Showing 138001 words to 141000 words out of 270744 words

Chapter 47 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2960

a face nasa har ya kasa hakura gari ta waye sosai ya je ya sayo mata magani, ko daga nan kun san abin ya kai mashi intaha, abin ya wuce misali a wajensa, kofa TRIPLETS nasa basa iya ganewa idan yana cikin damuwa or ɓacin rai ko kuma farinciki, saboda dakiya da juriya irin nasa, amma yau shi ne yake birkice haka, babu shakka abin ya wuce misali, soyayya tabarmar kaya, idan ka iya zama ka ji daɗi, akasinta kama? Kun san sauran.

"Saif nan fa ba U.s bane ba, they didn't open their shop's at this time around, sai irin 8 haka, now is to early ai". Ta kai karshen maganar tana mai kara yin kasa da muryarta sosai, tana yi mashi magana cikin sigar rarrashi da nuna tausayawa tare da tausasawa, dan ya ɗan ji sanyi a ransa, duk da ba ita ta renesu suka girma ba, bata san halinsu sosai ba, amma ta san cewa ba ƙaramin abu bane zai iya sanya jinin Dr William shiga damuwa har haka, bare kuma shi Lion da kusan komai irin na daddyn nasa ya ɗauko, Dr William akwai taurin zuciya na bala'i, to haka Lion ɗin ma yake, sun iya shanye abu.

Shiru ya ɗan yi yana mai cigaba da kallon kasa, kwata kwata baya son su haɗa idanu, duk wani irin yanayi yake ji a jikinsa.

"Kanaji ko Saif? In Sha Allah Meesharka zata samu lafiya, babu abin da zai sameta, yanzu abin da nake so da kai ka nutsu ka kwantar da hankalinka, ka yi mata addu'a, zan je na dubata ne dama yanzu, kada ka damu zata warke kamar ba'ayi ba cikin ƙanƙanin lokaci In Sha Allah". Tana magana tana kallon jikinsa yadda yake wani irin tsuma alamar still dai yana cikin tashin hankali.

Rumgumeta ya yi tare da fara magana kasa kasa kamar mai raɗa "Momma i know kawai kin gaya mani hakan ne dan naji daɗi, i already knew that ko da Meesha zata samu sauki not now, ban taɓa jin daɗi cikin bakinciki ba sai yau momma, ko ba komai yau for the first time a rayuwata bayan TRIPLETS na an gaya mani magana da zai kwantar mani da hankali, a ko da yaushe ina yawan jin Sheikh Sultan yana faɗin duk wanda ya rasa uwa, to tamkar ya rasa komai na duniya ne, komai kuɗinsa komai mulkinsa ba zai taɓa jin daɗi ba idan babu mahaifiya a gefensa, kasancewar ban ma san ya uwar take ba, ban taso da ita ba, sai ina ganin kamar dukka shirmensa kawai yake faɗa, ban taɓa jin ciwon rashinki a tattare damu ba sai yau, am really happy da jin kalamanki masu sanyi a gareni, a kodayaushe idan abin bakinciki ya sameni, sai dai na barshi a cikin zuciyata, dan babu mai iya fahimtarta a duniyar nan, even su Areef ba kasafai suke iya fahimtata ba bare har su gaya mani magana mai daɗi da zai sanya ɓacin ra'ina na wuce, kullum ni kaɗai nake faɗa da zuciyata, a yau ne na gane cewa Sheikh Sultan ya yi gaskiya da ya ce rashin uwa musifa ce, i really love our momma". Ya kai karshen maganar yana kara kwantar da kansa a saman kafaɗunta.

Ko da sunan wasa bai taɓa yin magana mai tsawon haka ba, bai kuma taɓa yin magana makamancin irin haka da wani ba, lallai uwa uwa ce ko da kuwa a kan bola take yawo, Allah sarki bawan Allah dole ma ya zamana yana da zafin zuciya, dole ya zamana yana da taurin rai, dole ya zamana mafaɗaci, a koda yaushe shi kaɗai yake shanye ɓacin rai, bakinciki, damuwa, da komai da komai nasa shi da TRIPLETS nasa, ya shanye bakincikinsa ya kuma shanye nasu Areef, bashi da wanda zai gayawa damuwarsa, already kun sani tun farko shi baya magana, bai saba da kowa ba, TRIPLETS nasa ma iya wasanni na nishaɗi suke yi idan sun haɗu, ga ciwon Aseef, kunsan ba yadda za'ayi ya zauna yana gayawa Aseef damuwarsa, Areef kuma ba zama ma yake yi a gidan ba time ɗin bare ya fahimci shi, kusan za'a ce shi kaɗai yake rayuwarsa ta baɗini, baya shigo da kowa, bawan Allah.

Sosai gwaggon ta ji wani irin mugu mugun tausayinsu ya kara kamata, duk abin da ya faɗa gaskiya ne, ba shakka ya yi ƙoƙarin da sai a tara zaratan maza 100 ba'a sami biyu da zasu iya kamanta abin da ya shanye na tsawon shekaru 25 ba, tun da suka fara girma keman har zuwa yanzu, dama ance babba juji ne, komai a kansa take karewa shi kaɗai, damuwar ciwon Aseef na shawon shakaru shi ya shanyeta a ransa, sau da dama Areef yana jefa shi cikin damuwa, amma haka yake shanyewa kamar ba'ayi ba, ba shakka ya cancaci a yi mashi babbar jinjina.

"Saif bawai kawai ina gaya maka Rimsha zata samu lafiya dan na maka daɗin baki ko kuma na kwantar maka da hankali bane, da iya gaskiyata nake gaya maka In Sha Allah bazata jima ba zata samu lafiya, keep praying for her ka ji my son?". Ta kai karshen maganar tare da ɗaura hannunta a saman lallausan dark black curly hairnsa tana ɗan shafawa.

Shiru ya kwanta, ban da tunanin Rimsha babu wani abin da yake a cikin zuciyarsa, shi kaɗai yasan meyake ji. Cigaba da shafa kan nasa ta yi tana kara gaya mashi kalaman da zasu kwantar mashi da hankali, dan ta lura idan bata yi da gaske ba, to zata zama mai jinyar majinyata biyu, saboda ba shakka idan bata bada himma ta kwantar mashi da hankali sosai ba, zai iya faɗuwa, dan Rimsha ta zama jinin jikinsa, ba zai iya jurar ganinta a cikin wani hali ba, kamar yanda ba zai iya jure gani Aseef ko Areef a cikin wani hali ba, to ita ma hakance a wajensa, ta zama wani ɓari na rayuwarsa, so dole gwaggo ta mayar da hankali sosai, dan kada ta yi jinya biyu.

Ba ita ta kyale shi ba sai da ta ji ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya har sau biyu, alamar ya ɗan samu nutsuwa kaɗan, sannan ne ta raba jikinta da nasa tana mai kara jaddada mashi Rimsha zata samu lafiya nan bada jimawa ba, dan haka ya je ya kwanta ya huta, ya yi barci, saboda daren jiya bai yi ba.

"Momman i can't sleep, bana ma jin barci, zan je garden na ɗan samu hutu ni kaɗai". Ya yi maganar cikin wannan nutsuwa tasa, har gobe akwai zallar madarar izza a voice nasa, da alama hakan a cikin jininsa take.

"Tom shikenan bari ni kuma na kara duba Rimshar, by 8:00 dai'dai sai ka zo ka saya mata abubuwan da ake buƙata ko?".

Jinjina mata kai kawai ya yi tare da wucewa ya nufi stair case dan ya sauka kasa. Ita kuma ta wuce ta nufi bedroom nasa dan ta duba jikin Rimshar.

Yana shiga garden ya zauna a saman sofa mai zaman mutun uku, shiru ya jingina kansa da jikin sofar yana tunanin yanda ya yi wa Meeshansa kaca kaca, abin ya ɗaga mashi hankali. Wayarsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira, ko bai duba ba yasan su Areef ne, dan haka suke, idan basu a tare, da gari na waye zasu kira juna video call dan suka ga juna, tun suna ƴan samari 12 to 13 haka suke.

Nisawa ya yi kafin ya fito da wayar daga aljihunsa. Su ɗin ne kuwa suke kiransa, kuma video call ne. Shiru ya ɗan yi, ba dan TRIPLETS nasa bane, da ba abin da zai sanya ya ɗauki kiran wani a wannan halin da yake a ciki, amma su sun kasance bugawar zuciyarsa ce, dole ya ɗauka dan ya kalli kyawawan face nasu, yana kewarsu shi ma.

Picking na call ɗin ya yi cikin nutsuwa. Areef ne kaɗai kwance a saman tampatsetsiyar lallausan bed nasa, ya tada kai da lallasan pillow, daga shi sai short, babu riga a jikinsa, ya sakarwa Jehan wannan Lion chest nata da zata rinƙa kwanciyar a buɗe, ko singlet bai saka ya rufe mata kayanta ba, ya saki gashi har tsakiyar bayansa, dama kunsan shi a cikinsu dukka ya fisu tara gashi, nasa ta kai har tsakiyar baya, while na Lion a iya bayan wuya take, shi kam Aseef ma ai dukka yake datse kayansa, baya son takura ya ce.

"Good morning our Lion". Ya yi maganar voice nasa cike da zolaya.

Lumshe idanuwa Lion ɗin ya ɗan yi tare da buɗesu a kan wayar tasa. "Where is Heartbeat?". Ya faɗa a sanyaye. "Kai da ka sani, yana barci mana, time na tashinsa bai yi ba".

Jinjina kai kawai ya yi, yau ji yake yi ma magana ta zame mashi tamkar maɗaci, sam bai son motsa laɓɓansa, dama shi ba gonin yin magana bane, sai ta kuke mashi yake buɗe baki ya yi magana, da ido ma ya isa ya amsawa mutun, bare yau da yake cikin wannan hali, ai sai a slow kawai.

"Ka je wajen Sheikh Sultan ɗin ne?". Cewar Lion ɗin.

"Wlh Lion baka da gaskiya, ji idanunka kamar na momma a yau, duk sai wani kawar da kallonka kake yi, ni nasan dole akwai wani abin da ka aikata, faɗa mani me kayi?". Cikin zolaya ya yi maganar, dama already kun san halinsa sarai da iya zolaya da neman tsokana.

"Areef zaka bani amsa nane ko kuma dai you're asking me this silly silly questions marasa amfani?".

"I can't amsa you har sai nima ka gaya mani me ka aikata, where is Rimsha and momma ma first? I asked Jehan about Rimsha, she said she don't know where is she, to kai faɗa mani ina take, dole kai ka sani". Areef akwai neman magana ta karshe, daga kansa an rufe kofa in dai wajen neman tsokana ne, har da yi wa Jehan karya, duk dan ya sanya Lion yin magana, Jehan ɗin da ko tashi daga barci bata yi ba, amma dan neman tsonana wai ya tambayeta ina Rimsha? Neman tsonace kawai, ai yasan tun da Lion ɗin yana gari tare zasu kwana da Rimshar, ba da Jehan zata kwana ba, sai ya yi kamar bai san hakan ba, dan shegen iya tsokana

"Areef wai ni kam am i play with you? Am I your mate?". "Yeah you're my mate, and we're playing together mana, what's next?".

Ji Lion yake yi tamkar ya damko shi ya makure shi, amma ba hali, da'a tare suke, da ba abin da zai hana shi yau bai shake shi ba, a kage yake da ya ji amsa, amma tsabar iskanci irin na Areef yaki bashi amsar abin da yake son ji, yana son jin ya suka yi da Shaikh Sultan ne, amma ya tsaya sai tsiya yake yi mashi.

"Lion do you now something?".

Ko kallon in da yake Lion ɗin bai yi ba, bai kuma da niyar sake tanka mashi.

"Am seeing your face like wanda ya kwana da mace suna chaskalen ma'aurata, anya kana da gaskiya kuwa? Tell me the truth ba dai chaskale mana our Rimsha ka yi ba?". Ya kai karshen maganar yana karewa face ɗin Lion ɗin kallo. Areef akwai kwakwalwa sosai, sarai ya gane matsalar Lion ɗin, kada ku manta shi ya zauna da mutane daban daban, kuma ya zauna a wajaje daban daban, tun kallon farko da ya yi wa ɗan uwan nasa ya fahimci dole akwai wani abin da ya aikata, musamman yanda damuwa ta bayyana a saman face nasa, ai dole kowama a wannan gaɓar ya gane cewa e lallai Lion yana a cikin damuwa.

Ɗago idanuwansa ya yi izuwa saman screenshot ɗin wayar, calmly ya ce "Ka kammala aikin da na baka ne?". Gabaɗaya Lion so yake yi ya canzawa Areef ɗin topic na hiran, dan baya jin kamar zai iya gaya mashi ga abin da ya faru, sai dai shi kuma Areef ɗin ya matsa mashi da tambayar sai ya gaya mashi meyafaru da shi haka.

Bashi da zaɓi dole ya gaya mashi ga abin da ya faru kawai. A wani irin dubu ɗari Areef ɗin ya miƙe zaune, wani irin zaro idanu waje ya yi, ya rasa me ma zai ce da Lion ɗin.

Wani irin kallo Lion ɗin ya wurga mashi, irin kallon nan na lafiya kake wani gani na haka? Irinsa ya wurga mashi da waɗan nan dara daran idanuwan nasa.

Marairaice murya Areef ɗin ya yi tamkar wani maraya yana cikin tsaka mai wuya ya ce "Allah sarki our Rimsha". Abin ma gwanin ban dariya, dan da iskanci Areef ya faɗi wannan kalmar.

Ganin serious ɗan uwan nasa yana a cikin damuwa ne yasa ya kawar da duk wata shiririta tare da gyara nutsuwarsa ya tattare hankalinsa wajen guda, cikin sanyin murya ya ce "Sorry our Lion, ba laifinka bane, kuma ba laifin Rimsha bane, dama kowace mace sai ta fuskanci makamancin haka, amma ba irin naka ba, naka ai ya wuce tunani, fatana dai yanzu Allah ya bata lafiya yasa kuma mun samu baby's, yasa kwallo uku kamar mu ka zura a raga........" Kasa karisa maganar ya yi sakamaƙon wani irin kallo wanda ya fi harara kuna Lion ɗin ya wurga mashi, dan kawai ya yi maganar babys, idan baku manta ba shi fa Lion baya son yara, sam sam baya son hayaniyarsu ko kaɗan, so baya shiri da duk wanda zai yi mashi addu'ar samun yara, a tunanin Areef tun da yanzu sun kai ga yin aure, wata kila Lion ɗin ya sauya yana son yaran a yanzu, bai san cewa babu abin da ta sauya ba, har yanzu yana a kan bakarsa na baya son yara. Tashin sense lallai akwai kura ba kaɗan ba.

"Sorry our Lion ba baby's nake son cewa ba, mantawa na yi, sai ya yi mani kamar da Aseef muke hira ne".

Shiru ya yi bai sake tanka mashi ba, dan shi kaɗai yasan me yake ji. Sosai Areef ɗin ya yi ta rarrashinsa tare da kwantar mashi da hankali, har karfe 8 ya cika, sannan ne ya miƙe tare da yi wa Areef ɗin sallama, ya katse kiransa ya nufi cikin gida.

Kai tsaye bedroom nasa ya nufa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, a nan ya isko gwaggon a zaune kusa da Rimshar, har yanzu dai Rimsha ko motsawa bata yi ba.

Wajen bed ɗin ya kariso, barka da safiya ya yi wa gwaggo, yana magana yana kallon face ɗin Meeshan tasa, har yanzu dai tana nan yadda take ba sauyi.

Miƙa mashi takardan duk abin da zai sayo mata ta yi, tana mai karfafa mashi gwiwa tare da kwantar mashi da hankali, ta lura zai iya jure komai na rayuwa, amma banda damuwar TRIPLETS and Rimsha, daga kanta ita gwaggon, TRIPLETS nasa da kuma Rimshar sune rauninsa a rayuwa.

Karɓa kawai ya yi ya fito waje, kai tsaye bedroom na uncle T ya nufa, dan su tafi a tare. Ita kuma gwaggon mikewa ta yi ta fita izuwa nata bedroom ɗin, saboda gari ya waye tasan yanzu Jehan zata zo ta fara zuba mata shagwaɓa, so bata son su san abin da ya faru da Rimshar ma bare su kuma su tsorata.

Tana shiga bedroom nata Jehan ɗin ta shigo bakinta ɗauke da sallama tana aikun turo baki, kayan barci riga da wando dogaye ne a jikinta, launin pink color masu matuƙar kyau, ga cup mai bala'in kyau a hannunta,

A dubu ɗari gwaggon ta ce "Jehan mekike sha?". Ba tare da ta kalli in da gwaggon take ba ta bata amsa da "Abin da kuka haɗa mana nan ne, ba dama kafin mu ci komai da safe shi muke fara sha ba? Wai gwaggo ko dai kin fara tsufane waɗan nan idanun naki manya manyan kamar na Dr Salman ɗin nan sun dai'na gani? Ka gansu manya manyan da su kuma ace baki gani sosai, sai na kai ki asibiti". Ta kai karshen maganar tare da hayewa bakin bed ta zauna tana ƙoƙarin kai cup ɗin ɗan bakinta.

"Ke dakata tukun nan". Gwaggo ta faɗa a hanzarce. Ɗago fararen idanuwanta ta yi tare da saukesu a kan face ɗin gwaggon, fuskarta cike da mamakin meyasa ta dakatar da ita daga sha kuma.

Zama a gefenta gwaggon ta zo ta yi, cikin sanyin murya ta ce "Jehan kada ki ɓoye mani, faɗa mani gaskiya, shin kun taɓa kwanciya ta sunnah da Areef ne?".

A ɗari ta zaro ido tana kallon gwaggon, kafin kuma ta tuntsure da dariya tana faɗin "E lallai yau dai gwaggo bake bace, Queen ta canzo mana ke, au ashe Queen ɗin ta mutu ma, yanzu gwaggo kawai sai ki tambaye ni?".

Harara gwaggon ta wurga mata kafin ta fara magana "Ke bada wasa nake yi ba, faɗa mani gaskiya yanzun nan".

Girgiza mata kai ta yi tana bata amsa da "A'a bamu taɓa ba......."
Ai tun bata kai karshen maganar ba gwaggon ta kwace cup ɗin daga hannunta tana faɗin "Daga yau kada ki kara shan wannan abin, komai ma da muka haɗa kada ki sake sha, maza jeki duba idan Akila ta tashi daga barci ki kira mani ita".

Mamaki sosai ne ya bayyana a saman face nata, tambayar kanta take yi shin meyasa gwaggo zata hanata sha? Ita da kullum take takura masu a kan su sha maganin nan sosai, kada su tsallake kona minti ɗaya, shi ne yau kuma zata hanata? Abin da mamaki.

"Akila nace ki kira mani ne ko kuma tunani na ce ki shiga yi?". Turo baki ta yi kafin ta ce "Gwaggo Akila fa bata tashi daga barci ba, kin sani sai almost 12 take tashi fa".

Da Akila da Aseef dai sarakan barci ne, su ne last na tashi barci a gidan, da daddare kwana suke yi manne da waya suna kashe juna da kalaman love, duk iya soyayya na Areef ya basu hanya, dan fa su macewa juna suke yi, sai su kwana makale da waya, sai anyi sallar asuba suke samu su kwanta, shi ne idan suka fara barci sai 12 na rana, suna tashi kuma ko abinci basu nema suke sake makale waya, wani lokaci ma suna wayar video call suna breakfast, Aseef and Akil halinsu babu wani banbanci, duk zani ne ta tattada muje, shagwaɓaɓɓune na gasken gaske, na kin karawa, haka zasu yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login