Showing 228001 words to 231000 words out of 270744 words
wajen daddynsa su ɗan yi hira na tsakanin uba da ɗa.
A ɓangaren uncle T kuma, rungumeta sosai ya yi yana ɗan bubbuga mata bayanta ba tare da ya yi magana ba, har sai da ta sami nutsuwa. Sai da hankalinta ya dawo jikinta, a zabure ta miƙe zaune tana ƙoƙarin raba jikin nata da nasa.
Riƙota da kyau ya yi tare da sanya hannu ya ɗago haɓarta. Ganin face nasa yasata nutsuwar dole, nan take ta ji wasu malaman nutsuwa sun sauko mata a jikinta. Ƙoƙarin kawar da kanta gefe guda ta yi, dan kada ta cigaba da kallon face nasa, abin da kuka sani ne kullum a ɗaure face ɗin take kamar ta Lion.
Hata kawar da kan nata ya yi ta hanyar matso da nasa face ɗin dab da tata, har suna iya jiyo sautin numfashin juna, ga dogayen hancinsu suna gogar na juna.
"What's wrong with you Aafia?". Ya faɗa a nutse.
Runtse idanuwanta gam ta yi kafin ta iya bashi amsa da Nothing. Haƙiƙa ba zata iya yi mashi musu ba idan ya yi magana, ba zata iya kin amsa mashi ba kuma ko da bata so, saboda abin a jinin familyn Dr William yake, kwarjinin bala'i ga kuma shegen shiga rai garesu kamar me.
"Why are you doing something like you have brain problem?". Ya yi maganar yana kara jawota jikinsa sosai, saboda tana ƙoƙarin zille mashi ne, cikin dabara take ƙoƙarin raba jikinta da nashi, to ya ganota, shi ne yasa ya kara riketa gam.
"Babu abin da yake damuna, nima dai haka kawai nake jina wani iri". Ta bashi amsa.
Kawar da zancen ya yi da cewa. "Do you love me?". Ya tambayeta yana mai dawo da kallonsa a saman wuyarta, da waɗan nan shegun idanuwan nasa irin na Areef.
A dubu ɗari ta buɗe idanuwanta babu shiri, jin wannan tambaya tasa ta taɓa mata brain, dan ita fa har yanzu ma bata yarda cewa da Tga take tare ba, ganin abin kawai take yi a mafarkin da ta saba yi nasa tun kafin ta yi aure ne.
"Aafia talk to me, do you love me?".
Mayar da idanuwanta ta yi ta datsesu tana tunanin iko irin na Ubangiji, wato duk yadda kake a duniyar nan akwai mai sonka a haka, mutun ma mai daraja da kima, Allah mai iko, duk wanda ya riki Allah ya huta.
Kara matso da face nasa sosai ya yi har sai da ya haɗe fuskokin nasu, a karo na uku ya sake tambayarta tana son shi?.
A wannan karon girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.
"Why baki Sona?". Ya tambaya a ɗan ruɗe.
"Saboda ni ba class taka bace, kafi karfina, kuma ni na taɓa yin aure mijina ya rasu, and kuma nasan koba ma haka ba kafi karfina, ni ban yarda da cewa ma akwai wanda zai sake cewa yana sona ba, ban taɓa.........."
Katse mata maganar ya yi ta hanyar sumbatar lips nata da wannan ɗan bakin nasa irin na Areef, yadda take magana ne yasa ya ji ba zai iya ba sai ya sumbaceta.
Da sauri ta waro idanuwanta waje, kai tsaye sai cikin nasa idanun, shi ma kallonta yake yi sosai.
"Ni ke nake so ai, ba ruwana da kin taɓa yin aure, so stop talking all this miscellaneous excuse, just kawai tell me, do you love me or not?".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "I love you since before, amma kuma for now dai........."
Sake katseta ya yi a karo na biyu, nan ma ta hanyar sumbatar lips nata kafin ya ce "You love me that's all, i don't want to hear any excuse, so now get ready, dan zan gayawa momma abin da yake faruwa, bana son ki sake kawo mun wani miscellaneous talk talk kuma". Ya kai karshen maganar tare da zaro mata dara daran idanuwansa yana kara sumbatar lips ɗin nata.
Suma kwance kawai ta yi mashi, ta rasa me zata sake ce mashi, ya goge mata hadda. Shi kuwa ganin bata ce da shi komai bane yasa ya kara matseta sosai a jikinsa tare da matso da lips nasa ya haɗe bakinsu waje guda, shi a wajensa hakance soyayya.
Da sauri ta sanya hanayenta dukka biyu tana ƙoƙarin ture shi ta raba jikinsu.
Ganin haka ne yasa ya zame ɗan bakin nasa daga nata ya kuma raba jikin nasu yana kallonta har cikin ido.
Miƙewa ta yi da sauri ta nufi hanyar fita waje.
Da ido ya bita ba tare da ya dakatar da ita ba. Sai da ya kalli ficewarta sannan shi ma ya miƙe jiki duk babu kwari, abubuwa sun motsa, a haka ya fito waje ya nufi part nasa.
A ɓangaren Akila da mummyn Rimsha kuwa, sai da suka yi da gaske kafin Akilar ta farfaɗo, nan ma sai can rana ta yi sanyi sannan ne ta farfaɗo, hakan ma da taimakon gwaggo, sai da gwaggo ta sa hannu kafin su samu ta farfaɗo, shi kam Aseef sai kuka yake yi musu a kan kada su bari Heartbeat ɗinsa ta mutu, wlh yana sonta, idan ta mutu zai bita.
Da kyar gwaggo ta samu ta shawo kansa ya hakura ya nufi bedroom na daddynsa, ya barsu su yi aikinsu, a can ma ko da yaje ya saka daddyn nasu a gaba da kuka a kan lallai shi dai Heartbeat ɗinsa ta tashi, haka daddyn suka haɗu shi da Areef suka yi ta ɗannarsa har suka samu ya yi barci.
Sai misalin karfe 4 na yamma ya farka daga barcin, yana farkawa kuma da sunanta ya tashi, a lokacin su daddy basu cikin bedroom ɗin, da sauri ya diro kasa daga saman bed ɗin ya nufi part nasa dan ya duba Heartbeat ɗinsa.
Yana shiga cikin bedroom ɗin lokacin ita kuma Akilar ta farfaɗo su gwaggo sun tallabota zasu kaita toilet a gasa mata jiki sosai.
A hanzarce ya kariso wajensu yana tambayar lafiya ina zasu Kaita? A gefe guda kuma yana yi wa Allah godiya da Allah yasa bata mutu ba tana da rai.
Gwaggon ce ta bashi amsa da cewa zasu je ne su gasa mata jiki, dan sai an gasata sosai, ta sha bakar wahala ita ma, yaran Dr William dukka ba sauki, gado suka yi, dan shi ma daddynsu fa babu sauki.
Jin cewa gasata za'a je ayi, nan fa ya saka masu kuka a kan shi ma wlh in dai haka ne sai su Lion sun gasa shi.
Dariya kamar gwaggo zata yi yaya, amma ta danne dariyar ta ɓoye bata bari ya kubce mata ba. Aseef ikon Allah, wai sai su Lion sun gasa mashi jiki, duk abin da yake yi fa yana sane yake yi, kawai shagwaɓar ce tabi jikinsa, amma wlh tsayayyen namiji ne shi ma, meyasa bai ce su gwaggon su gasa mashi jiki ba sai ya ce su Lion? Kun ga kuwa sarai yana sane yake zuba tsiyarsa dan yaga suna biye mashi.
(Amma kuma fa ni for me yana da gaskiya, gara ya yi musu kafin lokacinsa ta kure, yanzu ai idan suka haifi yara ba zasu rinƙa biye mashi ba, kunga kuwa ya yi abin da yake so yanzu, ni dai PRINCESS TEEMA ina goya mashi baya😂 saura naji wata readers ta yi magana😒 yauwa ina goyon bayansa, ban ga laifinsa ba, ya mori lokacinsa, dan nan gaba kaɗan gwaggo zata fara renon jikoki, su Areef su fara renon yaransu, kunga ba zasu wani biye mashi ba)
Da kyar nan ma gwaggon ta lallaɓa shi ta ce ya je su Lion ɗin su gasa mashi jikin nasa to. Haka kuwa aka yi, wajen su Lion ɗin ya wuce abinsa, ya tsayar masu da rigimar sai sun gasa mashi jiki shi ma, saboda ai ya sha wahala ba kaɗan ba shi ma.
Areef ne ya ce to su je toilet ya gasa mashi tun da haka yake so, Lion kam ko kallon in da yake ma bai yi ba, sir Arvin ma yana rike da Pinky a saman laps nasa ya ce to su je a gasa mashi mana, abu mai sauki ne ai wannan, ita kuma Rimsha tana cikin bedroom na Lion ɗin tana zuba barcinta abinta, dan kunga bata da lafiya, tana period, ba isshasshen lafiya ke gareta ba, shi ne yasa Lion ɗin ya kyaleta ta yi barci ya fito parlourn part ɗin nasa suna hira da su sir Arvin ɗin.
Da gasken gaske kuwa Sir Arvin da Areef suka je suka gasawa Aseef jikinsa a cikin toilet da ruwa mai zafi, harda towel suke matsa mashi jiki, kada ku manta sun iya gashi sosai, saboda suna yi idan sun je wani aikin sun dawo, ko idan suka yi faɗa da wasu, musamman ma shi Areef da ya yi rayuwa da ƴan ta'adda, so suna iya faɗa a tsakaninsu su daki juna da har sai sun gasa jiki, to haka suka gasawa Aseef ɗin ma jikinsa, ko yaya suka gudanar da hakan? Su dai suka sani, yaran gwaggo sai gwaggo, my readers Allah ma ya rufa mana asiri da yaran gwaggo suka tsaya a iya QUADRUPLE ɗin nan, ba dan haka ba da jinin Dr William zamu ga abubuwa kala kala da bamu taɓa ji da gani ba, ga sir Arvin ma ya zamo irinsu, da yake abin nasu a jini yake, dama bai da abokan da za su yi ne yasa yake a haka, amma yanzu ai sai abin da muka gani kawai......😂
Areef kam da karawa abin armashi har da ɗauko wata katuwar towel mai girman gaske ya lulluɓe Aseef ɗin da shi, suka haɗu da sir Arvin suka shafa mashi lotions kala kala masu daɗin kamshi, sannan suka ɗauko mashi kaya masu matuƙar kyau da tsada sosai.
Sai dai fa ko da suka bashi kayan sai ya ce shi ba zai sanya da kansa ba, dan Heartbeat ma yasan saka mata kaya su gwaggo zasu yi, dan haka shi ma sai dai su saka mashi. Areef dai ya ce ba zai saka mashi ba, ya gasa mashi jiki ta isa, kaya kuma ya saka wa kansa.
Kuka ya fara ƙoƙarin saka masu, da sauri sir Arvin ya karɓi kayar tare da cewa A'a ba sai ya yi kuka ba, bari ya saka mashi, abu mai sauki Areef yake son ɓata mashi a rai a kansa, to ya yi shiru ya kwnatar da hankalinsa, dole shi zai saka mashi kayan.
Narkewa ya yi a jikin sir Arvin ɗin yana turo baki, shi a dole an mashi ba dai'dai ba. Wucewa Areef ya yi ya koma parlourn, dan iskancin Aseef sai shi. Sir Arvin kuwa ya saka mashi kayan kamar yadda ya ce, sannan ya ce su koma parlourn.
Ko da suka fito Pinky baiwar Allah har ta yi barci kwance kusa da Lion, ta tada kai da laps nasa, shi kuma yana aikin latsar waya.
Mu koma baya kaɗan, da sir Arvin da kuma Alex sun karɓi kalmar shahada lokacin da suka je sallar jumma'a, kowa ya zaɓi kalar sunan da yake so, shi Sir Arvin Lion ya ce a saka mashi Safwan, shi kuma Alex daddyn Rimsha ya ce a saka mashi Mahhir, so a yanzu su ba Kristen bane ba, sun shiga addinin Musulunci addini mai ni'ima da tsarki wanda babu biyunsa, Allah ka kashe mu a cikinta, ka karɓi rayukanmu muna masu imani da kai ya, daga karshe ka karɓi rayukanmu muna masu tsananin son manzonka, manzon tsira Manzon rahma ɗan Amina da Abdullahi fiyayyen halitta ɗan gatan Allah, kalmar shahada ta zama abu na karshe da zata fito daga bakunanmu, Amin ya rabbussamawati wal'ardi.
After some days.
Da Akila da Jehan duk sun tare a ɗakin gwaggo, sam sun ki yarda su koma wajen mazajensu, kuma sarai sun sami lafiya, ita kuma gwaggon bata son ta ce su koma wajen mazajen nasu dan kada ace ta yi son kai, da dai ba yaranta bane suke aure, da sai ta tsaya tsayin daka sai sun koma, amma da yake yaranta suke aure, sai ta yi kara bata ce masu komai ba.
Ai kuwa mazajen nasu kamar zasu yi hauka, sam sun kasa hakuri, barema shi Aseef, dan ma gwaggon ta ce mashi Akilar bata da lafiya ne yasa ya yarda ya barta ta ɗan yi kwanaki a wajen gwaggon, ba dan haka ba da ko kwana ɗaya ba zai iya hakuri ba.
Shi kuwa Areef bawan Allah, kwata kwata Jehan taki yarda ma ta sake haɗa hanya ɗa shi ne, ko ya shigo wajen gwaggon sai ta yi kamar bata gan shi ba, idan tana kwance ne sai ta juya masu baya ta rufe idanu, idan kuma tana zaune ne sai ta kwanta ta basu baya, haka take yi.
Areef ɗin ya yi magiya har ya godewa Allah, amma taki sauraronsa, taki ma ai su haɗa ido, gwaggo kuma ta bi bayanta, dan haka yana cikin damuwa sosai bawan Allah.
Rimsha da Lion kuwa soyayyarsu suke zubawa son ransu mai tsabta, kamar zasu cinye juna dan so.
Zaɓe yana ta matsowa sosai, sai kara samun nasarori Lion yake yi, su His Excellence dai kamar babu su a duniya, sun yi cif, sai dai Lion duk abin da yake yi yana lura da lamuransu, dan ba shirun lafiya suka yi ba, bare ma yanzu da suka gane cewa Dr William na gaskiya da sir Safwan basu a hannunsu, sai suka kara ɗaura ɗamarar hallaka gabaɗaya familyn Dr William ɗin, sannan kuma suka ce shi ma uncle Herry da yake hannunsu wanda shi ne sarkinsu a yanzu, ya gaji Jacob, ya karɓi karagar mulki, dama idan baku manta ba shi ba wai an sadaukar da shi ne dan a kashe shi ba, a'a shi dan ya gaji karagar mulkin Jacob aka sadaukar da shi, to yanzu shi ne sarkin Daular tasu, shi yake mulkarsu, to shi ma yanzu suna kullah yadda za'ayi su kashe shi, dan sun san idan Lion ya juyo ta kansu ba zasu yi saura ba, shi ne yasa suke hanzari su aiwatar da abubuwansu cikin lokacin kafin komai ya kwaɓe musu, hakan ce ma tasa basu wani bi ta kan siyasar sosai ba, suna ƙoƙarin yadda za su kamo gwaggo ne su kasheta, dan a cewarsu gwaggo ita ce bangon rayuwar gabaɗaya familyn, idan suka kasheta dole kowa ya girgiza ya yi kuka sai idanuwnasa ta kumbura, hakan zai sa Lion ya yi laushi a cewarsu, to shi ne suke shirin yadda za'ayi su ɗaukota ba tare da ɓata lokaci ba, daga ita kuma suka ce sai Rimsha, ita ce ta biyu kafin su ɗauki su Dr Salman and Dr William.
E lallai su Anderson sun shirya sanya ilahirin familyn Dr Salman kukan jini ma bana hawaye ba, sai dai muce Allah ya tsare mana familyn Dr Salman ɗin mu kawai, ga shi sai sha'aninsu suke sha basu san me ake shirya masu ba, Allah sarki.
To yau dai Aseef yazo har wuya, hakurinsa ta kare, da misalin karfe 9 na dare, shirye yake a cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, kai tsaye part na gwaggon ya nufa. A tare ya sameta da ƴan matan nata suna hira, ita kuma Aafia ta basu baya tana kwance a saman bed tana chatting da Uncle T a Whatsapp ta wayar gwaggon, ya yi ya yi da ita a kan tafito waje suga juna, amma taki fitowa, ta maƙale a saman bed tana zuba mashi tsiya, ya ce idan bata fito ba shi zai zo ai ya ɗauketa, hakuri ta fara bashi tana ce mashi sai zuwa anjuma zata fito, dan tasan halinsa sarai, zai iya shigowa ya ɗauketa ɗin kamar yadda ya faɗa.
A bakin bed ɗin Aseef ya tsaya yana faɗin "Momma tazo mu tafi mana tun da dai yanzu komai normal ta ji sauki".
Gwaggon na ƙoƙarin yin magana, cikin sauri Akilar ta riga ta da cewa "Wlh ni gwaggo a'a, a nan zan zauna kawai, ni ba zan bishi ba, ya tafi abinsa".
Kallon shi gwaggon ta yi kafin ta ce "Shikenan ɗan autan mommansa, jeka ka barta a nan ɗin tun da ta ce ba zata bika ba, ka barmun ita ɗin a nan kamar yadda take so". Ta kai karshen maganar tare da kashe mashi ido ɗaya kamar ba uwa da ɗa ba.
Murmushi ya yi tare da manna mata sumbata a goshi kafin ya juya
FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*
Date: 5/6/2024
E46
Murmushi ya yi tare da manna mata sumbata a goshi kafin ya juya ya fice daga cikin ɗakin.
Yana fita ita ma Aafia ta miƙe zaune tare da zuro kafafunta kasan bed ɗin tana faɗin. "Gwaggo zan je parlour, uncle T ne yake kirana".
Siririn murmushi gwaggon ta yi kafin ta ce "To a dawo lafiya, ke kuma Akila zo mu je bedroom naku mu yi sirri". Ta kai karshen maganar tare