Showing 51001 words to 54000 words out of 270744 words

Chapter 18 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2938

yanzu idan gaskiya ta gama bayyana, shi Aseef me makomansa? Kenan idan ba mutun bane tafiya zai yi ya barsu? Ko yaya ne? Ya ilahi ya lillahi.

Gwaggo ce ta matso tana faɗin "Saif ka tashi dan Allah".

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da waro idanuwansa a hankali, kai tsaye sai saman face nata kallonsa ya sauka. Shiru ya ɗan yi kafin ya kai hannu ya ɓalle karin ruwan da aka sanya mashi, ya cire, sannan ya yunkura ya mike zaune.

"Saif meyasa ka cire ruwan kuma?". Cewar gwaggo. Girgiza mata kai ya yi alamar baya da bukatar ruwan. Matsowa ta yi tare da dafa kafaɗarsa tana shafa kansa da hannu ɗaya.

Ɗago idanu ya yi yana kallon TGA dake tsaye a gefe guda, tun da yake da Uncle T ɗin nasa, bai taɓa tsura mashi idanu yana kare mashi kallo irin na yau ba, zuciyarsa na gaya mashi cewa har da uncle T ɗin yanzu a tafiyar su Josephine ɗin, amma yaki yarda da hakan, saboda wasu dalilan guda biyu, na farko TGA yana sonsu so na tsakani da Allah, dan an taɓa yin yunkurin harbin Lion ɗin ma da bingida, GTA ya tare, ya shiga tsakaninsu bullet ɗin ta same shi, na biyu kuma, TGA yana ɗan ƙaramin yaro lokacin da abubuwan suka fara faruwa, sai dai abin da ya sanyawa Lion ɗin shakku a kan Tga ɗin shi ne, meyake kai shi wajen Josephine a yanzu? A gaban idanunsu zai nuna baya son Josephine, amma a bayan idanunsu zai saci kafa ya je wajenta, ga uncle Herry ma, a gaban idanunsu yana nunawa baya sonta, amma a bayansu kuma 5 and 6 suke da ita. Wannan abin akwai matukar ɗaure kai over.

Ganin ya mike zaune ne yasa uncle T ɗin ya kariso wajen nasa da sauri, shi ma Mark karisowa wajen ya yi yana yi mashi sannu.

Zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan gadon ya yi ba tare da ya ce masu komai ba. A hanzarce Mark ya bashi takalmar dake kafansa, dan ya sanya, saboda ya san halin Ogan nasa da bala'in kyankyani.

"Momma let's go". Shi ne kawai abin da ya iya furtawa, sannan ya mike tsaye. Daga Mark har TGA kallon gwaggo da ya kira da momman suka yi, mamaki Mark yake yi, tambayar kansa yake yi wacece gwaggo kuma? Shi dai ya shiga duhu.

Wani irin jiri yake gani da ya mike, har wani layi yake yi. Ganin hakan yasa da sauri Mark da Tga suka yi ƙoƙarin tallafa mashi. Hannu ya ɗaga masu alamar baya bukata, sannan ya juyo da kallonsa a kan Aseef dake ta binshi da kallo. Alama da hannu ya yi mashi a kan ya zo ya tallafa mashi su fita, Allah sarki sam baya son Aseef ɗin ya fahimci komai, ya zai ji a rayuwarsa? Ya zai yi da ransa idan ya san gaskiya?.

Mikewa ya yi, duk jikinsa a mace, ya nufo Lion ɗin. Ɗan rungumo shi Lion ɗin ya yi yana shafa kansa gwanin ban tausayi, haka suka nufi waje. Da sauri gwaggon ta mike ta rufa masu baya, su Tga suka rufa mata baya. Shi dai Mark kansa ta shiga duhu....... NI KO NA CE MARK BA KAI KAƊAI BA, KOWA MA KANSA TA SHIGA DUHU, WAI KAI DAN MA BAKA SAN ABIN DA MUKA SANI BA, AI DA DUHUN DA ZAKA SHIGA MA BA ZAI FAƊU BA!!.

Suna fita sojojinsa suka rufa masu baya izuwa wajen motocinsu. Lion haka kawai yake jin babu daɗi zuciyarsa, tunanin Rimsha dake ta faman sheka barci a gida ne ya faɗo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa, nan take ya ji kirjinsa ta buga, tasbihi ya fara yi a cikin zuciyar nasa, dan ya samu salama, abubuwan sun yi mashi yawa, tunani yake yi bai kamata ya yi nisa da duk waɗan da suke da kusanci da shi ba, dan a wannan point da suke a yanzu, kamata ya yi ya haɗe familyn gwaggon gabaɗaya waje guda, domin kuwa, a yanzu koma suwaye suke bibiyar rayuwarsu, sun san ya san komai, ba shakka za'a cutar da su, kuma tabbas familyn gwaggon za'a cutar, dan familyn daddynsu kam suna da hannu dumu dumu a kan komai, so yana da kyau ya haɗa gabaɗaya ƴaƴa da jikokin Dr Salman waje guda, sannan a saka masu matakan tsaro, idan ba haka ba, za'ayi masu ɗauki ɗai'ɗai!!. Babbar magana.

Wayar Aseef ne ta fara kara dai'dai lokacin da suka shiga cikin motar. A hanzarce ya cirota daga aljihunsa, ya sha ruwan mamakin ganin uban miss call na Areef, dan lokacin da Areef ɗin ya yi ta kiransa, sam bai ji ba, baya a cikin hayyacinsa.

My uncle, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. A hanzarce ya ɗauki kiran, a lokacin kuma har motocin nasu sun fara tafiya, sun fito daga asibitin, yana zaune kusa da Lion, shi da gwaggo sun saka Lion ɗin a tsakiya a gidan baya na motar.

A hand-free ya sanya wayar, daga ɗayan ɓangaren daddyn Rimsha ya ce "Aseef kuna tare da Akila ne? Ta zo asibitin ne?". Jin tambayar daddyn Rimshar yasa Lion ya juyo da kallonsa a kan wayar.

"A'a uncle, ni tun da kuka tafi da ita jiya, ban sake ganinta ba, na kira numberta da safe ma a kashe". "E ba shakka wayarta a kashe, muma mun kira bata shiga, amma ina zuwa".

A hanzarce Aseef ɗin ya ce "Uncle lafiya dai ko? Meyasameta? Bata gidan ne? Ina ta ce dama zata je?". Ya yi maganar a rikice.

"A'a babu abin da ya sameta Aseef, ka kwantar da hankali, ina zuwa zan sake kiranka". Bai jira masar da zai bashi ba, kawai ya katse kiran.

TOH FAH INA AKILA KUMA TA SHIGA⁉️

Karɓar wayar Lion ɗin ya yi, cikin sauri ya fara kiran number Rimsha, dan dama ya kawo wa ransa za'ayi wa matan familynsu gwaggo ɗauki ɗai'ɗai, kuma idan basu yi saurin ɗaukar mataki ba, duk za'a kashe matan ne, dan da alama babu wasa a lamarin masu aikata hakan, bare ma da suka san yanzu asirinsu na gab da tonuwa, ai sai dai wanda Allah ya ƙaddara kwanansa na gaba, amma za'a zubar da jini kam ba kaɗan ba!, Kuma dole hankalinsa zai tashi, saboda a halin yanzu Rimsha ta fi kusa da shi sama da kowa, kuma ga shi shi ne yake shirin bankaɗo gaskiya, shi ne babban makiyin mutanan, ko dan a sanya shi ya rusina, za'a iya yi mata wani mummunar abin, so dole ta kasance a tare da shi a ko da yaushe, rayuwarta yana cikin hadari sosai, da alama ya yi shigar sauri wa mutane, bai shirya ba ya shiga yakin, hakan kuma zai wahalar da shi da na kusa da shi ba kaɗan ba!!.

Sai kiran wayar yake yi, amma ina bata ɗauka ba, number Areef ya kira, su kuma a lokacin sun kamo hanyar Kaduna, babu network sam, number bata shiga, tsaki ya ja tare da dakawa Mark tsawa a kan ya taka motar nan da sauri su kai gida da wuri, dan ya duba ya tabbatar Rimsha tana gida or not. Babbar magana.

Mikawa gwaggon wayar Aseef ɗin ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Momma ki gayawa dukka uncles namu yanzu ba sai anjuma ba mu haɗu a gida, dukkansu da ƴaƴansu gabaɗaya".

"Saif meyake faruwa ne? Ɗazun Abban Imran ya kirani ya ce Ayla matar uncle naku Maik ta ɓata, daga baya ya sake gaya mani mijin Aafia ya rasu, ita kuma Aafiar bama su san a wani point zasu ajiye ta ba, yanzu kuma na ji Nawazuddeen yana tambayar Aseef ina Akila, me dukka wannan ne?".

Nisawa ya yi kafin ya ce "Momma babu komai, just tell them what i said kawai, and ki yi sauri ki bani wayar ina son in gayawa Areef a duk in da yake, ya yi sauri ya zo gida ina son yin magana da shi......." Bai kai ga rufe baki ba Mark ya ja wata mahaukaciyar burki, waddata sanya su suka tafi luuuu suka buga kansu da jikin sofar motar, shi ma Mark ɗin sai da ya buga kansa da jikin steering motar.

Kusan a tare suka ɗago kawunansu tare da kai kallonsu a gaban motar, dan suga menene ya sanya Mark ɗin taka irin wannan burki haka...................

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E9


Kusan a tare suka ɗago kawunansu tare da kai kallonsu a gaban motar, dan suga menene ya sanya Mark ɗin taka irin wannan uban burki haka.

Ko da suka ɗago kansu, babu komai a wajen, kan hanyar wayam, da mamaki Aseef yake kallon Mark ɗin, bawan Allah shi kuma wata halitta ya gani tsaye a tsakiyar hanyar, shiyasa ya yi kokarin kauce mata, ashe gizo kawai aka yi mashi, da alama an shirya masu hakan ne domin su yi accident, sai kuma Allah ya karesu da kariyarsa.

Aseef ɗin zai yi magana, Lion ya dakatar da shi, sannan ya ce da Mark ɗin su tafi kawai.

Kunna motar ya yi suka cigaba da tafiya, ita kuma gwaggon ta kira su Abba kamar yanda Lion ya ce mata, daga haka babu wanda ya sake yin magana a cikin motar.

Har sun kusa isa gida, kome Lion ya tuna, sai ya karɓi wayar Aseef ɗin ya turawa Areef massage a kan ya tsananta addu'a sosai a duk in da yake, kada ya bari askar ta kubce daga bakinsa, dan fa akwai gagarumin matsala ba kaɗan ba.

Motarsu na yin parking a cikin gida, motar su daddyn Rimsha ma ya shigo cikin gidan, gabaɗaya familyn sun haɗu waje guda, ita ma Akilar sun ganta, ashe makwabtansu ta shiga, ta je su gaisa ne, dan kunga tun da ta yi aure, ai bata je ba, shi ne yanzu da dama ya samu, sai ta leƙasu. Ita kuma Ayla shiru, babu ita babu labarinta.

Mark yana kashe motar Lion ya fita daga cikin motar, bai bi ta kan kowa ba ya wuce cikin gida da sauri. Kai tsaye bedroom nasa ya nufa, ya sha ruwan mamakin ganin Rimsha tana zuba barci har iyanzu, kai kallonsa a kan agogon bangon dake manne a cikin ɗakin ya yi. Almost 4 to 5 hours tana zuba barci, anya barcin nan na lafiya ne kuwa? Ya tambayi kansa.

Karisawa cikin ɗakin ya yi, cikin nutsuwa ya haye saman bed ɗin, hannu ɗaya ya sanya ya tallabo kanta, sannan ya sanya ɗayar hannunsa ya shafa kyakkyawar face nata.

Cool murmushi ta saki har sai da dimples nata suka yi wani irin lotsawa mai matuƙar ɗaukar hankali. Cikin magagin barci ta fara faɗin "Kai Noorish ka bari mana". Kamar tasan shi yake taɓata.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai ɗan bakinsa ya sumbaci lallausan lips nata, sannan ya kankameta gam a kirjinsa, yana mai jin wani irin tsananin kaunarta tana ratsa shi. Ya ɗan ɗauki lokaci a hakan kafin ya mayar da ita a hankali ya kwantar, sannan ya diro kasa ya nufi toilet, ita kuma, cigaba da barcinta ta yi cikin kwanciyar hankali.

Hakika tabbas an so ɗaukar Rimshar kamar yanda Lion ɗin ya yi tunani, Malika ta ɓoyeta, ko da aka zo ɗaukarta ba'a ganta ba, Malika ta lulluɓeta da nasu siddabarun na aljanu, a gaskiya Malika tana kaunar Rimsha sosai, sannan kuma tana kula da ita sosai, sau da dama tana tare mata abubuwa da dama wanda idan ba ta gaya maku ba, ba zaku taɓa zaton ita ce ta tare ba, so ake ta karfi da ya ji a ladabtar da Lion, so suke su rufe mashi baki a kan case ɗin, so dole suna son yin amfani da rauninsa, dan su sanya ya rusina, sai dai kuma kash, dukka raunin nasa baza su taɓu ba, barema Rimsha da take tare da Malika, ba zata taɓa taɓuwa ba, sai dai idan shammatar Malikar aka yi, tun da dukka abune na tsafi da aljanun, so babu abin da ba zai iya faruwa ba.

Wanka Lion ɗin ya yi, sannan ya fito ya shirya cikin kanana kaya, wando three cuter fara kal, da T-shirt sky blue bara nauyi, bai ɗaure gashin kansa ba, ya saketa.

Wayarsa ya zo ya ɗauka a saman bed, number Areef ya sake gwada kira, still dai bata shiga, zama ya yi a bakin bed ɗin, number Mark ya kira a kan ya zo ya gyara mashi bedroom nasa, ya kwashe laptop da ya fasar nan.

Yana katse kiran ya ji saukar hannayenta a saman kugunsa ta wajen flat tummynsa, ta rungume shi ta baya, a hankali ta kwanto da kanta a saman bayansa, da murya irin na mai barci ta fara magana. "Noorish shi ne baka tashe ni daga barci ba ko?".

Nisawa ya yi, har cikin ransa ya ji sassauci na abin da yake ji, ya ji sanyi sosai, hannun nata ya riko ba tare da ya yi magana ba.

"Noorish na yi mafarkin wani waje, in gaya maka ina ne?". Tana magana kamar wadda barci bai isheta ba.

Juyowa ya yi a hankali, sannan ya jawowata ta dawo saman kirjinsa, zubawa face nata idanu sosai ya yi. Idanunta a rufe ruf take zuba surutu, sai guntun murmushi dake a saman face nata, ga dimples nata duk sun lotsa sosai, sai ta kara kyau matuƙa.

"Meesha tun da na bar gidan nan baki tashi daga barci ba?". Ya faɗa cike da tantamar irin barcin da ta rinƙa zubawa kamar ba gobe, abin da bai sani ba shi ne, Malika ce ta sakata yin wannan barci, dan da ta farka, to babu abin da zai hana Josephine bata ɗauketa ba! Saboda yanzu farautar rayuwarta suke yi tamkar ruwa mai sanyi a sahara mai tsananin zafin rana, a gefe guda, ga Queen of Daular Mutuwa tana nemanta ruwa a jallo, daga ɗayan gefen kuma, su Josephine suna nemanta ko ta halin kaka ne su ɗauketa, dan hawai su karyar da zuciyar Lion ɗin, hakan tasa Malikar ta sakata wannan uban barci kamar ba goben, har sai da ya dawo, sannan ta tafi ta basu waje, shi ne ma Rimshar ta iya farkawa.

"Noorish ban tashi ba, nifa yanzu na tashi, dama ka fita ne? Shi ne baka tashe ni na raka ba? Na ɓata da kai to". Ta kai karshen maganar tana haɗe mashi fuska, irin ta yi fushin nan.

"Open your eyes first, sai ki kalli cikin idanuna ki ce mun ɓata". Make mashi kafaɗa ta yi.

Hannu ya kai ya shafi lallausar wuyarta dake kara ɗaukar hankalinsa a koda yaushe. "Open your eyes". Ya faɗa yana gangaro da hannun nasa izuwa kirjinta.

A hankali ta waro idanun bata tare kumbura kumatu. Zubawa juna idanu suka yi, yau ɗaya ta iya dakewa ta kalli cikin kwayar idanunsa, anya ita ce ta iya wannan juriya na kallon cikin idanunsa kuwa? Anya babu sa hannun Malika a ciki kuwa? Shi ma ya ɗan yi mamakin yanda ta zuba mashi idanu tana kallon shi, babu ko kyaftawa.

"Noorish meyasameka?". Ta yi maganar tana kai hannunta a saman kumatunsa. Riko hannun nata ya yi tare da manna shi da jikin kumatunsa ba tare da ya saki ba, ya haɗe hannayen nasu waje guda a wajen, shiru bai yi mata magana ba, ita kuma sai kallon mamaki take yi mashi, taga ya yi wani irin rama ne, ita dai tasan kafin ta yi barci, ba haka ta barshi ba, ga idanunsa sun kara girma, alamar ya rame kenan.

Baki ɗauke da sallama Aseef ya shigo cikin ɗakin. Juyawa ta yi tana kallonsa, sai kuma ta yunkura zata bar jikin Lion ɗin, sai dai bai sake ta ba, yana rike da ita, yana ta kallon face nata, shi kaɗai yasan me yake ji a duk lokacin da yake kallonta.

Sam Aseef bai bi ta kansu ba, saman bed ya haye abinsa, ya kwanta tare da ciro wayarsa ya fara aikin latsawa, sai dai fa ya sha ruwan mamakin na ganinsu a manne da juna, kawai baya son ya yi magana ne, dan kada ya katse masu jin daɗinsu.

Mark ne ya sake shigowa cikin ɗakin, kallo ɗaya ya yi masu ya kawar da kansa gefe, sannan ya wuce dan ya yi aikin da ya kawosa.

"Meesha zaki raka ni ƙasar China?". Ya faɗa a sanyaye, tamkar bai san da Mark da kuma Aseef a cikin ɗakin ba.

Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "E zan raka ka".

Shiru ya yi yana tunanin a ina zai sami Cherish? Dan ba shakka duk yadda aka yi, tana da sa hannu a duk abubuwan da suke faru, saboda very close friend ɗin gwaggo ce, ya za'ayi daga haihuwar gwaggon shikenan ace Cherish ta ɓace? Ko dai dama ita ma ba mutun ba ce? Wannan abin da akwai ruɗani, dole ya nemo jigon haɗa wannan rikicin dukka.

Sallamar Areef ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, tun da Areef ɗin ya shigo, ya tsare shi da idanu har ya kariso cikin ɗakin, a saman bedside drawer ya zauna yana faɗin "Kai Aseef momma tana nemanka kana nan ko?".

Turo baki ya yi yana faɗin "Ni ba zan je ba, kuma fushi nake yi da su, saboda sun ce wai ba zan yi punishing na Heartbeat ba, a kan me zata fita bata tambaye ni ba? Ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login