Showing 36001 words to 39000 words out of 270744 words

Chapter 13 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2948

ajiyar zuciya take yi.

Zazzaƙar sexy voice nasa ne ya daki dodan kunne, a in da ya ce mata "Muje gida in dubaki ko? Daga nan kuma, sai ki gaya mani meyasa baki kirani a waya kin gaya mani baki da lafiya ba, meyasa kuma kika fita ba tare da sani na ba?".

Kara kankame shi ta yi tana faɗin "Kai NooRi yanzu ai na ji sauki, ni ba sai ka dubani ba, dan kada ka yi mani allura".

Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi, kasa kasa ya ce "Alluran ne baki so?". Jinjina mashi kai ta yi tana kara lafewa a jikin nasa, har ta mance da zancen cewa bata son shi......... Yo ba dole ta mance ba, soyayya wasa ce😂

"Okey to ba zan yi maki ba, dubaki kawai zan yi". "Noorish ina gwaggona?".

Ba tare da ya bata amsa ba, ya sanya hannu ya fara tattare mata gashin kanta da yake a watse. "Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye.

Turo baki ta yi tana ɗan waro idanun nata a hankali. Gyara mata kwanciya ya yi tare da ciro wayarsa, number Areef ya shiga, massage ya rubuta mashi a kan ya fito mata da hijabi.

"NooRi ba zaka gaya mani ina gwaggona take ba?". Ta yi maganar tamkar zata saka mashi kuka. Matso da face nasa daf da ita ya yi, kasa kasa ya fara magana kamar mai raɗa. "Ba kin gujeta jiya ba? Dan haka kada ki tambayeni".

Ɗan ɗago idanu ta yi tana kallon kyakkyawar sajensa dake a kwance luf, a hankali ta kai hannu tana shafawa. "NooRi waye ya taɓa maka sajenka?".

Ɗan zaro idanu ya yi yana kallonta, ko ya akayi tasan an taba oho mata, yarinyar nan ta gama karance face nasa tsab, yanzu taɓa sajen da gwaggo ta yi ma sai da ta gane, kai Rimsha ba dai basira ba, akwai kaifin ƙwaƙwalwa.

"Waye ya gaya maki an taɓa sajen nawa?". Turo baki ta yi tana faɗin "Ai nasan ba haka kake gyarawa ba, idan ka gyara ba haka yake kasancewa ba, dole bayan da ka gama gyarawa, akwai wanda ya taɓa shi, nasan yanda gyaranka yake ai". E lallai Rimsha ta daban ce, wato har ta haddace yanda yake gyara shagen nasa.

Wani irin daɗi ya ji har cikin zuciyarsa, hakan na nufin yana nan a cikin ranta fiye da komai, tana sane da komai na mijin nata.

Tsabar farinciki bai ma san time da ya kara matseta a jikinsa ba. "Wash Noori zaka balla ni fa". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai.

Ɗago haɓarta ya yi tare da manna mata sumbata a ɗan bakin nata, buɗe bakin nata ta yi, da ɗan karfi ta cije shi a lips nasa. Tsareta da ido ya yi ba tare da ya ce komai ba, ga face nasa kuma tamkar hadari, a ɗaure tamau. Ganin hakan yasa ta yi ƙoƙarin sake cizon nasa.

Bata kai ga sakewa ba Areef ya yi masu knocking na glass ɗin motar. Da sauri ta ɗago kanta, ganin Areef ne yasa ta yi ƙoƙarin barin jikin Lion ɗin. Bai hanata ba, sai ma sauke glass ɗin motar da ya yi ya karɓi hijabin nata.

Juyawa Areef ɗin ya yi ya koma cikin gida, shi kuma Lion ya miƙa mata hijabin a kan ta sanya, da sauri ta karɓa ta sanya. Umarni ya yi wa Donal a kan yazo su tafi. A hanzarce ya dawo cikin motar tare da kunnata suka bar gidan.

Lokacin da suka dawo gida, da gudu Rimshar ta wuce ɗakinsu, dan tana tunanin gwaggo tana can, sai da ta shiga, taga bata nan, da sauri ta dawo izuwa ɗakin Lion, nan ma bata nan, ɗakin daddynta ta nufa kai tsaye, a nan ta sami gwaggo kwance a saman bed, ta gama cin abinci ta yi wanka.

Da gudu ta haye saman bed ɗin tana dariya, shi kuwa Lion, juyawa ya yi ya fice izuwa harabar gidan gabaɗaya.

Miƙewa gwaggon ta yi zaune, nan ta rungumo Rimshar suka fara hira, labari Rimshar ta fara bata na abubuwan da suka faru a baya, har da aurensu da Lion, irin rayuwar da suke yi da shi, da tafiyarsu ƙasar Russia da suka yi, sai dai ko kusa ko alama bata bata labarin Daular Mutuwa ba, da alama an shafe mata labarinsa a cikin brain nata.

Sosai gwaggon ta yi mata nasiha a kan kula da miji, sannan ta kara mata da cewa, tun da har haka ne, to Lion yana sonta, dan Allah ita ma ta nuna mashi soyayya sosai, ta ga akwai ciwo sosai a cikin rayuwarsa, ta kula da shi, a yanzu tana a sahun gaba cikin mutanan da suke saka shi farinciki, dan Allah ta kasance mai saka shi farinciki sosai.

Gabaɗaya sai Rimshar ta ji jikinta ya yi sanyi, ba shakka akwai ciwo sosai a cikin rayuwar TRIPLETS, ga kuɗi, ga mulki, ga mukami, ga isa da izza, ga kyau, dukka Allah ya hore masu, amma kuma tun suna cikin mahaifiyarsu suke fuskantar jarabawa, babbar bala'i ce tashi da girma cikin kafurci, hakika ba kowa da kake kallon cikin Daula na ɗumbin dukiya bane bashi da damuwa da matsaloli na rayuwa, kowa da kowa yana iya fuskantar jarabawar Ubangiji ta kowace siga a kuma lokacin da baka yi tsammani ba, so yana da kyau mu runƙa kyautatawa al'umma zato, mu kuma mayar da hankulanmu a kan abubuwan da suke gabanmu, kada mu sakawa wani mai ɗan arziki idanu, dan bamu san halin da yake ciki ba, mu kyalkyalin arzikin kawai muke gani, amma na ciki, tana ciki, Allah ka bamu dacewa, ka kuma bamu ikon cin jarabawarka a duk lokacin da ka jarrabemu.

Sosai Rimsha ta ji jikinta ya yi sanyi, ta kuma yi wa gwaggon alkawarin zata yi iyaka bakin kokarinta wajen ganin ta sanya Lion farinciki. Tambayarta gwaggon ta yi a kan ina Lion ɗin yake, shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Nima ban san ina yake ba, lokacin da muka shigo dai na barshi a palon sama".

Ɗaga idanu gwaggon ta yi, ta kai kallonta a saman katafaren agogon bango da yake manne a jikin bangon ɗakin, karfe 11:30 dai'dai, dawo da kallonta a kan Rimshar ta yi tana faɗin "Rimsha ashe fa mun ɗan ɗauki lokaci muna hira fa, labarin naki ne akwai tsawo, yanzu dai jeki ki duba mani Saif ɗin nan, bai ci abincin safe ba, ki kai mashi abinci ya ci dan Allah". Ta yi maganar cike da nuna kulawa ga ƴaƴan nata.

To Rimshar ta amsa da shi tare da miƙewa, ta sauko kasa daga saman bed ɗin, waje kai tsaye ta nufa. Tana fita ta wuce bedroom nasu. Wanka ta tsala tare da zuba shirinta cikin wandon jeans fari tas da T-shirt pink color, ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai tare da zubo jelar a bayanta, ta yi matuƙar kyau tamkar ita ta yi kanta. Perfume nata ta zuba, nan take ta fara zuba kamshi tamkar ba gobe.

High heel ta sanya a kafarta, sannan ta nufo waje. A palo ta kalli ɗayar wayarta a saman sofa, cikin hanzari ta ɗauki wayar ta nufo palon kasa. Kitchen ta nufa ta ɗauko abincin Lion tare da ficewa da sauri.

Garden ta nufa da abincin, dan tana tunanin zata same shi a wajen, sai dai ina baya nan, ta sha ruwan mamaki sosai. Saman table ta ɗaura kayan abincin tare da zama a saman sofa ta ciro wayarta. Numbersa ta kira, wayar ta yi ringin har ta katse bai ɗauka ba.

Turo ɗan baki ta yi tare da sake kiransa, nan ma shiru bai ɗauka ba. A kule ta ɗaga wayar zata buga da kasa, ƴar kara wayar ta yi alamar shigowar sako. Cikin sauri ta fasa bugata da kasa tare da buɗe sakon.

Cool murmushi ta saki ganin sunan Noorinta, tun bata ga me sakon ya kunsa ba. A hanzarce ta buɗe ta fara karantawa kamar haka. "Idan kika fasa wayar nan, babu mai saya maki wani, ke da waya har abada ƴar rigima kawai". Shi ne abin da ya rubuta mata a sakon. Ta sani sarai ba wai yana kallonta bane, kawai ya riga da ya san hali ne, ya san abin da zai biyo baya idan bai ɗauki kiran ba, ya san rigimarta sarai, shi ne yasa ya yi mata sakon tun wuri.

Juya dara daran fararen Sleeping eyes nata sama ta yi, har wani walwali suka yi, ɗan girgiza kai ta yi tana magana kasa kasa ta yanda ita kaɗai zata san me take faɗa. "Allah Noorin nan nawa ya rainani da yawa". Shi ne abin da take faɗa.

(E lallai Rimsha kin girma, wai NooRi ya rai'na ta?🤔 Ba shakka kin ga gadon kwanan Lion, dole ki ce haka😂)

Shi kuwa, sai da ya gama ja mata rai son ransa, sannan ya yi mata massage a kan ta zo boys quarters na gidan ta same shi. Da kamar ba zata je ba, dan ta yi fushi na shanyata da ya yi tun ɗazun tana jiranshi. Sai kuma ta tuna cewa bai ci komai ba bawan Allah, yunwa yake ji ga kuma ɓacin ran da ya shiga. Tuna hakan yasa ta ɗauki abincin na nufi wajen. Shi ma bene ne mai hawa ɗaya, babu wanda ya taɓa kwana a wajen, komai na cikin wajen sabbi ne.

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin palon kasan. Babu kowa sai sanyin Ac da kamshin air freshener da kuma kamshin perfume ɗin na Lion ɗin dake tashi.

Haurawa sama ta yi, sai aikin turo baki take yi.

Bakinta ɗauke da sallama ta shiga bedroom ɗin da ta ji kamshin perfume ɗin nasa ya fi yawa a ta wajen.

Yana kwance saman bed, daga shi sai ƴar wando short zuwa kaɗan daga cinyoyinsa, ga wandon ya kama shi sosai, ya manne da fatar jikinsa, ba dan kalar wandon da yake fari ba, da ba zaka taɓa tunanin ma ya saka ba, saboda mannewa da jikinsa da ta yi. Sai dai ya ja bargon dake saman bed ɗin izuwa kugunsa. Da alama wanka ya yi, dan ga gashin kansa da akwai danshin ruwa. Daga ta sama kuma, yana sanye da ƴar riga mara nauyi, irin waɗan nan T-shirt ɗin masu laushi sosai, sannan masu kananan hannu.

Tun da ta shigo ya tsareta da waɗan nan dara daran idanuwan nasa masu rikitarwa yana kallonta, tamkar zai cinyeta. Ta yi kyau ne over, ji ya yi tamkar ya tashi ya rungumota. Ita kuwa, sai aikin turo mashi ɗan bakin nan nata take yi, ita a dole tana fushi.

A tsakiyar Chinese carpet dake a cikin bedroom ɗin ta ajiye abincin. Zama ta yi a gefen abincin ba tare da ta kalli in da yake ba, ta fara magana "Yaya Saif sannu da hutawa, ga abinci nan na kawo maka, ka zo ka ci dan nasan kana jin yunwa".

Nisawa ya yi yana mai cigaba da kallonta, bai ce komai ba.

Almost 10 mins suka ɗauka a haka, bai ce mata ko sannu ba, yana ta kallonta, ita kuma taki ɗagowa su haɗa idanuwa.

Da ta ga bashi da niyar motsawa, sai ta miƙe tana kumbura kumatu ta nufi waje, ta ki yarda dai ta kalli in da yake. Ko sannu bai ce mata ba. Har ta fice daga cikin ɗakin.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo wayarsa, ya yi mata massage a kan ko taku ɗaya bai yarda ta kara ba a wajen tafiyarta, ta juyo ta dawo.

Tana gama karanta sakon ta zunduba ihu tamkar wanda aka kwalawa itace a tsakiyar kai, haushi kamar ta je ta shakesa, ga shi bata isa ta ki zuwa ba, dan idan har ta kara taku ɗaya ɗin ta shiga tsinuwan Mala'ikun Allah ne, har sai time ɗin da ta zo ta bashi hakuri ya kuma yafe mata, sannan Mala'ikun za su dai'na tsine mata, wannan babban musifa ce bijirewa maganar miji, ko ba daɗi ayi hakuri a bi, shi ne zaman lafiya!!!.

Juyowa ta yi tana kuka da hawaye bibbiyu, da farko tafiyar yanga take yi ta kawo abincin, yanzu kuwa jan kafar take yi tana kuka dan haushi.

Yana kwance in da yake, bai motsa ba. Gaban bed ɗin ta zo ta tsaya, kusa da shi, tana kuka, bata ce mashi ko kala ba.

Hannu ya kai ya jawota ta faɗa jikinsa, gyara mata kwanciya ya yi izuwa saman faffaɗar kirjinsa, ɗago haɓarta ya yi ya fara lashe hawayen da ya sa suka zubo ɗin. Duka ta fara kai mashi a kirjin nasa tana faɗin "Allah Noori mun ɓata". Ta yi maganar a shagwaɓe. Kara matseta a jikin nasa ya yi tare da matse ɗan bakin nata, kasa kasa ya ce ta yi shiru ya gaya mata wani abin mai daɗi.

Jin hakan yasa ta yi shiru tana shesshekar shagwaɓa tare da kumbura kumatu. "Meyasa kika cika rigima ne?". Ya faɗa a sanyaye. Turo baki ta yi bata bashi amsa ba.

"Don't you know that you're my happiness? You know how sad I was before you came here? Kin san da na kalli face naki ya naji kuwa?".

Da sauri ta ɗago tana faɗin "Ya ka ji to?". Lumshe idanuwansa ya yi, dan yanda ta ɗago fararen idanun nan nata, ba ƙaramin tafiya da shi suka yi ba, dan yanda ta ɗagosu, har wani walwali wal wal suka yi mashi.

"NooRi to ka gaya mani ya ka ji mana?". Tana magana tana shafa lallausan bakin gashin dake kwance a hannunsa da yake rungume da ita. Bai amsa mata ba, kuma bai buɗe idanuwansa ba. Sake tambayarsa ta yi tare da saka mashi kukan shagwaɓa.

Ba tare da ya buɗe idanuwansa ba, ya matso da ɗan bakinsa sai tin kunnanta, murya kasa kasa kamar mai raɗa, sai ka rantse da Allah baya motsa laɓɓansa, cikin wata iriyar murya mai tsayawa a ran masoya ya fara yi mata raɗa idanuwansa a lumshe. "Kina shigowa cikin bedroom nan, ina ganin beautiful face naki, sai na ji na mance komai, i feel like ban taɓa jin wani ɓacin rai ba, you're special!".

Da sauri ta zaro idanuwanta tare da juyowa da kallonta izuwa kan face nasa sosai. Idanuwansa a lumshe, magana yake yi cike da class tare da izza, cikin kuma kwanciyar hankali da nutsuwa, a ko da yaushe babu ko ɗigon na hayaniya a cikin voice nasa, so silent zaka ji ta, bare kuma yanzu yanda yake magana kasa kasa, ya kuke tunanin muryar zata kasance? Hmmmm......

Hakika ya ji tsakanin kaunarta a ransa sosai saboda gwaggo, saboda yanda babanta ya kula da gwaggon, a haka ma bai san cewa Gwaggon ta fi son su Rimshar sama da kowa a cikin ƴan uwanta ba, wata kila idan ya san hakan, ko kasa ba zai bari Meeshar tasa ta sake takawa ba, saboda so........ Mu dai je zuwa, uwa ai ba wasa ba, bare su da suka ɗauki tsawon shakaru 31 zuwa 32 basu tare da ita, ai dole su so duk abin da uwar tasu take so fiye da tunanin mai tunani. Yau wani irin jin Rimsha yake yi a cikin ransa fiye da misali!.

Sosai ta zuba mashi idanu tana mamakin kalaman da yake yi, tamkar wanda ake gayamawa. Idan a baya ne ka ce mata ya iya wannan kalamai, ba zata taɓa yarda ba, babu ma wanda zai yi gigin yarda, ko TRIPLETS nasa ba za su taɓa yarda da cewa shi yake furta kalamai haka ba.

Duk da idanuwansa a rufe, a jikinsa ya ji tana kare mashi kallo, hakan yasa ya ɗaga mata gera ɗaya. Wani irin sihirtatcen kyau ya kara, ga gashin gerar nasa kullum kara cika suke yi sosai, tamkar ana saka masu taki, har ta kusa haɗe mashi, gasu a kwance luff, kyakkyawar jajir ɗin kumatunsa, wani irin laushi ne da su kamar fatar jariri, sai kyalli soft skin nasa take yi sosai da sosai, dogon hancin nan nasa, tamkar shi ya bawa kansa saboda yanda ya zauna ɗas a face nasa, sak hancin Dr William, lips nasa kuwa, ba'a magana, dan gabaɗayansu TRIPLETS Allah ya yi masu halittar lips mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, lips nasu na saman design of heart ne, na kasan kuma yana da ɗan faɗi kaɗan, gasu jajir dasu tamkar an saka masu red janbaki, ga laushi kamar fure, ga ɗan bakin nasu ɗan karami da shi, sai dara daran idanu tamkar na Dr Salman.

"Noorish, meyasa nake sanyaka farinciki idan ka kalleni?". Sai a lokacin ya waro idanunsa a kanta. A cikin idanunta ya kalli tsananin son ya ce yana sonta da take yi, tana tsananin so ta ji kalmar so daga bakinsa.

Shiru ya ɗan, kafin ya ce "Ni ma ban san dalili ba, kawai dai idan na ganki, ina shiga farinciki".

Wani irin yawu ta haɗiye, dan ba hakan take son ji daga gare shi ba, amma ba komai. Shi ma yasan ba hakan take son ji ba, tana so ne ta ji ya ce saboda yana sonta, da gangan ya bata wani amsa da ban, yana tsananin jin daɗi idan yana ja mata rai.

"Noorish kazo ka ci abinci". Ta faɗa a takaice.

"Meesha saboda ban baki amsar da kike so bane zaki nuna mani baki son cigaba da yin hira da ni?."
Girgiza mashi kai ta yi tana sunkuyar da kanta ƙasa.

"To meyasa zaki nuna kin gaji da hirarmu?".

"Noorish ni fa nafi son ne ka ci abinci, gwaggo ta ce mani baka ci komai ba, to ka zo ka ci ga ji?". "Meesha meyasa kike koyan yin karya ne?".

Zaro idanu ta yi tana kallon wuyarsa.

"Yau sau biyu kina yi mani karya, ɗazun kince mani ciwon ciki ne ya saka ki yin kuka, kuma ba haka bane, na san ba haka bane, kewata ce ta saki kuka, duba da yanda action naki ya kasance lokacin da na shigo cikin bedroom ɗin naki, wanda cikinsa yake ciwo, har ya kasa yin kuka da karfi su dad su ji su kawo ɗauki, ba zai diro kasa daga saman gado da gudu har ya nufoni zai rungumeni ba, yanzu kuma kin sake yi mani karya na biyu, why?".

"Noorish kenan kasan cewa ina sonka?". Ta tambaya tana hawaye, dan bata taɓa tunanin duk abin da take yi yana sane ba.

Ɗago haɓarta ya yi yana goge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login