Showing 177001 words to 180000 words out of 270744 words

Chapter 60 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4645

ta yi, sai zare idanuwa take yi. Matsowa kusa da table ɗin nata Lion ya yi, cikin tafasar jini ya ɗago da idanuwansa da suka yi jajir, ya saukesu a kanta, fuskarsa tamkar wanda aka aikowa da sakon mahaifiyarsa ta mutu, jikinsa har wani irin tsuma yake yi, kansa na wani irin sara mashi, yanzu ko ba'a bashi amsa ba ya sami amsarsa, domin wannan likitan da ya shigo yanzu ba kowa bane face ainahin Dr William, kuma ga dukkan alamu mijin Cherish ne, a yanzu komai ya bayyana, abu ɗaya Lion yake son sani, tayaya aka yi hakan?!! Shi dai yasan Dr William a wajen matsafan can yake, to ya aka yi ya dawo wajen su Cherish? Shi fa Lion dama ya zo bincike ne a kan Cherish ta gaya mashi ina ne gidan tsafin kakan nasu, dan a binciken da ya yi tana da masaniyar in da gidan yake, kuma tabbas before ta taɓa aiki da su, bai taɓa kawowa ransa Dr William yana tare da ita ba, to ya aka yi hakan?!!.

"How!!! How you did all this?!! How Cherish?!!!" Cewar Lion ɗin, ya faɗa cikin ɗaga murya.

Tsawa Dr William ɗin ya daka mashi a kan waye shi? Kuma waye ya bashi dama ya shigo cikin office na matarsa ya yi magana da ita? Har kuma ya ɗaure mashi yaro da kyalle?.

Wani irin mahaukacin tsawa Lion ɗin ya dakawa Cherish ɗin har sai da ya sanyata ta buɗe baki babu shi, sam bai bi ta kan Dr William ɗin ba, yanzu daga bakin Cherish yake son jin magana, shi kuma sir Arvin yana ta ƙoƙarin kwance hannunsa dan ya yi faɗa da Lion ɗin a kan iyayen nasa da yake ƙoƙarin cinwa zarafi, duk cikinsu an rasa wanda zai iya kiran security's, da alama duk jini ne yake fusgarsu yasa suka kasa kiranwa Lion ɗin security's.

Murya na kerma Cherish ɗin ta ce zata gaya mashi gaskiyar abin da ya faru, ya zauna. Cikin tsawa ya ce mata ba zai zauna ba, babu ruwanta da shi, kawai ta gaya mashi gaskiya ko kuma yanzu ba sai anjuma ba ya kasheta har lahira!!.

Cikin sauri Dr William ya tambayeta wai wanene Lion ɗin nan? Daga ina ta san shi?.

Ɗaga wa Dr ɗin hannu ta yi, alamar ya yi shiru kawai su saurareta su ji.

Shirun suka yi, suna sauranta, ita kuma zama ta gyara tare da fara yin magana kamar haka.

"A takaice dai tun muna one hundred level a school namu Harvard university Washington DC nake tsananin son Dr William, sai dai shi baya kula kowa, tsoronsa ma nake ji, because he is a dangerous boss, ba shi da sauki ga zafin rai, duk wanda ya bi ta hanyarsa ma take shi yake yi ya wuce, ina tsananin tsoronsa da yasa ban iya bayyana mashi soyayyata ba, muka cigaba da tafiya a haka har na haɗu da wata friend ɗina ƴar kasar Russia mai suna A'isha (gwaggo kenan, dan su ainahi basu san gwaggo tana da alaƙa da Nigeria ba, dan duk takardun makarantarta ya nuna daga kasar Russia ta fito, idan baku mance ba bata yi zaman Nigeria ba, so takardan ɗan kasa da komai nata na Russia ne, shiyasa suka san ita ƴar Russia ce kasarsu Naurat kenan, idan baku manta ba ita ma gwaggo ta faɗa lokacin da suka haɗu da fake William, ta ce mashi dama baka san ni ƴar Nigeria ba ce ko? So basu san tana da alaƙa da Nigeria ba sam, haka zalika a yanzu Cherish bata san Lion ɗan gwaggon bane, yanzu labari take basu ba tare da tasan waye shi ba, fatan kun gane?.) Mun yi ƙawance mai nisa tare da A'isha, ina sonta sosai, saboda tana da kirki, kuma in the first place da gaske muke ƙawancen namu, da gaske nake sonta har cikin ra'ina, shigowar Dr William rayuwarta ne yasa na tsaneta, saboda ina son Dr William tun kafin A'isha ta san shi, shi kuma sai ya zo ya fara sonta, amma haka na danne na jure muka cigaba da tarayya da A'isha ba tare da na nuna mata cewa ina son Dr ba, na yi ƙoƙarin cire Dr a ra'ina, amma abin ya ci tura, na kasa, saboda ina son shi da gaskiya, wani abin haushinma shi ne, son nashi karuwa mani yake yi a kullum, hakan yasa na fara tunanin kashe A'isha, sai dai ban kai ga aiwatar da hakan ba suka yi aure da Dr kuma iyayen Dr suka mutu, wannan dalilin yasa na ɗan dakata da shirin kasheta da nake yi, muka yi zama a haka tsawon watanni kafin na zo nan kasarmu hutu, to a nan ne na sanar da auntyna halin da ake ciki, sai ta ce to na juyarwa da Dr ɗin tunani ta yadda zai tsani Aishar mana kawai, ba sai na kasheta ba tun da nace ina sonta, hakan tasa na ɗauki shawarar aunty na cusawa Dr tsanar A'isha, time da na koma hutu na sami A'ishan da Dr sun yi faɗa har sun raba gida, a lokacin har A'isha ta ce ba zata kyale shi ba sai ta kashe shi, saboda ya ci amanarta, ga ciki a jikinta ya barta da shi, na rinƙa bata hakuri tamkar ban san komai ba, alhalin kuma nasan komai, so in takaice maku labari ban san ya aka yi uncles ɗin Dr suka san cewa na tsani A'isha ba, ina zaune a gidana uncle na Dr wani wai Anderson ya zo gidana a daddare, to a nan ne suka bani aikin na ɗaukewa Josephine hankali ta dai'na ibada ita da A'ishan na tsawon awanni, saboda zasu yi amfani da hakan su juyarwa da Josephine tunani, ita kuma A'isha zasu sanyata ta amsa da bakinta ta bada ɗan da zata haifa domin su ɗauki fansar jinin Roshan da Dr William ya salwantar, suka yi mani alkawarin zasu bani Dr William idan na yi masu hakan, ni kuma ina son Dr sosai, dan haka sai na yi iya kan ƙoƙarina na aikata abin da suka ce, bayan sun juyarwa da Josephine kwakwalwa, suka sanyata ta sa A'isha ta bada ɗan da zata haifa da kanta, (Kunsan labarin yadda gwaggo ta kare da Dr William, so ba sai na sake maimaita shi ba, dan haka zan tsallake.) So a takaice bayan A'isha ta haihu sun ɗauki yaron, sai suka ki cika mani alkawarina da suka ɗauka mani na bani Dr William, sai suka ce mani ai shi ma mai laifi ne, dan haka kashe shi zasu yi, shi ne ni kuma na gwada masu cewa duk duniya babu in da ya kai ƙasar China iya tsafi da makirci, na yi wasa da hankalinsu na ra'ina masu wayon da har yanzu basu iya gane gaskiya ba, na yi amfani da tsafin kanana ni ma na shiga har cikin Daular tasu na ɗauki ainahin Dr William na sanya masu na karya, har zan tafi sai na kalli ɗan A'isha suna ƙoƙarin yin tsafi da shi, shi ne shi ma na ɗauke shi na yi amsani da tsafina na basu wani yaro na karya, abin da yasa na ɗauki yaron kuma, saboda da iya gaskiyata ina son A'isha, kawai soyayyar Dr William ce ta rufe mani idanu yasa na tsaneta, amma da na san na sami Dr, sai na ɗauko ɗan nata na rike, daga nan muka dawo ƙasar nan China da zama, na shafewa Dr William tunanin kowa a rayuwarsa sai ni da ɗansa kuma ɗan A'isha wato Arvin, mu biyu kawai yake tunani, dama already mun gama karatu, sai na buɗe mana karamar hospital kafin muzo mu boɗe babban nan da kuɗi ta zauna, mun yi aure da Dr William kuma mun haifi yara biyu, da Handsome da Pinky, su ne yaranmu, shi kuma Arvin ɗan A'isha ne, amma bai taɓa sanin cewa shi ba ɗana bane, saboda na rike shi da amana, a kullum ina jin zafin cin amanar mahaifiyarsa da nayi hakan yasa na rike shi da amana ko zan goge zunubina dana aikata, su Pinky basu san shi ba ɗana bane, kuma tun daga lokacin ban sake jin labarin A'isha ba, su Josephine duk na rufe babinsu, muna rayuwarmu cikin tsantsar farinciki da kaunar juna, Dr William ma ba ya iya tuna kowa sai mu, saboda na juyar mashi da kwakwalwa, har yau yanzu da nake yi maka magana su His Excellence basu iya gane cewa na ɗauki Dr William da kuma Arvin na gaskiya na sanya masu na karya ba, dan tsafinsu karami ne, mune iyayensu a tsafi, wannan shi ne a takaice labarin abin da ya faru, amma kai kuma da kake kama da Arvin nawa waye kai?!!". BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE GABA DA GABANTA WAI ALJANI YA TAKA WUTA, GA IYAYEN SU HIS EXCELLENCE A IYA TANTIRANCI.

Ta kai karshen maganar cikin raunin murya.

Haƙiƙa Cherish ta cuci gwaggo, babban cuta mafi muni da ta yi mata ma shi ne yadda ta bar Arvin ya taso a Kriste, kenan daman musulcin karya ita ta yi? Duk dan ta ci amanar gwaggon, duk dan ta sami kusanci da su ta cutar da su, yanzu Arvin yana da 32 years, amma yana Kristen, ta cuci Dr William ta bar shi a Kristen tsawon shekaru bayan ya musulunta a da can baya, ko iya wannan cuta aka barta da shi ta gama cutar gwaggo sosai.

Shiru Lion ɗin ya yi yana tunanin me ya dace ya yi wa wannan shaiɗaniyar? Bawan Allah kullum yana cikin jin bala'in da karamar kwakwalwa ba zata iya ɗauka ba, ya gama jin nasu His Excellence, yanzu kuma ga wani sabo na Cherish, sai kuma waye next? Dole Malika ta ce suna da ciwo a cikin rayuwarsu, ciwo kam babba kuma ba karama ba, bayin Allah, ga uban makudan dukiya, ga mulki, ga isa da izza, komai sun tara, amma suna cikin matsanancin ciwo da tarin tarihi marasa kyau da rashin daɗin ji!!

Shi kuwa Dr William ko kaɗai ma bai iya tuna komai ba, duk wannan labari da Cherish ɗin ta bada, bai iya tunano komai ba, saboda ta juya mashi ƙwaƙwalwar ne, amma shi Arvin ya ji komai, saboda shi babu abin da ta yi mashi, bata juya mashi ƙwaƙwalwa ba, kawai dan yana jariri ta ɗauke shi ta rike shi har ya girma ne yasa yake ɗaukarta a uwa, amma ba abin da ta taɓa daga jikinsa.

Dan haka ya ji komai, a yanzu ya ji ba ita ta haife shi ba, saura Dr William...... Yau ake yinta gaskiya, TRIPLETS gidan surprise, yau kuma kun ji ta in da muka juya, gidan cakwakiya gidan ruɗani, waye ya taɓa tunanin Dr William yana ƙasar China? Waye ya taɓa tunanin su Lion suna da wasu ƴan uwa, Arvin, Handsome da kuma Pinky? Tun da kuka fara karatun littafin TRIPLETS waye ya taɓa wannan tunani? To dai ga shi yau gaskiya ta fito cewa su Pinky dai ubansu ɗaya da su Lion, tashin hankali da ba'a sanya mashi date! Wannan shiri rikici da cakwakiya!! Kada dai daɗin labari yasa ku manta da cewa kuna karanta wannan daddaɗar labarin ne daga Alkalamin FATEEMA ZAHRA MUSA, A.K.A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA MAI ABIN BAN MAMAKI 🤙, zan fa tashi kanku a next book na ina kara gaya maku, ku shirya da kyau, dan TRIPLETS dai remain few pages mu kai karshensa In Sha Allah ❤️

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



Date: 20/5/2024




E35


Dan haka ya ji komai, a yanzu ya ji ba ita ta haife shi ba, saura Dr William.

Ya jima shiru yana tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kafin ya ɗago kai ya kalleta. "Let's go". Shi ne abin da ya furta mata a sanyaye. Ya kai karshen maganar kuma tare da juyawa ya kwance wa sir Arvin hannayensa da ya ɗaure mashi, sannan ya juyo da kallonsa a kan Dr William da yake tsaye yake binsu da kallon kawai.

"Before we go, I want to know who are you?". Ta faɗa tana mai dafe sai tin zuciyarta, dan a tsananin tsorace take, tana tsoron ta ji cewa Lion ɗan gwaggo ne, duba da yanayin uban kamanin nan da yake a tsakaninsa da sir Arvin, idan har ya zamana da gaske ɗan gwaggo ne kamar yadda take tunani, to ta san ba makawa sai ya hukuntata.

Ko kallon in da take bai sake yi ba, dan wani haushinta ma na musamman yake ji, yadda ta bar mashi ɗan uwa ya taso a Kristen, ta mayar mashi da mahaifi Kristen, bugu da kari ta raba zuciyar masoya, ta raba gwaggo da mijinta, sannan ta rabasu da iyayensu, basu ta so da ko guda ɗaya daga cikin iyayen nasu ba, ba uwar ba ba uban ba, kuma kaso tamani cikin ɗari na laifin ita ta aikata shi, domin da bata shiga tsakanin Dr William da gwaggo ba, wlh su Anderson basu isa su rabasu ba, basu isa su shiga tsakaninsu ba, saboda idan suna haɗe da kai, suna ibada sosai, to fa babu abin da ya isa ya rabasu sai mutuwa, shiga tsakanin nasu da ta yi ne, yasa suka rabu, bayan sun rabu kuma hankalin kowannansu a tashe, saboda suna son juna, dole damuwar da suke ciki ta rabuwar tasa ba zasu rinƙa ibada yadda ya kamata ba, da wannan dama su Anderson kuma suka fara yin amfani, so idan kuka duba abin kaso tamanin cikin ɗari laifin Cherish ɗin ce, hakan yasa Lion ɗin ya ji sam baya son sake ganin face nata ma a rayuwarsa!!.

Yana kwance sir Arvin ya miƙe tsaye tare da fara bin Cherish ɗin da kallo, yana mamakin yadda ta zauna ta zayyano waɗan nan bayanai dallah dallah kamar wadda ta aikatasu a yanzu, tsawon shekaru 32 bata mance komai ba, tsabar ita da kanta ta san ta zalinci mutane dayawa, wannan akwai mai bakar zuciya!.

Kasa ce mata ko uppan ya yi, saboda wani irin jiri ma da yake gani, kansa yana sara mashi, jin abin yake yi tamkar a mafarki. A hankali ya dawo da kallonsa a kan Lion dake ta faman latsa wayarsa kamar mai tura wata saƙon. Kyawawan laɓɓansa irin na TRIPLETS ya motsa yana son ya wa Lion ɗin magana, sai dai ina, bai kai ga yin maganar ba numfashinsa ta ɗauke diff.

Sulalewa ya yi zai zube ƙasa, tamkar Lion ɗin yana ganinsa, bai bari ya kai ƙasar ba ya taro shi da sauri, sir Arvin ɗin ya faɗa a saman Lion chest nasa. Hankali a tashe Dr William ya nufo wajen yana ambatar ARVIN!!! ARVIN!!! Yana magana ne da ɗaga murya.

Ita ma Dr Cherish cikin ɗaga murya ta fara ambatar sunansa tare da baro in da take da nufin ta kariso wajen. Wani irin gigitaccen tsawa da Lion ya daka masu ne yasa daga Dr William har Dr Cherish ɗin suka kasa karisowa in da yake, ya ce baya bukatar ganin Dr Cherish a kusa da su. Mayar da wayarsa cikin aljihunsa ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya saɓi sir Arvin ɗin a saman kafaɗunsa, kai tsaye waje ya nufa da shi ba tare da ya bi ta kansu ba.

Da sauri suka rufa mashi baya, a haka suka fito harabar katafaren hospital ɗin.

Ganinsu a haka yasa jiga jigan bodyguards ɗin sir Arvin ɗin suka yi sauri fara buɗe masu gidan baya na motocin nasu, a gidan baya na motar sir Arvin ɗin ya kwantar da shi, sannan ya ciro kuɗi dollars in his pocket ya bawa ɗaya daga cikin bodyguards ɗin a kan ya kaiwa mai taxi ɗin da ya kawosa. Lion yana da adalci sosai, baya taɓa tauye haƙƙin wani, baya taɓa tauye wani, a koma ina yake yana ƙoƙarin saukewa kowa hakkinsa da ya rataya a wuyarsa, ya ci sunansa na shi kaɗai ma gayyace mai zaman kanta, yana da tarin abubuwar da kwakwalwar zaratan maza dayawa ba zasu iya ɗauka ba, amma duk da haka baya barin wani abin nasa ta taɓa haƙƙin wani, a kowani hali yana ƙoƙarin yaga dai bai tauye wani ba, shiyasa mutanen U.s suke bala'in son shi, duk da bala'in zuciya, turin kai, zafin rai da kafiya da yake da shi, to yana da adalci sosai na wuce misali.

A haka su Cherish suka shiga wannan motocin, saboda sir Arvin, kai tsaye airport Lion ya ce da drivers ɗin su wuce, dan ya kammala aikinsa, so bai ga abin da zai tsaya jira ba.

Abin mamaki kuma abin al'ajabi shi ne, suna isa airport suka isko gabaɗaya bodyguards na Lion ɗin a tare da su Handsome and Pinky. Sosai Dr Cherish ta yi mamakin ya aka yi su Pinky suka zo airport?. (Ni kuwa na ce mata an gaya maki Lion ɗin wasa ne? Ai bai fito ba sai da ya shirya, kuma kafin ya kai muƙamin da yake kai ya take irinku dayawa, ya takeku kamar ƙuda a gabansa🥱🧐)

Suna isa airport

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login