Showing 69001 words to 72000 words out of 270744 words
ransu, sai zuba mashi shagwaɓa take yi, shi kuma yana biye mata, tana tsaka da yi mashi magana, bata ankara ba sai jin saukar lips nasa a saman tata ta yi, ga shi tana kwance a jikinsa, kun san su a wajensu hakan ce soyayya.
Bata hana shi ba da farko, daga baya da ta tuna da maganganun da Rimsha ta yi mata a school, sai ta yi maza ta mike daga jikin nasa tare da komawa gefe da sauri.
Da mamaki yake kallonta, kafin ya yi magana da gudu ta bar wajen, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, fatan ta ɗaya, shi ne kada ta samu ciki kamar yanda Rimsha ta ce mata idan wani ya taɓata zata samu ciki.. BABBAR MAGANA.
Tana shiga cikin gida, kai tsaye ɗakinsu Rimshar ta nufa, a lokacin kowa ya yi barci, saman bed ta haye tare da kudundunewa a cikin bargo, nan take ta fara hawaye tare da danasani. Shi kuwa Mark, wayarsa ya ɗauka ya fara kiran numberta, amma ina taki ɗagawa, daga karshe dai ya hakura ya kyaleta, dan bashi da zaɓi. A haka barci ya yi awon gaba da ita.
A ɓangaren shi kuma Aseef, da kyar da makyarkyata ya samu barci ta yi awon gaba da shi, Allah sarki, yana tsananin kewar Heartbeat nasa, har wani zazzaɓi mai tsananin zafi ne ya rufe shi, a haka dai barci ɓarawo ya ɗauke shi.
Ummin Nawid ƴan uwanta na Katsina sun zo sun ɗauketa, dan sun sami labarin rasuwar Dr Nawid, abin gwanin ban tausayi.
After one day.
Haɗe suke gabaɗaya a palo, a yau ne su Lion suka shirya tafiya Daular Mutuwa, suna hira a palon na ban kwana da ƴan uwan nasu.
Gwaggo ce ta ce da Lion "Amma Saif ba da Rimsha zaku tafi ba? Naga ita kaɗai ta san hanya ai". Kai kallonsa a kanta ya yi, tana kwance a saman cinyar daddynta. Shi ba don hanyar ma yasa yake son tafiya da ita ba, saboda su Josephine yasa yake son tafiya da ita, baya son barinta a nan, dan kada su Josephine ɗin su yi mata wani abin, hankalinsa zai fi kwanciya idan ya tafi tare da ita.
"Yeah momma da ita zan tafi......" Bai gama rufe baki ba ta zunduma ihu tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Wlh ni ba zan je Daular Mutuwa ba, in dai a kan Daular Mutuwa ne to wlh sai dai mu ɓata da yaya Saif ɗin, kowa ya kama gabansa, ni sai dai idan gawata za'a mayar can, amma da kafata, wlh ba zan je ba, na shiga uku na lalace, wayyo daddyna kasheni kawai gwaggo take so aje ayi, kila ta gaji da ganina ne a duniya, daddy ka gaya mata kai kana sona tun da ita ta dai'na sona, mummy dama nasan ke kinfi kowa sona, ki gaya masu kada su taɓa maki ƴarki". Ta kai karshen maganar tata tare da watsawa a guje ta nufi cikin bedroom nasu, sai kuka take yi tamkar ranta zai fita.
Shiru palon ya yi, babu wanda bai tausaya mata ba, harta shi kansa Lion ɗin ya yi mugun tausaya mata, ba'a banza take waɗan nan surutan ba akan Daular Mutuwar, baiwar Allah.
Miƙewa Areef ya yi ya bi bayanta izuwa cikin ɗakin nata, su kuma suka cigaba da tattauna yanda za'ayi.
Yana shiga ya sameta kwance a saman bed, ta yi shiru ga hawaye a jaga jaga a saman face nata, sai tunanin yanda ta baro Daular Mutuwar take yi.
Saman bedside drawer ya zo ya zauna, cikin zolaya ya fara magana
"Rimsha ƴar Queen of Daular Mutuwa fa ta ga Yaya Saif naki, kuma ta ce idan ba shi ba wlh mutuwa zata yi, ita shi take so, Queen ɗin kuma ta ce ta kwantar da hankalinta babu shakka sai ta mallaki Lion ko ana ha maza ha mata".
A dubu ɗari ta mike zaune, tare da zaro idanunta waje tamkar zasu faɗi kasa, kome ta tuna, sai ta zunduma ihu da iya karfinta tana faɗin "Ni wlh babu wanda yaya Saif zai sake aura, ni kaɗai na ishe shi, Allah koma Queen ɗin ce bata isa ta taɓa mani shi ba, ai ba tsoronta nake ji ba, a kan shi zan iya yin komai, shegiyar mata mai bakar aniya, wlh azumi da tsayuwar dare zan yi mata, dan taga yaya Saif na kyakkyawan gaske ko? Bakar azzaluma, to wlh yaya Saif yafi karfinta, kuma shi baya son aljana, Allah idan ta sake ta kalle shi da ido ma kawai, sai na kwakwale mata idanu!!".
(Ko a ina zata gan Queen ɗin har ta ga idanun da zata kwakwale mata ɗin?🤔 Anya Rimsha ƙwaƙwalwarta bai taɓu ba kuwa?)
Tana magana tana ihu. Areef me zai yi? Ai yau dariya har da rike ciki, Allah mai iko, kamar ba yanzu ta gama cewa ita ta dai'na son yaya Saif ɗin ba, in dai a kan Daular Mutuwa ne, to wlh babu ruwanta da shi, amma daga jin batun zai auri ƴar Queen, har ta mance bala'in dake cikin Daular ta fara kishi kuma, kai jama'a Rimsha tana yin son ranta.
Ganin irin dariyar da yake yi mata ne yasa ta kara tsananta kukan nata. Tana ƙoƙarin sauka daga saman bed ɗin idanunta suka sauka a saman face ɗin Lion, yana tsaye a bakin kofar shigowa bedroom ɗin. Wani irin yawun wahala ta haɗiye, nan take ta yi shiru, dan yanda ta ga face nasa babu almun wasa a tattare da shi, nan take ta haɗe malaman jikinta waje guda ta nutsu tsit.
Wani irin muguwar harara ya wurgawa Areef dake kallonshi yana dariya. A takaice ya ce mata "Zoki wuce mu tafi". Ba musu sumui sumui ta sauko kasa daga saman gadon ta nufe shi.
Gaba ya yi ta rufa mashi baya, kai tsaye bedroom nasa ya wuce, cikin jin kunya ta keta jama'ar dake a cikin palon ta bi bayansa zuwa bedroom ɗin nasa............
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E12
Date: 22/4/2024
Gaba ya yi ta rufa mashi baya, kai tsaye bedroom nasa ya wuce, cikin jin kunya ta keta jama'ar dake a cikin palon ta bi bayansa zuwa bedroom ɗin nasa.
A zaune a bakin bed ta isko shi, kusa da shi ta zauna tare da kwanto da kanta a saman laps nasa. Nisawa ya yi tare da kai hannunsa yana goge mata guntun hawayen dake a saman face nata.
"Meyasa kike son yin kuka sosai ne?". Ya yi maganar yana mai da kallonsa a saman zanen sunansa dake saman tudun tula tulanta da suka ɗan bayyana saboda yanayin kwanciyar da ta yi.
Hannu ya kai wajen yana ɗan shafa zanen, kasa kasa ya ce "I really like it". Ɗan turo baki ta yi tana mai kamo hannunsa ɗayar dake a saman kumatunta.
"Noorish ni dan Allah kada ka bari a mayar da ni Daular Mutuwa ka ji ko?". Dawo da kallonsa a saman face nata ya yi, zuba mata idanu ya yi na tsawon mintocin da a kallah zasu kai biyar, kafin ya ja godon numfashi sosai ya fara magana a nutse. "I will going to miss you my Meesha, ba zan tafi da ke ba, kuma babu wanda ya isa ya kai min ke can, stay with your dad and mum safe, ki kula mani da kanki sosai, don't come out without hijab, even wajen momma zaki je, you now i hate that, so be careful kin ji ko? I really love you from the button of my heart". Ya kai karshen maganar yana shafa lallausan wuyarta.
Nan take ta ji jikinta ya yi mugun sanyi, mikewa ta yi zaune tare da faɗawa jikinsa da kyau. Rumgumeta sosai ya yi, ji yake yi tamkar idan ya tafi ya barta, wani abin zai iya faruwa da ita, yana jin tamkar za'a rabasu.
"My Noorish i really love, ban taɓa son wani abu a rayuwata kamar yanda na so ka ba, tun ban san wacece ni ba nake dakon sonka, hotonka kawai idan na gani yana ɗaukata tsawon lokaci ina cikin tsananin farinciki, a duk lokacin da na tunaka, ina jin tamkar ba'a duniya nake ba saboda daɗi, ban taɓa kawowa a ra'ina zan ganka ido da ido ba, ban taɓa kawowa a ra'ina zan zauna a kusa da kai ba, amma duk da haka, a kullum sonka karawu take yi a cikin zuciyata, bani da abin da zan ce ga Allah sai dai Alhamdulillah, Alhamdulillah daya mallaka mani kai a matsayin miji, ya kuma sa kana sona nima, ko yau na mutu wlh nayi farinciki, burina kuma ya cika, ka kula mani da kanka sosai ka ji?". Ta kai karshen maganar tana ruwan hawaye sosai.
Kara matseta sosai a jikinsa ya yi, da wata iriyar murya wanda bai san yana da ita ba, cikin tsananin so da kuma kaunarta ya fara magana "Hakane my Meesha, duk abin da kika faɗa gaskiya ce, kin soni tun baki san ke kanki wacece ba, na shaida hakan ni da kaina, amma fa ki sani a yanzu na fi sonki sama da yanda kike sona, ban taɓa tunanin zan ɗaga idanu na kalli wata ƴa mace ba a rayuwata sai a kanki, ranar da na fara ganin zanen sunana a kirjinki, abin ya tsaya mani a ra'ina sosai, sai dai a lokacin zuciyata a rufe ruf take, kece da kanki kika nemo key ɗinta, kika buɗeta, kika shiga cikinta, sannan kika mayar kika rufe, you are so special my Meesha".
Ɗago kanta daga saman kirjin nasa ta yi, face nasa ta zubawa idanu sosai tana kallon shi, hawaye wasu suna bin wasu a saman kuncinta. Shi ma ita yake kallo, sun tsare juna da idanu babu ko kyaftawa.
Almost 5 mins suna a haka, sannan ne ta matso da face nata dab da tasa, lallausan lips nasa ta sumbata, tare da kai hannu ta sakalo wuyarsa. Ganin yana bata wahala ne dan ya fita tsawo sosai, yasa ya rankwafo mata kaɗan, hakan ya bata damar samu ta fara kissing nasa cikin nutsuwa.
Kara kankameta sosai ya yi, yau wani irin kiss take yi mashi tamkar babu gobe, cikin salo ya shiga mayar mata da martani shima, tamkar zasu cinye juna.
Sun jima suna kissing na junansu kafin nan ya zame bakinsa daga nata, kasa kasa ya ce "Zan tafi, time ya cika, ki kula sosai my happiness". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa.
Kai tsaye palo ya nufa, har lokacin su daddy suna zaune suna ta mayar da zantuka. A tsakiyar palon ya sauketa, kunya tamkar zata shige cikin kasa, shi kuwa ko a jikinsa, sai ma kallon gwaggo da ya yi yana faɗin "Momma pray for us, zamu tafi". Ya kai karshen maganar tasa tare da nufar hanyar sauka kasa.
Gabaɗaya family suka rufa mashi baya, gwaggo idanunta sun cika taf da kwallah, ƴaƴanta har guda biyu zasu tafi Daular Mutuwa, waje mafi haɗari da bata taɓa jin biyunsa ba, ji take tamkar ta dakatar da su, sai dai kuma mahaifinta yana a can, tana kaunarsa shi ma, dole su je su ɗauko mata shi, hakan yasa ta danne ta jure, Aseef sai kuka yake yi a kan shi gaskiya zai bisu, ba zai yarda su tafi su barshi ba, koma yaya ne sai dai su tafi tare. Da kyar Lion ya shawo kansa ya hakura, suka ce mashi ya zauna ya kula da gwaggo da ƴan gida.
Shi kuwa Areef yana can yana haɗa kaya, sam bai sanar da Jehan da shi za su tafi ba. Bayan ya kammala haɗawa ne ya fito waje harabar gidan, a nan ya sami kowa da kowa, kai tsaye cikin mota ya fara nufa, sai da ya ajiye jakar tasa, sannan ya fito, kusa da gwaggo ya zo, cikin nustuwa ya ce mata "Momma be strong please, just pray for us, everything will going to be normal In Sha Allah".
Har lokacin idanunta cike tab da kwallah, addu'a ta fara zuba masu babu kama hannun yaro, sai amin amin kowa yake amsawa da shi.
Bayan ta kai karshen addu'ar ne, ba zato ba tsammani Jehan ta saki baki tana kallon jama'a, sai ji ta yi ya jawota ta faɗa jikinsa, rumgumeta sosai ya yi yana faɗin "Zan tafi my baby, ki kula mani da kanki sosai kin ji ko?".
Tamkar zata yi kuka ta ce "Dama har da kai za'a tafi Daular Mutuwar ne? Shi ne baka gaya mani ba?". Kara matseta sosai ya yi a jikinsa yana faɗin "Am so so sorry, mantawa nayi".
Dukan wasa ta fara kai mashi a kirjinsa tana faɗin "Ni bana son kaje, dan bana son wani abin ya sameka, ni dai ka fasa zuwa"."Da gaske baki son wani abin ya sameni?".
Da sauri ta gyaɗa mashi kai "E bana son wani abin mana ya sameka, ni bana son na rabu da kai". "To shikenan, pray for us, In Sha Allah babu abin da zai same mu". Ya kai karshen maganar yana mai kara matseta sosai a jikinsa.
Da alama sun mance da cewa a gaban family suke. Haka suka cigaba da zubawa juna kalaman kauna har sai da ya ishe su, while shi kuma Lion yana magana da gwaggo da kuma daddyn Rimsha. Bayan sun gama zuba kalaman love ɗin ne ya saketa tare da nufar wajen motar tasu, sam yaki yarda ya juyo su haɗa idanu da ita, dan baya son ganin kukanta, ita kuwa hawaye wani na bin wani.
After some minutes Lion ya kammala maganarsa da su gwaggo, sannan ya juya ya nufi wajen motar, har Donal ya buɗe mashi kofar motar zai shiga, da gudu Rimsha ta tafi ta faɗa bayansa, tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin kukan nata tana faɗin "Noorish ni zan bika, bazan iya bari ka tafi kai kaɗai ba, gara muje tare kawai, gara komai zai faru ya faru a kan idona, ina tare da kai, ko mutuwa zan yi, nafi son na mutu a hannunka, please Noorish".
A hankali ya juyo ya rungumeta, har cikin ransa shi ma baya son rabuwa da ita, rabuwarsu babban ciwoce a gare shi, yasan zai sha wahala sosai, amma ba shi da zaɓi, dole ne ya barta a gida, dan bai san me zai je ya tarar a wajen ba.
Hakika har cikin zuciyarsa yake jin wannan kuka da take rerawa, amma sam ya kasa yi mata magana, ganin haka yasa daddynta ya kariso wajen, hannu yasa ya karɓeta daga jikin Lion ɗin. Ihu take zunduma masu bana wasa ba, faɗi take yi "Daddy ka ce ya tafi da ni, bana son ya barni, bana son rabuwa da shi".
Wucewa ya yi ya shiga cikin mota zuciyarsa na yi mashi zafin rabuwa da ita, shi kuma daddy wucewa da ita ya yi izuwa wajensu gwaggo. Yana zuwa gwaggo ta karɓeta suka hau rarrashi, amma ina, taki yin shiru, ihu take yi tana faɗin ita wlh zata bi mijinta........... RIMSHA MANYA MAI MIJI, TATTABARA UWAR SOYAYYA❤️😂
Da gudu Jehan ta juya ta bar wajen, ta koma cikin gida, dan ba zata iya ganin tafiyarsu ba, shi ma Aseef da sauri ya bar wajen, dan ba zai iya jurewa ba, dama da kyar Lion ya lallaɓa shi ya yi masu shiru.
Mark ne ya nufi motar su Lion ɗin, dan ya ja su su tafi airport. Dai'dai zai buɗe kofar motar, Anaya ce ta zunduma ihu tana faɗin "Nashiga ukuna! Dama my da kai za'a tafi? Wlh ba zan iya jure rashinka ba! Ka dawo wlh ba zaka je ba, Rimsha fa ta ce mutuwa ake yi a can". Yau ga ikon Allah, iyaye dai suna ganin tsantsar rashin kunya ta yayan zamani, amma da yake duk jirgi ɗaya ya kwasosu, wato duk jinin turawan ne, sai ya zama ko a jikinsu, basu damu da abin da ƴaƴan nasu suke yi ba.
Da gudu Anayar ta tafi wajen Mark ɗin, ta kuwa yi sa'a dai'dai lokacin ya juyo domin ya kalleta. Tana zuwa ta faɗa saman kirjinsa tana kuka, ita wlh ba zata bari ya tafi ba, ai ta ji Rimsha ta ce mutuwa ake yi a wajen.
Shi dai Azharuddin Bature, wato daddynta, baki ya saki yana ganin ikon Allah, a iya saninsa bai taɓa sanin ƴarsa tana soyayya ba, kwatsam sai ya ganta da wani? Lallai kuwa ya yi sakaci ba kaɗan ba. Ita dai Brr Naurat ko a jikinta, daɗi ma ta ji na cewa duk jikokin nata sai auren family suke yi, zumunci na kara ninkuwa.
Babu kunya Mark ya rungumeta sosai, kasa kasa ya fara rarrashinta. Ina ai kin sauraronsa ta yi, sai kuka take zuba mashi. Daddyn Rimsha bawan Allah, yana ganin abubuwa, shi ne dai ya sake zuwa ya kama Anayar, daddynta kam ya kasa motswa daga in da yake, duk ya yi la'asar, mamaki kamar zai kashe shi, wai ace kamar su Anaya sun san so? Shi yana matsayin daddynta sam bai san da zancen ba?! Abin ya bashi mamaki, sai kallon mummynta yake yi, ita ma shi take