Showing 186001 words to 189000 words out of 270744 words

Chapter 63 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4635

manta karon mu ta farko kenan? To a da can baya ma kenan, bare kuma yanzu da ke ko da ido kika ganni kin san na wuce dukan kato ko katuwa, sai dai dukan ruwan sama da kuma iyaye wanda suma nasan ba zasu ɗaura hannunsu mai albarka a jikina da nufin duka ba, sai dai su ɗaura hannunsu a jikina dan su samin albarka, ke yanzu kinsan zaren ba kalar yadin bane, ni yanzu bani da lokacinku, kawai ku bani su Adiva nake so, banzaye kazaman banza, sai warin bleaching kuke yi, kamar mutun ya yi amai, shashasshu, karyoyi, kadangarun bariki masu bakin iyaye kawai!!".

Hannu Zinariyar ta cire zata zabga mata mari, cikin hanzari Jehan ɗin ta yi ƙoƙarin kai hannunta ta tare mari, sai dai bata kai ga yin hakan ba Areef dake tsaye a gefe yana binsu da kallo yana mamakin confidence irin ta matar tasa ya rigata, damke hannun Zinariyar ya yi tare da ɗauketa da wani gigitaccen mari da ɗayan hannunsa, kafin kuma ya sauke hannun nasa daga marin da ya yi mata ɗin, tuni numfashinta ya ɗauke diff ta sume, dama kunsan ita Zinariya ƴar a lallaɓace, duk duniya ya cinyeta, ta zama ragwaɓaɓɓiya, maza sun yi bidirinsu a kanta ba iyaka, babu wani abin azo a gani da ya saura a jikinta, sai uban talauci, ga muni da bleaching kamar ya kashesu, shegu sai wari suke yi, sun sayar da duk wasu albarkatun da ni'imar da Allah ya yi wa jikinsu, amma har yau sun kasa yin dukiya, kullum suna cikin talauci, dama in dai ta hanyar saɓon Allah ne ba zaka taɓa yin arziki ba, sai dai ka rasa komai naka, daga karshe ka faɗa cikin musifa, ga tsinuwar Mala'iku ga kuma fushin Ubangiji, bugu da kari ga azabar da Allah zai maka, me ribarka na saɓawa Allah to? Tun farkon duniya har kashenta babu wanda ya taɓa cin riba a saɓon Allah, hakan ma ta isa bawa ishara da kuma aya mai girman gaske, duk wanda ya saɓawa Allah tasa bata kyau, Allah ka iya mana ka mana mai kyau, su dai su Zinariya tasu bata yi kyau ba sam sam.

Ganin ta sume ne yasa ya saki hannun nata ta zube kasa wanwar kamar wata kayan wanki, guntun tsaki ya ja tare da ɗago da kallonsa a kan Hjyr daɗin. Duk sun yi wani tsuru tsuru da su, tsantsar tsoro ya bayyana a saman face nasu. Jiki na rawa Hjyr ta fara ƙoƙarin kiran waya dan mutanenta masu ɗaure mata gindi su kawo mata agaji.

Shiru Areef ɗin ya yi mata, ko a jikinsa, dan yasan call ba zata tafi ba a wannan gida dai, bai shigo ba sai da ya shirya, tsawon watanni huɗu yana bincike a kansu, ya sha aiki kafin ya iya gane komai a kansu, har waɗan da suke ɗaure mata gindi a kasar duk ya sansu, sai dai a yanzu bashi da isasshen lokacin da zai tsaya ya ce zai bisu ɗai ɗai ya kashesu, saboda kurar da suka tayar a U.s ma kawai ta ishesu, ga zaɓe na gabatowa, bugu da kari a yanzu basu da goyan bayan His Excellence, hasalima faɗa suke yi da shi, kuma wasu manya ne daga cikin manyan kasar suke tallafawa Hjyr, so dole sai a gwamnatance za'ayi maganinsu, hakan yasa kawai ya bar batun rushe gidan sai bayan zaɓen U.s, su Adiva ɗin ma abin da yasa ya zo ɗaukarsu shi ne, Jehan tana damuwa sosai a kansu kullum, yasan da hakan, sannan Adiva ƴar uncle ɗin su Jehan ɗin ce, ba zai so wani abin ya sameta ba, ko dan amanar da mahaifinta ya rike wa daddyn Rimshar, shi ne yasa yazo ɗaukarsu kawai.

Sam call yaki tafiya, ganin haka yasa Hjyr ta fara ƙoƙarin gudu ta fita daga cikin office ɗin, ita ma ƴar gold ƙoƙarin guduwa ta fara yi dan ta fita.

Tsawa ya daka masu wanda yasa dole suka dakata, cikin fusata ya ce ko ta gaya mashi a in da su Adiva suke, ko kuma ya kasheta a nan ya kashe banza! Shi su Adiva kawai ya zo ɗauka, babu ruwansa da su.

Bata da zaɓin da ya wuce ta gaya mashi, murya na rawa ta gaya mashi cewa Maryam tana cikin ɗakinsu bata da lafiya, ita kuma Adiva jiya a daddare an fita da ita.

Idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci a wannan lokaci, sam bai san time da ya ɗauke Hjyr da wani ɗan iskar matsiyacin mari ba.

Wani irin ihun azaba ta saki, tsabar azaba bata ma san time da bakinta ya furta masu address ɗin in da aka kai Adiva ɗin ba, sake kara mata wani matsiyacin lafiyayyen marin ya yi, sai gata a kasa ta zube kamar kayan wanki, kamar wata mushen doki.

Ita kuwa Jehan tana jin abin da ta ce ta juya a guje ta nufi ɗakin nasu tun da already ta san hanya. Ƴar gold kuwa, tuni idanu ya rai'na fata, jiki sai kerma yake yi, tana jiran ta ji nata saukar marin. Sai dai bai bi ta kanta ba, juyawa ya yi ya bi bayan Jehan ɗin.

A kwance rai a hannun Allah suka isko Maryam, sam bata a cikin hayyacinta, bata iya gane su waye ne ma a kanta, ga dai idanuwanta a buɗe, ta yi wani uban rama tamkar wata figaggiyar kaza mai kwanci, harta gashin kanta sai da ya sauya launi, sai Allah ne kaɗai yasan me wannan tsinanniyar Hjyr ta yi mata, ko da Jehan ta ambaci sunanta ma, sam bata iya amsawa, bata iya magana, kusan irin ciwon da A'isha ta yi suka je suka jefar da ita, to kusan hakance ita ma Maryam ɗin take fama da shi.

A hanzarce Areef ɗin ya ɗauketa cak, dan gani suke tamkar zata mutu kafin ma su fita da ita daga cikin gida, dan idan baku manta ba a tsakanin ginin farko ba gidan da kuma in da su Jehan ɗin suke da akwai tazara mai yawa, hope baku manta yadda tsarin ginin gidan yake ba?.

A hanzarce suka fito da ita, bai sake bi ta kan kowa da yake a gidan ba suka fice. A gidan baya na motarsu suka sanyata, da gudu Jehan ta shiga gidan gaba, shi ma ya shiga mazaunin driver, a haukace ya tashi motar suka bar gidan.

Ita kuma Hjyr daɗi tana baje a kasa kamar mushen doki, sai Allah ne ma kaɗai yasan tana raye ko ta mutu, haka zalika ita ma Zinariya, sun ji hannun maza, ƴar gold kuwa, gabaɗaya a tsorace take, sai mamaki take yi ta yaya aka yi su Areef suka iya shigowa wannan gidan nasu da mutane basu iya ganinsa sai wanda Hjyr ta zaɓa zai shigo mata? Abin ya ɗaure mata kai, basu san cewa a shirye da addu'a sosai Areef ɗin ya zo ba.

Hospital mafi kusa da gari suka fara kai Maryam ɗin, idan baku mance ba gidan Hjyr daɗi yana ɗan bayan gari ne. Sai da suka tabbatar da likitoci sun dukufa a kanta, sannan ne ya ce su je su ɗauko Adiva kuma a wannan address ɗin da Hjyr daɗin ta gaya masu, haka kuwa aka yi, suka baro asibitin, sun baro likitoci a kan Maryam ɗin sunata fama, a haka suka nufi in da Hjyr ta gaya masu.

Bayan sun fito daga cikin hospital ɗin, tambayar Jehan ɗin ya yi a kan ko tasan wannan address ɗin da Hjyr daɗin ta faɗa?.

"A'a Yah Areef ban sani ba, amma mu tambayi mutanen da suke wucewar nan mana, kila zasu sani".

Jinjina mata kai ya yi tare da yin parking na motar a gefen hanya ya sauke glass ɗinta kasa.

Can wani matashi yazo zai wuce, dakatar da shi ya yi tare da yi mashi sannu, sannan ya gaya mashi abin da suke nema.

Ɗan zaro idanu matashin ya yi kafin ya basu amsa da cewa "Kai wannan waje fa ba wajen zuwa bane, yana da uban nisa sosai daga nan, sannan kuma............

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



Date: 22/5/2024



E37


Ɗan zaro idanu matashin ya yi kafin ya basu amsa da cewa "Kai wannan waje fa ba wajen zuwa bane! Yana da uban nisa sosai daga nan, sannan kuma kungurmin daji ne sosai, zaku sha tafiya".

Kallon Jehan Areef ya yi, saboda da Hausa matashin ya yi magana, su kuma TRIPLETS kun san basa jin hausa ko kaɗan, so bai ji me guy ɗin ya ce ba.

Mayar mashi da abin da guy ɗin ya faɗa da turanci ta yi, sannan ta ɗaura da cewa guy ɗin ta ina ne hanyar da zasu je wannan waje?.

Kwatance ya yi masu ta hanyar, sai ka fita daga cikin Abujar, sannan ka sauka daga titi ka fara kutsawa cikin daji, sai sun yi tafiyar sama da awa guda kafin su kai wajen, a wajen akwai wani katon dutse mai aman ruwa, daga wajen wannan dutse nen wannan address ɗin yake, tashin hankali!!.

Sake gayawa Areef ɗin abin da guy ɗin ya faɗa Jehan ɗin ta yi. Shiru ya ɗan zubawa guy ɗin idanu yana tunanin to ya akayi guy ɗin ya san da wannan waje kenan?. Kamar zai tambaye shi, sai kuma ya share, saboda mugaye a duniya dai ba zasu kare ba, sai dai kawai Allah ya yi mana tsari da su!.

Kunna motar ya yi bayan sun yi wa guy ɗin godiya, ɗaukar hanya suka yi babu kama hannun yaro, gudu sosai Areef yake shararawa kamar babu gobe, ita kuwa Hjy D.P.O lefewa ta yi a jikin kujerar motar tare da lumshe idanuwanta tana jin sanyin A.c na ratsa ta.

A ɓangaren su Lion kuwa, sun isha Washington DC lafiya, kasancewar ba tafiyar sirri bace, kamar yadda kuka sani ne airport ɗin a cike take tab da manya manyan jiga jigan masu faɗa a ji a kasar, ga jiga jigan sojoji ta ko'ina rike da jiga jigan bindigu masu aika sako babu saɓa saiti, suma ƴan'sanda ba'a barsu a baya ba, sun cike ko'ina suna shawagi, sannan ga ƴan jaridu rirrike da cameras a hannunsu ta ko'ina, jira kawai ake yi ya fito su fara aikin ɗaukarsa a hoto.

Sai dai kuma fitowarsa ta tada hazo mai matuƙar kurar gaske, dan kuwa ya fito ne ɗauke da sir Arvin a saman kafaɗunsa, wadda kuma kunsani kamansu ɗaya sak, wasu daga cikin mutanen dake a airport ɗin ma sun kasa banbance Lion na gaskiya, wasu su ce shi aka ɗauko a saman kafaɗa, wasu kuma su ce shi ne ya ɗauko wani mai kama da shi. Kan kace me magana ta karaɗe kasa bakiɗaya, kowa so yake yi yasan wanene ɗayan? Sai dai kuma an rasa mai iya tunkararsa ya tambayesa wanene sir Arvin? Abin da kuka sani ne, kowa tsoronsa yake ji.

Aseef dake cikin mota yana jiransu ma bai san time da ya fito waje daga cikin motar ba, saboda sir Arvin, sam Lion bai gaya masu zancen sir Arvin ba, ko Areef yaki sanarwa, kai har gwaggo bata sani ba, ya barsu ne sai ya dawo gidan kawai suga zahiriya da idanuwansu, so abin ya girgiza Aseef sosai, ya kasa hakuri ma har sai da ya tambayi Lion ɗin wanene sir Arvin?. Jama'a duk sun kasa kunne dan su ji amsar da Lion ɗin zai bada, duk wasu ƴan siyasa dake a wajen burinsu kenan su ji amsar da zai bada. Sai dai kuma kamar yadda kuka sani ne ko kallon Aseef ɗin ma bai yi ba bare ya amsa mashi, ya wuce kawai ya kwantar da sir Arvin a cikin mota, sannan ya shiga gidan gaba.

Da dai Aseef ɗin yaga da gaske ba zai amsa mashi ba, sai ya daure ya juya ya nufi motar, sai dai bai kai ga shiga ba su Handsome suka fito daga cikin jet ɗin, bodyguards na Lion ɗin suna a biye da su a baya.

Da sauri Aseef ya kara zaro idanuwa yana kallon Handsome mai kama da shi, ba shakka Handsome ya yi kama da shi, sai dai ba cancan sosai ba, kama ce dai ta jini, amma Handsome ya fi kama da jinin Chinawa, bai yi zubin Americawa sosai ba.

Gabaɗaya jama'a haɗe da Aseef ɗin basu gama tsinkewa ba sai da suka ɗaura idanuwansu a kan Pinky dake rike da hannun Handsome gam, yarinya kyakkyawar gaske kamar ita ta yi kanta, ga shegen shiga rai kamar Rimshar Lion, sannan babbar abin rikitarwa shi ne kama da su Lion ɗin da take yi, kunga kuwa dole ta yi kyau iya kyau ai, saboda wannan kama, ga idanuwanta dara dara kamar nasu, kuma idanuwan blue eyes, ya kuke tunanin kyanta zai kasance? Kama da Lion fa aka ce maku, ai dole nema kowa idan ya kalleta sai ya sake kallonta, mummynta ta ɗaure mata kyakkyawar gashin kanta gida biyu, an zuba mata rebons masu flowers, sai gashin ya yi matuƙar kyau, ga shi dark black, sai kyalli yake yi, sai dai bai kai nasu Lion curly ba.

Kai tsaye wajen sauran motocin dake a bayan na Aseef ɗin suka nufa. Sai da suka shiga ciki, sannan ne Aseef ɗin ya iya shiga cikin motarsa shi ma, banda haka ya tsaya ne yana kare masu kallo, ga Dr William a tare da su, sai ya ji tamkar ya je ya tambayi Dr William ɗin cewa shi ne na gaske ko? Kada a sake ra'ina masu hankali, amma ganin yadda airport ɗin yake cike da mutane, kuma kowa jiran kiris yake yi a saki magana wa duniya, hakan tasa ya ja bakinsa ya yi shiru tare da komawa cikin mota zuciyarsa cike tab da mamakin wannan al'amari.

Bayan sun kammala shiga ne motocin suka tashi a tare, jama'a kowa bakinciki yake yi na rashin buɗe bakin Lion ya yi magana ko da word ɗaya ne, kowa so yake yi ya sami abin faɗa, sai dai Lion ya wuce tunaninsu, shi ko a gida ma yaushe yake buɗe baki ya yi magana balantana a wajen, wajen ma a airport, a airport ɗin ma wajen da yasan abokan hamayyarsa suna wajen, bugu da kari ga siyasar da yake a gabansa, ai dole ma su datse bakunansu dan samun zaman lafiya, in ba haka ba yanzu sai a canza masu magana idan suka yi, saboda mutun ɗan adam ya wuce tunanin mai tunani!!.

Su Cherish sun ga duniya a lokacin da suka sauke idanuwansu a gidan Lion, sai suka ga nasu gidan ma ashe kurkuku ne, su suna jin cewa su masu kuɗi ne, ashe ga nan in da kuɗin kam yake, su nasu ma duk wasan yara ne! Gidansu ko kwatan na Lion ɗin bai kai ba a girma, kyau da kuma tsaruwa, komai ma basu haɗa hanya ba, Lion ya yi masu nisa, dan ma sun yi sa'a sun zo a time da ya kwashe gabaɗaya sojojin an mayar da su barack, ai da sai sun san cewa yes nan fa gidan General of the Army's suka zo, a yanzu kuma His Excellence mai jiran gado, kai gaskiya Lion duniya ne, His Excellence ne mai jiran gado da kansa!.

Kauyanci ne karara ya bayyana a fuskokinsu, dan wasu abubuwa da suke cikin gidan Lion sam basu taɓa ganinsu ba, tun daga kan tsarin ginin gidan sun san Daula ce mai zaman kanta, sun san ba wajen wasan yara bane, Handsome dai sai kalle kalle yake yi abinsa, ba zai bari kansa ta kulle ba, duk abin da ya yi mashi kyau sai ya kallah ya sake kallah, ita ma Pinky sai kallo ko'ina take yi, idan ta ga wani abin da bata taɓa gani ba, sai ta tambayi Handsome menene wannan? Shi ma sai dai ya ce mata bai sani ba ta bari anjima zai tanbaya mata sir Arvin idan ya tashi daga barci, Okey kawai take amsa mashi da shi.

Basu kara tsinkewa da lamarin wannan Daula ta Lion ba har sai da suka shiga parlourn kasa, a nan ne suka zama ainahin ƴan kauye.

Shi kuwa Lion kai tsaye saman doguwar sofa ya wuce ya kwantar da sir Arvin ɗin, sannan ya buƙaci Aseef da ya bashi ruwa. Cike da mamaki Aseef ya wuce ya ɗauko mashi ruwa roba guda, kawo mashi ya zo ya yi, bayan ya karɓa sai ya tsaya a gefensa yana kallon wannan iko na Allah.

Su Pinky kuwa har tsoron zama a saman sofas ɗin suke yi, saboda yanayin yadda tsaruwan sofas ɗin suke, sun sha banban da sofas da kuka sani, idan ka gansu ma kai kace wasu jiragene, saboda wasu irin luntsuma luntsuma ne masu numfashi, sun ƙoshi ainun.

Shafawa sir Arvin ruwan ya yi. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, sannan ya fara ɗan motsa idanuwansa da suke a rufe a hankali hankali. Ganin ya farfaɗo ne yasa Lion ɗin ya mike daga kusa da shi ya koma saman wata sofar, zama ya yi tare da ciro wayarsa ya kunnata, dama ya yi off nata ne, saboda tafiya.

Sam bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login