na kara faɗa, idan zasu yi soyayya to da iya gaskiyarsu suke yinta, gabaɗaya zuciyar suke bawa mace, so dole kuga Lion a irin wannan hali, dan ya riga da ya bata gabaɗaya zuciyarsa, sai kuma abin da hali ya yi.

(Under 15 years girl da ruke zuciyar Lion, abin da ban mamaki gaskiya, Rimsha ta ciri tutan da babu wata macen da ta taɓa ciran irin sa gaskiya.)

Haka Aseef ya kammala rakinsa son ransa kafin su yi sallama da Akilar tasa. Ɗaura wayar a saman table ɗin gaban nasu ya yi tare da kara narkewa a jikin Lion ɗin yana wani tura baki, shi dai gaskiyar magana ya gaji, a barshi ya koma Naija. Areef dai sai guntse dariyar mugunta yake yi, yana tsoron yin dariyar ne, kada ya ja su sauke mashi haushin a kansa.

A can gida Nigeria kuwa, da misalin karfe 6 na mangariba, gwaggo na zaune a bakin bed ɗin Lion ɗin tana ƙoƙarin cirewa Rimshar drip ɗin dake makale a hannun nata, dan ya kare, tana son saka mata wani ne. A hankali Rimshar ta fara motsa yatsun kafafunta, babu kowa a cikin ɗakin, Jehan tana ɗakin gwaggon ita da Aafia suna kwance, ita Aafia tana barci, ta kuma samu lafiya masha Allah, ita kuma Jehan tana ruwan hawaye, dan abin ya kai mata kololuwar makura a yanzu.

Kafin gwaggon ta yi wani yunkuri Rimshar ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka yi mata wani irin nauyi, ji ta yi tamkar an sanya masu super glue an datse mata su, da kyar ta iya ɗan warosu kaɗan, sai kuma ta yi maza ta rufesu, saboda hasken da ya haske mata idanun nata.

Sunanta gwaggon ta fara ambata cike da ƙaguwa tare da zumuɗi. "Rimsha! Rimsha". Ga mamakinta sai ta ji ta amsa mata da na'am, sai dai ta amsa ne kasa kasa, muryar tata baya fita, kuma yana a dashe kamar mai yin mura.

Wani irin azababben daɗi gwaggon ta ji tamkar ta zunduma ihun murna, tun da Rimshar ta iya gane sunanta har ta amsa da na'am da aka kirata, to ba shakka tana a cikin hayyacinta, da alama kwakwalwar tata da suke zaton ya taɓu, to bai taɓu ba, Allah ya tsare, kuma ta sami tsananin kulawa ce ta musamman daga ƙwararriyar likitan, wato gwaggon, gaskiya babu zancen wasa gwaggon ta kula da ita fiye da tunanin mai tunani, ta yi treated nata fiye da tunaninku, ba dare ba rana tana a kanta kullum, shiyasa abin ma ya zo masu da sauki, Allah ya taimakesu bata sami taɓin kwakwalwa ko kuma wani ciwo daga ta ciki ba, amma batun azabtu ba'a maganarsa shi kam, baki ya yi kaɗan ya faɗi kalar wanda ta sha.

"Rimsha kina jina?". Gwaggon ta faɗa cike da zumuɗi da kuma ƙaguwa.

Can kasan maƙoshinta ta yi magana a kasale "E gwaggo ina jinki". Rimsha akwai kwakwalwa, bata buɗe ido ta ga wacece ke magana ba, duk da yanzu ta tashi daga ciwo na tsawon kwanaki 29 a sume, amma ta ɗauki muryar gwaggon, bai shige mata ba voice ɗin.

Matsowa gwaggon ta yi tare da ɗago kanta ta ɗaura a saman laps ɗinta tana faɗin "Buɗe idanunki ki kalleni ko?".

Da kyar take iya motsa laɓɓanta baiwar Allah, saboda sun yi mata nauyi sosai, kasa kasa ta yi magana "Gwaggo hasken ɗakin ne yana kashe mani idanuna". Allah sarki, yanda ta yi maganar gwanin ban tausayi.

"Ki buɗe su a hankali hankali ba zai kashe maki ba, dan kin jima baki buɗe idanun bane shiyasa, amma yanzu dai gwada buɗesu a hankali ko?". Okey kawai ta ce tare da fata ɗan buɗe idanun nata, tana yi tana sake mayar da su ta rufe, a haka har ta buɗesu gabaɗaya.

Idanun nata sun yi jajir kamar jini, saboda sun jima a datse. Hamdala ga Allah gwaggon ta yi, ita kuma Rimshar fara bin ɗakin da kallo ta yi, shiru ta yi tana tunanin abin da ya faru da ita, a iya saninta dai tasan cewa ita da Noorish nata ne kawai a cikin ɗakin nan, kuma soyayya suke zubawa juna tare da nuna tsantsar kewar juna, abu ɗaya zata iya tunawa kuma ta rike a ranta shi ne, tabbas lokacin da ya shigeta ta ji wani azababben zafi, bayan wannan zafin ita bata sake sanin komai ba, duk bidirin da Lion ya yi bata sani ba, dan tana sume baiwar Allah.

"Gwaggo ina Yah Saif ɗin?". Ta faɗa murya can kasa kasa.

Da mamaki gwaggon take kallonta, saboda bata taɓa tunanin cewa Rimshar zata tashi kuma ta nemi Lion ba, ta yi tunanin sai an kai ruwa rana da ita kafin ma ta sake yarda su haɗa ido da shi, sai kuma ta ga akasin haka.

Abin da gwaggon bata sani ba shi ne, ita fa Rimsha bata san aika aikan da Lion ya yi mata ba, idan da ta sani ne wata kila ta guje shi, amma sam ita bayan buɗe hanyar shigarta da ya yi, bata sake sanin komai ba, kuma in da Allah ya kara taimakonta shi ne, kafin ta farfaɗo daga doguwar sumar, ta sami lafiya, dan har ɗinkin da aka yi mata ma gwaggon ta kwance shi tun last two weeks ago, so babu wani sauran ciwo a jikinta da zai iya sanyawa ta gane ga abin da ya faru, sai dai idan ta zo miƙewa ne zata ji jikinta ya yi mata nauyi, kuma kunga ita yarinya ce sosai, ba zata iya fahimtar halin da ake a ciki cikin sauki haka ba, misali koda ta je toilet yin wani uzuri nata, idan ta ji gabanta yana zafi, bazata taɓa tunani kwatankwacin abin da ya faru kenan ba, zata dai ce ko saboda shigarta da Lion ɗin ya yi ne yasa hakan, shekarunta sun yi ƙanƙanta na sanin wannan karatu a yanzu, ko zama aka yi aka bata labarin abin da ya faru da halin da ta shiga caf, kananun shakarunta ba zai kai ta hango wahalar da ta sha ɗin ta kai ko kwatan hakan ba.

Shiru gwaggon ta yi, tana tsoron ta gaya mata Lion ya koma, saboda bazata ji daɗi ba, ya dawo ne fa suna tsaka da rungumar juna na kewar juna da suka yi, ko fuskarsa mai kyau bata samu ta gani ba ta shiga doguwar suma, sannan yanzu daga farfaɗowarta a sake ce mata ya koma, ai zasu sanyata ta sake suma, tana tsananin son Lion sosai baiwar Allah, shi ma yana tsananin kaunarta over. Dan haka sai gwaggon ta kasa iya samun dakiya da kwarin zuciyar iya gaya mata ya koma, kawai sai ta ce mata ya fita yana zuwa.

"Amma gwaggo ki faɗa mani me Noorish ya yi mani? Ina jin jikina yana ɗan yi mani zafi, kuma ni dai nasan tabbas ya........." Kasa karisa maganar ta yi, dan sai da ta fara maganar ne ainahin abin ya yi mata ɗin ya faɗo mata a cikin tunaninta, ba wai ta tuna abin da ya faru bane, no, ta tuna cewa mumynta ta gaya mata haka ake mu'amala ta auratayya, so abin da Noorish ya yi mata shi ne aure, hakan yasa ta kasa iya karisa gayawa gwaggon maganar, saboda wani irin azababben kunyar gwaggon da ta ji ya dira mata a ranta lokaci guda, duk sai ta ji ta takure waje guda, sai ta ji ba zata iya cigaba da yin magana da gwaggon ba, tana buƙatar matsawa daga kusa da ita, saboda kunya.

Ita kanta gwaggon ta ji matuƙar daɗin yaddan Rimshar ta yanke maganar ta kasa karisa tambayar tata, abin ya yi mata daɗi, dan dama bata san wani amsa zata bata ba idan da ta idasa maganar.

"Gwaggo ina Jehan da mumyna?". "Jehan tana ɗakina, mumynki ma tana ɗakinta, ƴar gidan mummy".

Murmushi kaɗan ta yi, kafin ta yunkura zata miƙe, amma ina gaɓɓanta sun ki bata haɗin kan ta miƙe, ta kasa iya miƙewar. Komawa ta yi ta lafe shiru, kamar zata sake tambayar gwaggo meyake faruwa da ita ne ta kasa miƙewa? Sai kuma ta sake tuna last abin da ya faru a tsakaninta da shi, hakan yasa ta yi tunanin to ko abin da ya yi mata ɗin ne yasakata ciwon jiki? In kuwa haka ne ba zata iya tambayar gwaggon ba, dan ita tana da kunya sosai.

Ganin haka yasa gwaggo ta ce "Ina zaki je dama?". "Wajen mumy".

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To bari na kira maki mumyn naki ko?". Ta kai karshen maganar tare da mayar mata da kanta a hankali ta kwantar mata, sannan ta miƙe ta nufi wajen.

Da kallo Rimshar ta bita har sai da ta fice, sannan ta dawo da kallonta izuwa saman kayan magunguna da alluran dake ɗaure daman table da yake a kusa da gadon.

Sai mamaki take yi a kan waye aka zandumawa waɗan nan uban alluran dukka, bata san dukka a jikinta suka kare ba, baiwar Allah bata san komai ba.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



Date: 10/5/2024



E29


Sai mamaki take yi a kan waye aka zankaɗawa waɗan nan uban alluran dukka, bata san dukka a jikinta suka kare ba, baiwar Allah bata san komai ba.

Gwaggon tana fita ta so ta kira Lion a waya ta sanar da shi Rimshar ta farfaɗo, kuma sun yi sa'a bata gane komai da ya faru da ita ba, saboda suman da ta yi. Da ta duba time a wayarta, sai ta kalli lokacin yin sallar issha ne a Washington yanzu, dan haka sai ta ce bari ta kyale shi sai anjuma ta sanar mashi, kamar tasan yana cikin yanayi mara daɗi.

Bedroom na mum ta nufa, ba ɓata lokaci ba ta gaya mata halin da ake ciki. Murna tamkar mum ta zuba ruwa a kasa ta sha, babban abin da ya fi sanyata murna ma shi ne yanda Rimsha bata gane komai da ya faru ba, da idanunta biyu aka yi komai ta sha wannan bakar azaba, da wlh ba zata koma wajen Lion ta daɗin rai ba, amma Alhdulimmahi da Allah yasa bata san komai ba, yanzu zata yi begen mijin nata, zata koma wajensa cikin so da kauna, ba za kuma ta ji tsoronsa ko ta rinƙa gudun shi ba, abin ya yi masu daɗi sosai, su wannan suma da ta yi ma taimaka masu sosai da sosai ya yi.

A tare suka nufo ɗakin Lion ɗin, sai godiya ga Allah subhanahu wata'ala suke yi. Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga cikin ɗakin, tana kwance kamar yadda gwaggon ta barta.

Kusa da ita mum ɗin ta zo ta zauna tana tambayarta ya jiki?. Hannun mum ɗin ta riko tana faɗin. "Alhamdulillah mum".

Sannu ta cigaba da yi mata, ita kuma gwaggo alwala ta ɗauro dan ta yi sallar mangariba ta godewa Ubangiji da ya tashin masu Rimshar cikin ƙoshin lafiya.

Sosai Rimshar ta sha mamakin irin yanda suke ta ce mata sannu, abin ya ɗan dameta, ta ji sannun yaki karewa, ita yanzu duk ba sannunsu bane a gabanta, Noorish nata kawai take son ya dawo su ga juna.

A ɓangaren shi kuma Lion ɗin, bayan sun yi sallar mangariba da issha, saman table suka haye dan su ci abinci, sam Lion baya jin ra'ayin cin abincin, saboda yanayi na sha'awa da yake a ciki, ga kuma damuwa na rashin farfaɗowar Meeshar tasa. Sai dai yunwarce ta yi mashi yawa over da har tasa ya haye saman table ɗin zai ci abincin.

Shi ma Areef ba dan daɗi zai ci abincin ba, dan kawar da yunwa kawai zai ci, banda haka yanayin da yake a ciki na kewar Jehan ya hana shi sukuni.

Shi kuwa Aseef suna zama a saman table ya kira Akila video call tare da ajiye wayar a yadda zasu ga juna, haka yake yi kullum, dan ya ce ba zai iya cin abinci ba tare da suna kallon juna ba. (Aseef ɗan dirama ne wlh😂 iskanci kala kala ya iya.)

Kamar dai kullum, sai da ya karɓi first spoon na ƴan uwan nasa, yana yi yana karewa Akila dake kwance a saman bed kallo, daga ita sai kayan barci riga da wando a jikinta, ta lafe a saman bed tare da rungume pillow a kirjinta tana kallonsa, Jehan dai har wa yau tana bedroom na gwaggo, ita kuma Akilar a normal bedroom nasu ita da su Jehan ɗin take, ba'a bedroom na mijin nata ba, tun da ya bar kasar ita ma ta baro bedroom ɗin.

Sai kallon shi take yi, ya kara kyau, ji take yi kamar ta zuro hannu ta shafi wannan lallausan kumatun nasa mai matuƙar ɗaukar hankali, ga sajensa ta kara kwanciya luf, duk sai ta shiga santin kyau ɗin da ya kara yi.

A nashi ɓangaren shi ma santin kyau ɗin gyaran da ta sha yake yi, ta yi fresh, ji yake yi kamar ya jawota ya rungume, sai zubawa juna shagwaɓa suke yi, ko kunyar su Lion basu ji, su kuwa su Lion ɗin ko a jikinsu, tamkar babu su a wajen, abincinsu sama sama kawai suke ci.

Kaɗan Lion ya tsakuri abincin ya miƙe bayan ya goge bakinsa, bedroom nasa ya nufa dan ya yi wanka ya fito ya duba ya jikin Mark yake, dan yau sam bai leƙa shi ba.

Mark ɗin yana part dake kusa da na Aseef, a nan yake jinya, an ɗaura mashi kafar tasa, yana samun lafiya Alhamdulillah, likitoci har huɗu Lion ya sanya suka zo suna kula da shi, dan already kun riga kun sani cewa Lion yana Kaunar Mark sosai, shi ne ma yasa ya ce a dawo mashi da shi gida ya yi jinya a gabansu, dan su rinƙa kallon halin da yake a ciki.

Bawan Allah yana shan wahala ba kaɗan ba, duk ya rame, kunsan yadda karaya take da azaba!. Kullum Anaya tana gefensa, bata taɓa yin nesa da shi, idan kuka ga ta fita daga bedroom ɗin, to sai dai idan likitoci ne suka zo zasu yi aikinsu, shi ne zata fita ta koma ɗayar ɗakin, dan a cikin part ɗin ɗakuna uku ne da palo guda, so ɗaya nata ne ɗaya na Mark ɗin, ɗayan babu kowa a ciki, idan likitoci sun zo, sai ta koma nata ɗakin, dan ta basu waje.

Mark yana kaunarta sosai, ita ma ba sai na sake faɗa ba kun sani, ita ce ma ta fara son shi kafin shi ya faɗa mata. Duk da yana a halin ciwo, amma hakan baya hanashi ya rinƙa kula da ita tare da gaya mata kalamai masu daɗi, dan ya rinƙa kwantar mata da hankali, saboda tana cikin damuwa sosai wlh, dayawan lokuta idan ta zauna bata da aikin yi sai yi mashi kuka, shiyasa yake iyaka bakin kokarinsa dan ya ga ta dai'na shiga damuwa tana farinciki. A yanzu dai kafar tasa ta kai matakin da za'a kwance mashi ita ya ɗan fara takawa, umarnin Lion kawai likitocin suke jira, dan su kwance mashi ya ɗan fara takawa.

Bayan ya yi wankar ya shirya cikin kayan barcinsa masu bala'in kyau da tsada, sai zuba kamshi yake yi tamkar a jikinsa ake kera perfume. Bedroom na Mark ɗin ya nufa, yana tafiya cikin wannan nutsuwa tasa.

Kasa kasa ya yi sallama tare da shiga cikin ɗakin. Anaya tana zaune a saman bed ɗin kusa da mijin nata, hannunta na a ruke da cup mai ɗauke da coffee, sai tiririn zafi yake yi, shi kuma Mark ɗin yana ɗan gefenta, yana zaune, daga bayansa ta sanya mashi pillow, da alama ma coffee ɗin take ba shi a baki, ga ɗaya daga cikin Drs dake kula da shi yana zaune a saman bedside drawer, da alama ita Anayar ita ta ce zata bashi coffee ɗin a baki, hakan yasa Dr ya kyale mata ta bashi, dan duk abin da ta ce zata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login