Showing 147001 words to 150000 words out of 270744 words

Chapter 50 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2989

matashi mai jini a jika idan yana son ɗaukarta. Dan haka sai ya fara ƙoƙarin canzawa izuwa matashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya canza izuwa santalelen matashi, da yake dare ne, jama'a sam babu kowa a saman titin, dama kuma kunsan irin waɗan nan manyan unguwanni ba kasafai ka cika ganin mutane a waje ba, sai dai jefi jefi kaga giftawarsu, hakan tasa babu wanda ya nufi in da suke.

Yana ƙoƙarin ɗaukarta wasu matasa su biyu daga bayansa suka yi mashi sallama tare da tambayarsa ko lafiya? Accident aka yi ne?.

"Mota ce ta buge mani yarinya ta, kuma mai motar ya gudu, shi ne zan ɗauketa zuwa gida, daga nan sai mu wuce asibiti".

A hanzarce matasan suka ce "Innallilahi wa inna ilahirrajiun, wannan ai gaggawar kaita asibiti zamu yi, idan ba haka ba tana iya rasa ranta, bakaga yadda take zubar da jini bane? Ameer mu taimaka mashi".

Jin haka yasa Abbon ya juya idanun tsafin nasa tare da juyowa ya kallesu, nan take suka juya suka kama kansu, da alama shi ne nan ya kawar wa da mutanen arean gabaɗaya hankalinsu daga kansu, haka su Ameer dai suka juya salamun salamun suka bar wajen, tun da suka juya kuma basu sake waigo shi ba, da haka suka tafi.

Santalelen matashi mai jini a jika ya rikiɗa ya koma, hannu ya kai a karo na uku zai ɗauketa, kamar daga sama ya ji daga bayansa an ce "Am doubting about what you said, this girl isn't your daughter, am a soldier, you look like a criminal in my eyes, so i have to be come back and check you very well, that's why am here!". Cikin nustuwa ya yi maganar, kamar Lion idan yana magana.

A razane ya juyo, dan ya ga wanene, kun san ɗazun dama bai ɗago ya kalli Tga ɗin ba.

Yana juyowa kuma ya jefa kwakwalwar Tga ɗin a cikin tunani, saboda a iya saninsa dai ɗazun babban mutun ya gani ba matashi ba, ya aka yi yanzu kuma ya dawo yaga mata shi? Shi ne abin da ya ɗan juyar mashi da tunani kenan.

Shi kuwa Abbon, ganin Tga ɗin ba karamar razana shi ya yi ba, saboda abin da kuka sani ne, Tga tsayayyen namiji ne mai jini a jika, lafiyayye kuma horarre, ga kirar karfi, idan ka ganshi kamar TRIPLETS yake, basu da banbanci sai ɗan abin da ba'a rasa ba, so dole duk wani mutun idan ya gansu sai ya ji gabansa ya faɗi, musamman ma wannan Lion face ɗin nasu, da yake cike da kwarjini na wuce misali, ga kuma hasken fitillu a kan hanyar ko'ina, so suna iya ganin juna sosai.

Ƙoƙarin juyarwa da Tga ɗin hankali Abbon ya yi, amma ina ya kasa, tsafinsa taki yin aiki a kansa, abin ya razana shi, ya kuma yi mugu mugun ɗaure mashi kai, meyasa tsafinsa ta ƙi kama Tga? Ya tambayi kansa. (Ni kuma nace saboda Josephine tana kula da su😒🤧 ba zata taɓa bari a cutar da su ba, sai dai idan an shanmaceta)

Shi kuma Tga ganin cewa wanda ya gani ɗazun da wanda ya gani yanzu ba mutun ɗaya bane yasa ya nufe shi gadan gadan, yana taku cikin nuna jarumta tare da nuna cewa shi ɗin tsantsar lafiyayye ne.

Yana zuwa bai yi wata wata ba ya damko wuyar Abbon tare da shakesa da karfin, calmly ya ce "Who are you? What do you want to do for her? Where's that man that i saw in the first place?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga Abbon da hannu ɗaya kuma da wuyarsa da ya damke, ya raba shi da kasa sannan ya yi wurgi da shi gefe guda. Dama kunsan halin uncle T da iya mugunta, baka yi mashi laifi bama ya iya zalunci bare kuma yana zarginka, ai sai abin da hali ya yi kawai, sai ya baka a jikinka kafin ya baka damar ka yi mashi bayani.

Gadan gadan ya sake nufarsa, sai dai abin al'ajabi kafin ya kai in da yake yashe a kasar ya yi amfani da tsafinsa ya ɓace ɓat ya bar wajen. Dakatawa da nufar wajen Tga ɗin ya yi, da mamaki yake kallon wajen, da gaske ya ɓace, babu shi babu labarinsa, abin mamaki. Abin ya ɗan ɗaure mashi kai, sai dai ko kaɗan bai bashi tsoro ba, babu tsoro ko ɗigo a jinin familyn Roshan, haka suke tun ainahi, daga manyansu har kananansu basu da tsoro, bare kuma shi Tga da yake horon Lion, ai dama tsoro ma bataga wajen zama a wajensu ba.

Juyawa ya yi ya nufi wajen da take kwance cikin jini, da farko kamar ba zai ɗauketa ba, amma da ya tuna yanda Abbon ya ɓace, sai ya sawa ransa cewa cutar da ita zasu yi, dan haka bari ya taimaka mata.

A gabanta ya zo ya tsugunna, dan ya duba ta ina zai fara ɗaukar tata. Zubawa face nata idanu ya yi, sosai ya ga kamanninta da su Imran, kun san an ce jini ba wasa ba, a zahirin gaskiya bata wani kama da su Imran, amma da yake jini ya wuce wasa, akwai kaman jini a jikkunansu, kuma kowa da yanayin yanda yake kallon mutun, sai kaga mutun ya yi maka kama da wani, idan ka tambayi jama'a kuma sai su ce maka a'a babu kamar da kai kake gani, so kowa da yanayin yanda yake ganin mutun, shi dai Uncle T ta yi mashi mugu mugun kama da su Imran, sai dai kuma fa ba iya kamar kawai ya tsaya gani a face ɗin nata ba, tsintar kansa ya yi da jin sha'awar kallon face ɗin nata duk da baya son bakaken fata kuma bashi da wata ra'ayi a kan mace, amma ba shakka face ɗin Aafia ta tafi da tunaninsa a kallon farko.

Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin nan ya tsinci kansa da kai hannu ya taɓa kumatunta. Wani irin sanyi kamar daskararren ƙanƙara da ya ji a tattare da face ɗin nata ne yasa ya ɗauke hannunsa da wuri tare da miƙewa ya saɓeta da hannu ɗaya a saman kafaɗarsa, alama ta nuna babu jini a jikinta, baiwar Allah dama ba isshasshen lafiya yake gareta ba.

Anya basu Abbon bane suka zuƙe mata jinin⁉️

Gidan baya na motar ya buɗe tare da shumfuɗeta a saman lallausan kujerar motar, sannan ya koma mazaunin driver da sauri, saboda tana zubar da jini kuma alama ta nuna babu jini a jikinta sosai.

Da gudun gaske ya figi motar ya bar wajen, dama fitowa ya yi zai je shopping, saboda akwai abubun amfaninsa da suka kare, dama shi already kun sani kamar Areef yake, akwai shi da yawace yawace idan ya zo waje, kun tuna farkon zuwansa Naija wani lokaci ma baya kwana a gida? Kun tuna lokacin? Yawonsa yake tafiya dan ya ga gari, hakan tasa ya san wajaje da dama a cikin garin Kaduna.

Kai tsaye gida ya koma da ita. A haukace yake taka motar, dan su isa da wuri. Wani irin horn mai sauti ya fara dakarawa gateman tun bai kariso bakin gate ɗin ba. A hanzarce suka wangale mashi gate ɗin.

A guje ya danna hancin motar ciki, yana kashe motar a parking space ya fito tare da buɗe gidan bayan, babu ɓata lokaci ya saɓeta a kafadarsa zuwa cikin gidan.

Kai tsaye bed nasa ya wuce da ita, sai zubar da jini kanta yake yi, a iya kai ne kawai ta samu buguwa, kuma fashewar ba dayawa bane, amma da yake shi jini kofa kaɗan idan aka yi mashi ya samu hanya, to zuba kawai zai yi ta yi, buguwar da kan nata ya yi ne kuma yasa ta sumewa.

Katafaren bed nasa na'a shunfuɗe da white bed sheet, a haka ya kwantar da ita a kai da jinin nata, bai wani damu ba. (Abin mamaki, Uncle T da ya tsani bakar fata yau shi ne da taimakon bakar fata? Kuma har ya ɗaga hankalinsa haka?🤔 Abin da mamaki)

Fitowa ya yi tare da haurawa saman benen. A bakin kofar bedroom na Lion ya tsaya tare da yi mashi excuse, dan Lion ɗin ya shata masu layi da shiga ɗakinsa a yanzu, ya ce kada su rinƙa shiga mashi kai tsaye, dan matarsa tana kwance a ciki, baya da bukatar kowa ya kallah mashi ita a kwance, idan ta fito da kafafunta, wannan suna iya kallon face nata, amma tana a kwance a cikin bedroom nasa kam bai lamunta wani ya ganta ba, hakan yasa suke yi mashi excuse su kuma tsaya sai ya fito.

Ya ɗauki tsawon a kallah minti 10 a tsaye a wajen lafin Lion ɗin ya fito, jikinsa na sanye da kayan barcin masu matukar kyau, launin milk color, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikin nasa.

Ko da ya fito ma bai yi magana ba, sannan kuma tun da ya ɗaura idanuwansa a kan uncle T ɗin nasu, kallo ɗaya ya yi mashi yasan ba lafiya ba, ga jini a hannunsa da jikinsa, sai dai bai tambaye shi meyake faruwa ba, ya tsaya shiru dai ya zuba mashi idanu.

"Lion I need A box and the rest". Ya faɗa cikin nutsuwa. Shiru Lion ɗin ya yi mashi na tsawon mintoci kafin calmly ya ce "What is going on?".

Ba tare da ɓata lokaci ba ya bashi labarin abin da ya faru sama sama, daga karshe ya gaya mashi cewa yarinyar da ya buge ɗin tana dakinsa a sume, shi ne yake son dubata.

Jinjina mashi kai Lion ɗin ya yi, saboda yasan uncle T ɗin ma ba baya ba wajen sani da kuma karantar aikin likita daga wajen daddynsu na karya, ko ace photocopy, an cucesu aka sanya mashi komai na ainahin Dr William, harta ilimi da komai, da yake abu ne na tsafi, sai dai ko ba komai sun karu da shi, ga shi yanzu suna iya treating na kawunansu idan basu da lafiya, sam basu zuwa hospital sai idan abu ya zama mai matuƙar zafin gaske, amma ciwo irin na yau da kullum tsab suke duba kawunansu.

Ciki ɗakin Lion ɗin ya koma, jim kaɗan ya fito mashi da duk abubuwan da yake buƙata ɗin, dan su a wajensu dan Tga ya kawo mace wanda ya buge da mota, dan zai dubata ba su ɗauki hakan a bakin komai ba.

A hanzarce ya karɓa tare da juyawa ya nufi bedroom ɗin nasa. Shi kuma Lion ya koma ciki, har yanzu dai Rimsha shiru shiru bata farfaɗo ba, kusa da ita ya kwanta yana ta kallon face nata, ta kara wani irin azababben kyau, saboda karin ruwa da ake ta yi mata, tana kwance a sume, babu ci babu sha, drip kawai ake ta loda mata, dan ya taimakawa jikinta kada ta nakasa, hakance tasa ta kara kyau, kun san dama fa shi drip yana sanya mutun ya yi ƙiba ya kuma kara haske da kyau, duk wanda aka yi wa karin ruwa a hospital, zaku gan shi ya kara ƙiba, sai dai idan dama ba mai jikin ƙibar bane ba, amma koma yaya zai ɗan murmure.

Sosai ya zuba mata idanu babu ko kyaftawa, idan ya kalleta sosai, sai ya kai kyawawan lips nasa saman nata ya sumbata, sannan ya cigaba da kallonta kamar wani ya ce zai kwace mashi ita, ko ance za'a rabasu.

Shi kuwa uncle T, yana shiga bedroom ɗin nasa ya fara dubata cikin hanzari. Da yake bata ji wani ciwo sosai ba, a iya kai ne kawai, cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala komai tare da yi mata alkuran barci, sannan ya nufi toilet dan ya yi wanka, sai tunanin face nata yake yi, ta tsaya mashi a ransa, sai dai bai ɗauki hakan a matsayin wani abin ba, ya mayar kawai taimako ne.

Bayan ya yi wanka ya fito, shiryawa ya yi cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, kusan irin na jikin Lion. Saman bed ɗin nasa ya haye abinsa, tana gefe guda, shi ma ya kwanta a gefe guda tare da ɗan rage gudun A.c, dan kada sanyi ya daketa. A hankali ya lumshe idanuwansa, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.

A ɓangaren su Abbi kuwa, time da suka dawo gida, ba ƙaramar tashin hankali suka shi ga ba ganin Aafia bata a gidan, kasancewar dare ne, sai basu kira su Abba sun tayar masu da hankali ba, suka fara nemanta a cikin unguwar, ita kuwa Hjy Hadiza tana can wani kauye wajen wani malami, a can zata kwana, Aunty baiwar Allah ta shiga damuwa na wuce misali.

Sun sha yawo kamar ba gobe, amma babu Aafia babu dalilinta, haka suka dawo gida har wuraren 12 na dare, ga gajiyar hanyar Katsina, ga wahalar yawo a cikin unguwa, mai gadi dai ya shaida masu Aafia da kafarta ta fita gidan da gudu, ga shi babu waya a hannunta bare su kirata, haka suka kwanta jugum jugum, a wannan dare dai barci ya gagaresu, dan suna cikin tsaka mai wuya, Allah Allah suke yi kawai gari ya waye su shiga nemanta babu kakkautawa, baiwar Allah ga shi ba lafiya yake gareta ba. Ita kuma Hanan sun barta a Katsina, dan next week za'a ɗaura auren nasu, A'A ya ce baya son ɓata lokaci, ayi komai da wuri a wuce wajen, to shi ne yasa suka barota a can zata yi kwana biyu, dan ta bi ƴan uwa su yi ban kwana, daga nan sai ta dawo gidan Abbin, dan a nan za'ayi komai na bikin, Abbin ya ce ba zasu sake zuwa wajen babanta ba, gara ayi komai a gidansa cikin mutunci tun da baban ya amince.

Washegari tafiya ce ta kama Lion cikin gaggawa, bashi da zaɓin da ya wuce ya koma U.s, sam baya jin kamar zai iya tafiya ya bar Rimsha ba tare da ta farfaɗo a gabansa ba, amma dole ce tasa sai ya tafi ɗin, saboda primary election da sauran abubuwa, ba zai yi wu ya tafi da ita ba, dole zai barta a nan.

Gwaggo ce ta yi ta kara mashi kwarin gwiwa a kan ya je kawai zata kula da Rimshar sosai, kada ya damu. Shiru ya yi bai amsa mata ba, dan shi gani yake yi ma ita fa gwaggo sam bata san me yake ji ba, ba zata gane halin da yake a ciki bane, da zata shiga cikin zuciyarsa ta ga irin azababben son da yake yi wa Rimsha, da sam ba zata taɓa yin gigin ce mashi ya yi hakuri ya tafi ya barta ba.

Karfe 7 na safe ya kamata jirginsa ya ɗaga, amma sai ya ɗaga tafiyar zuwa da yamma, duk saboda Rimsha, duk da baya jin cewa zata iya farfaɗowa a cikin wannan satin ma gabaɗaya ba yau ba, amma ya jinkirta tafiyar tasa zuwa yamma, dan ya kara kula da ita sosai kafin ya tafi.

A ɓangaren Jehan kuwa, duk ta yi laushi, ta rame sosai, amma har yanzu taki yarda ta kira Areef ɗin a waya ma bare ta bashi hakurin.

Sam Areef baya son wannan rama da take yi, abin yana kona mashi rai, sai dai bashi da zaɓin da ya wuce ya bi maganar mum, a koda yaushe yake son ganinta, zai ganta, amma ita ba zata gan shi ba, saboda bata san cewa yana da hanyar ganinta ɗin ba, sai dai fa shi ganinta bai wadatar da shi ba, ba iya ganinta da ido yake da buƙata ba, yana bukatar jin voice nata, duk da kullum dama cikin dirama suke, ba wasu kamai da take gaya mashi, amma yana son diramar, yana son jin muryarta tana yi mashi diramar, ba wai ya ji muryarta tana magana da su gwaggo ba, in takaice maku shi fa komai Jehan ta yi burgesa take yi, pure love na kin karawa yake yi mata, tsayawa zayyana irin son da yake yi mata ma ɓata baki ne, dan bakin ya yi kaɗan wajen iya zayyana shi.

A takaice sai misalin karfe 5 jirgin Lion ya ɗaga zuwa U.s, zuciyarsa sam babu daɗi na rabuwa da Meesharsa, babban abin da ya fi ɓata mashi rai ma shi ne, yanda tafiyar ya kama shi ba tare da Meeshar tasa ta farfaɗo a gaban idanunsa ba, shi ne ya ɓata mashi rai a game da tafiyar kawai.

A ɓangaren Tga kuwa, washegari da safe da ya tashi, wanka ya fara yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kayansa, ya fito ya nufi motarsa ta jiya, bai bi ta kan Aafia ba, duk da tana kwance a saman bed nasa, kuma ya ganta sarai, sai dai wani abin ya sha gabansa, akwai in da zai je.

Da ya je shiga motar ne ya ga kujerar duk jini, hakan tasa ya ɗauki motar Aseef ya fice daga gidan, ya barta sume a saman bed nasa, ga shi babu wanda yasan tana ɗakin bare a sanar da su Abbi dake ta faman yawon nemanta a gari, duk sun karaɗe gari da nemanta, police station ne, gidajen Radios duk sun baza bayananta ana cikiya, shi kuma ya kai ta ɗaki ya kwantar ya kama kansa abinsa, dama kun san daren jiya ya fita zai ke shopping ne, dan gaskiya yana da bukatar abubuwa dayawa, har da mayukan goge baki, shi ne yasa ya fita da wuri dan ya je ya yi shopping nasa, saboda abubuwa ne na amfaninsa mafi muhimmanci zai saya.

Su gwaggo sam basu san da Aafiar a gidan ba, ga shi su ba shiga ɗakinsa suke yi ba, bare ace idan sun shiga za su ganta har su ganeta su kira su Abbi, to bama su san tana gidan ba. Shi kuma Lion da yasan cewa Tga ɗin ya buge wata yarinya da mota, ai kun san halinsa, baya shiga abin da bata shafe shi ba, dan haka babu ruwansa da zuwa ya duba waye Tga ya buge, hakan ma sam ba zai yiwu ba.

Duk hankulan family ya tashi ana neman Aafia, izuwa yanzu su gwaggo duk sun sami labarin halin da ake ciki, sai kiraye kirayen waya suke yi wa ƴan uwa, dan su ji ko dai an samu wani labari, amma shiru. Sai dai sunki gayawa Dr Salman da Brr Naurat halin da ake ciki, dan kada su shiga tashin hankali sosai, dama har yanzu basu gama warkewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login