Showing 105001 words to 108000 words out of 270744 words
kamar yanda babu wanda ya san ya bar Nigeria sai gwaggo, haka babu wanda ya san ya dira a cikin Washington sai his excellence, ko Tga ma sai da ya kusa sauka ne ya kira shi a kan ya zo airport ya ɗaukesa, so babu wanda ya sani.
Kai tsaye gida suka wuce da Tga ɗin, yana zuwa ya yi wanka tare da shiryawa, sannan ya samu ya zauna ya nutsu ya ci abincin mai yawa sosai, tun daren jiya yake jin yunwa, amma wannan matsala ta tsaya mashi a rai da har ta hana shi cin abincin, ji yake yi idan bai dira a cikin Washington ba, to ba zai iya samun sukuni ba, shi ne yasa bai iya zama ya ci abinci a gida Nigeria ba, ya daure sai da ya dawo nan, amma fa ya wahala matuƙa a cikin jirgin, dan ma dai ya yi ta shan Maltina ne.
Bayan ya ci abinci ya ɗan huta na ƴan mintoci, sai ya sake shiri tare da sanya face mask a fuskarsa ya fito, Tga ya so ya raka shi, amma ya hana kowa binsa, ya ce shi kaɗai zai tafi, basu da zaɓi, dole su hakura su kyale shi, amma sam basu so hakan ba, sojojin dake jibge a gidan nasu ba ƙaramin mamakin ganinsa suka yi ba, sun jima rabonsu da shi, sun yi kawarsa.
Da kansa ya ja mota, bai tsaya ko'ina ba sai white house wajen His excellence. Abu ne da kuka riga da kuka sani, baya neman permission a wajen kowa idan zai ga his excellence, kai tsaye ma yau palon gidan ya nufa, sam bai je fadar shugaban kasa ba, da yake already his excellence ɗin ya san da zuwansa, sai ya bar duk abin da yake yi, ya tashi ya je ya samesa a cikin babbar palon nasa kawai.
Sannu da zuwa His excellence ɗin ya yi mashi tare da fara tambayarsa ina su Michael nasa? Dakatar da shi Lion ɗin ya yi, a takaice ya ce mashi "Where is Anderson?"
A tsananin razane his excellence ɗin ya ce "Romeo what... What... What are you saying? Anderson is already died you know that... And now.......". Yana magana yana samun sarkewar word. Dakatar da shi Lion ɗin ya yi ta hanyar ɗaga mashi hannu ba tare da ya barshi ya kammala maganarsa ba, ya sake cewa mashi "Uncle i said where is Anderson?." Tashin hankali!.
"Romeo i told and you already know that Anderson is d......" Katse shi Lion ɗin ya yi ta hanyar ɗaga mashi hannu a karo na uku tare da miƙewa tsaye. Bai sake cewa da shi komai ba ya nufi waje abinsa.
A tsananin firgice his excellence ɗin ya miƙe tsaye, kana ganinsa kaga zallar mara gaskiya, nan take wata zufar wahala da shiga ruɗu ta fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa, idanuwansa duk sun raina fata, ya yi wani wiki wiki da shi, duk wata alama ta rashin gaskiya tare da shiga tsananin tashin hankali sun bayyana a tattare da shi, a kiɗime ya nufi saman bene dan ya kai ga isa bedroom nasa.
Shi kuma Lion yana fita daga gidan bai zame ko'ina ba sai gidan kanin his excellence ɗin, mai sunan Michael kenan.
Yana shiga palon bai sami kowa ba, kai tsaye ya haura sama izuwa bedroom ɗin na kakan nasu, rabonsa da ya taka kafa ya zo wannan gida yau ya kai tsawon shekaru takwas zuwa goma, yanzu ma ko da yazo securityn gidan basu gane shi ba, har sun nemi su ɓata mashi lokaci ta hanyar dakatar da shi, sai da ya cire masu face mask na face na shi sannan suka gane shi, cikin girmamawa suka barshi ya wuce, ya cire masu face mask ɗin ne kuma saboda baya son hayaniya, aikin da ya kawo shi kawai yake da bukatar yi ya fita.
Kamar yanda kuka sanine, dukka ilahirin familyn Roshan shahrarrun masu kuɗaɗene ta duniya, duniya na damawa da su, suna da karfin faɗa a ji a duniya bakiɗaya, ko'ina ka je ka ambaci sunansu an sansu, dan haka shima wannan kakan nasu shahrarren biloniya ne ta duniya, tsayawa zayyana maku kyan gidansa ma ba zai yiwu ba, saboda baki ba zata iya zayyana adadin dukiyar familyn Roshan ba, sai daidai kawai ku ƙawata a ranku.
Lion yana hayewa sama kai tsaye ya nufi bedroom ɗin na kakan nasu, yana shigowa ya fara jin sautin karar tapi rap, rap, rap, tamkar jiransa ake yi ya shigo dama. Ba kowa ne yake wannan tapi ba face kakan nasa, da alama yasan da zuwan nasa, sam Lion ɗin bai yi mamaki ba, sai ma karisa shigo cikin bedroom ɗin da ya yi ba tare da ya jira an yi mashi izini ba.
A bakin katafaren bed na kakan nasa ya zauna tare da zubawa kakan nasa idanu yana yi mashi wani irin kallo wanda babu wani mahaluƙi da ya isa ya fassara ma'anarta sai shi da kansa, kallo ne mai cike da abubuwa da dama a cikinta. Dama daga ganin idanuwan Lion ɗin a halin yanzu kasan da akwai gagarumar abu a kasa.
"Romeo' Romeo Romeo' you are so special our Lion, you really try". Cewar kakan nasa.
Mai da kallonsa a saman yatsun hannunsa ya yi, sannan ya yi kasa da kansa, cikin sanyin murya ya ce "Why uncle? Why? Why you people did all that to us? Ina cikon TRIPLETS na? What happened to him?" And lastly where's Anderson?".
Cike da izza kakan nasa ya fara magana. "Romeo the time is out! And the game is over! Bari ka ji mu bamu ɗauki ɗaya daga cikin TRIPLETS naka haka kawai bisa raɗin kanmu ba, ina son ka sani mahaifiyarku ita ce da kanta ta sadaukar mana da cikonku, ita da kanta ta ɗauke shi ta bayar, meyasa baka tambayeta ba? Ai ita zaku zarga! Mu a tsarin mu bamu amfani da yaron da ba iyayensa ne suka ɗauke shi da kansu suka bamu ba, idan ma mun ɗauki yaron da iyayensa basu bamu ba, to yaron ba zai yi mana amfani ba, dole sai wanda iyayensa suka bamu ne yake yin amfani a wajenmu, kamar yanda William ya gaya maku tun farko na cewa mahaifiyarku ta badaku, to hakan ce gaskiya! Mahaifiyarku ta bada guda ɗaya ne daga cikinku, William ɗin ma bai faɗi dai'dai ba, guda ɗaya ta bada ba dukkanku ba, shi ne yasa Anderson ya ɗauki wanda ta badan, dan haka ka dai'na neman Anderson, dan bashi da laifi, idan kuma kana ganin ba haka bane, ka koma Nigeriar ka je ka tambayi mahaifiyar taka, zata gaya maka ai, kada ka matsa a cikin wannan al'amari, idan ka matsa to ba shakka zaka fara danasanin zuwanka duniya, ka koma wajen mahaifiyarku ta gaya maka gaskiya!!"....................
Tashin hankali, wannan wani irin azababben cakwakiya ce? Gwaggo ce da kanta ta sadaukar da cikon TRIPLETS kenan? Kenan kila shiyasa bata yi maganar yaro ɗaya mai blue eyes ɗin ba tun da ta ganesu? Kenan dama tasan baya nan? Meyasa to zata yi hakan? In dai haka ne kenan tana da sa hannu a ciwon Rimsha? To wai meyasa? Menene dukka wannan abin? Wanene shi wannan Anderson ɗin? Abin da ɗaure kai! Ya ake son Lion ya yi da ransa? Kashe shi suke son yi ne? Wannan bala'i ai sai ta sa zuciyarsa ta buga, uwa fa! Ya ilahi ya lillahi. Ni kai'na PRINCESS TEEMA a wannan gaɓar ka'ina ya yi wani mummunar bugawa, zazzaɓi nake ji my peoples 🥺🥲💔 littafin TRIPLETS wan kill me with more cakwakiya and sarkakiyar.
HAR WA YAU TAKUCE FATEEMAH ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA MAI ABIN BAN MAMAKI🤙❤️ ASHA KARATU LAFIYA🥲💔
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E18
Date: 28/4/2024
*Page na yau ban samu na yi editing nasa yanda ya kamata ba, saboda rashin chaji, so zaku iya samun typing errors, amin afuwa.*
Nisawa Lion ɗin ya yi ba tare da ya ce komai ba, dan yana tattauna maganganun ne ma tukunnan.
"Haƙiƙa babu wasa a wannan al'amari, tun kuna cikin cikinta, tun cikinta yana da wata biyar aduniya ta bayar da ɗa ɗaya daga cikinku, wannan dalilin yasa da aka haifeku muka ɗauki guda ɗayan, wannan zance haka take, kuma duk in da zaka je ka zo hakan ce! Babu makawa kuma babu tantama a cikinta, muna da shaidu a kan hakan, na san dama zaka zo, zaka zo garemu Romeo, saboda tun da ka fara girma muka fahimci ka ci sunanka da WILLIAM ya sanya maka wato Lion, so our Lion already we know that you're special! Hakan yasa muka ajiye maka tarin hujjoji da zaka gansu a aikace, sai dai bamu yi tunanin zaka zo garemu da wuri haka ba, bamu yi tunanin zaka gane mu da wuri haka ba, anywhere mu bamu cutar da ku ba, ku tuhumi mahaifiyarku da kuma Josephine, sune suka yi komai!!".
Haƙiƙa a maganar kakan nasa babu karya a cikinsu, tabbas duk abinda ya faɗa gaskiya ce, gwaggo da bakinta tun cikinta yana da wata biyar, tun bata ma san me zata haifaba, ta bada guda ɗaya, to su kuma basu mantuwa, shiyasa da ta haihu suka ɗauki ɗayan, sai dai da akwai abin da ya saɓa a cikin maganar, wanda kuma dole a wajen Josephine da Cherish ne kawai za'a san ainahin menene wannan!. Wannan shi ne cakwakiya, Lion dai yana tsaka mai matuƙa wuya wanda fitarta sai Allah ya ƙaddara.
Nan ma dai shiru ya yi mashi bai yi magana ba. Gabaɗaya kakan nasa ya shiga ruɗu, saboda yin shiru Lion ba alkhairi bane, sun san shi tun yana ƙarami, idan ya yi shiru, to wani abin yake ƙullawa a cikin ransa, so haka har ya girma, shirunsa musiface a wajen marasa gaskiya masu cin amana da tauye haƙƙin ƴan adam.
Ganin yanda ya yi shirun ba ƙaramar ɗaga mashi hankali ya yi ba, dan haka sai ya sake cewa "Ni zan je office ana jirana".
Ya ɗauki tsawon lokacin da a kallah zai kai 10mins kafin ya sake nisawa tare da ɗago idanuwansa ya sauke a kan kakan nasa, cikin tsananin nutsuwa ya fara magana. "Ni ban tambayeka waye ya baku cikon TRIPLETS da kuka ɗauka ba, ni kawai na ce maka ne ina yake? Me kuka yi da shi? And lastly where's Anderson? Wanda ya baku wannan duk daga baya ne, zamu zo kan zance, for now dai amsa this two questions that i asked you! Where is my TRIPLETS? And where is Anderson?".
"Anderson is already died, you know that, so i don't know what do you want us to tell you again kuma".
Jinjina kai ya yi tare da faɗin "Okey Anderson is already died, wow this is so nice, agreed, amsa me da remaining question, where's my brother?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye.
"Romeo your brother has gone since that time".
Sake jinjina mashi kai ya yi kafin nan ya fara takawa a hankali ya nufe shi, dama yana tsaye ne ta wajen mirror, ba halin yin baya baya, bashi da zaɓin da ya wuce ya tsaya kawai har Lion ɗin ya iso gare shi.
A hankali ya iso in da yake, hannu ya ɗaga cikin nutsuwa ya shafi lallausa kuma jajir ɗin kumatun kakan nasa, cikin sanyin murya ya ce "Okey let me try something, let me send you to the place that you send my brother!". Ya kai karshen maganar yana gangaro da hannunsa izuwa wuyar kakan nasa. Da karfi sosai ya shake ɗan tsohon, ransa a tsananin ɓace over, amma saboda ya gane suna neman hassala shi ne, sai ya ki bari ɓacin ran nasa ta yi tasiri, sai ya danne kawai.
Cikin kwanciyar hankali kakan nasa ya sanya hannu a saman hannun Lion ɗin, tamkar wanda ya kama hannun ƴar baby haka ya ɓanɓaro hannun Lion ɗin daga jikin wuyarsa tare kuma da murɗe ta baya da karfi, nan take yanayin kakan nasa ya fara sauyawa, cikin tsawa da wata iriyar murya wadda da ka ji ta kasan ba nasa bane, dan murya ce ta irin kartin mazan nan, da ita ya dakawa Lion ɗin tsawa, sam Muryar bata da daɗin ji, tamkar an tada injin jiƙa lalatatce.
Ba shakka abin mamaki ne canzawar kaka nasa da kuma irin karfin da yake da shi a matsayinsa na dattijo, sai dai kuma ko kaɗan Lion ɗin bai yi mamakin hakan ba, dan ya san fin hakan ma zasu aikata. Kasancewar yana da ciwo a hannun, sai murɗe mashi hannun da kakan nasa ya yi ta yi mashi muguwar zafi, hanan tasa ya kai ɗayar hannunsa yana ƙoƙarin sake shako wuyar kakan nasa, dan tsananin zafi da yake ji.
Sam kakan nasa bai bari hannunsa ya sake taɓa jikinsa ba, sai ya yi ƙoƙarin haɗe hannayen nasa dukka biyu ya ruke da hannu ɗaya. Da Lion ɗin ya fahimci wannan karfi fa ba na kakansa bane, dan haka yana da kyau su yi fito na fito, idan ba haka ba, idan ya zuba masu idanu to zasu yi mashi illa mai girma. Tuna hakan ne yasa bai bari kakan nasa ya kama ɗayar hannun nasa, sai ya yi ƙoƙarin kaucewa, hakan ya bawa kakan haushi ba kaɗan ba, sai ya yi wani irin kurma kururuwa kamar kukan giwa a dawa, nan take ya canza halittarsa izuwa wata halitta mai matuƙar girman, tana kama da ɓauna, wato saniyar dawa, ga wasu kawo guda biyu a kai.
Ko kaɗan Lion bai ji tsoro ba, sai ma nishaɗi da abin ya bashi, shi da ya yi faɗa da su barbushi jibga jibga mutane masu kama da samudawa, dan haka sai ya gyara tsayuwa tare da dakewa, shi hakan ma ta fi mashi, ya fi jin daɗi su yi fito na fito da su, ya ci ubansu Roshan babu sirki, ya kuma sanyasu su duka su gaya mashi gaskiya!!.
Gadan gadan wannan halitta da kakan nasa ya koma ya tunkarosa. Yana zuwa Lion ɗin ya furta kalmar bismillahi tare da fara kokawa da shi. Sai dai ina ya riga da ya ambaci sunan Allah, babu wata tsafi da zata yi amfani a wajen, haka yasa suna fara yin faɗa kakan nasa ya koma ainahin halittarsa, sarai Lion ɗin yasan da hakan, amma sai bai kyale shi ba, ya jibge shi da kyau da kyau, wani irin wawan mari ya kai mashi a kumatunsa wanda har sai da ya sanya shi ganin wani haske ya gilma mashi ta cikin idanuwansa, bai barshi ya dawo dai'dai ba ya kwashe kafafunsa, sai ga ɗan tsoho ya zube kasa wargajam.
Guntun tsaki Lion ɗin ya ja, ya so ace da matashin mai jini a jika zasu gwabza, dan ya ci ubansa, ya sauke mashi duk wata haushi da yake ji a kansa, ya jibgi banza, amma sai ya zamana da tsoho ne ba matashi ba, wannan tsohon idan ma ya ce zai dake shi, ai sai dai ya karisa gawar da ba tasa ba, dan wannan idan ya yi mashi duka ɗaya lafiyayyiya ba makawa sai dai a ɗauki gawarsa.
Wayar makekiyar Tv dake a ɗakin Lion ɗin ya tsinko, da karfi ya ja har sai da Tv ta faɗo kasa ta tarwatse, ko a jikinsa ya zo ya ɗaure kakan nasa ɗaurin goro, ta baya ya ɗaure hannayen nasa, sannan ya ɗaga shi cancak, bai sauke shi a ko'ina ba sai a saman tsakiyar bed nasa.
Ya sauke shi tare da zama a saman bedside drawer, kasa ya ɗan yi da kansa yana ɗan murza ƴatsun hannunsa, ya ɗan ɗauki lokaci da a kallah zasu kai 10mins kafin ya ɗago kai tare da kai kallonsa izuwa kan ɗan tsohon, a takaice ya ce "Are you ready to tell me the truth or not?".
Murya a tsarke, cike da tsoro ya ce "Zan faɗa maka komai". Yana magana yana zare ash eyes nasa, haƙiƙa ya tsorata na ganin tsafinsa taki yin aiki a kan Lion ɗin, ya ji matuƙar rashin daɗi, sam ba haka ya so ba, ya so ne ya jibgi Lion ɗin har sai ya yi laushi, sannan ya ɗaure shi kansa a kasa kafafuwansa a sama, sai dai bai san cewa ta Allah ba tasa ba, bai san cewa shi Lion ya rigada ya ruke Allah hannu bibbiyu ba, wanda kuma ya ruke Allah, tabbas babu shi babu taɓewa, wanda ya ce Allah shi ne komai nasa, to babu shakka Allah ba zai taɓa bashi kunya ba, Allah zai kula da lamuransa ba zai taɓa bashi kunya ba, ya Allah ka iya mana da iyawarka!.
Jinjina mashi kai Lion ɗin ya yi tare da yi mashi alamar ya yi maganarsa yana jinsa.
"Magana ta gaskiya dai, na farko a nan shi ne, da gaske mahaifiyarku ce ta bamu yaro ɗaya, babu wasa a cikin wannan maganar, shi kuma maganar Anderson, ba shakka Anderson yana raye kamar yanda ka yi hasashe, maganar ɗan uwanka cikon TRIPLETS naka kuma, i don't know har yanzu yana raye or not, wannan