Showing 216001 words to 219000 words out of 270744 words
har wani glowing zai rinƙa yi, to haƙiƙa ta tafi da imaninsa sosai ta yadda ya kafeta da idanu babu ko kyaftawa.
Turo baki ta yi kamar zata sa kuka. "Noorish ni gaskiya in dai da akwai mata a wajen bazaka je ba, ko ta online ɗin nema bana so". A shagwaɓe sosai ta yi maganar.
Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi, kasa kasa ya raɗa mata."To ai ke kaɗai kin ishe ni, ni bana ma haɗa hanya da mace, because dukka ina ɗaukarsu a abu guda, keda momma ce kawai kuke daban".
"Ni gaskiya duk da haka dai mu zauna tare a nan, ai idan kai baka kulasu su zasu kula mani kai, kaga kyau ɗin da kayi kuwa? Shi ne kuma zaka fita? Tab kana son ka saka mata su yi ta suma a kan hanya ko? Wata ma mayya mai kafar shamuwa nasan sai ta yi maka magana koda ba zaka kulata ba". Ta kai karshen maganar tare da sanya mashi wani irin kuka mai kama da na shagwaɓa, sai dai kuma na soyayya ce.
Shiru ya zuba mata idanu har ta gama zuba surutun nata tana aikin turo baki. Shi dai Lion kamar kullum, har yau murmushi sam bata ga gurbin zama a face nasa ba, Rimsha ta yi juyin duniyar nan dukka a kan ya yi mata murmushi ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa, amma ya ce sam shi bai iya ba, bai san ya ake yi ba, kullum fuska a ɗaure tamau, bata da zaɓin da ta wuce dole ta hakura ta rabu da shi, dan a yanzu ta fahimci rashin murmushin nan haka yake, ba zai taɓa yi ba, gara kawai ta kyale shi har Allah ya kaita ranar da zata ga murmushinsa koda sau ɗaya ne a rayuwarta.
"See your beautiful mouth like mace zata yi mani magana, aww ke yanzu Meesha kina tunanin yadda nake dake a nan haka nake magana da kowa a waje ne?".
Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.
Nisawa ya yi kafin ya ɗaura da cewa "Ai in dai ni ne yanzu ki fita ki zuba makudan kuɗaɗe ki ce namiji ma ya tinkare ni ya yi mani magana zaki bashi kuɗin, zaki ga ikon Allah, babu wanda zai kulaki ko me zaki basu, namiji ma bare kuma mace, ni ai kowa tsorona yake ji a kasar nan, i don't know the reason why, but wani lokaci zaki gani idan muka fita, yanzu haka idan kika tara mutane ɗari ba lallai biyar daga cikinsu sun san kalar voice nawa ba, yanzu dai jeki shirya kizo mu yi attending meeting ɗin a tare da ke, ba shikenan ba?".
Kai ta gyaɗa mashi tare da shigewa jikinsa tana murmushi, ita a dole ta ji kunya, ga wani guntun hawaye na iyashege a face nata.
Miƙewa da ita ya yi zuwa toilet, a tsakiyar toilet ɗin ya sauketa, sannan ya juya izuwa waje yana mai gaya mata idan ta gama wanka da akwai kayanta a drawer a cikin dressing room nasa, ta shirya sai ta zo ta same shi a ɗakin computers nasu, ya gama mata kwatance ya fito abinsa.
Ya ilahi ya lillahi, ai sake baki ta yi tana kallon toilet ɗin, duniya ne guda, ku dai my readers kun san yadda katafaren Daular Lion take, su Rimsha ce basu sani ba, ai sai tazama ƴar kauye, tun da take a rayuwarta ma bata taɓa ganin jacuzzi irin na Lion ba, ga wasu kyawawan kwan yantarki masu bada hasken blue light a ciki masu matuƙar ɗaukar hankali, duk sai ta rasa ina ma zata bi, girman toilet ɗin kawai ya kai girman ɗakuna da koma na gidan wani, wajen mayukan wanke kansa ma kawai tamkar shop na sai da mayuka mai girman gaske, show glass na jera mayukan goge bakinsa kawai abin kallo ne, bare azo kan sauran abubuwa, duk sai Rimsha ta rasa ma wanne yafi haɗuwa, toilet ɗin ko bedroom ɗin. (Ni kuwa nace dan ma baki shiga dressing room bane, ai da sai kin wuni kina kalle kalle.)
Tafi 30 mins tana kalle kalle kafin ta nufi wajen jacuzzin nasa, sam bata san taya zata haɗa ruwan wankar ba, saboda kusan komai na cikin toilet ɗin da remote da kuma madannai suke amfani, show glass ɗin nan ma da na'ura suke amfani, shi kuma Lion shap na mance da bazata iya amfani da abubuwansa ba har sai idan shi ya koya mata, ya mance ne ya sauketa ya fice kawai.
Almost 20 mins tana tsaye a wajen jacuzzin ta rasa ta ina zata taɓa ruwan zafi dana sanyi su zubo. Kamar daga sama ta ji kamshin perfume nasa ya daki kofofin hancinta.
Da sauri ta kai kallonta izuwa bakin kofar shegowa. Yana tsaye ya goya hannu a Lion chest nasa. Turo mashi ɗan bakin nan ta yi tare da wurga mashi harara da waɗan nan dara daran fararen Sleeping eyes ɗin nata.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da karisowa izuwa cikin toilet ɗin, dama ya jita shiru ne yasa ya tuna cewa da wuya idan zata iya amfani da toilet ɗin nasa, shi ne ya zo dubata, ashe kuwa haka ɗin ne.
Sumbata ya manna mata a ɗan bakin da tare turo mashi ɗin kafin ya haɗa mata ruwan, zuba mashi idanuwa ta yi tana kallon abubuwan da yake dannawa a jikin remove ɗin ruwan yana fitowa, sai da ya zuba na zafi mai ɗan yawa kafin ya dakata ya zuba mata na sanyi.
Ba tare da ya taɓa ruwan ya ji ta yi dai'dai ne ko bata yi ba ya ajiye remove ɗin a mazauninsa, saboda already haka yake haɗa nasa ruwan kullum, so ita ma a haka zata shiga koda ya yi mata zafi. Wajen brush ya nufa, yana kai hannunsa saitin wajen kofar glass ɗin ta buɗu mashi, brush ne dayawa tamkar a shagon sai da su, dik masu kyau ne da tsada sosai, amma sai da ya tsaya ya zaɓa mata karshen haɗuwa a cikinsu, sannan ya fito mata da mayukan goge baki.
Ita dai tana tsaye tana kallo ikon god, ta zama ƴar kauye putuk, wannan abubuwa haka ina zata iya? Komai an wani zuba mashi matakan tsaro an killace, to ina ga kuma ita da take matarsa?.......... Dole ki tambaya kam Rimsha, komai na amfani a cikin toilet ma kawai a killace suke da tsari har haka ina ga ke kuma matarsa? Ai zaman ɗaki ne ya kamaki, dan Lion dai ba zai bari kina fita waje ba, saboda tsananin kishi.
Ta shagala da kalle kalle sai ji ta yi ya hura mata iskar bakinsa a face nata. Kara turo baki ta yi kamar zata yi mashi kuka. "Remain 30 mins mu fara meeting, ki yi sauri". Ya faɗa tare da juyawa ya fice abinsa.
Da kallo mai cike da tsantsar kaunarsa ta bishi da shi, har sai da ya kurewa ganinta, sannan ne ta juya ta nufi cikin Jacuzzin bayan ta cire kayan jikinta dikka.
Sosai ruwan ya yi mata zafi, amma bata da zaɓin da ya wuce ta shiga ciki, dan yana jiranta ne. Bata ɓata lokacin wajen yin wankar ba, ta fito ɗaure da towel a kirjinta, dressing room ɗin nasa ta shiga, nan fa sabon kallo ya ɓalle, nan taga duniya, tamkar super market na sayar da kaya kawai, glass na jera watch's nasa ma kawai ya isa mutun ya wuni yana kallo. Dik da tasan yana jiranta, hakan bai hanata tsayawa ta bawa idanuwanta abinci ba, sosai ta rinƙa bin duk wasu glass tana dubawa, harta na takalmarsa da su nasu glasa ɗin ma kamar fridge aka yi su, dik sai da ta leƙa. Almost 20 mins tana a ciki tana kalle kalle tare da kauyanci kafin ta nufi wajen drawer da ya ce mata kayanta suna a ciki.
Cikin sauri ta fara duba wanda zata sanya a jikinta, duk babu kayan kirki a ciki, kaya ne irin nasu na turawa, to dama shi da bai ma san ya dressing na hausawa yake ba ta ina zai samo maki irin namu? Ai dole ne kawai ku koma amfani da irin nasu, ɗan gara ma Areef da ya nuna sha'awarsa a kan Atamfa idan Jehan ta sanya, so shi zai iya sanyawa ɗaya daga cikin family ta yi mashi order Atamfa a yiwa Jehan ɗin ɗinki a can a sako a jirgi, amma shi Lion da Aseef da basu ma san me atamfar ba ta ina matansu zasu gansu har ma su sanya? Ai Akila da Rimsha sun sallami su Atamfa, sai dai idan wajen Jehan zasu rinƙa zuwa suna kwasa.
Wasu ƴan kananan kwali ta gani a cikin drawer, guda ɗaya ta ɗauko ta fitar, wani irin shegiyar doguwar riga ce a ciki, ba irin dogayen rigunar da kuka sani bace, a'a wannan tsarinta daban take, tana da tsagu daga cinya har kasa ta gefe guda, ga cof na breast part a jikinta, bata da hannu sam sam rigar, sai dai tana da bala'in kyau na wuce tunanin mai tunani, ta tsaru ga fitinar tsada.
Ɗaukar shi ta yi tare da ɗauko wani always and pant ɗin ta fito izuwa cikin ɗakin, da sauri sauri ta shirya cikin kayan. Tamkar dan halittar jikinta aka yi kayan, ta fita sosai, sai kuma zanen sunansa da yake a saman tudun tula tulanta ya bayyana, saboda rigar bata da hannu, cof na breast part ɗin nata ma bashi da girmar da zai rufe har sunan nasa, sai zanen ta fito ɓaro ɓaro sosai. Ta haɗu karshen haɗuwa, ga wani irin shegen high heels da ta zuba a ƴan kyawawan kafafun nan nata, tamkar wadda zata tafi wajen dinner party, gyara gashin kanta da kyau da kyau ta yi, sannan ta bul bula perfume nasa a jikinta, wlh baki ya yi kaɗan ya zayyana irin kyan da ta yi, ga shi launin kalar rigar pink color, abin sai ya yi mugun haɗuwa.
Da kyar take iya tafiya, saboda high heels ɗin, ga kuma tiles mai tsantsi, sannan ga kafarta dama yana ciwo. A haka ta fito wajen da kyar tana jan kafafu, ta zuba gashin nan nata a baya kamar wata indiyana.
Kai tsaye in da ya kwatanta mata ta nufa, da yake ta hanyar da ya ce tabi ba hanyar kowa bane face nasa shi kaɗai, sai ya zamana bata ci karo da kowa na gidan ba har ta isa ɗakin.
Yana zaune a saman wata shegiyar haɗaɗɗiyar sofa mai bala'in laushi, sai aikin latsa wayarsa yake yi. Jin sautin karar takalmarta a tiles ɗin ne yasa shi ya ɗago da kallonsa izuwa hanyar shigowa. Ai bai san time ɗin da ya kawar da wayar tasa daga saitin face nasa dan ya sami damar kallonta da kyau da kyau ba, ta haɗu iya haɗuwa, nan take ya ji wani irin azababben sha'awarta ta kara motsa mashi, dama tun daren jiya yake fama da hakan, dannewa kawai ya yi bai taɓata ba, saboda tsaro, amma yanzu ta sake taso mashi da sabon tsumi.
Kusa da shi ta kariso ta zauna tana wani yauki da turo ɗan baki. Tun da ta shigo idanuwansa yake a saman tudun tula tulanta, zanen sunan nan nasa kawai yake kallo, abin yana kayatar da shi a yanzu, tsareta da idanuwa ya yi bai iya ce da ita ko uppan ba.
"Noorish kayan sun yi mani kyau?". Zazzaƙar muryarta ne ta katse mashi tunani.
Doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, hannu kawai ya kai ya jawota jikinsa ba tare da ya yi magana ba, har wani irin zir zir yake jin Heronsa tana yi mashi, saboda tsananin sha'awarta da yake ji.
"Noorish baka gaya mani na yi kyau ko ban yi ba?". Ta faɗa a shagwaɓe sosai.
Haɓarta ya ɗago tare da haɗe fuskokinsu waje guda. "Kullum ke mai kyau ce, kuma a haka kike, amma na yau the kyau is too much for me, kin jefani a cikin wahala".
Tongue ɗinta ta fitar ta ɗan lashi lips nasa, tana murmushi bata ce komai ba. Ya ilahi, ji ya yi kamar ya tashi ya cireta tsab ya shiga kayarsa, sai dai kuma ina tana period, ba shi da zaɓin da ya wuce ya hakura kawai.
Sun ɗauki almost 10 mins a haka kafin nan ya saketa tare da bata wani kwali karami. Karɓa ta yi ta buɗe, ƙaramin hijabi mai matuƙar kyau ne a ciki, sanyawa ta yi a jikinta, a iya dai'dai flat tummynta ya tsaya, dama yasan kalar kayayyakin da suke a cikin drawer tata, shi ne yasa ma ya tanada mata hijabi.
Hannunta ya riko suka nufi saman wasu haɗaɗɗun chair dake a gaban tables na desktop computers ɗin, ya zauna a saman chair ɗaya ita ma ta zauna a saman ɗaya, sannan ya kunna computer ya yi setting nata.
A lokacin duk waɗan da za'a yi meeting ɗin da su sun hallara saura shi kaɗai suke jira, dama already tun da Rimsha ta ce ita bata so ya je, sai ya sanar masu da zai yi attending meeting ɗin amma ta online, dan haka su shirya, hakan yasa suka san da zancen ta yadda zai yi attending ɗin, sai suka shirya nasu computer kawai suna jiransa.
Gabaɗaya jiga jigan ƴan siyasar da suke a cikin wannan katafaren office ɗin babu wanda bai sha ruwan mamaki ya kuma girgiza da ganin Lion a tare da mace ba, duk da wasu daga cikinsu sun gan shi a airport lokacin da ya ɗauketa, basu ɗauka cewa yana tare da ita har a yanzu ba, duk sai suka tsareta da waɗan nan idanuwansu na turawa masu kama da glass ɗin, sai kallonta suke yi, hakan ba ƙaramin ɓata mashi rai ya yi ba, kun san shi da ɗan banzan kishi, duk da cewa dukka waɗan da suke cikin office ɗin sun haura sheƙaru hamsin, ba yara bane, shi ne ma kawai matashi mai jini a jika a cikinsu, amma kishi yasa ya daka masu wata uwar tsawa, wadda ya sanyasu wata uwar firgita, ba su kaɗai suka firgita ba harda ita kanta Rimshar.
Sarai yasan sun haife shi, wasu daga cikinsu ma sun yi jika da shi, amma hakan bai hana ya daka masu tsawar ba!.
Babu wanda bai razana na jin tsawar tasa ba a cikinsu, cike da izza da nuna isa ya tambayesu meeting suka zo yi ne ko kuma kallon matarsa?.
Wani irin mamaki ne ya kama Rimshar na ganin yadda waɗan nan jiga jigan ƙusoshin gwamnati kuma tattijawa suke girmama shi, kuma suke tsoronsa, bugu da kari ta ga ba yadda yake magana da ita ko TRIPLETS nasa haka yake magana da su ba, a nan yana magana ne da kaifi ɗaya da kuma tsantsar madarar isa da izza, magana ɗaya ba sake maimaitawa!!. E yanzu kam ta yarda ita kaɗai Lion ya canzawa, ita kaɗai yake yi wa magana cikin sanyi da tausasawa, a waje shi ɗin zaki ne mai firgita manya da kananan halittu da gaske!!.
Kusan gabaɗaya waɗan da suke a cikin office ɗin sai da suka yi kasa da kansu alamar suna bashi hakuri, saboda duk da yake yaro a cikinsu, shi ne shugaba a samansu, shi ne president nasu nan gaba kaɗan In Sha Allah, so basu da zaɓin da ya wuce su bashi hakuri tare da girmamawa.
Kara ɗaure fuska tamau kamar hadari ya yi tare da ce masu shi ya fasa attending na meeting ɗin ma, idan akwai wani abin da suka tattauna very important suna iya tura mashi ta massage's, zai duba ya gani idan ta yi mashi.
Yana kai karshen maganar bai saurari amsarsu ba ya kashe computer yana wani huci kamar wani zaki, sun ɓata mashi rai na irin kallon da suka tsare Rimsha da shi
Areef and sir Arvin ne suka shigo cikin computer room ɗin, bakin Areef ɗauke da sallama.
Ganin Lion a tare da Rimsha yasa Areef ɗin ɗan yin murmushi kaɗan, duk da yana cikin matsananciyar damuwa na halin da Jehan take a ciki, hakan bai hana ya ɗan yi murmushin ba, shi ma sir Arvin duk da dama bai san wacece Rimshar ba, bai san face nata ba, sunanta kawai yake ji, ganin ɗan uwan nasa a tare da ita yasa ya ɗan yi murmushi yana faɗin "Kun haɗu kenan?".
Wani kallo Lion ɗin ya jefa masu, dan shi ransa a ɓace take basu sani ba, ya yi nadamar meyasa ma bai sanyata ta sa face mask ba da zasu yi attending na meeting ɗin, kawai sun tashi sun kalle mashi face ɗin mata a banza, da wasu shegun idanuwansu kamar ball.
"Saif kazo ka duba jikin Aseef fa baya jin daɗi". Cewar sir Arvin.
Ɗan zaro idanu Lion ɗin ya yi, no wonder mana yake jinsa duk sai a hankali, ashe da biyu, dole ya ji jikinsa tana yi mashi babu daɗi.
"What's wrong with him?". Ya faɗa yana kallonsu.
Hannu Areef ya kyastawa Rimshar da ta tsare Lion ɗin da kallo a saman face nata yana faɗin "Zazzaɓi ne yake damunsa, ke kuma Our Queen mu fa ba ɗaukar Lion muka zo yi ba, kin wani tsare shi da idanu kamar mun ce zamu gudun maki da shi".
Turo baki ta yi. "Kai Yah Areef ni ba shi nake kallo ba". Ta faɗa kamar zata yi kuka.
"To kai Areef ina ruwanka da ita? Kafa cika sa ido, ai gara ta tsare shi da idanu mana, ba nata bane shi ɗin? Mallakinta ne fa, kin ji yi ta kallon abinki, naki ne ke kaɗai". Cewar sir Arvin.
"Good morning". Ta faɗa tana satar kallon sir Arvin ɗin, tana son kallon shi kai tsaye, saboda ta kalli mai kama da Noorish nata, amma tana jin kunyar su haɗa idanu.
Matsowa kusa da ita ya yi ya ɗan rungumota kaɗan yana faɗin." Morning my sister how was your night?".
Kallon Lion Areef ya yi, dan yasan ba zasu shirya da sir Arvin ba, duk da cewa al'adarsu ce rungume mutun idan suna gaisawa, ko kuma su bashi hannu, to wlh shi dai Lion ya yaye wannan al'adar, matarsa da shi kaɗai zata haɗa hannu, sannan shi kaɗai zai rungumi kayarsa, sir Arvin bawan Allah shi bai sani bane, bai san kishin ɗan uwan nasa har ya kai haka ba, da ya sani shi ma ba zai taɓata ba.
Lion ɗin kuwa dama can ransa a ɓace na