Showing 258001 words to 261000 words out of 270744 words

Chapter 87 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2986

QUADRUPLE, haka zalika matan nasu ma gabaɗaya kwalliya iri ɗaya Josephine ta yi masu, dukkansu sari Pink color suka sanya.

Rimsha sarkin son ta yi kyau, tuni ta saki dark black curly hair nan nata har baya, ga wani uban sarkar diamond da gwaggo ta ɗaura mata a ƙugunta, abin sai ya tashi kai matuƙa gaya, ta yi wani irin azababben kyau.

Dukkansu Josephine ta feshesu da perfume mai bala'in daɗin kamshi.

Sai santin kyan da suka yi gwaggo take yi, ta yaba ta sake yabawa.

An shirya baby's cikin wasu shegun kaya masu matuƙar kyau, sannan aka jibga masu wasu uban kayan sanyi masu bala'in kyau da tsada a saman kayan nasu, sai wani irin bala'in kamanninsu da iyayensu maza ya bayyana, a cikin baby's ɗin Areef guda ɗaya ya fito mai tsananin kama da gwaggo sosai, ɗayan kuma tamkar Aseef, biyun kuma da shi suke kama, kuma biyu daga cikin baby's ɗin ne suka ɗauki kalar idanuwnasa wato ash color, saura biyun dukka idanunsu irin na Jehan ɗin ne, suma baby's dai sun yi gadon dara daran idanuwan Dr Salman, dattijon nan ya rabar masu gadon idanu kam, akwai su da dara dara ba karya, da wannan idanu ake iya gane cewa jinin Dr Salman ne, dan duk kusan design na idanun nasu iri guda ne, sai dai na wani ya fi na wani girma, amma duk idanun Dr Salman ɗin ne.

Har karfe 11 ana ta wannan uban shirye shiryen, baki ma ya yi kaɗan ya zayyano irin shirin da suka yi wa walimar nan, sun yi kyau na wuce misali.

A cikin waɗan nan sabbin motocin da aka saiwa His Excellence Saif za su tafi, Lion ɗin ne ya ce a ɗaukesu a cikin motocin, duk da cewa already an sayawa mahaifiyar His Excellence nata motar, haka zalika ita ma matarsa, amma ya ce ina su tafi a nasa motocin.

Suna ƙoƙarin fita, wasu ma har sun yi gaba sun sauka parlourn kasa, part ɗin ya rage daga Jehan, Rimsha sai kuma gwaggon, su ne suka yi bayan sauka kasa, ana can kasa an haɗu a parlourn ana jiransu, su kuma sun tsaya jiran Rimsha tana aikin ɗaure igiyar uban high heels da take sanye da su a kyawawan kafafunta.

Bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin.

Wani irin cool murmushi gwaggon ta sakar mashi tana faɗin.
"Sai yanzu ka tashi?".

"No sai yanzu dai na iya fitowa, amma tashi kam tun ɗazun na yi shi".

Ya faɗa yana ƙarisowa cikin ɗakin. Tun da ya sako kyawawan kafafunsa cikin wannan ɗakin idanuwansa suke a kan babyn tasa, ta tashi kansa over, sai ya ji ina, ai ba zai ma iya barinta ta tafi ba, wani irin zir zir ya ji a jikinsa, sabuwar tsumi ta tashi mashi.

Ita ma a nata ɓangaren sai kallon shi take yi kamar nace zan kwace mata shi, ya yi matuƙar kyau cikin shigar three cuter fara kal mai bala'in kyau and shirt sky blue, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hairn nan nasa a baya, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin yake yi.

"Good afternoon Momma". Ya faɗa har lokacin ya kasa kawar da idanunsa daga kanta.

Fuska a ɗauke da fara'a gwaggon ta amsa mashi gaisuwar tare da tambayarsa ya ya tashi?.

"Na tashi cikin farinciki da ban taɓa shiga irinsa ba my Momma".

Ya bata amsa yana dawo da kallonsa a kanta.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce Alhamdulillah ya Allah, sannan ta yi mashi sallama a kan kowa yana parlourn kasa yana jiranta, to sun wuce.

Addu'ar Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya ya yi masu.

Gaba gwaggon ta yi rike da hannun Jehan, ita ma Rimsha ta rufa masu baya.

Cikin sauri ya riƙo kyawawan hannayenta tare da ɗan jawota jikinsa. Bai yi magana ba sai dai ya zubawa gwaggo da Jehan idanu har sai da suka fita, sannan ya dawo da kallonsa a kan matar tasa.

Cak ya ɗauketa sai cikin bedroom nasu, ko uppan bai ce mata ba, ita ma bata ce mashi ko uppan ba, kawai ta bishi da kallo ne.

Sai saman katafaren bed nasa ya direta. A kusa da ita ya haye ya zauna yana ta kallonta.

Kwantowa ta yi a jikinsa, cikin shagwaɓa ta ce.
"Noorish lafiya?".

Hannunta ɗaya ya riƙo cikin nasa kafin ya fara magana.

"Meesha anya zan iya bari ki je wajen walimar nan kuwa? Kin yi kyau over ne".

Kyawawan fararen yatsunsa ta riƙo, a shagwaɓe ta ce.

"To shikenan Noorish ai sai na fasa zuwa! Dama me zan je nayi a wajen da mijina aljannata baya nan? Me zan je nayi awajen da farincikina baya wajen, na san ma kona je wajen tunaninka kawai zan yi ta yi, dan haka gara mun kawai na zauna a tare da kai king of my heart".

Tana magana tana murza mashi ƴan yatsunsa.

"Meesha da gaske zaki fasa zuwa ki zauna da ni?".

Da sauri ta gyaɗa mashi kai tana faɗin. "Mai zai hana my Noorish, ai bama zan fasa zuwa ba, na rigada na fasa zuwa, zan zauna da mijina".

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali.
"Me kike so ni kuma na yi maki my wife?".

Nisawa ta ɗan yi kafin ta kamo hannunsa ta ɗaura a saman shafaffen cikinta, cikin nutsuwa ta fara magana.

"Abu biyu nake so, na farko in samu ciki nima in haifi baby's nawa masu kama da kai, abu na biyu kuma shi ne bakin ruwa, kullum da ina ƙarama idan zan yi mafarkinka ina yinsa ne muna a bakin ruwa muna zuba Love, to wajen nake son ka kai'ni Noorish na".

"Iya su kawai?".

Da sauri ta gyaɗa mashi kai.

Ƙanƙameta ya yi a jikinsa sosai tare da gaya mata cewa tabbas zasu je bakin ruwan nan kamar yadda ta buƙata, maganar ciki kuma yana addu'ar Allah ya basu, Allah yasa wasan da zai buga a yanzu ya samu nasarar zura kwallo a raga.

Da amin ta amsa mashi da shi kafin ta gyara kwanciyarta a jikinsa.

Hannunsa ya zuro a ta cikin kayan nata ya fara shafa plat tummyn nata.

Narke mashi ta fara yi tana kara shigewa jikinsa. Kan ka ce me ya birkice mata, tuni ya cire duk wannan uban kwalliya da Josephine ta zauna ta yi mata ɗin, duk ya rabata da komai kafin ya fara aikin juyata son ransa, tamkar ba ɗazun suka hau network suka sauƙa ba.

Ita ma haka ta cigaba da biye mashi babu kama hannun yaro, lamarinsu sai dai mu ce azimun.......🥱

Su kuwa ƴan zuwa walima, sun jima a parlourn ƙasa suna jiran Rimshar ta fito, amma shiru bata fito ba.

Da Areef ya ga haka sai ya ce da gwaggon wai ina Rimshar suka barota ne dama?.

"Tana tare da Saif a part nawa". Gwaggo ta bashi amsa.

Guntun murmushi Areef ɗin ya saki kafin ya ce. "Ku mu tafi abinmu, dan in zaku kwana a nan Rimsha ba zata zo ba, tab Lion fa, ai tun da suka yi wannan kwalliyar suka yi kyau to ita Rimsha sai dai hakuri, kishi ba zai kyale shi ya iya barinta ta fito ba, ai muje kawai".

Da farko Gwaggo ta so ta ce su ɗan kara jira ko kuma Aseef ya je ya dubota, daga baya kuma sai ta ce to su tafi ɗin kawai, idan ma zata je shi Lion ɗin ya kawota da kansa.

Haka suka tafi abinsu, ita kuma Rimsha tana cikin bedroom tana manne da babynta suna aikin da suka saba.

Walima ya yi walima, waje ya yi waje, sun yi rabon kuɗi ba karya, sai dai fa kowa kallon Lion yake yi wa Sir Safwan, saboda ba mai iya banbantasu idan ba Rimsha da kuma su gwaggo ba, su gwaggon ma ba su jima da fara iya banbantasu ba, kunsan idan kana zaune da mutane waje guda, to dole dole a kwana a tashi watarana zaku iya rabesu komai kamanninsu kuwa, to hakan ce tasa su gwaggon ma suke iya rabesu, dan sun zauna da su, shi Areef ma dama already yana iya rabesu, ga kuma Aseef da Mahhir wato Alex, suma kada ku manta kamanninsu ɗaya, banbancin kwayar idanu ne kawai.

Kowa idan yazo kallon Sir Safwan a matsayin Lion suke yi, babu wani bare daga waje da ya iya banbanta su ko ya iya gane cewa ba Lion bane a wajen.

Anyi bidiri ba karya, gwaggo ita ce ta rinƙa rabon abubuwa, sai hotuna ƴan jaridu suke yi mata, ga shi ta sha kyau sosai da sosai, shi kam Dr William bawan Allah ɗan baruwana, duk abin da gwaggo ta faɗa hakan za'a yi, baya ja da maganarta, kamar wani mijin Hajiya, kuma ba haka bane, kawai tsananin sonta da yake yi ne, da kuma yasan halin kayarsa, tun tana ƴanmata har izuwa yanzu bata canza hali ba, ya santa da shegen son girma ga nuna izza, isa da taƙama, ai ba'a ƙasa su Lion suka ɗauko wannan dabi'u ba, a jiki yake.

Hakan yasa Dr William kam yake biye mata, komai ta ce sai ya ce Okey baby.

Taro ya yi taro, dan tsayawa zayyana maku irin taron da aka yi sai ya cike mun ɗan filin da ya rage mun dan na kammala book nan, dan haka ku kawata wannan taro a ranku ya zai kasance? Haɗuwa iya haɗuwa ne, iyalan His Excellence Saif da kansa ne a wajen, kunga kuwa ai abin ba'a magana.

Suna dawowa daga wajen walimar nan naƙuda ya kama Aylar daddyn Jelly, zata haifo masu ɗan U.s kenan, kamar dai yadda aka saba gwaggo ce ta karɓi haihuwar, yaro namiji kyakkyawar gaske fari tas da shi suka samu.

Family sun yi murna, sai samun karuwa suke ta yi, amma kuma kowa so yake yi ya kalli yaron Lion and sir Safwan, kowa a ƙage yake da ya kalli nasu.

Abin har ya fara yi wa gwaggo daɗi, yadda taga in dai za'ayi maganar yara to fa yaran Lion da babu su babu alamarsu su ne a farkon magana, sai jinkirin haihuwar na Lion ɗin ya yi mata daɗi, dan ga shi gabaɗaya family har kasa bakiɗaya jiran ƴanƴan nasa suke yi, yaran Lion masu tsada da kuma wuyar gani, su Imran duk zancensu kenan, kowa ƴaƴan Lion, kowa Rimsha shiru har yanzu, gara Sir Safwan basu cika maganar nasa sosai ba, saboda Maryam tana da ciki, ita kuma Rimsha jiya eyau, babu wani canji sai shegen kyau da take karawa tana kara rikita mana Lion ɗin mu........😌

Mummynta da daddynta ma dukka yanzu ƴaƴan nata kawai suke da muradin gani, sun ga na Jehan kam, bare ma mummy da kunsan tafi son Rimshar, sun fi shakuwa, dan haka sai ta fi jin ƙaguwar ganin ƴaƴan Rimshar, shi kansa Dr William ƴaƴan Lion kawai yake jiran ya gani.

(Yaran Lion namu masu tsada ne fa, kowa jira yake yi ya gansu?🤔 Sun saka mana ido fa😒😌)

Wannan family guda biyu, wato familyn Dr Salman and Dr William za'a ce ne ko kuma Jacob Roshan, to dai waɗan nan two families da suka cure waje gudan ba ƙaramin farinciki suke yi ba, Adiva taga daddynta, ta makale mashi da wani cikinta a gaba.

Baki ya yi kaɗan ya iya zayyano maku irin tsantsar farincikin da waɗan nan family suke a ciki. Satinsu Abba biyu suka koma Nigeria abinsu.

Ranar da suka koma tamkar sun koma ne da lafiyar Rimsha, tun daga ranar ta fara ciwo, ciwo, zazzaɓi bini bini, shi Lion ya san matsalar kayarsa, domin kuwa ko ciwon kai Rimsha ta yi baya iya barci sai ya binciko dalili ya kuma nema mata lafiya, so a yanzu ma hakance, sarai yasan dalilin rashin lafiyar tata, sai dai yaki sanar da kowa, idan su sir Safwan sun tambaye shi, sai ya ce babu ruwansu.

Gwaggo ma ta yi tambayar duniyar nan amma yaki gaya mata menene yake damun matar tasa, ta ce zata duba lafiyarta, nan ma ya ce a'a ta bar mashi matarsa, ai shima Dr ne, dan haka su barsu kawai.

Haka gabaɗaya family suka zuba masu idanu suna kallonsu, sai fama da ciwo Rimsha take yi kamar zata mutu, su Areef sun kasa jurewa, hakan yasa suke takura mashi a kan dole su kaita hospital, saboda su ciwon nata yana damunsu.

Da dai yaga sun takura masu a gidan, sai ya shirya tsab tare da sanar da tsofaffin sojojinsa wato su Donal kenan, ya ɗauki Mark, Donal, Tyrone da kuma wasu sojoji guda biyu, ya ce su shirya su kaɗai yake da buƙata zasu raka shi wani waje.

Bayan ya sanar da su ne ya dawo cikin bedroom nasa, Rimshar tana kwance a saman bed ta yi shiru kamar mai tunanin wani abin, duk ta rame baiwar Allah, kamar ba ita ba, sai gulu gulun idanuwa zaka gani.

A kusa da ita ya zo ya zauna bayan ya ɗauko A box, cikin dabara ya lallaɓata ya yi mata alluran barci, sannan ya kira Sir Safwan a waya a kan ya zo bedroom nasa ya same sa.

Ba tare da ɓata lokaci ba Sir Safwan ya zo. Cike da so da kauna ya ce mashi.

"Zan yi tafiya na ɗan lokaci, dan haka ka shiga office nawa a matsayin kai ne ni, dama babu mai iya banbanta mu, so ka rike mun aikina sai na dawo, tafiyar sirri zan yi shiyasa na yi wa Meesha alluran barci, so ka kula da komai, and lastly jibi zaku koma white house da zama, tun da komai ya dai'dai a yanzu".

Ya kai karshen maganar tare da miƙe ya hau shirya duk wani abin da zai buƙata.


"Amma ina zaka je haka?". Cewar sir Safwan ɗin.

Da mamaki ɗauke a saman face nasa ya jefa mashi wannan tambayar.

"In da Meesha ta fi so a rayuwarta, wajen mafarkinta zamu je mu huta, dan kun saka mata idanu sosai a gidan nan, gara na ɗauketa muje ta huta a wani wajen ko ta huta da jin muryoyinku na tambayarta ya jiki, musamman ma kai ɗin nan, kafi kowa takura mata da ya jiki".

"Amma akwai waya a wajen ai? What I mean here is zamu iya samunku a waya ko?".

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E54


"Amma akwai waya a wajen ai? What I mean here is zamu iya samunku a waya ko?".

Jinjina mashi kai ya yi alamar e ba tare da ya yi magana ba.

"Okey tom Allah ya tsare hanya, ka dai kula mana da our Meeshar mu, dan naga kamar ba ita kaɗai ba ce".

Nan ma jinjina mashi kai ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Juyawa Sir Safwan ɗin ya yi ya fice daga cikin ɗakin, shi kuma Lion ya hau shiri na duk abin da zasu buƙata.

Ta kofar sirri wanda yake ta bayan ya fice, gwaggo and Dr William kawai ya sanarwa da ga in da za su je sai sir Safwan ɗin.

Addu'a sosai iyayen nasa suka yi mashi tare da sanya mashi albarka, sannan suka ce ya kuka masu da Rimsha sosai. Amin ya rinƙa amsawa da shi kafin ya sa kai ya wuce abinsa.

Iya waɗan nan sojoji daya ware ne kawai suka bisa, bayan ya fita ta baya ɗauke da Rimshar tasa dake barci, sai sojojin suka zago suka same shi, da motoci biyu suka tafi.

Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin su isa baƙin wata dam, already an shirya masu jirgin ruwa ɗan ma dai'daici, yana zuwa kawai suka kama hanyar tafiya.

Gabaɗaya tsallake arear su suka yi, suka nufi ɗayar tsagin, tamkar yadda Rimshar take damunsa tana son rayuwa a irin wannan waje, haka ya kaita yau, a bakin ruwan su Mark suka yi aikin haɗa masu irin wannan ɗakin da take magana a kai ɗin.

Da yake ya san in zasu je, sai ya tanaji komai, harta electric katifa dake aiki da wuta, kuma yana aiki da Power bank, to haka su Mark suka sha aikin shirya waɗan nan abubuwa, jirgin ruwansu kuma suka baro shi a can jefe.

Sai zuba barci Rimshar take yi, bata san me yake faruwa ba, sai dai ta farka taga surprise.

Baya su Mark sun kammala aikin haɗa masu komai, ɗauko Rimshar ya yi daga cikin jirgin ruwan ya kawota cikin ɗakin, suna da komai a cikin jirgin ruwan, har da katafaren bed, amma dan ya cikawa Rimshar mafarkinta, sai yasa aka yi mata irin wannan ɗakin da take so a rayuwarta, suka rufo jirgin ruwan nasu kuma.

Kwantar da ita ya yi a saman electric bed ɗin nasu, sannan yasa su Mark su kawo masu trolleynsu. Mark kam mamaki ne kamar zai kashe shi, yarasa dalilin da yasa Lion ya zo nan wajen, me ya kawo shi? Ga shi ba halin tambaya.

Bayan sun kawo mashi trolleyn ya karɓa ya koma cikin ɗakin, su kuma suka tsaitsaya a gaba da bayan ɗakin dan bashi tsaro.

Kayan jikinta ya cire mata ya sanya mata pajama mara nauyi, dan ya ga duk da sanyin da yake a ƙasar tasu ita zufa take haɗawa, hakan yasa ya canza mata kaya izuwa shara shara mara nauyi.

Daya kammala sai ya ɗauki kayan da zai buƙata ya koma cikin jirgin ruwansu dan ya yi wanka ya shirya, ya rufota a cikin ɗakin. Tyrone ne ya bi bayansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login