Showing 84001 words to 87000 words out of 270744 words

Chapter 29 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2981

ratan watanni, wato da Jalila, Anaya, da kuma Jehan kenan, sai dai fa ko da muka haifi Jehan ɗin, bamu wani jata a jiki sosai ba, dan muna ganin kamar ita ma mutuwa zata yi, amma da yake uwa da ƴa ba mai shiga tsakani, ita Maryam ta jata a jiki sosai, ni kam baya baya nake yi da ita, dan rasuwar Hussainin namu ya girgizani, na saba da shi sosai, ko ina zanje muna tare, yaro ɗan wata biyar amma ya san yawo, saboda fita da nake yi da shi, lokacin da ya rasu nasha wahala, har firgita nake yi a cikin barci ina kiran sunansa, to shi ne yasa na ki yarda na ja Jehan sosai a jikina, dan kada na sake shan wata wahala, sai da na ga Jehan ta cika shekara guda bata mutu ba, sannan ne na jata a jiki sosai, na fara nuna mata soyayya, mun so Jehan fiye da kanmu, baki ma ba zata iya faɗar adaddin soyayyar ba, haka muka cigaba da bata kulawa tamkar kwai a saman bajajjen faranti, Aunty Aisha ta fi mu nuna kula a kan Jehan, daga karshe ma haka muka hakura muka bar mata Jehan ɗin tana kwana a ɗakinta, dan ta kwace mana ita, shiyasa kuke gani a yanzu sun fi shakuwa, shakuwa ce da suka yi ta tun tile tile, ba ta yanzu bace ba, tun daga kan Jehan ɗin kuma bamu sake samun haihuwa ba har matar Hassan ta haifi Zaira, bayan haihuwar Zaira da wata ɗaya muma muka sami ciki, nan muka fara tattalin kayanmu, har Allah ya sauketa lafiya muka sake samun ƴa mace, a baya duk ƴaƴan da muka binne maza ne, yanzu kuma mata muka samu, ƴarmu ta biyu wato Rimsha, kama take da Maryam sak, while ita kuma Jehan kama take yi da ni sak, haka muka ɗauki son duniya muka ɗaurawa ƴaƴan nan namu guda biyu, muka cigaba da basu kulawa na wuce misali, sai dai sun fi shakuwa da Aunty Aisha, dan sun fi zama a wajenta, ni kuma ina kyale mata su ne dan su ɗebe mata kewar TRIPLETS nata da ta rasa, kullum maganar Aunty Aisha ɗaya idan tana yi wa su Jehan wasa, shi ne idan ta ga TRIPLETS nata, to sune mazajensu Jehan ba makawa, kuma zata yi ta addu'a a kan hakan, in dai tana raye ta gane ƴaƴan nata, to wlh ko sun yi aure sai sun auri su Jehan, kullum shi ne zancenta, a hankali hankali har ta zo ta fara dai'na zancen TRIPLETS ɗin nata, kamar wasa duk zancen ya bar bakinta baiwar Allah, haka muka rayu cikin farinciki, kullum muna waya da Shitu, shi ma ya jima da yin aure, suna da ƴarsu ɗaya Adiva, sa'ar Jehan ce yarinyar. Bamu tashi dawowa Nigeria ba har sai da su Jehan suka yi wayo, sai da Jehan ta kai primary 4 a school, wannan dalilin yasa sam basu jin Hausa, daga larabci, sai English da kuma yaren mamansu wato shuwa Arab, sai kuma kanuri da take yi masu kaɗan kaɗan, nima time to time ina yi masu fullanci, dan na koya wajen daddyna, sai dai Rimsha ce kawai ta ɗan iya fullanci, ita Jehan ko yaren mummyn nasu ma taki ta koya sosai, ita dai a barta da English, da shi kawai take magana, larabcinma sai taga daman yi, ga kafiyar bala'i, ga zafin rai, akwaita da iya tsare gida sosai, kuma dukka Aunty Aisha take zugata, ni dai bani da ta cewa, idan nayi magana Aunty Aisha ta hau surfa mani masifa, haka na zuba masu idanu, sai da muka dawo Nigeria ne na shiga harkar siyasa, da farko ina tsananin son siyasar, daga baya dana shiga cikinta, naga kazantar dake cikinta, sai naji ba zan iya ba, naso na barta, amma Maryam ta hanani, ta kuma kara mani kwarin gwiwa a kan lalllai na yi siyasa, lallai siyasa tana da bukatar mutun irina, zai tallafawa kasa ba kaɗan ba, ta dai nuna mani alfanonta sosai, na kuma gamsu, dan haka sai na sake zage dantse sosai, ina da abokan hamayya sosai, amma ban taɓa mayar da hankali nabi ta kansu ba, kawai harkar gabana nake yi, a lokacin ne Allah ya haɗani da Abubakar Salahuddeen, muka fara takun saka da shi, in takaice maku labari shi ne ya zama sanadiyar rugujewar farincikina da ni da familyna bakiɗaya, saboda na kama shi yana dillanci kayan maye da kuma mata izuwa kasashen waje, ya yi ya yi na rufa mashi asiri, dan takarar da zai tsaya, naki yarda na rufa mashi asiri, sai ya bukaci da na shigo cikin tafiyar tasu, nan ma naki yarda, to shi ne ya nemi salwantar mani da rayuwata da ta familyna, a lokacin da na shiga siyasa sunana ya fito, kamar hauka haka su yaya Deen suka yi ta nemana, har gida sun zo wajena, amma sai nece masu ni ban sansu ba, bani da wata alaƙa da su, dan haka su kama kansu, shi ma Hassan yazo har gida, naki yarda da shi, kuma sarai na san komai ma da yake tafiya a rayuwarsu, dan ina aika masu da makudan kuɗaɗe tun ina Dubai, har na dawo Nigeria ban dai'na idan suna cikin matsala ta kuɗi na taimaka masu ba, wannan shi ne labarina da abin da ya faru da ni a takaice kenan, kun san komai ba zai faɗu lokaci guda ba, amma ku ruke wannan ɗin kawai". Ya kai karshen maganar yana mai gyarawa ya kwanta, tare kuma da tada kansa da laps na Brr Naurat.

Ajiyar zuciya kowa dake cikin wajen suka sauke, Brr Naurat ce ta ce "Sannu ɗana, kasha gwagwarmaya kai ma". Tana magana tana shafa kansa.

Abbi ne ya kai mashi duka yana faɗin "Kana ji muna nemanka a lokacin, amma sai ka sheremu ko?". Jinjina masu kai ya yi alamar e ɗin ya share.

Nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, shiru ya yi masu kamar baya wajen. Haka suka kasance cikin tsantsar farinciki da kuma yi wa ƴaƴansu dake Daular Mutuwa addu'a.

After some minutes gwaggo ce ta ce "Ni kam wai Aseef bai dawo daga shopping ɗin da ya ce mani zai je bane?".

Daddyn jelly ne ya amsa mata da "Gaskiya fa kamar bai dawo ba, wata kila ya wuce wani wajen ne".

Da mamaki Abban Imran ya ce "Kai ba Saif ya ce kada kowa ya fita daga cikin gidan nan ba? Ya za'ayi A'isha ki barshi ya fita? Suma sojojin ya za'ayi su karya maganar Saif? Ko da yake sun fi kusa da shi, kila ya ce masu idan Aseef zai fita su bashi hanya ne"

"Hmmm yaya babba kenan, Aseef ɗan rigimar ne za'a hana fita, ai idan suka hana shi fita,to wlh gidan nan babu zaman lafiya, ni kai'na idan na ce ba zai je ko'ina ba, to babu ni babu zaman lafiya, shi ne yasa kawai na ce mashi sai ya dawo". Cewar gwaggo.

"Gaskiya kam Aseef ɗan rigima ne wlh". Cewar Abbi.

Abba ne ya tari nunfashinsu da cewa "Ni ne nan zan baku labarin rigimarsa, yaron da ya je ya tasani a gaba ya rinƙa kuka lokacin da na ce ba zan bashi auren AKILA ba, Irfan ya riga shi, hmmmm ni zan gaya maku rigimar Aseef wlh".

Murmushi gwaggon ta yi, ita kaɗai tasan me take tunawa take sakin wannan murmushi. Haka dai suka cigaba da hirarsu na tsawon mintocin kafin nan a kira sallar azzahar kowa ya watse, dan suje su yi sallah.

After some days.

Abubuwa da yawa sun faru a cikin kwanakin nan da suka shuɗe, ciki harda neman Aseef da su gwaggo suka rinƙa yi, amma shiru babu shi babu labarinsa, hakan yasa hankulansu ya kara mummunar tashi, nan fa suka dukufa wajen addu'a babu kama hannun yaro, suma fa sauran sojojin da suke a bakin gate, hankulansu ya yi mummunar tashi ba kaɗan ba, dan idan har Aseef baya gidan, to ba shakka sun shiga uku da Lion idan ya dawo, dan sun karya mashi doka na barin wani daga cikin family ya fita, su kuma wlh sam basu ga fitar Aseef ɗin ba, ba su san time da ya fita ba, Allah ya gani, bayin Allan sun shiga tsananin damuwa na wuce misali.

Daular Mutuwa.

Sun shafe kwanaki a cikinta suna neman ƴan uwansu, amma san basu gansu ba, duk wani part da zasu faɗa a cikin Daular, sai su ga kamar sun bar duniya, ga shi su da suke rayenma sun raba hanya, Aseef ya yi gabas, Areef ya yi yamma, sun sha matukar bakar wahala, har shi kansa Aseef ɗin ya wahala, kuma bai gane ina Fadar Queen ɗin take ba.

Areef ne ke a kan wata hanya yana tafiya, sai wuce ɗakuna da abubuwa na ban tsoro da tsafe tsafe yake yi, tunanin ina Lion yake kawai yake yi, wani irin azababben yunwa yake ji, akwai snacks and drinks a cikin jakar dake goye a bayansa, amma ya kasa saukewa ya samu waje ya nutsu ya ci ya ƙoshi, shi burinsa kawai yaga ƴan uwansa. Duk wannan wahala da yake sha, bai dai'na ambato sunan Allah ba, hakan yasa Queen ta kasa ganin wai shin a ina ma yake, ya ɓace daga idanun tsafinta, sai nemansu take yi shi da Aseef, amma ko alamar mai kama da su bata gani ba.

Ya zo dai'dai wata mararraba, hanyoyi ne suka rabu gida biyu, ɗaya ta yi gabas ɗaya ta yi yamma. A dai'dai wajen ya tsaya yana tunane tunane ya zai yi a yanzu? Shi dai ko mutuwa zai yi wlh sai dai ya mutu, amma ba zai taɓa yarda ya bar cikin Daular nan ba tare da ƴan uwansa ba. Idan ma ya ce zai bar cikin Daular ta ina ne hanyar fita?.

A hankali ya fara jin motsi ta hanyar dake kallon yamma, shiru ya surara yana son tantance motsin menene?. Jin kamar sautin numfashin mutane ne yasa ya nufi hanyar babu tsoro ko miskala zarratin a tattare da shi.

Ko da ya isa wajen sai ganin su Mark ya yi gabaɗayansu da sauran sojojin a ɗaure da sarkoki masu karfin gaske, sai dai babu Lion a cikinsu. Hamdala ya yi ga Allah, ko ba komai ya ga wasu daga cikin tawagarsu, saura su Ayla da kuma Lion, sai Heartbeat nasu, wato Aseef shalele ɗan rigima.

Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin kwarin gwiwa ya fara ƙoƙarin buɗe kofar karfen, a rufe kofar take ruf da matakan tsaron Queen. Sai kuma me? Yana ƙoƙarin sakawa kofar karfi ya buɗe ta, kamar daga sama ya ji wani uban jijjiga da ginin ya fara yi, kafin nan ya yi wata yunkuri ginin ta rufta, kofar ɗakin ya toshe.

Hakika a wannan karon ba ƙaramar tashin hankali ya shiga ba, ya shiga ruɗu ta yadda kwata kwata baya iya gane ina ya dosa. Da sauri ya bar wajen saboda wani irin turnukin kura da ya taso, dan ma Allah yasa kofofin ɗakunan irin na karafunan nan ne masu kama da prison, so kofar ta tare ginin bai ruguzo a kansa ba.

Da sauri ya fito daga hanyar idanuwansa sun yi jajir tamkar wuta, sai wani huci yake yi, Hakika ya ji takaicin mutuwarsu Mark, har wani pat, pat, pat zuciyarsa take harba mashi, wani irin tukukin bakin ciki ne ya tokare mashi maƙoshi, da kyar yake haɗiyar wahalallen yawu, kansa sara mashi take yi tamkar zata fashi, har wani irin jiri ya fara gani.

Yana fitowa daga wannan hanya ya faɗa cikin wata tapkekiyar waje, wannan waje kuma ba ko'ina bane face wajen da su Rimsha suka taɓa zama, already dama kunsan ya yanayin wajen yake, ga faɗi da girma, ga kuma ɗakuna da yawa a cikinsu.

Zubawa wajen idanu ya yi yana kallon yanda yake, kamar daga sama ya ga dirowan mutane a gabansa. Jiga jigan matsafane masu ji da karfi, dama Queen ta turosu ne su nemo shi, tasbihi da yake yi ne yasa basu iya ganinsa ba, to a yanzu kuma ya dai'na ambaton Allah, saboda bala'in da ya shiga na ganin abin da ya faru da su Mark, a lokacin ne ma ya kamata ya ambaci sunan Allah da kyau, sai kuma tashin hankali ta hana shi, ya shiga ruɗu na ganin yanda wannan gini ta ruguzo.

Ganin mutanen yasa ya kara shiga tashin hankali, dama already bai dawo dai'dai ba.

Kafin ya yi wani yunkuri waɗan nan jiga jigan matsafa, ɗaya daga cikinsu ya sanya hannu ya sunkuce shi sama, wurgi ya yi da shi can gefe, ta fiya ya yi zai bugu da jikin wannan gunki na karfe mai kifiyoyin tsafi a jikinsa.

Tamkar wani walkiya haka Aseef ya bayyana a wajen ya tare shi, a tare suka faɗi kasa ba tare da sun isa ga wannan gunki ba. Ash suka furta a tare. Shi Aseef da Areef ya faɗo a kansa ma yana a cikin hayyacinsa sosai, shi kuma Areef ɗin saboda already yana cikin ruɗani, sai hakan ta kara gusar mashi da hankalinsa daga jikinsa, hakan yasa ya kasa koda motsawa.

Kwantar da shi a gefe Aseef ɗin ya yi tare da mikewa tsaye, a hankali ya ɗago da dara daran brown eyes nasa izuwa kan waɗan nan matsafa, sun kasance su biyarne cif, jibga jibga da su madaka karti. Kallon up and down ya yi masu kafin ya mai do da kallonsa a kan Areef dake motsi yana ƙoƙarin dawowa dai'dai.

Wani irin taunan hakwara waɗan nan matsafan suka fara yi, tare kuma da wani lankwashe kasusuwan jikkunansu, tamkar wasu macizai. Shiru Aseef ɗin ya zuba masu idanu yana kallonsu, har suka gama duk abin da za su yi, sannan suka tunkare shi da nufin su yi kutsi kutsi da su, su cinyesu ɗanye. Dai'dai lokacin shi ma Areef ya mike tsaye, ya dawo cikin hayyacinsa bawan Allah, ga uban yunwa da yake ji.

Wucewa gaba Aseef ɗin ya yi, ya tari waɗan nan matsafa gadan gadan suka fara faɗa babu kama hannun yaro. Areef ya so ya taimaka mashi, sai dai kuma faɗar tafi karfinsa, ta wuce tunaninsa, daga karshe sai ya rabu da su suna faɗar, shi kuma ya fara duba ɗakunan da suke wajen, a cikin zuciyarsa yana ta mamaki tare da tunanin a ina Aseef ya samu wannan karfi har haka, sai dai kuma a baki ya kasa furta hakan, ya kasa iya tambayar Aseef ɗin komai, sai dai kawai ya bishi da idanu, komai zai yi ba zai iya tambayarsa menene yasa ya yi ba....... E lallai da akwai cakwakiyar gaske kenan.

Binciken ɗaku nan da ya fara yi ne, a nan ne ya cikaro da Dr Salman da kuma Ayla a ɗaki ɗaya suna zauna, sun buga uban tagumi, dama idan baku manta ba, Ayla mutuniyar Dr Salman ce sosai, sun saba tun zamanta a Daular a shekarun baya, dan haka ko da ta sake dawowa a yanzu, sai kawai ta koma ɗakinsa ma da zama tun da bata da abokan hira. Bayin Allan, da kallo ɗaya zaka yi masu kasan suna cikin tsananin firgici da tashin hankali, sun wahala over, duk sun yi wani tsuru tsuru da su.

Da kallo ɗaya ya yi wa Dr Salman duk da tsufan da ya yi, ya gane cewa shi ne kakansu, dan babu in da Abbi ya baro shi a kamanni, akwai kaman ƴaƴansa a tattare da fuskarsa.

Bai ɓata lokacin ba ya faɗa cikin ɗakin tare da yi masu bayani a tsaitsaye na cewa sun zo fitar da su ne, sannan ya ce su je ba ɓata lokaci, suma basu ɓata lokaci ba wajen mikewa su bi bayansa, saboda Allah ya gani sun gaji da wannan bakar gida ta bakaken azzaluman.

Kafin su fito Aseef ya kashe waɗan nan mutane dukka, yana tsaye a harabar wajen yana aikin gyara agogon hannunsa da suka kwance mashi a wajen faɗa, ko a jikinsa, bai sha wahalar faɗa da su ba sam sam.

Nunawa su Dr Salman Aseef ɗin Areef ya yi yana faɗa masu su je wajensa, shi kuma bari ya nemo sauran jama'ar da suka zo ɗauka. Ba musu suka amsa da to, suka wuce izuwa wajen Aseef ɗin, shi kuma Areef ya sake komawa yana leƙa ɗakunan.

Suna zuwa Aseef ya rungumi Dr Salman yana faɗin "Welcome ɗan tsoho". Duk da cewa Dr Salman bai san su waye su ba a gare shi, bai hana ya rungumi Aseef ɗin ba shi ma. Yana ƙoƙarin yiwa Aseef ɗin magana ne suka jiyo muryar Areef daga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen yana faɗin "Aseef come and see something".

Kallon Dr Salman Aseef ɗin ya yi. "Ɗan tsoho ku jirani a nan kada ku motsa ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sakin Dr Salman ɗin, da sauri ya nufi in da suka jiyo muryar Areef ɗin.

Yana zuwa ya faɗa cikin ɗakin, sai kallonsa Dr Salman yake yi har ya kurewa ganinsa, ɗan tsoho yaga rayuwa iya ganin idanunsa, baki ma ba zai iya faɗar irin abin da Dr Salman ya fuskanta na kalubalen rayuwa ba, sai dai muce Allah ya kuɓutar da su.

Aseef yana faɗawa cikin wannan ɗaki me zai gani? Heartbeat nasa ne a ɗaure cikin wasu sarkoki. Wani irin sanyi ya ji a ransa, da sauri ya karisa gareta, Areef yana ta ƙoƙarin yanda zai yi ya kwance waɗan nan sarkokin, shi kuwa Aseef ɗin yana zuwa ya rungumota yana faɗin ya yi missing nata over. Ita kuwa tana ganinsa ta sa mashi kuka, yi take yi babu kama hannu yaro, haka ya hau rarrashi, sai gaya mashi abin da ta gani da abin da suka yi mata take yi, baya sauraronta ma, shi dai burinsa kawai ta yi shiru, amma ta kiyi sam sam, shi kuma Areef yana ta ƙoƙarin yanke waɗan nan sarkoki.

Can kuma ko me ya tuna, sai ya fara karantawa sarkokin karatun Alqur'ani mai girma, nan take suka fara kwancewa suna zubawa kasa, kan kace me sarkokin duk sun zama gari, hakan kuma tasa ɗakin ya yi wani irin haske, sannan kuma ya fara wani irin rugugi tare da surutai da wasu irin muryoyi marasa daɗin ji.

Cikin hanzari Areef ɗin ya ce "Kai Aseef da matsala fa a dakin nan, ku wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login