Showing 108001 words to 111000 words out of 270744 words

Chapter 37 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2957

shi ne iya gaskiyar da na sani".

Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya sake cewa "Tun ainahi menene matsalar, and meyasa kuka karɓi cikon TRIPLETS nawa?".

A tsananin razane tare da kiɗima kakan nasa ya fara magana "Please Romeo don't ask me this questions! I don't want to die, i have alot of things da nake son cinmawa, idan har na gaya maka gaskiya, to ba shakka zan mutu a yau, please save my life, leave me like that!". Ya kai karshen maganar yana zare idanu kamar an tare ɓera a tarko.

Nisawa ya yi nafin a takaice ya ce "I don't want all this miscellaneous excuse, just amsa me, meyasa suka ɗauki cikon TRIPLETS nawa? Me kuka yi da shi?".

Allah sarki Lion bawan Allah, yasan cewa baba shakka gwaggo da bakinta ta bada ɗaya daga cikinsu, amma shi ba hakan ce a gabansa ba, dan ya san wlh gwaggo ba zata bayar da su haka kawai ba, dole da kawai kwakkwaran dalili, shi yanzu so yake yasan menene yasa aka yi hakan dukka, ba damuwarsa wanda ya bayarba, a gaskiya sai mai karfin Imani mai kuma tawakkali da yarda da ƙaddara ne kawai zai iya ɗaukar abin da Lion yake ɗauka, bugu da kari shi duk abin da zaka gaya mashi sai ya yi doguwar nazari a kan maganar, shiyasa yana da matuƙar wahala kaga ya yanke kuhunci ba dai'dai ba, saboda aiki da kwakwalwa da basira, a yanzu da wani ne ya ji abin da kakan nan nasu ya ce, to ba shakka da ba zai yi wani dogon tunani ba, kawai zai ɗauki karan tsana ne ya ɗaurawa gwaggo ɗin, alhalin kuma dole da akwai dalilinta na yin hakan, Allah ka bamu ikon yin amfani da kwakwalwarmu wajen yin tunani a koda yaushe.

"Romeo it's a long story, please and please let me go........" Kasa karisa maganar ya yi saboda wani irin kallo da Lion ɗin ya wurga mashi, hakance tasa ya haɗiye maganar.

"Uncle you know that bana repeating na word ko? And them bana cancel na magana idan nayi ko?".

Jinjina mashi kai kakan nasa ya yi, ba shakka yasan da cewa Lion ba zai canza maganar nan ba, ya gaya mashi gaskiya shi ne kawai zai zama mafi a'ala a garesa, idan ba haka ba, wlh Lion zai gana mashi azabar da sai ya gwammaci mutuwa a kanta, dan haka sai ya fara magana cike da iya gaskiyar da ya sani kamar haka.

"Romeo ainahin wannan matsala ta samo farko ne daga kan kakanku Jacob mahaifin William, shi ne makasudin shigarku dukka wannan matsala, Jacob wato mahaifin William shi ma member ne na kungiyarmu, kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyarmu wanda ya kasance shi ne Anderson, Anderson shi ne shugaba, Jacob mai take mashi baya, to dama a ƙa'ida ta kungiyarmu kowa dole zai kawo yaro daga cikin yaransa wanda ko ya mutu wannan yaro zai gajesa, hakan ce kawai zata sanya kungiyar ta cigaba da haɓaka, so shi Jacob sai ya bada yaronsa Herry, daga baya sai ya sake bada Josephine, saboda yana son zama shugaba, a ƙa'idarmu dama hakance, wanda ya fi sadaukarwa uwargijiyarmu, shi ne zai zama shugaba, kai baka yi mamakin meyasa Jacob ya fi kaunar William a cikin ƴaƴansa ba? Saboda yasan cewa William ɗin shi ne kawai ɗansa, a lokacin sam ba'a san za'a haifi Tga ba, to a takaice dai da Herry da Josephine Jacob ya bayar da su, ya rage saura mashi William kawai, shiyasa ya fifita William ɗin sama da su, ya kaunace shi sosai, dan yasan shi ne kawai zai gajesa a duniyar mutane, su Josephine ba nasa bane, nan da ɗan lokaci za'a ɗaukesu, haka muka cigaba da tafiya a kan tsarukanmu, nima na bada yaro ɗaya daga cikin yarana, dan ya zama magajina a kungiyar, kowannanmu dai ya bada na shi, kwatsam sai William ya zo da batun auren mahaifiyarku wadda ta kasance musulma, shigowar musulma gidan Jacob zai iya zama barazana ga gariyarsa a kungiya, dan haka sai ya tsaneta, na nuna baya goyan bayan tarayyar ɗansa da ita, to da yake abin ya zo da karar kwana, shi William kaifi ɗaya ne, ba'a isa a tankwara shi ba, ai kaga yadda suka kare, William ya zama sanadiyar mutuwar Jacob ɗin, to mukuma abu ne da ka rigada ka sani cewa bamu yafe jininmu, dan haka ba zamu iya yafewa William wannan laifi da ya yi na kashe mana ɗaya daga cikin member kungiyarmu mai karfin faɗa aji ba, bugu da kari kuma yayanmu na jini, hakan yasa muka fara shirye shiryen yadda zamu ɗauki fansa a kan William, a dai'dai lokacin ne kuma muka fuskanci babban barazana da ya yi ƙoƙarin rugujemu, wannan barazana kuma ba komai bane face musuluntar William da su Josephine, mun shiga tsananin tashin hankali na wuce misali, saboda Josephine da Herry namu ne ba naku ba, idan aka ce sun musulunta mun shiga uku, zamu iya rasa rayukansu a kan hakan, ga shi lokacin ya zo a dai'dai Herry zai maye gurbin Jacob tun da ya mutu, kuma suna matsayin musulmai ba ta yadda za'ayi su kasance a cikinmu, saboda suna yin sallah da sauransu, duk musulman da zaka gani a ire iren kungiyarmu, to basu yin sallah da sauran ibadunsu ne, dan tsafi baya haɗuwa da sunan Allah, to su Josephine bayan sun musulunta suna sallah har da karatu, hakan ba ƙaramar ɗaga mana hankali da jefamu cikin bala'i ya yi ba, a wannan lokacin ne Anderson ya fuskanci mummunar ukuba daga wajen uwargijiyarmu, dan shi ne shugaba a wajen, komai ya faru za'a ga laifinsa a matsayinsa na shugabanmu, dan haka sai uwargijiyarmu ta hukunta shi a kan musuluntar su Josephine, wanda hakance tasa duniya take ganin kamar ya mutu, dan ya sha bakar wahalar da kowa ya bashi mutuwa, bayan ya dawo cikin hayyacinsa, uwargijiyarmu ta saukaka mashi ne sai ya koma cikin kungiya da zama mai gabaɗaya, kuma a lokacin ne uwargijiyarmu ta ce ta bamu lokaci ƙanƙani mu ɗauki mataki a kan abin da yake faruwa, kuma mu san yanda zamu yi mu dawo da Josephine da Herry cikin sauri, a takaice hakan tasa muka yi ƙoƙarin dawo da su cikinmu, hakan kuma ba zai taɓa yiwuwa ba har sai mun rabasu da mahaifiyarku, dan tana koya masu abubuwan addini, (Addu'a da karatun Alqur'ani mai girma) idan kuma suka karanta wani abin ma (addu'a) da mu bamu san menene bane suna iya ɓace mana daga idanun tsafinmu, hanan tasa muka fara ƙoƙarin rabasu, sai muka fara da WILLIAM, dan munfi jin haushinsa sama da kowa, shi ne sanadiyyar komai da ya faru, shi ya kawo mahaifiyarku a cikinmu, ya yi mana laifi dayawa, shi ne ya zama sanadiyar mutuwar Jacob, sannan ya janye su Josephine daga garemu, ya kuma kawo mana mahaifiyarku ta zo da addininta tana ƙoƙarin ruguzamu, wannan dalilin yasa muka yi iyaka bakin ƙoƙarinmu wajen cusawa William tsanarta, kuma a lokacin sai muka yi sa'a yazo dai'dai tana da ciki, sai muka cusa mashi tsanar cikin da ita kanta, to hakan ce tasa muka yi nasarar nesanta ta da William ɗin, ta koma gefe guda tana rayuwa, sai mukuma kuka kama William ɗin muka ɗaure shi, sai muka kawo wani mai kama da shi muka yi replacing, a takaice dai William da kuke tare da shi a yanzu ba naku bane, ba shi ne mahaifinku na gaskiya ba, namu ne, naku har wa yau yana ɗaure a kungiyarmu, dan ya yi mana laifi dayawa, Anderson ya ce kada a kashe shi, a barshi a ɗaure har ya mutu, to har yanzu dai bai mutu ba, yana dai shan bakar wahala, sai dai babu wanda ya san da cewa William da yake tare da ku ba naku bane namu ne. Bayan mun ɗauki William na ainahi, sai muka koma kan Josephine, munyi munyi mu juyar da tunaninta, amma da yake ita ta yi sabo sosai da mahaifiyarku, tana tare da ita kullum, sai muka kasa, hakan ba ƙaramin ɓatawa Anderson rai ya yi ba, sai ya yanke shawarar dole ita ma mahaifiyarku mu hukuntata, dan ita ma ta kawo mana barazana a cikin harkokinmu, hakan yasa muka yanke shawarar karɓar ɗanta idan ta haifa, wannan shawara da muka yanke yasa sai muka barta a tare da Josephine ɗin, shi kuma Herry muka juya mashi tunani, muka kife ƙwaƙwalwarsa ma gabaɗaya, sai ya zama bai ma san menene addinin musulunci ko kuma mahaifiyarku ba, muka mantar da shi komai kamar yanda muka yi wa Rimsha a yanzu, haka muka cigaba da saka idanu a kan mahaifiyarku da Josephine, cikin dabara muka fara controlling na Josephine ɗin ita ma, mun sami nasarar yin hakan ne kuma a lokacin da take jinin haila, babu tsarki a tattare da ita, shiyasa muka yi nasarar aikata hakan, daga nan sai muka cigaba da amfani da ita dan muna son mahaifiyarku ta aihu mu ɗauki yaron, ita Josephine ita ce ta sanya mahaifiyarku ta bada yaro guda ɗaya, da bakinta ta ce ta bamu ɗaya, ban dai san ya suka yi da Josephine ɗin har ta yarda ta bada yaron ba, abin da na sani shi ne ta yarda ta bada babban ɗanta, so ba kai bane babba, wanda muka ɗauka shi ne yayanku, shi ne aka fara haifa, tun cikinta yana da wata biyar a duniya ta yarda ta bada ɗan da zata fara haifa, wanda zai fara faɗowa duniya, to shi ne yasa bayan ta haihu muka turo Herry ya karɓi yaron, a lokacin ita ma Josephine ɗin bata isa ta yi mana musu ba, ba a cikin hayyacinta ta bada yaron ba, sai dai abin mamakin shi ne, Bayan Josephine ɗin ta bada yaron, lokacin da mahaifiyarku ta koma gidanta tana kuka, idan baku manta ba Josephine ɗin ta bita ai, a lokacin sun sake zama na ƴan kwana biyu a tare, wannan zama da suka yi ne yasa Josephine ta sake kubce mana, dan mahaifiyarku ta sake ɗaurata a kan turbar musulunci sosai, kuma time da mahaifiyar taku zata bar kasar nan, akwai wani littafin adduo'i da ta bawa Josephine ɗin, ta ce kada ta yi wasa da shi, ta rinƙa karantawa, hakan yasa Josephine ta kubce mana mai gabaɗaya, dama ita sau biyu ta taɓa halaktar kungiyarmu, a lokacin muna controlling nata ne, to tun da mahaifiyarku ta bata wannan littafin, sai muka rasata, wannan dalilin kuma yasa da William namu dake wajen ku, da kuma Herry basu kaunarta, sun tsaneta sosai, saboda idan ta kusancesu, za su iya konewa, William dake wajenku mun sanya shi ya reneku kamar uba, sai dai mun sanya shi ya cusa maku tsanar Josephine ɗin, dan saboda kada ku kusanceta ta gaya maku gaskiya, bamu son ku zama Musulmai, idan kuka zama hakan za'a sami gagarumin matsala, kuma ita Josephine musulmace, to kusantarta a gareku babban haɗari ne a garemu, hakan yasa muka shiryawa William abin da zai gaya maku yasa ku tsaneta, da Josephine ɗin ta fahimci hakan, sai ta yi amfani da wasu abubuwa nata na tsafi da ta koya daga wajen wata kawar mamanku mai su na Cherish yar kasar China, kasan chinawa da iya tsafi, to ita ma Cherish ɗin ta iya, sai ta koyawa su Josephine, mahaifiyarku dai ta ce bata son koya a lokacin, dan babu kyau, ita kuma Josephine ta ce zata koya dan zai yi mata amfani, ai kuwa ya yi mata amfani, dan lokacin da ta farga muna son cutar da rayuwarku, mu tauye ku, bamu son gaya maku gaskiya, sai ta yi ƙoƙarin zuwa ta yi magana da kai, a lokacin kana da 15 years a duniya, amma saboda already William ya cusa maku tsanarta, sai kaki ka saurareta, har ma kayi yunkurin kasheta, to data ga hakan, sai ta fahimci me matsalar, shi ne sai ta yi amfani da ɗaya daga cikinku, wanda kuma mun rigada mun fara yin tsafi da shi a baya, wato Michael, sai ta yi amfani da shi da nata tsafin da ta koya a waje Cherish, sai tana baku kariya sosai, abin ya ɗaga mana hankali matuka, sai muka yi ƙoƙarin kasheta kawai mu huta, amma muka gagara, da muka matsa ma, sai kungiyarmu ta jijjiga tana neman rugujewa, bamu da zaɓi dole muka hakura muka kyaleta, muka kuma fita harkarku, dan mun lura idan muka matsa zamu iya jawowa kanmu gagarumin matsala, Josephine tana shirya maku abubuwa da dama da zai sanya ku zo in da take, dan ta gaya maku gaskiya, amma sai abin ya ci tura, kun rigada kun tsaneta tun farko, shi ne yasa komai zata yi ba zaku je in da take ba, sai dai kai Romeo mutun ne mai sa'a, duk shirin da muka yi wa William namu, duk kula da ya yi daku, kaki ka yarda ka ɗauke shi a matsayin uba, ka fi son Josephine sama da shi, tun daga nan muka gane cewa kai ɗan baiwa ne, kuma idan bamu yi da gaske ba, zaka iya kawo mana gagarumin matsala, mun yi niyar juyar maka da tunani sosai, sai wani gagarumin aiki ya taso mana a kungiya, hakan yasa muka mai da hankulanmu a kan aikin, kafin mu dawo shi ne muka tarar ka musulunta, abin ya yi mummunar ɗaga mana hankali, mun shirya maku abubuwa da dama da baki ba zai faɗe shi ba a kan kada ku kusanci musuluncin nan, amma mun rasa ya aka yi ka musulunta, abin fa ya jijjigamu ba kaɗan ba, daga nan muka fara neman ta yanda za'ayi mu kaika kasa koma ta yaya ne, dole mu kasheka dan zaka iya zama mana babban baraza wanda baki ba zai iya fadarta ba, Amma mun kasa yi maka komai, saboda taimako da kuke samu daga wajen Josephine da kuma mahaifiyarku, duk da bata a tare da ku, amma kullum sai ta yi maku addu'a, wani lokaci muna ganinta tana rabawa al'umma kuɗi sosai, duk a cewarta Allah ya kare ku a duk in da kuke, sau ba adadi muna kawo maku hari dan mu kasheka, amma Josephine tana shiga tsakaninmu da ku ta hanyar Michael, to a yanzu ne muke ganin mun sami dama da zamu kaika kasa ta hanyar matarka da ta kasance ita ce rauninka, a baya bamu iya gane menene rauninka ba, amma a yanzu ya fito karara matarka ita ce rauninka, munsan idan wani abin ya sameta dolenka ka shiga damuwa na wuce misali, idan ka shiga damuwa kuma, hankalin kowa zai karkata a kanka, hakan ne zai bamu damar kasheka cikin sauki ba tare da Josephine ko mahaifiyarka sun shiga tsakaninmu ba, sai dai kuma abin da ya bamu mamaki, duk halin da muka jefa matar taka a ciki, hakan bai sa ka ɗaga hankalinka ba ma bare har ka shiga damuwa, yanzu dai halin da ake ciki Anderson ya ce mu kashe matar taka, yin hakan shi zai sa dole ka shiga damuwar da zai sa hankalin kowa ya dawo kanka, kai Romeo ka bamu ciwon kai na wuce misali, ka sanya mu cikin bala'i ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, shi ne yasa Anderson ya ce mu kasheka kawai, wannan shi ne ɗan takaitaccen abubuwan da suka faru, saura amsa zaka samu a wajen Anderson.........". Ya kai karshen maganar yana mayar da numfashi.......

Nasan ko a iya haka my readers kun fahimci in da aka dosa, tsayawa nace zan yi dogon jawabi na bada labarin komai dallah dallah ba zai yiwu ba, dan haka ga shi nan a takaice na baku ta yanda zaku gane in da aka dosa.


Nisawa Lion ɗin ya yi kafin ya fara magana a nutse "Ni babu wanda ya kare ni face Allah da ya halicce ni, addu'a kuma bata faɗuwa kasa banza, koda kun sanya na faɗi kasa, to ba zaku iya yi mani komai ba, koda hankalin su Josephine ya bar kanmu, ba zaku iya yi mani komai ba, saboda Allah ne yake kareni ba kowa ba, Allah kuma baku isa ku karkatar da hankalinsa ba, kunsan meyasa cutar Meesha bai ɗaga mani hankali ba? Saboda already nasan Allah yana sane da komai, and them nasa evil eyes suna kewaye da mu, sannan na san so kuke ku ga na shiga ɓacin rai da har zata iya sanya zuciyata ta buga, already na san shirinku, shiyasa ban bari na ɗaga hankalinna ba, kai baka yi mamakin ya aka yi ban tunkari Josephine da wannan magana ba na tunkareku kai tsaye? Saboda already na jima da sanin cewa Josephine musulma ce ba krista ba, kuma a duk lokacin da zan yi addu'a a tsakanin iyayena, a kan Josephine ne kawai nake samun kwanciyar hankali ba William ba, tun daga nan na fahimci William ba shi ne ubanmu ba, shiyasa kaga ni ban kula shi ba, saboda bani da time nasa, yanzu duk ba ma wannan ba, ina son ka gaya mani wani yaro ne kuka sanya a cikinmu time da kuka ɗauki cikon TRIPLETS nawa?!".

"Yaron da muka sanya a cikinku muka ɗauki wancan ai ɗayan ku ne!". Ya bashi amsa yana wani irin jan numfashi tamkar wanda aka shake yake ƙoƙarin fito da numfashin nasa.

"How comes zai zamana ɗayanmu? Ban gane ba".

"Romeo kamar yanda na gaya maku ɗayanku ne, hakan yake, ku ba TRIPLETS bane, QUADRUPLE (Ƴan huɗu) ne Aisha ta haifa, to dama kasan ɗanta na fari ta ce ta bamu, kuma na gaya maka uwargijiyarmu bata karɓar ɗan da ba a bayar da shi ba, a lokacin da mahaifiyarku ta haifeku, sam bata a cikin hayyacinta, kuma a gida ta haihu ba a asibiti ba, dan ta ce ba zata je asibiti ba, sai dai a ɗebo mata likitoci a gida, Cherish ce ta jagoranci likitocin da suka karɓi haihuwar tata, so a lokacin mun yi amfani da Cherish ɗin da Josephine ne muka ɗauki yaro ɗaya, dama kasan idan aka haifi TWINS, TRIPLETS or QUADRUPLE ana ɗaurawa wanda ya fara faɗowa duniya wata ƴar agogo launin fara a hannu, alama ce da take nuna shi ne babba, shi ma na biyu haka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login