Showing 243001 words to 246000 words out of 270744 words

Chapter 82 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4668

zai iya zama sanadiyar rugujewarsu, domin ayar Allah ta wuce wasa, ya isa haka kukan nan, jeki ki kwanta a ɗaki ki huta kin ji? Bari mu fara bincikar a ina suke, da ban yi niyar shiga office this week ba, amma saboda uncle yau ba sai gobe ba zan fara aiki, so keep praying for us my pleasure". Yana magana yana shafa kanta izuwa bayanta.

Su Areef kam sun mayar dasu tamkar wasu Tv, sai kallonsu suke yi, sir Safwan kam duk sai ya ji wlh ba zai iya hakuri ba, dole shi ma a ɗaura mashi aure da Maryam ɗinsa, dan gaskiya shi ma yanzu a hannu yake, ya gaji da kallon irin wannan madarar soyayya da ƴan uwansa suke zubawa a tare da matansu, ga shi shi ne babba amma har matar Aseef da Areef suna da ciki shi ko auren ma bai yi ba bare ya yi tunanin ko ya zura kwallo a raga.

"Noorish ka barni a tare da kai, ka barni kusa da kai, Allah ba zan iya zuwa ɗaki na kwanta ba, ni dai zan zauna da kai".

Kasa kasa ya ce "Haka kike so?".

Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e haka take so.

Ɗan rungumarta da kyau ya yi yana faɗin. "To shikenan ki zauna a tare da ni ɗin, amma ki dai'na kukan nan, promise me that ba zaki sake zubar mun da hawayen nan naki mai tsada ba".

Zuro hannayenta ta yi ta bayansa ta ƙanƙame shi da kyau tana faɗin. "I promised you, ba zan sake hawaye ba".

Ɗan duƙo da kansa kasa kaɗan ya yi ya sumbaceta a 4head nata.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗago da kanta, har lokacin yana duke a kanta, hakan ya bata dama ta sumbaci lallausan lips nasa.

Kasa hakuri sir Safwan ya yi har sai da ya ce. "Wai ni kam Saif me ka mayar damu ne?".

Sai a lokacin Rimshar ma ta tuna da cewa ashe QUADRUPLE nasu suna wajen, wani irin kunya ne ta ji ya kamata, nan take ta hau ɓoye fuska a jikin Noorish ɗin nata.

Shi kuwa Lion kallon ina ruwanka ya wurgawa sir Safwan ɗin kafin ya ɗan raba jikinsa da nata, sannan ya riko hannunta suka isa gaban computers da suke a cikin room ɗin.

Zama ya yi a saman ɗaya daga cikin chairs dake a gaban computers ɗin, sannan ya ɗaurata a saman laps nasa tare da kwantar da kanta a saman Lion chest nasa, in a low voice ya ce.

"Kwanta ki yi barci, kada fa ki tashi, zan yi aiki ne".

Hannunta ɗaya ta kai ta saƙalo ta bayan wuyarsa tare da gyara kwanciyar tata tana faɗin.

"In kwanta dai in yi ta kallon kyakkyawar fuskar mijina domin na haifi mai kama da kai".

Jin ta kawo zancen haihuwa yasa ya kawar da zancen da cewa.

"Ta yaya aka yi ne ma kike iya banbanta ni da kowa Meesha?, ya aka yi kika gane bani bane na fita tare da daddynki?".

Ɗayar hannunta ta ɗaura a saman lallausan kumatunsa tana shafawa a hankali ta fara magana in a cool voice.

"Wanda ya fita a tare da daddyna yana da wani tambari na wani zane a wuyarsa, kai kuma baka da shi, sannan wanda ya fita a tare da daddyna sajensa bai kai naka kwanciya ba kuma bai kai naka baki da yawa ba, sannan kuma fuskarsa bata da kyau duk da yana kama da kai, da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci face ɗin sanyata ya yi, dan bata ma zauna dai'dai da jikin wanda aka sakawa face ɗin ba, jikinsa ma bata da kyan gani, kuma yana da wani huji kamar sami a wajen kunnensa ta sama, and kuma a hannunsa na dama akwai wani abin hannu wanda kai sam baka saka ire iren su, iya watch kawai kake ɗaurawa".

Tun da ta fara magana ya tsareta da idanu yana kallon ɗan bakin nan nata, ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, lallai tana da kaifin ƙwaƙwalwa, yanzu da kallo ɗaya ta yi wa wannan guy ɗin irin wannan sanin haka? Har ta san da akwai wani abu a hannunsa daya ɗaura, sannan har tasan da wani ɓuli ta wajen kunnensa, duk da suit da yake a jikin guy ɗin har ta iya gane akwai zane a wuyarsa, lallai tana da kaifin kwakwalwa, bai kamata ya bar kwakwalwar nan tata ta tafi a banza ba, dole ya mayar da ita school, dan shi kansa zata taimaka mashi a kujerar da yake kai a yanzu, ga shi yanzu ma ta taimaka mashi, domin bai lura da akwai zane a jikin guy ɗin ba, bai kuma lura da akwai wani abu a ɗaure a hannun guy ɗin ba, yanzu ta taimaka masu sosai, dole ya yi bincike a kan wannan zane da abin hannu, yasan ba shakka zasu taimaka mashi.

"You're special my Meesha".

Ya faɗa tare da kunna computer dake a gabansa.

Ganin ya kunna computer ne yasa Areef and sir Safwan suka kariso wajen, shi kuma Aseef ya yi suman tsaye ne ya faɗa duniyar tunani.

"Areef ka kawo mun video wajen taron nan yanzu, ina da buƙatar na sake ganin wannan guy ɗin". Cewar Lion ɗin.

A hanzarce Areef ɗin ya ciro wayarsa tare da kunnata, data ya kunna dan ya je ya ɗauko videon.

Aiki suka hau yi a kan guy ɗin babu kama hannun yaro, a tare suke yin komai, Lion, sir Safwan and Areef, shi kuwa Aseef sai dai ya bisu da ido kawai yana kallonsu, suna cikin damuwa, sosai Aseef ya rage zama a tare da Akila, kullum yana ɗakin bincike suna aiki, computers nasu gabaɗaya sun kasa iya binciko masu ainahin in da daddyn Rimshar yake, ko number daddy suka bi sai ya rinƙa nuna masu wajaje daban daban a kallah sun kai 20, kuma dukka manyan kasashe ne, number guda ɗaya a ƙasashe daban daban har guda 20 ai ku daga ji kunsan tsafi ce kawai take aiki, abin dai ya ci tura, ya sha gaban tunaninsu, duk yadda kuke tunani ya wuci hakan.

Wasa wasa har tsawon good three months babu daddyn Rimsha babu mummy babu labarinsu, idan hankalin QUADRUPLE ya yi dubu ɗari to fa ya tashi, sun shiga damuwa, sun rasa mafitar ta ina zasu nemo uncle ɗin nan nasu.

Ita kuma Rimsha, da yake baiwar Allah ce mai tawakkali, sai ta ragewa mijin nata zafi a kan zafi, sai ta janye daga jikinsa ta koma zaman cikin bedroom tana aikin yin sallah da yi masu addu'ar samun nasara, komai ya yi zafi maganinsa Allah, har azumi take yi sosai. Tabbas tana cikin damuwa na wuce misali, dan har rama sai da ta yi, amma hakan bai sa ta mance da cewa Allah shi ne maganin komai ba, bai sa ta mance da cewa Allah shi ne ya bata iyayen nata ba, baisa ta mance da cewa Allah ne kaɗai zai iya kawo masu mafita ba, dan haka ta koma ga Allah ta dukufa da azumi, sallolin nafila, karatun Alqur'ani mai girma babu kama hannun yaro.

Ba ƙaramin daɗi Lion ɗin ya ji ba, ya kara jinjina mata sosai, a kakanun shakarun nan nata tana da karfin imanin da ba kowani bawa ne yake samun baiwar hakan ba, da wani bawa ne wannan bala'i ta afka mash, rashi uwa da uba lokaci guda, da mantawa zai yi da addu'a ko sallah ya yi ta aikin rusa kuka, amma ita sam bata yi hakan ba, dan tasa babu wata mafita a kukan ma idan ta yi.

Yana da kyau muyi koyi da halin Rimsha my peoples, a duk lokacin da wata iftila'i ta afka mana komai girmanta, to muyi ƙoƙari mu tuna cewa babu mai fitar damu daga cikinta face Ubangijin talikai, mu yi ƙoƙarin danne zuciya mu kori shaiɗan mu koma ga Allah, hakan ce kawai zata sa mu rinƙa samu magungunar matsalolinmu, kada ki yarda wani damuwa ya sameki ki zauna kina kuka ko ki tafi kina yayatawa jama'a, babu abin da jama'a zasu iya yi maki wanda Allah bai rubuta maki ba, ko yaya jama'a suka kai ga son taimaka maki in dai Allah bai kaddaro shi a kaddararki ba to wlh a banza ne, gara maki ki koma ga Allah, ko ba komai zaki samu sauki!!. ALLAH KASA MU DACE.

Wasa wasa daddyn Rimsha and mum sun doshi wata na huɗu kenan a yanzu, babu su babu labari.

Gwaggo ta shiga tashin hankalin da yasa Lion bashi da zaɓin da ya wuce ya sanar da ita gaskiyar abin da yake faruwa, domin suna da buƙatar addu'arta.

Jin abin da ya faru da kanin nata ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba, hakan yasa har sai da ta kwanta a gadon word room nasu, sai da ta yi jinya na tsawon sati ɗaya.

Su brr Naurat kuwa, Lion ɗin ya barsu a matsayin ya aiki daddyn Rimsha yin wani aiki a kasar England, dan haka wata shidda zai yi ya dawo, hakan yasa basu tashi hankalinsu ba, Lion ɗin yana kwantar masu da hankali sosai, ya kuma ce masu ba zasu yi magana da daddyn a waya ba saboda yanayin aiki.

Ita kuwa gwaggo bata iya ɓoyewa Dr William nata gaskiyar da Lion ya sanar da ita ba, ta gaya mashi, domin ya shiga damuwa na wuce misali ganinta a cikin damuwa da yake yi, hakan yasa ta gaya mashi gaskiya.

Sosai hankalinsa ya tashi, dukufa suka yi a kan addu'a babu kama hannun yaro.

Jehan da Akila kuwa suna ta aikin tura cikinsu, cikin Akila wata shidda yanzu ya shiga na bakwai, na Jehan kuma ya shiga na shidda, batun zuwa Nigeria ɗaurin aurensu Aafia kam tuni ya kwanta, dan ba'a sake bi ta kan zancen ba, da dai gwaggo taga Tga ba zai iya hakura bane kawai ta ce gara a ɗaura auren a nan daga baya zasu je Nigeria a sake shagalin biki.

Hakan yasa a cikin satin nan Shaikh Sultan ya ɗaura aurarraki guda ukun, Aafia and Sudais, wato Tga, sai Mahhir and Adiva, sai kuma Sir Safwan and Maryam. Sam ƴan Nigeria basu san da zancen bikin ba, gwaggo ta ce a bari sai sun je kawai a sanar dasu, hakan kuwa aka yi.

Yau ta kama weekend, Lion bai je office ba, kuma har yau bai koma white house da familynsa ba, ya bari sai ya gano daddyn Rimsha, so har yanzu yana cikin Daularsa ne.

Kwance yake a saman katafaren bed nasa, jikinsa na sanye da pajamas launin sky blue, ya yi shiru yana tunani, while ita kuma Rimsha tana zaune a saman sofa tana shan ruwa. Daga ita har Lion ɗin sun yi wani irin rama sosai, duk suna cikin damuwa, sai dai su danne kawai suna ƙoƙarin farantawa juna.

Wayarsa da take a saman bedside drawer ne ta yi kara, lumshe idanuwansa ya yi tare da sake buɗesu a hankali kafin ya ɗan juyar da kansa izuwa kan wayar. Hannu ya miƙa ya jawota, dai'dai saitin face nasa ya kawota.

Ganin cewa...........

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*



E50


Ganin cewa massage ne da ɓoyayyiyar number yasa ya ji kamar ba zai buɗe ba, dan baya da bukatar karin ciwon kai a kan wanda yake fama da shi a yanzu.

Har ya mayar da wayar ya ajiye, sai kuma wani tunani ta faɗo mashi a ransa, idan sako ne a kan daddyn Rimsha fa?.

Tunawa da hakan ne yasa ya yi sauri sake ɗauko wayar tasa.

A hanzarce ya buɗe saƙon dan ya gani. Wani irin miƙewa a dubu ɗari ya yi lokacin da idanuwansa suka sauka a kan sako. To me ya gani haka?.

A ɗari ya zaro idanuwansa waje sosai kafin ya miƙe tsaye mai gabaɗaya.
Kofar fita daga cikin bedroom ɗin ya nufa ba tare da ya yi magana ba, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan ya shiga tsananin tashin hankali na wuce misali.

"Noorish ina zaka je?". Rimsha ce ta jefa mashi wannan tambayar.

Sam bai bi ta kanta ba, bai amsa mata ba, da alama ma bai ji me ta ce ba, baya a tare da ita, hankalinsa ya yi gaba. Waje kawai ya fice abinsa cikin tsananin tashin hankali.

Bin shi da kallo kawai ta yi, da farko kamar zata tashi ta bi bayansa, sai kuma ta yi tunanin irin halin da suke a ciki, dan haka sai kawai ta cigaba da zamanta.

Yana fita ɗakin bincikensu ya afka, a hanzarce ya dannawa Tga, Mark, sir Safwan and Areef kira.

Cikin ƴan mintocin da basu fi uku ba sai ga su nan sun shigo kusan a tare, Uncle T shi ne a gaba.

Lion ɗin yana a tsaye a gaban wata makekiyar desktop computer, ya harɗe hannayensa a saman Lion chest nasa yana jiran shigowarsu.

Cirko cirko suka tsaya ta bayansa suna kallon shi, dukkansu an rasa mai iya tambayarsa menene yake faruwa? Meyasa ya kirasu? Sun kasa iya tambaya, saboda yanayin yanda suka ga face nasa babu ɗigon annuri ko miskala zarratin.

Ganin sun shigo ne yasa ya yi connected na wayarsa da wata desktop computer da yake a gabansa, sannan ya juyo da kallonsa a kansu.

"General ka yi waya headquarter Major ya shirya tawaga kamar yadda na gaya maka jiya, tafiyar ta kamaku, Areef sai ka shirya saka kaki a yau, dama ai da gangan ka ce ba zaka shiga office this week ba, to tafiya ta kamaku, kuma dole kai da Tga and Mark ku zaku jagoranci tawagar sojojin". Cewar Lion ɗin.

Mu koma baya kaɗan, farkon shigar Lion office, a week da ya shiga ya fara aiki, ya rubuta later wa Chief of Army's Staff nasa, ya bukaci da Tga ya tashi daga matsayin General ya koma tsohuwar muka min Lion ɗin, wato General of The Army's, hakan kuwa aka yi, shi kuma Areef sai aka bashi muƙamin Tga ɗin, wato General, shi ne ya ce ba zai shiga office a yanzu ba, gaskiya shi sai ya sake shiryawa ya karɓi training na musamman daga wajen Uncle T ɗin, shi kuma Mark aka kara mashi matsayi zuwa lieutenant General, Aseef da Handsome sun koma school, Sir Safwan kuwa sun yi cancel na aikinsa da yake a kasar China, abinku da mulki yanzu tana a hannunsu, Lion ya bashi irin wannan aikin a nan U.s ɗin, so a yanzu Sir Safwan ɗin shi ne Defence minister. Wannan shi ne abubuwan da suka faru bayan shigar Lion ɗin office.

A zabure dukkansu suka kurawa screen ɗin wanna makekiyar desktop computer ido, da mamaki suka dawo da kallonsu a kan Lion ɗin.

"Saif what are we seeing?". Cewar sir Safwan.

Areef ne ya karɓi zancen da cewa. "Kenan Lion dama you know in da uncle yake? Kenan kasan komai? Kenan da sa hannunka aka ɗauki uncle ɗin? To meyasa ka yi hakan?" Ya jero mashi tambayoyin ne cikin tsananin tashin hankali, yana magana kuma idanuwansa suka a kan desktop computer, yana kallo babu ko kyaftawa.

Ba komai suke kalla a saman screen ɗin wannan computer ba face hoton daddyn Rimsha a ɗaure da sarkoki a cikin wani ƙungurmin daji, ga kuma map na computer tana nuna masu in da location na dajin yake! To ina mummyn Rimshar kuma?.

"Saif talk to us, amsa us, kenan kasan da cewa za'a ɗauki uncle? Meyasa ka yi hakan?". Cewar sir Safwan.

Mark kam ya kasa yin magana, kallon screen ɗin computer kawai yake yi babu ko kyafta idanu.

Areef zai sake yin magana Lion ɗin ya ɗaga masu hannu tare da cewa. "Amsa kuke son na baku ne, ko kuma dai cigaba da jero mun tambayoyi zaku yi?".

Shiru suka yi suka zuba mashi idanu.

Shiru shima ya yi na a kallah good 10 mins kafin ya yi ɗan gyaran murya, sannan ya fara magana in a cool voice, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

"Ban san cewa zasu ɗauki uncle ba, abin da na sani kawai shi ne dole zasu so ɗaukar ɗaya daga cikin family, kuma na yi hasashen maza zasu ɗauka ba mata ba, hakan yasa dukkanku na sanya maku na'urar bi diddigi a jikinku ba tare da saninku ba, duk wani namiji da yake a cikin gidan nan to akwai wannan na'urar a jikinsa, na yi mamakin ya aka yi tsawon watanni na'urar dake jikin uncle bata aiki sai yau, i think in da suka kai uncle ɗin da farko suna amfani da software na hana bin diddgi ne, a yanzu kuma sun canzawa uncle ɗin waje, sun fitar da shi zuwa wani wajen, sun yi hakan ne kuma domin su ɗauki hotonsa su turo mun kamar yadda suka yi ɗin, sun yi hakan ne kuma dan hankalina ya tashi, na shiga damuwa, sai dai basu san cewa hakan da suka yi shi ne zai kawo karshensu ba, dan fitar da Uncle ɗin da suka yi daga in da suka kai shi da farko ne yasa na'urar jikinsa ta fara aiki, dan haka ga location da komai da komai a jikin computer nan, sai ku fara aikinku, kada ku kuskura ku bar ko mutun ɗaya da rai face Anderson and His

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login