Showing 165001 words to 168000 words out of 270744 words

Chapter 56 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2983

da baki ba zai iya faɗa ba, now kaga bata da lafiya, please kada ka kara mata ciwo a kan ciwo, wannan mu zaka yi wa ba kanka ba, idan wani abin ya sameta ba zamu iya jurewa ba, please ka yi tunani a kan maganar". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihunsa.

Matsowa Lion ɗin ya yi suka rungumi juna kawai ba tare da ya yi magana ba, sumbata Areef ɗin ya kai mashi a kumatu kafin shi ma Lion ɗin ya sumbacesa. "Take care". Shi ne kawai abin da Lion ɗin ya furta tare da sakinsa ya wuce izuwa wajen nasa jerin motocin.

Juyawa shi ma Areef ɗin ya yi ya nufi nasa motocin. A tare motocin suka fice daga gidan.

After some minutes suka sauka a airport, jirgi daban daban suka shiga, Lion ya shiga jirgin kasar China, shi kuma Areef Nigeria zai je, amma da yake jirgin kasuwa ya bi, sai ya bi jirgin Spain, daga can zai hau jirgin Nigeria, shi kuma Lion da yake da nasa jirgin zai tafi, sai ya zama direct kawai zai nufi China, dama idan baku manta ba ya taɓa cewa Rimsha zasu je kasar China da ita, so yanzu yanayi yasa ba zai tafi da ita ba, kun ga dai halin da take a ciki, tafiya da ita ba zai yiwu ba, suna ma wajen daban daban da ba zai yiwu su tafi a tare ba, shi ne yasa ya wuce shi kaɗai. Shi kuma Areef zai je ya ɗauko su gwaggo ne gabaɗaya, Lion ya ce duk su tattara su dawo, shi ya sallami Nigeria kenan, ba zai sake komawa ba, so Areef ya je ya tattarosu su haɗu a U.s kawai nan da kwana uku zuwa biyar......... Babbar magana, akwai aiki kam!!.

After some hours.

Lafiya lou Lion ya yi landing a Daxing international airport Beijing dake a South Beijing ɗin. Da yake shi da wasu daga cikin bodyguards nasa kawai suka zo, sai ya ce da bodyguards ɗin su fita su nemi hotel su zauna a ciki yana zuwa, idan ya kammala abin da yake yi zai nemesu, ya yi maganar tare da sanya face mask a face nasa, sannan ya fito daga cikin jirgin bayan.

Yana fita kai tsaye wajen masu taxi ya nufa da yake a wajen airport ɗin, kun san kasar China da abin hawa kala kala, wata ma sai ka saki baki ka ɓata lokaci kana kallonta, sam su basu gajiya da kere kere, Allah ya yi masu fikira da basira ne over.

Wata kyakkyawar taxi ya hau, kai tsaye address na *GOLD CROSS HOSPITAL (GCH)* ya ce a kaisa. Su kuma bodyguards ɗin nasa suka fito tare da trolleynsa suka nufi waje dan su je su aiwatar da umarnin da ya ce masu su yi na neman hotel.

Lion baka gane gabansa baka gane ina ya dosa, yanzu duk rikicin da tarzomar da ya haɗa a U.s ya tashi kura, hakan bai hana shi ya shiryawa kansa zuwa kasar China kamar yanda ya yi niya a baya ba, yana da karfin hali sosai, komai zai aikata yana aikatawa ne cike da kwarin gwiwa ɗari bisa ɗari tare da yakiyi da kuma sanyawa a ransa tabbas zai yi nasara, ba komai ne yasa hakan ba kuma face rike Allah a zuciyarsa da ya yi, komai zai yi Allah yake fara sakawa a gaba, shi ne yasa yake samun kwarin gwiwar na cewa zai yi nasara a komai, kuma ya yi gaskiya, duk wanda ya saka Allah a gaba, to babu abin da zai hana shi yin nasara, babu wata barazana da zata tsorata shi, babu wata shamaki da zata gifta a tsakaninsa da nasararsa, shiyasa a koda yaushe TRIPLETS namu suka zamana masu yin nasara a rayuwarsu!! Allah ka bamu dacewa.

Kafin ya tako kafarsa a cikin ƙasar China, sai da ya shiryawa kansa komai da komai, harta in da zai je sai da ya nemo address, ya jima yana bincike a kan Cherish, tun lokacin da ya gano cewa an canza ɗaya daga cikinsu, idan baku manta ba tun bai zo U.s ya ji gaskiya a wajen kakansa ba ya yi maganar zuwansa kasar China ya nemo Cherish, so tun a lokacin ya fara bincike a kanta, duk wata hukunci da ya yanke har da shiga siyasa da ya yi, duk basu hana shi yin binciken nasa ba, dama after primary election ya tsara zai shiga ƙasar ta China, to shi ne ya cika abin da ya tsara a yau.

Yau dai ga mai kama da Arvin a cikin Beijing, ga kuma shi ma Arvin ɗin a nan, dama yana cewa zai je U.s ya haɗu da mai kama da shi, za su haɗu ko ba za su haɗu ba? Idan sun haɗu ya haɗuwar zata kasance?..... PRINCESS TEEMA ce kawai zata iya gaya maku wannan amsa!!.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



Date: 15/5/2024


E32



Dedicated to Halimatus Sadiya ƴar amanar Jehan ❤️ yau dai amanar Jehan page ɗin naki ne😂




A ɓangaren shi ma Areef ya sauka Nigeria lafiya lou, Tga ne ya zo airport ya ɗauke shi zuwa gida.

Sam Jehan bata san da zai zo ba, bata da labari, tana can tana fama da zazzabin sonsa kamar zai kasheta, amma taki sauƙa daga kan bakarta. Yana zuwa bedroom nasa ya wuce, duk da bashi da burin da ya wuce ya kalleta ɗin, amma kuma bai je in da take ba, sai ya wuce bedroom nasa.

A ɓangaren ita kuma Rimsha, sosai ta kara jin haushin Lion, saboda yadda suka kwana suka tashi bai nemeta ba, bata yi zaton haka daga gare shi ba, hakan yasa ta kara ji a ranta da gaske cewa baya sonta, kowa ya sani tana bala'in sonsa na kin karawa, baki ma ya yi kaɗan ya iya zayyana yadda take son shi.

Hakan yasa abin ya yi mugun taɓata sosai, har wani irin zazzaɓi mai zafi gaske take ji, idan baku manta ba ita fa time da daddynta ya hana ta kallon shi a Tv tun suna Abuja bata kai haka ba ma, sai da ta kwanta a gadon asibiti, a lokacin ma bata san menene matsayarsa a wajenta ba, bata san cewa tana son shi ne ko dai iya burgewa ɗin bace ba, bare kuma yanzu da ya zama mijinta, suka zama abu guda, ta saba da shi, soyayyarsa ya karu a zuciyarta na wuce misali.

Sai abin ya yi muguwar jijjigata, sai dai fa wani abu guda game da ita wanda nasan tabbas kun manta da shi, duk daɗi duk wuya, duk yadda Rimsha ta kai ga son abu, to fa bata jurar walaƙanci a kan wannan abin, nasan dayawanku kun manta zamanta a Ilorin kwara State, to PRINCESS TEEMA dai ban manta ba ni, kuma bari na tuna maku, time da kausar ta yi mata walaƙanci a kan abinci, a haka ta zauna da yunwa duk da Iya Kausar ɗin ta ce tayi hakuri ta ci, amma taki ci sai dai suka sayi drinks ita da Ayla, time da Kausar still ta sake yi mata rigima a kan kayan sakawarta, kun tuna ta ce ba zata sanya kayar ba, har ta ɗauko tsohon nata ta saka, kun tuna? Bugu da kari kunsan saboda ba zata iya jurar walaƙanci bane ba yasa suka baro gidansu Kausar, duk da abin ya haɗu da yi mata fyaɗen da Borda Jami'u ya so ya yi, so haka zuciyarta take, ba zata iya jurar walaƙanci ba, wasu abubuwa da kuke gani take yi wa Lion, sau da dama Malika ce take sanyata yi, amma banda haka ko shi ɗin ba bazata ɗauki walaƙanci daga wajensa ba, haka ƴaƴan Nawazuddeen suke, Malika tasan cewa shi Lion tamkar bugun zuciyar Rimshar ne, already ta yi saurin kamuwa da sonsa tun kananun shekarunta, so hakan yasa ta tayata yakin neman soyayyarsa, badon taimaka mata da ta yi ba, da ko kusa ko alama Lion ba zai so ta ba, Malika tana kaunarta sosai yasa take kaunar duk abin da take so, idan baku manta ba Rimsha bata sanya kananan kaya, bata sanya irinsu wandunan Jeans da sauransu, har Kausar tana mata horo da su idan bata son ta sanya mata kaya, amma baku yi mamakin meyasa take sanya kananan kaya a gidan Lion ba? Tun kuma basu fara soyayya ba, to Malika ce take sanyata sakawa saboda wasu dalilai guda biyu, na farko shi Lion bai ma san irin dressing na Hausawa ba, kuma ba kyau zata yi mashi ba ko da ya gani, saboda su a al'adarsu kowa ya sani mace ta bayyanar da surar jikinta shi ne kyau da birgewa, so idan mace bata yi hakan bama su ganin mahaukaciya mara sanin abin da take yi suke yi mata, kada ku ga laifinsu haka al'adar duk wani Bature yake, in ma musulmi ko Kristen, duk tafiyarsu kusan ɗaya ce, banbancin kawai ibada ne, wani Baturen ma idan ya kalli mace da common doguwar riga ce har kasa, tambayarta zai yi anya yau kanta lafiya kuwa? Ko dai mijinta ne ya mutu? Yasa ta sanya buyagin haukar da ta sanya a jikinta nan? So haka suke rayuwarsu tun iyaye da kakanin, na tabbata koda baku taɓa zama a cikinsu ba, to kuna kallonsu a Tv, yadda kuke ganinsu a Tv ma abin wasa ne, rayuwarsu ta zahiri ta fi hakan, a Tv ai sai sun kawata shi yadda zai ja ra'ayin ƴan kallo, kuma wani lokaci a film suna yin abin da zai ja ra'ayin jama'a ce kawai dan su cigaba da samawa kasarsu kuɗin shiga, banda haka rayuwarsu ta zahiriya ma ai ya ninninka haka, wannan dalilin yasa Malika take sanyata yin dressing irin nasu, dan kada ya ganta da shigar hausawa ya yi mata kallon wata mahaukaciya mai tsummokarai a jiki. Abu na biyu kuma Malikar ta yi amfani da rauninsa ne a wajen, tasan dayawan Turawa suna bala'in son mace mai shape, baya da kuma breast tula tula, abin yana tashin kansu sosai, so idan Rimsha tana sanya irinsu a baya ba zasu fitar mata da shape nata ba, hakan yasa ta sanyata rinƙa saka irin waɗan nan kaya, kuma ta dalilin hakan ne ya ja ra'ayin Lion ɗin, yana tsananin kaunar shape na Rimsha sosai, tudun mazaunanta ba ma sai na yi magana ba, kunsan yana bala'i sonsu, barema kuma tula tulanta, kunga kuwa Malika ta kafa mashi tarko ne kuma ya afka ba tare da sanin shi ba, Malika ta yi abubuwa da dama wa Rimsha wanda baki ba zai faɗesu ba, wasu lokuta idan Rimshar ta yi wani abin da bata saba yi ba, ko kuma ba'a al'adarmu ta Hausa Fulani ba, to idan kuka bincika da sa hannun Malika, ba komai yasa Malikar ta taimaka mata ba a lokacin face dalilai guda biyu, na farko tasan Rimshar ta yi shigar sauri wa soyayyar Lion ɗin, kuma tabbas a kansa tana iya mutuwa, dan idan baku manta ba ta sha suma a kansa sosai, na biyu kuma a time ɗin tana da matsala a ƙwaƙwalwarta na razana da birkicewa da ta samu daga Daular Mutuwa, abu kaɗan yana razanata ta suma, sai abin ya zo ya haɗe mata da soyayyarsa, wanda idan ba'ayi dace ba tsab zai kasheta har lahira, hakan yasa Malikar ta taimaka mata sosai dan tana kaunarta da iya gaskiya, ita ɗin aljanace mai mutunci kuma bata manta halacci, dama dayawan al'janu basu manta halacci a rayuwa, nasan kowa tana son sanin wacece Malika, lokacin sanin hakan ya kusa zuwa, zata gaya maku wacece ita da kanta.

So a wannan karon fushin da Rimshar ta yi ma da sa hannun Malika, ba wai kuma ta tayata yin fushin bane, a'a, dama kun san ita Malika a koda yaushe ita take ƙoƙarin ɓoyewa Rimshar duk wasu laifuka da Lion ya yi mata a baya, sai ta rufe mata idanu ba zata taɓa damuwa da laifin ba, ita dai soyayyrsa kawai ta sani, a lokacin tana yi mata hakan ce saboda ta ceci rayuwarta, sannan kuma su danne komai su hakura dan su sami soyayyarsa, banda haka da wlh Rimsha ba zata ɗauki wasu abubuwa da ya yi mata a bayaba, saboda bata da zuciyar jurar walaƙanci ko kaɗan, ba zata iya ɗauka ba. So a yanzu da Malikar ta fahimci Lion fa ko zai mutu ba zai dai'na son Rimshar ba, ta rigada ta zama jinin jikinsa, shi ne yasa sai ta tsame hannunta daga lamarinsu ta koma gefe guda tana kallon masoyan tana jin daɗi abinta, shiyasa Rimsha ta kalli laifinsa a wannan karon, shiyasa ta kalli kamar walaƙanci ya yi mata, hakan yasa ta ce ko zata mutu ba zata ɗauki hakan ba, shiyasa ta ɗauki fushi mai zafi da shi, dama mai hakuri bai iya fushi ba, idan ka kure mai hakuri to wlh ka kuka da kanka, dan sai ka ɗanɗani bakinciki, ga shi kuma ya kara ɓata mata rai yadda ya kwana ya tashi bai kirata ya rarrasheta ba, abin ya kara baƙanta mata rai, sai take ganin ai walakancin ya yi yawa over.

Shi kuma har ga Allah ba wai baya son kiranta ɗin bane, dannewa kawai ya yi bai kira ɗin ba, saboda abin da ya sanya a gabansa, a wannan point da yake a ciki sam baya son ya biye mata, dan zata caza mashi kai sosai bayan wanda yake ciki, shi ne dalilin da yasa ya danne ya jure ya kyaleta ɗin, amma shi da kansa yana ji a jikinsa, har wani zazzaɓi shi ma yake ji na barinta a cikin damuwa da ya yi, tun daren jiyan yasan bai kyauta ba, bayan abin ya faru da ya kwanta zai yi barci, zuciyarsa ta ɗan yi sanyi, shi da kansa yasan bai yi mata adalci ba duba da yanayin karantar shekarunta, bai kamata ya haɗa hankalinsa da nata ba, kuma gaskiya Areef ya gaya mashi, son shi yasa take damuwa da shi, idan da bata son shi ko zai shekara miliyan bai zo in da take ba, ba zata taɓa damuwa ba, bugu da kari kuma ga abin da ya yi mata 30 days back, ta bakin mommar tasu yanzu ne yakamata ya lallaɓata ya biyata dakon soyayyarsa da ta yi na tsawon shekaru, so a takaice dai shi da kansa yasan sam bai kyauta mata ba, ya danne zuciyarsa ce kawai ya kyaleta sai ya kammala aikin da yake gabansa, idan sun haɗu a U.s sai ya ɗauki kayansa ya lallaɓata, sai dai fa bai sawa ransa cewa zai bata hakuri ba, babu wannan tunanin a ransa, tunaninsa dai shi ne idan sun haɗu a U.s ba shikenan sun ga juna ba? A tunaninsa daga haka zata sauko su koma normal, abin da bai sani ba shi ne ita fa a wannan karon da gasken gaske take yin fushin nata, babu alamar zata sauko ma, dan ta zo har wuya, ga Malika ta zame hannunta, ta bar Rimshar ta ɗan wanashi kaɗan, wata kila daga haka ya fara sanin darajar mum da dad ɗinta, dan abin yana bakantawa Malikar rai yadda Lion ɗin yake yi wa mum da dad ɗin, sam bata so, to ita ma kenan, bare kuma Rimsha da take ƴar cikinsu, ai idan ta sani zasu yi yaki da shi ba kaɗan ba, dan wlh zata iya rabuwa da shi tsab akan iyayenta, barema mum ɗinta, bazata iya jurar wani ya yi masu walakanci ba.

Shi kuma Lion a zahirin gaskiya sam ba wai walaƙanci yake yi masu ba, a haka yanayinsa yake, idan zaku yi wa kanku adalci, ai ba iya mum da dad yake yi wa hakan ba, harta Dr William a time ɗin bai bari ba, ya yi wa Abbansu Imran, kuma ai Imran babban abokinsa ne wanda ma bashi da biyunsa a duniya, bugu da kari kuma ta dalilin Imran ɗin suka musulta, amma ya yi iyayen Imran ɗin hakan tun kafin ya yi wa iyayen Rimsha, ya yi wa Uncles nasu da kakanninsa na kasar Russia, su Uncle T da uncle Herry kam ma ai ba'a maganar irin walaƙanci da ya yi masu, shi fa bai bar kowa ba, taka kowa yake yi ya wuce, so su daddy dan sun bashi auren Rimsha ne yasa nasu yafi damun mutane, banda haka ai shi Lion haka halinsa yake tun ainahi, kuma ai ba shi kaɗai bane ba, harta Aseef idan kuka lura haka halinsa yake, baya damuwa da mutane, kuma baya ɗaga idanu ya kalli mutane, soyayyar Akila ta koya mashi sanin darajar wasu daga cikin mutane, a hakan ma ba kowa yake gani da daraja ba, so shi Aseef idan kuka nutsu zaku fahimci babu in da ya baro Lion ɗin a wasu ɗabi'u, shi dai kawai soyayya ce ta yi saurin canza shi, amma shi ma me bai yi wa su Uncle T ba? Ai shi ma ya yi abubuwa son ransa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login