Showing 129001 words to 132000 words out of 270744 words

Chapter 44 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2954

mashi bed, yau a bedroom nasa za su kwana, haka ya kwanta a kusa da su bayan ya yi addu'ar barci, tun bai kai ga tafiya ba har ya fara kewarsu, su ɗin jini ne da hanta bayin Allan, ko ina cikon QUADRUPLE ɗin nasu yake? Ya mutu ne ko yana raye? Allah masani sai kuma alƙalamina Ni PRINCESS TEEMA taku ta amana, dan haka mu kasance a tare kawai dan jin komai.

Yana kwanciya ba jimawa ya yi barci abinsa.

A gida Nigeria kuwa, washegari gwaggo ta gayawa Tga da akwai in da zai kai'su. Cikin girmamawa ya ce mata Lion ya gaya mashi tun jiya. Tun da Tga yake a rayuwarsa bai taɓa girmama wani in ma mace ko namiji bayan Lion da yake ogansa ba, sai a kan gwaggo, har cikin ransa yake jin Kaunar gwaggon, tun da ya ji cewa ita ce ainahin mahaifiyarsu Lion, daga nan ya ji yana mugu mugun respecting nata.

Shiryawa suka yi, gwaggo, mummyn Rimsha, Jehan, Akila, and Rimsha, TGA ya ɗaukesu a mota suka bar gidan, shi kuma daddyn Rimsha a yau ya bar kasar, dan Lion ya ce mashi ya zo Washington ya samu Areef da akwai abin da zasu yi a tare. (Sai shiryawa su his excellence kitimurmura Lion yake yi fa, kome su Areef suke sake shiryawa kuma?🤔 Namu ido ko my peoples?.)

Kai tsaye wani katafaren shop na gyaran gashi, lalle da kuma kitso gwaggo tasa Tga ya wuce da su. Ko da suka isa wajen yaki yarda ya jiransu a mota, har cikin wajen ya rakasu, dan ya tabbatar suna cikin lafiya da tsaro, ya tabbatar babu abin da ya samesu, dan haka sai ya bisu har ciki, sai kallon shi tsala tsalan ƴan matan da suka zo wanke kai suke yi, manyan mata ne masu ji da class, ƴaƴan manya, dan shop ɗin bana yara bane, na manyan mata ne.

Shi kuwa Tga abin da kuka sani ne, kallo wannan ma babu wacce ta samu ya ɗaga idanu ya kalleta, dan shi bai ma san suna yi ba, ga fuskarsa tamkar ta shanu, ya wani murtuketa gam, babu alamar ya taɓa sanin menene murmushi ma, sak face ɗin Lion haka yake shi ma, abu ne da kuka rigada kuka sani.

Duk waɗan nan awannan da su Rimsha suka kwashe ana zuba masu zanen flowers na lalle mai bala'in kyau tare da gyaran gashi, duk yana tsaye bai ko motsa ba, kuma sam bai zauna ba, yana tsaye a matsayinsa na cikakken soja mai jini a jika, yana ta kula da su, dan Lion ya jaddada mashi a kan ya kula da su over, shi ne yasa yake ƙoƙarin jaddada hakan.

Sam Rimsha ta mance da cewa Lion baya son lalle, haka ta bari aka zuba mata zanensa ya fito reras, ya yi matukar kyau na wuce misali.

Ita gwaggo a tunaninta gabaɗaya TRIPLETS zasu zo a tare, shiyasa ta tattaro har da su Jehan ɗin dukka dan ayi masu gyaran kai, bata san iya Lion ne kawai yake hanya ba.

Haka suka gama abin da za su yi, suka je shopping suka yi sayayya, Lion yasa Imran ya biya kuɗi ta hanyar yi wa masu shops ɗin transfer, sannan suka nufi gida, sai murna Rimsha take zabawa, baki yaki rufuwa, an zuba mata lalle kam kamar ba gobe.

Sai da suka koma gida ta shiga bedroom ɗin na Noorish ɗin nata dan ta yi wanka ta yi sallar azzahar, a nan ne ta tuna cewa Noorish baya son lalle, nan take hankalinta ya yi mummunar tashi na wuce misali, wani irin tukukin bakin ciki ta ji ya taso mata, kullum tana damunshi a waya akan yazo ta yi kewarsa, ya taso yana zuwa kuma ta je ta yi abin da zai bakanta mashi rai, sam bata ji daɗin hakan ba. Zama ta yi a saman bed ta murji kukanta iya son ranta, sai da ta ji kanta ya fara yi mata ciwo ne ta hakura, ga kan nata ya sha gyara na gasken gaske kuwa, sai wani kyalli curly hair nata yake zubawa, kamar ka sace ta ku gudu, ta yi kyau ne har ta gaji da kyau, dole ma Noorish ya ruɗe idan ya zo ya ganta.

Bayan ta gama murzan kukan ne ta miƙe ta nufi toilet, wanka ta yi tare da fitowa ta shirya, sannan ta yi sallah kafin ta fita zuwa kitchen ta ɗebo abinci, ta dawo cikin bedroom ɗin nasa ta zauna ta fara cin abincin nata, suma su Jehan abincin suke ci a bedroom na gwaggo.

Bayan ta ci ta yi nak, sai ta hau gyara mashi bedroom ɗin babu kama hannun yaro, da ta kammala sai ta rufe ko'ina tare da zuba mashi air freshener irin wanda yafi kauna, ta bulbula son ranta, tana kammalawa ta wuce bedroom ɗin mummynta.

Babu kowa a cikin ɗakin, dan haka sai ta dawo bedroom na gwaggo. A nan ta samesu dukkansu, mummynta da gwaggo suna a zaune a saman bedside drawers dake gefe da gefen bed ɗin, ita kuma Brr Naurat tana zaune a saman bed ɗin, Jehan ta tada kai da cinyar Brr Naurat, ita kuma Akila tana kwance a gefe guda tana aikin latsa waya, sai sakin uban murmushi take yi, da alama ita da Heartbeat nata suke chatting, dan minti minti sai kuga ta turo baki alamar kalmar shagwaɓa ya turo mata, sai magana Brr Naurat take yi mata, amma ina hankalinta na'a kan wayar, sai da mummyn Rimsha ta miƙe ta kwace wayar, sannan ne ta farga ashe ma a cikin mutane take.

Rufe fuska da hannunta ta yi tana dariya kasa kasa. "Akila sarkin soyayya ba". Cewar mummyn Rimsha, ta yi maganar cikin zolaya........ Hmmm Mummyn Rimsha fa bata san cewa Rimshar tattabara ce uwar soyayya ba, dan bata san yanda take birkitawa General of the army's kuma ɗan takarar shugaban kasa a yanzu lissafi ba ne, duk ta susutar da bawan Allah, ya fita waje ya yi wa mutane zarra, idan ya dawo gida kuma ya cigaba da biyewa Rimsha ya zama kamar wani ƙaramin yaro, oh Rimsha duniya ne wlh, mum tana cewa Akila sarkin soyayya, ai ga sarkin soyayya kam nan ta fito daga cikinta.

"Ku bani hankulanku waje guda". Cewar Brr Naurat. Nutsuwa suka yi tare da tattare mata hankulansu, Rimsha dake a tsaye ma Brr ta ce tazo ta zauna, dama magana za'ayi a kanta ai, dan ita ce mijinta yake hanyar dawowa yau, ita za'ayiwa nasiha, su Jehan dai zasu ji nata ne kawai kafin azo yi masu nasu idan mazansu zasu dawo.

Shiru suka nutsu kamar ba su ba, da Brr Naurat da gwaggo ne suka fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya ta sanya zuciya yin laushi, sai da suka gaya masu girman Allah, suka tausasa masu zuciya, sannan suka fara gaya masu menene miji ma first, kafin suka gaya masu hakkokin miji da yake a kansu, daga karshe suka ɗaura da zancen biyayya, kada su kuskura su ɗaga muryoyinsu ya fi na mazajensu sauti, yin hakan ya kansa mace ta shiga tsinuwar Mala'ikun Allah ta'ala, kome zai yi masu su daure kada su ɗaga mashi murya, Allah baya barci yana ganin komai da yake faruwa, su kula sosai da mazajensu, su kasance masu sanyasu farinciki na wuce misali, su yi masu duk abin da suke so matuƙar bai saɓawa Allah ba, koda su basu so, to su daure su yi mashi biyayya, ranar gobe kiya zasu samu kaso mai tsoka a wajen Allah, zasu shiga rahmar Ubangiji a lokacin da ubangijin al'arshi ya sauko da rana dai'dai kawunan mutane, to a wannan lokaci Allah zai sanyasu cikin karkashin inuwar al'arshinsa, dan haka su dage sosai, su jure su yi hakuri, duniya ba madawwama bace, lahira ita ce madawwamiya, dan haka su nemi madawwamiyarsu ta yi kyau, kada su biyewa duniya lokaci kaɗan yake a gareta.

Sun sha kuka sosai, barema Rimsha, tafi kowa yin kuka a cikinsu, ita kuwa Jehan hawayenma bai gama barin kusa da idanunta ba, da alama ƙaƙalo kukan ma ta yi (ni ko wai menene zai sanya zuciyar Jehan da Lion yin laushi sosai ne?🤔 Wai duk wannan abin Jehan bata yi laushi ba?🤔 Kukan ma ƙaƙalo shi ta yi dan kada ace bata yi ba😂 kai jama'a Jehan dai har gobe da sauranta, shi dama Lion ba'a sanya shi a lissafi, dan ni na juya na juyo banga abin da zai sa zuciyarsa ta yi laushi ba, dan ko yanzu Rimsha ta yi mashi ba dai'dai ba zai bata a jikinta ne, sai dai daga baya ya yi dana sani, amma zuciyar nan tana nan babu abin da ya ragu a jikinta)

Akila ma ta sha kuka sosai, daga haka har barci ya ɗaukesu.

After some hours.

Bayan sun yi sallar mangariba da issha ne Rimsha ta je wajen mummynta, dan dama mum ɗin ta ce mata ta sameta a ɗakinta. Tana zuwa mum ta zaunar da ita a bakin bed ta hau yi mata tata nasihar, ta ɗaura daga kan nasu Brr Naurat, duk wata kunya ajiyeta a gefe mum ta yi, ta rungumi ƴarta ta koya mata yadda zata zauna da mijinta lafiya, harta abin da yafi sanya namiji farinciki sai da mum ta gaya mata, ta ce ba zata tsaya nuna jin kunya ta cuci ƴaƴanta a banza ba, su je gidan miji basu san yanda zasu kula da mijinsu ba, aure ya zo ya yi ta tangal tangal, gara mata ta ajiye kunya, ta jasu a jiki, ta gaya masu komai dallah dallah, hakan ne kawai zai bata daman samun kwanciyar hankalin kasancewarsu a gidan miji, barema Rimsha da take ƴar yarinya, ga mijin nata ba irin sauran maza bane ba, ai dole sai an koya mata abubuwa dallah dallah, ɗan gara Jehan ma ta ɗan girma.

Haka ta rinƙa yi mata nasiha sosai har sai da gwaggo ta zo ɗakin ta samesu, sai kuka Rimshar take yi sosai, gwaggon ce ta rarrasheta sannan ta ce tazo su tafi bari ta shiryata dan mijin nata ya iso. Wani irin daɗi ta ji Noorish nata ya iso, kamar zata tambayi gwaggon ina yake, sai kuma ta danne ta fasa dan ganin idon mummynta, da gwaggo ce kawai sai ta tambayeta ina yake, amma tun da mum tana nan, sai ta danne bata tambaya ba.

Riko hannunta gwaggon ta yi tare da mikar da ita suka nufi waje suna yi wa mum sai da safe.

Fitowa suka yi daga side na boys quarters ɗin suka nufi cikin gidan. Sosai Rimsha ta yi mamakin ganin tsadaddun sabbin motoci dal dal har guda uku a parking space na gidan, motoci ne da suka amsa sunansu motoci masu numfashi, ko ba'a gaya mata ba, tasan dole su ne suka ɗauko Noorish nata daga airport.

Wucewa suka yi izuwa cikin gida, tana sanya kafarta a palourn kasa kamshin perfume nasa ne ya fara dukan kofofin hancinta, sai ka rantse da Allah yanzu ya wuce a wajen, amma kuma ya jima da wucewa zuwa sama, dan Rimshar tana fita zuwa wajen mummynta, shi kuma yana shigowa, kasancewar tana part na boys quarters ne yasa bata ji diran motocin nasu ba, dan boys quarters ɗin ta baya yake, kuma motocin sabbi ne dal masu matuƙar tsada, kukansu a hankali yake fitowa, shi ne yasa basu ji ba.

Haurawa sama suka yi, kai tsaye bedroom na gwaggo gwaggon ta wuce da ita, shi kuma Lion yana cikin nasa bedroom ɗin, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barcinsa tsadaddu masu kyan gaske, launin white color, ya zauna a balcony yana amsa waya nasu Aseef, sai kuka Aseef yake yi mashi a kan ya shammacesu ya tafi, shi dai Areef ya sani tun time da Lion ɗin ya bar gidan, Aseef ɗin suka ɓoyewa, sai yanzu ya sani, shi ne yake cewa shi wlh ba zai yarda ba, to rigimar da suke yi da Lion ɗin kenan.

Wanka gwaggo tasa Rimsha ta yi, bayan ta fito, gwaggon da kanta ta shiryata cikin wata dankareriyar doguwar riga mai matuƙar kyau, da suka fita da Tga ne gwaggon ta saya masu su ukun dukka iri ɗaya, da yake du Jehan mazajensu basu zo ba, sai ta ajiye masu nasu, ita kuma Rimsha suka hau shiryata, sai ta fito cas kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta haɗu iya haɗuwa, gwaggo bata yi mata make up ba, ta ce su bar mata natural beautynta tafi kyau a haka.

Sai tsiya Akila take yi mata, sai kus, kus suke yi na munafurci, Akila tana gaya mata wasu zantukar a kunne, ita kuwa Jehan tuni ta fice zuwa bedroom nasu dan ta yi waya da Areef nata, ita kuma Akila ta tsaya ganin gulma, sai da aka yi wa Rimsha komai a gaban idanuwanta, gwaggo ta rufawa Rimshar wani haɗaɗɗen kuma tsadadden mayafi wanda ta feshe shi da tsadaddun Dubai perfume, ta rufa mata a kai ya sauko har saman face nata, tamkar za'a kai amarya, sai tsokanarta Akila take yi wai ta zama sabuwar amarya, gwaggo ta mai da ita sabuwar amarya.

A kule ta ce "Aunty Akila dama can ni sabuwar amarya ce, kuma kullum a sabuwa nake, ni ba zan zama tsohuwa ba bare yaya Saif ya auri wata".

Dariya sosai Brr Naurat ta kwashe da shi, Rimsha manya iyayen soyayya, wato dai bazata tsufa ba bare yaya Saif ya kara wani aure. Kuka ta saka masu, saboda Brr Naurat tana yi mata dariya.

Rungumota gwaggon ta yi tana faɗin "Babu wadda ta isa ta shigo maki gidanki, ko kin tsufa Saif ba zai kara aure ba, ki sha kuruminki abinki, ai ke Saif ne ma zai tsufa ya barki, dan ya ninka shekarunki sau biyu a yanzu, dan haka rabu da su, ke kaɗai zaki yi zamanki a gidansa, ki ci karenki babu babbaka, ke da kike da Ni? Ai kawai kyalesu".

Brr Naurat ma cewa ta yi "A'a mayar da wukar sarkin raki, ai kishiya bana yi maki fatanta, ita ce musabbabin ruguje mana farincikinmu, amma kuma ke kin gudu baki tsira ba, dan already ni Saif ya fara aura kafin ke".

Buɗe nayafin da gwaggon ta rufa mata ta ɗan yi, ta fito da face nata tare da wurgawa Brr Naurat ɗin harara tana faɗin "Yaya Saif ɗin ne ya aure ki kafin Ni?". Yadda ta yi maganar sai da ta sanya su gwaggo wani irin mugun dariya sosai, Akila har da rike ciki, kai Rimsha duniya, ita fa idan akan Noorish nata ne zasu ɓata da kowa, kamar ba yanzu gwaggo ta gama gaya mata ita kaɗai ce a wajen Saif ba.

Rarrashinta gwaggon ta sake yi tare da riko hannunta tana faɗin "Zo mu tafi na kai ki wajen mijinki hai, yana can yana kewarki, daga shigowarsa ya tambayeni ina kike, na ce mashi zan kawo mashi ke, rabu da su Brr, so kawai suke yi ki ɓata kwalliyarki dan kada Noorish naki ya ga kyanki".

Da sauri ta ɗago daga cikin mayafin tana kallon gwaggon, tambayar kanta ta fara yi a kan a ina kuma gwaggo ta jiyo sunan Noorish? Ita Brr Naurat ta ruke sunan Meesha, ita kuma gwaggo ta ruke Noorish, wai yane suka sanyawa masoyan nan ido haka ne?.

Tana can tana tunani har suka shiga bedroom ɗin bakin gwaggo ɗauke da sallama.

Har lokacin yana zaune a balcony suna hira da TRIPLETS nasa a waya, kewarsu sosai yake yi, Allah ya gani sune bugun numfashinsa, yana sonsu fiye da baki ya musulta.

Jin sallamar gwaggo yasa ya miƙe ya dawo cikin bedroom ɗin.

Kallonta ya fara yi daga sama har kasa, shi baya iya ganin face nata, saboda tana cikin mayafi, ita kuma tana iya ganin face nasa, saboda mayafin bashi da wani kauri sosai, shara shara ne. A hankali ya zane wayar daga kunnensa tare da katse kiran yana mai cigaba da kallonsu har suka isa wajen bed nasa.

Karisowa cikin ɗakin shima ya yi. A bakin bed gwaggo ta zaunar da Rimshar, ita kuma ta zauna a saman bedside drawer. Da ya zo shi ma sai ya zauna a bakin bed ɗin kusa da Meeshan nasa. A hankali ya shaki kamshin perfume nata tare da lumshe idanuwansa, har cikin farfajiyar zuciyarsa ya ji wani irin sanyi na daban.

Calmly ya furta "Good evening momma".

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce "Ɗazun mun gaisa ai, yanzu dai ka Rimshar taka na kawo maka ita, amana na baka yarinyar nan Saif, kamar yanda na gaya maka ɗazun, yanzu ma zan sake gaya maka, ka kula da ita tamkar yanda kake kula da su Aseef, zamu yi magana dai da safe yanzu zan je na kwanta". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa.

Good night ya yi mata yana mai kallonta, wucewa ta yi ta fice ta basu waje.

Tana fita ya fara latsa wayarsa, jim kaɗan ya kara wayar a kunne tare da mikewa tsaye, balcony ya sake komawa, Areef ya kira, bayan ya ɗauka ne sai ya ce mashi da safe ya tabbatar bai manta ba ya kai Aseef wajen Sheikh Sultan, dama ya gaya mashi yau da safe, to sake tuna mashi ya yi, dan kada su mance, yana son Aseef ya sami lafiya sosai, yanzu ne ya gane menene matsalar ciwon na Aseef, tun da abu ne na tsafi, to babu maganinsa sai ayar Allah, shi ne yasa ya ce su kai shi wajen Sheikh Sultan ya yi koda sati ɗaya ne, In Sha Allah za su sami sauki komai.

Bayan ya gama jaddadawa Areef ɗin, sai ya yi mashi sallama tare da dawowa cikin bedroom ɗin. Tana zaune tamkar yadda gwaggo ta ajiyeta, ta kudundune a cikin mayafi ta wani sunkuyar da kai. Kusa da ita ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu.

Calmly ya ce "Yau kuma kamar bake ba, duk kewata da kike cewa kin yi ba zaki iya rungumata ki yi mani oyoyo ba? Kin dameni a waya mazo ki ganni, ina zuwa ke na fara tambaya, amma ke kuma baki nemeni ba, since nake gidan nan, amma bama ki sani ba". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu zai cire mata mayafin nata, dan ya samu damar ganin face nata da kyau.

A hanzarce ta ɓoye hannayenta da suka ji kunshi suka yi maroon color

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login