Showing 180001 words to 183000 words out of 270744 words
ɗin ya fito tare da sake saɓar sir Arvin ɗin a kafaɗarsa, cikin jet nasa ya nufa da shi, da mamaki su Cherish suka tsaya a baya suna kallon ikon Allah.
Jim kaɗan ya fito daga cikin jet ɗin bayan ya kwantar da sir Arvin a saman luntsuma luntsuman sofas dake a ciki. A kofar shiga jet ɗin ya tsaya tare da yi wa Handsome alama da hannu a kan yazo. Gabaɗaya Handsome ɗin yana ruɗe, sai wani kallon Lion ɗin yake yi, saboda tsananin kamar da ya gani na sir Arvin, ita kuwa Pinky tana ganinsa ta taho da gudu ta rungume shi tana ambatar sunan sir Arvin, dan a tunaninta sir Arvin ne.
Hannu Lion ɗin ya kai ya ɗauketa cancak tamkar yadda sir Arvin ɗin yake yi mata, a saman Lion chest nasa ya ɗaurata, ba tare da ya kallin face nata ba ya juya tare da yi wa su Dr William dake tsaye alama da hannu a kan su zo, dai'dai lokacin kuma Handsome ɗin ya kariso wajen hannunsa ɗauke da password nasu shi da iyayen nasa, dan Lion ɗin da ya tura a ɗauko mashi su, sai ya ce bodyguards ɗin nasa su sanyasu su taho da password ɗin su gabaɗaya, dan U.s zasu wuce, bai ga dalilin zamansu a ƙasar China ba, ya gama aikin da zai yi, ba mai sake dakatar da shi kuma.
Sumbata Pinky ta kai mashi a kumatu tana tambayarsa yau ma yawo zasu je wata kasar kamar ranar? Duk a tunaninta sir Arvin ne, sai da Lion ɗin ya juyo da face nasa tare da kallonsa a kanta da kyau, sannan ne ta zaro blue eyes nata waje sosai, dan ta ga ba sir Arvin bane, dama na gaya maku in dai ka yi wa ɗaya daga cikinsu farin sani, to zaka iya banbantasu, dan suna da banbanci, ita kuma Pinky ai bama wanda ya kaita sanin sir Arvin, dole ta gane ba shi bane.
Ƙoƙarin sauka daga jikinsa ta yi, ta tsorata sosai har jikinta ya fara kerma, shiru Lion ɗin ya ɗan zuba mata idanu ba tare da ya ce mata ko uppan ba, sannan kuma bai sauketa ba, sai mutsu mutsu take yi tana son sauka daga jikin nasa, dan ta tsorata, kallon yadda jikinta yake kerma ya yi kafin ya mayar da kallonsa a kansu Dr William da suka iso wajen a yanzu, hanya ya basu a kan su wuce su shiga cikin jet ɗin da sauri kada su ɓata mashi lokaci.
Hannu Pinky ta kai ta ƙanƙame Handsome dake a kusa da Lion ɗin, kuka ta fara yi tana faɗin "Please Yah Handsome who's this man? Where's my baby?". Dama mafiya yawan lokuta baby take cewa sir Arvin.
Kasa bata amsa Handsome ɗin ya yi, saboda shi ma dai bai san wanene bane, abin da zai iya cewa kawai shi ne yana jin Lion ɗin tamkar ɗan uwansa sir Arvin, shi ne kawai.
Ganin tana kuka ne yasa Lion ɗin ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman kyawawan lips nasa yana yi mata alama da ta yi mashi shiru, ya yi hakan kuma ba tare da ya sauketa daga ɗaukarta da ya yi ba. Tsananin tsoronsa yasa ta nutsu tsit ta dai'na kukan da take yi, bata da zaɓin da ya wuce ta kwantar da kanta a saman kafaɗunsa duk da tana tsoronsa.
Hannu ya sa ya nunawa Handsome ɗin ma cikin jet ɗin a kan ya wuce ciki su tafi. Ba musu ya shiga ciki tun da ya ga su Dr William ma sun shiga. A takaice sai da duk suka gama shi, Lion ɗin shi ne na ƙarshen da ya shiga, sannan aka rufe jet ɗin.
Zama ya yi a saman nasa luntsumemiyar sofar ba tare da ya sauke Pinky ɗin daga jikinsa ba, duk da mahaifiyarta ta cuce su, hakan bai hana ya ji yana kaunar Pinky ɗin da Handsome ba, saboda ba laifinsu bane, laifin wani baya shafar wani, bare kuma Pinky yarinyar akwai shiga rai ita ma kamar Rimsha.
Daga Dr William har Dr Cherish ɗin sun kasa iya nufar in da sir Arvin yake a kwance a sume, saboda tsoron Lion suke ji sosai, suna son duba lafiyar ɗan nasu su ga menene yasa ya suma? Amma sun kasa iya koda ƙwaƙƙwarar motsi, haka zalika shi ma Handsome, yana son tambayar menene ya sami yayan nasa? Amma kuma ruɗani da tsoro sun hana shi, yana cikin ruɗanin ganin mai kama da yayan nasa da kuma daddynsu over, ga Pinky a gefe, sannan yana tsoron tambayar me ya sami sir Arvin ɗin, dan bai ga fuskar da za'a kawowa wargi ba a tattare da Lion!!.
A takaice dai a haka jirginsu ya ɗaga, tafiyar dole, tafiyar da bada son ransu ba, tafiyar da basu shirya mata ba, dan ma dai Lion ɗin ya shirya masu tafiyar ce tun kafin ya zo, dama ya shirya a kan idan ya zo dole ya koma da Cherish U.s, sai dai shi kansa bai san da su Pinky ba sai da ya zo, dole ya sake shirya tafiyar har da su, dan ba barinsu zai yi ba, dole ya ɗaukesu ko dan su karɓi kalmar shahada, ba yadda suka iya tun da ubansu ɗaya, dole kawai su rikesu hannu biyu.
To tun da jirginsu ya ɗaga bari mu koma Nigeria muga me ake ciki, wata kila kafin mu dawo sun sauka a U.s lafiya.
NIGERIA❤️
Areef dai bai kyale Jehan ba sai da ya sami nutsuwa, ta yi kukanta har ta gaji, ya yi ta juyata son ransa, bayan ya sami nutsuwa kuma sai ya hau rarrashinta a kan ta yi hakuri ba zai sake ba, ƙin kula shi ta yi, ta ki yi mashi magana, sai da ta ga ya miƙe zai kunna wutar ɗakin ne ta yi maza ta rike hannunsa, a kule ta ce "Ni ka mayar mani da kayana jikina kafin ka kunna wutar".
Kamar zai yi dariya, sai kuma ya fasa, saboda yanzu ma ya yi laifi sosai, idan ya yi dariya kara yin wani laifin zai yi, dan haka sai ya rufawa kansa asiri kada ya kara takalo faɗa, yasan halin kayarsa sarai.
Ita kuma Jehan abin da baku sani ba shi ne, ba dan Allah ta kawo kanta gare shi ba, ba dan Allah ta biye mashi ba, abu take nema a wajensa, kuma kunsan Jehan haka kawai wlh ba zata durkusar da kanta kasa ba, taurin kanta ya wuce tunaninku, duk da yes tana son shi, amma ba zata zo ta bashi hakuri cikin sauki haka ba, kawai tana so ne ta yi amfani da shi ta fito da su Adiva daga gidan Hjyr daɗi, tasan dai shi kaɗai ne zai iya taimaka mata da gaskiya, tana ganin hukuma ba zasu yi gaskiya a kan al'amarin ba, ta yarda da shi sama da kowa, ko daddynta bata yardanwa da zuciyarta ta gaya mashi ba, saboda idan ta gayawa daddyn nata ma bai wuce ya ce su shigar da kara ga hukuma ba, kunga ta gudu ne bata tsira ba, ita kuma tasan da cewa Hjyr daɗi tana da manya manyan mutanen da hukuma ba zasu iya yi mata komai ba, maganinta kawai sai dai a sami tantiri irinta, wannan shi ne dalilin dayasa Jehan ta bada kai lokaci guda, saboda kullum da tunanin su Adiva take kwana take kuma tashi, abin yana ranta sosai, shiyasa ta yi wa Areef kwanciyar ɗaukar rai. Sai dai abin da bata sani ba, shi ne sarai Areef yasan dole da akwai abin da take so yasa ta yarda ta bashi hakuri, ya san halinta sarai fiye da kowa, saboda yasanta a ɓaɗini, idan kasan mutun a baɗini to shi ne kasan shi ba'a zahiri ba, yadda aka yi ya santa a baɗininta kuma shi ne, yana ganin duk abin da take yi a lokacin da take ita kaɗai, a lokacin da kake kai kaɗai shi ne ainahin halayyarka take bayyana, ainahin wanenen kai yake bayyana, so yasan ta a wannan lokaci, yana ganinta ta Camera, ita ce dai bata sani ba, so a takaice ya yi mata sanin da su mummynta ma basu sani ba, dan su zahirinta suka sani ba baɗini ba, yasan abin da zai sanya Jehan ta karya maganarta ta duƙar da kai ba ƙaramin abu bane, dan ta faɗa wa kanta sai dai Yah Areef ya nemeta ba dai ta neme shi ba koda zata mutu, so abin da zai sa ta karya wannan magana ba ƙaramin abu bane, koda kuwa zata mutu, haka take tamkar kanwar Lion a shegen taurin kai.
Kayan nata ya ɗauko ya mayar mata a jikinta, yana yi yana ce mata sorry, kin kula shi ta yi, ta ce dai fushi take yi da shi. "Zaki yi wanka a tare da ni?" Ya raɗa mata hakan ne a kunne.
Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba zata yi ba. Why ya tambaya, mikewa zaune ta yi tana faɗa mashi babu wani dalili, kawai ba zata yi bane. Kara jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Please mana my Jehan".
Ɗan ture shi ta yi. "Ni karabu da ni mun ɓata".
Ɗan bakinsa ya sake mayarwa saitin kunnenta ya fara yi mata raɗa "Haba nana my baby, na ce fa na tuba ba zan sake ba, please mana, mu yi wanka a tare, zan kashe wutar toilet ɗin sai na kunna blue light, kinga shi babu haske sosai".
"Kana son mu yi wanka a tare? Kuma kana son na dai'na fushi?". Ta tambaya tana ɗaura hannunta a saman ɓul ɓul ɗin breast nasa, dan ma kada ya yi mata musu a maganar da zata gaya mashi.
(Ba shakka Jehan ta cika ƴar duniya 😂 bafa abin da bata sani ba yarinyar nan😂 harda fara matsa mashi ɓul ɓul nasa dan kada ya yi mata musu idan ta faɗi bukatarta 😂 Maman Yasmin come forward, irin tarbiyar da kika bata kenan ba?🤔😂 Yaudara kiri kiri😂 zata cuci bawan Allah bai ji bai gani ba🧐😂)
"Yeah my baby, ina son muyi wanka a tare".
"Okey promise me that duk abin da nace kayi mani zaka yi?". Shiru ya ɗan yi, dan yasan halinta sarai, yanzu sai ta jefa shi cikin wata cakwakiyar, amma tun da yana sonta, sai ya ce "I promised you in dai abin bai kaucewa Shari'a ba, bai kuma saɓawa Allah ba, to tabbas zan yi maki my baby".
Kara matsa mashi ɓul ɓul ɗin breast ɗin nasa da ɗan ƙarfi ta yi har sai da ya ce "Wash my baby, so kike na koma ruwa ko?".
Hannu ta kai ta ɗaura a saman kyakkyawar lips nasa tana faɗin "To ai ko ka koma ruwan ma kayan ka ne, ni taka ce, yanzu dai muje mu yi wankar, sai kazo na baka abinci a baki kafin na gaya maka abin da nake son ka yi mani, nasan kana jin yunwa sosai, ka bari can cikin dare sai ka koma ruwan".
Haƙiƙa ya yi mamaki sosai da jin maganar nan tata, saboda bai taɓa tunanin ta iya magana har haka ba, wai zata bashi abinci a baki dan tasan yana jin yunwa, kuma da tsakar dare ya koma ruwa, wato cikin dare zasu yi wasa, bai taɓa tunanin ta iya waɗan nan abubuwa dukka ba, yarinyar nan ba shakka idan aka barta da namiji sai ta kwance mashi notikan kwakwalwa, dama an ce ka guji mutun mai shiru shiru, dan ya wuce tunaninka, wannan shiru shirun da yake ɗin ka barshi a haka, idan ka sake ka bari ya buɗe baki, to sai ka zama wawa a gabansa, kuma ba shakka hakance, idan namiji ya kuskura ya shiga hannun Jehan, wlh sai Allah ne kawai zai kwacesa, dan ta iya duk wani duniyanci, barema idan tana da bukatar ayi mata abu, tamkar mage mai kwanciyar ɗaukar rai take zama, sa'ar Areef ɗin dai ɗaya da Allah yasa da iya gaskiyarta take son shi, tsakani da Allah take son shi, banda haka da zata wahalar da zuciyar bawan Allah'n nan ba kaɗan ba, sai dai Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawa ya zalinci kansa, da Allah ya tashi kamata sai ya cusa mata son mijin nata kamar hauka, ba zata iya rayuwa babu shi a gefenta ba.
Ganin ya yi shiru ya faɗa duniyar tunani ne yasa ta shige cikin Lion chest nasa tana saka mashi kukan shagwaɓa tare da fara shafa ɓul ɓul nasa. Rungumeta sosai ya yi yana faɗin "Menene kuma?". "Katashi muje mu yi wanka mana, amma ka zauna kana wani tunani, yanzu tunanin me ma kake yi? Ba dai na wata macen ba ne?".
Nisawa ya yi kafin ya miƙe tare da ɗaukarta cak, duk kaifin ƙwaƙwalwa irin nasa yau Jehan tana neman sanya shi ya ji duk tunaninsa ta tsaya cak, tana neman kwance mashi lissafin ƙwaƙwalwa, ya rasa a wani point zai ajiyeta, ga shi ma taki yarda ya kunna wutar ɗakin bare ya ganta ido da ido, bai san cewa gara mashi ma da bai kunna wutar ba, dan idan ya kunna waɗan nan shegun sexy eyes ɗin nata kara birkita shi zasu yi, dama can yana kaunar idanuwan nata, shiyasa yake ce mata da idanunta kamar ball, to idan ya kunna wuta suna ganin juna, idan ta juta mashi fararen idanun nan sama cikin kisisina ai sai ya kara ruɗewa ya birkice ya rasa ina zai sa kansa.
(Akwai ƴan duniya kala kala a TRIPLETS, amma bana jin akwai biyun Lion da Jehan 😂 kamar dukkansu nonon gwaggo suka sha😂)
Bai sauketa a ko'ina ba sai a cikin tsakiyar toilet, da yake da akwai haske wuta a toilet ɗin, sai ya zubawa face nata idanu yana kallonta cike da tsantsar so da kauna. Wani irin kallon soyayya ta wurga mashi tare da ɗan turo baki a shagwaɓe ta ce "To me kake wani kallona kuma? Kafa ce zaka kashe wutar toilet ɗin".
"Ina, ina my baby, ba zan iya kashe wannan wutar ba, barni na kalli matata". Ya kai karshen maganar tare da jawota jikinsa sosai, sai a lokacin ta lura da babu kaya a jikinsa, tamkar zata zunduma mashi ihu, sai kuma ta daure ta cije ta kwantar da kanta a saman Lion chest nasa tare da runtse idanuwanta gam.
"Jehan". Ya ambaci sunanta cikin sanyin murya. "Na'am my baby". Ta amsa mashi. Shiru ya ɗan yi yana jin sautin sunan my baby da ta faɗa, ko da sunan wasa bata taɓa kiransa da hakan ba, wani irin daɗi na musamman ya ji tana ratsa shi.
"Muje nayi wa matata wanka ko?". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta izuwa tsakiyar bayanta. Kai kawai ta gyaɗa mashi kafin ta ɗan raba jikinta da na shi, sai dai taki buɗe idanuwanta, dan tsoron ganinsa babu kaya take ji.
Wucewa ya yi ya je ya haɗa masu ruwan wanka, tana tsaye idanu a rufe har ya dawo wajen nata, cancak ya ɗauketa sai cikin jacuzzin. Wash ta ɗan furta saboda yadda ruwan yake da zafi sosai, su kuma TRIPLETS sun saba yin wanka da ruwa mai zafi sosai, saboda sanyin kasarsu, so abin sai ya zamar masu jiki.
A takaice a cikin ruwan ma bai kyaleta ba, sai da ya yi ta wasa da ita son ransa, sannan ya yi mata wanka, ya yi ya yi a kan ta yi mashi wankar shi ma, amma taki yarda ta yi mashi, haka ya hakura ya yi wa kansa, ya naɗota a towel suka koma cikin ɗakin, a saman bakin bed ya sauketa tare da wucewa ya kunna wutar ɗakin, sannan ne ya wuce izuwa dressing room nasa.
Kayan barcinsa masu kyau da tsada ya sanya a jikinsa, sannan ya ɗauko mata kala ɗaya, da kansa ya sanya mata, bata hana shi ba.
Bayan sun kammala ta sauko kasa ta fara zuba mashi abinci, kusa da ita ya zo ya zauna, sai kallon face nata yake yi cike da so da tsananin kaunarta tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita.
"Baby gobe zaki rakani wani waje fa". Ya faɗa yana tara mata gashin kanta dake zubo mata a wuyarta idan ta sunkuyar da kai kasa tana zuba abincin, kayan barcin nasa babu hula, hakan yasa kanta yake a buɗe, ga gashin da danshin ruwa a jikinsa, basu busar da kan nasu ba, saboda Areef ɗin yana jin yunwa sosai, sai ta ce ya fara cin abinci kafin su kammala komai daga baya.
"Okey tom". Ta faɗa tana dago da kallonta a kansa. A duk lokacin da ta sauke idanuwanta a kansa, sai ta ji tamkar ta shige cikin jikinsa su cure su zamo abu guda kawai, saboda tsananin son da take yi mashi.
"You are so very very beautiful my baby". Ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan shafi gefen face nata. Wani irin kallon ta wurga mashi da waɗan nan dara daran idanuwan nata masu rikita shi. "Ban kai ka kyau ba ai my baby, yanzu dai ka ci abinci". Ta kai karshen maganar tare da ɗebo abincin a spoon ta kawo mashi saitin ɗan bakinsa.
(Idan ba wani abin Jehan ta shirya ba yaushe zata tsaya zuba waɗan nan kalamai fisabilillahi 🤌😂 kun ji fa har da nuna damuwa da ya ci abinci yana jin yunwa 😂 har da bashi a baki yau🤌 innallilahi Jehan wan kill me with laugh 🤌😂 harda kiransa da baby, dan ma Allah yasa shi ma Areef ɗin ba tayan baya bane, da ai ba mai kwatarsa a hannun wannan yarinya ta maman Yasmin 😂)
A hankali ya buɗe ɗan bakin ta zuba mashi, lumshe idanuwansa ya yi yana mai matuƙar jin wani irin daɗi yana ratsa shi
kai, kai, kai nima haka nake jin daɗi idan ina shan Maltina mai sanyi 🧐 haba mana, ni masoyan nan sun fara isata🥲 dan haka zan dakata a nan sai gobe kawai in Allah ya kai mu, ina dalili? Kowa sai love yake sha sun barni da kayan takaici🤌😂 na fara kishi🥱😂
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai