Showing 21001 words to 24000 words out of 270744 words

Chapter 8 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2925

kasheta ita da abin da yake cikin nata. A ranar Josephine ce ta tseratar da ita daga hannunsa, a in da ta gudu da ita izuwa ɗaya daga cikin gidajen daddynsu, wato Jacob Roshan, suka bar Dr William uncle Herry sai TGA, ita dama Cherish bata san me yake faruwa ba.

A nan suka cigaba da rayuwa da gwaggon da ita Josephine ɗin, dan ta ce wlh ba zata koma wajen Dr ba ita ma, zata zauna ta kula da gwaggon, baiwar Allah tana da tausayi sosai ga kirki na wuce misali. A lokacin Cherish tana kasarsu ta je hutu. Ita kuwa gwaggo bata je hutu ba, kuma ba'a nemeta a gida ba, dan a lokacin gidan nasu ya rushe bata sani ba, tana nan ta biyewa Dr ya kaita ya barota, da ba dan Josephine ba, da bata san in da zata sanya rayuwarta ba, da kila izuwa yanzu ma ta mutu. Allah sarki rayuwa kenan.

Hakika Gwaggo ta sha bakar azabar wahala na rabuwarta da Dr, tamkar ba zata yi rai ba, dan tana tsananin kaunarsa fiye da tunanin mai tunani. Shi kuwa yana can ko a jikinsa, sai ma sharholiyarsa da yake sha, da alama ya mance da ita ma, da alama fa dama ba sonta tsakani da Allah yake yi ba! Kawai ya yaudareta ne!. (Wata kila shiyasa su Lion basu jinsa sam sam a ransu🤔 to lokaci dai zai nuna mana komai, amma ni da ku duk mun san cewa alhaki kwaikwayo ne! Ga mutuwar su Jacob ma dai..hmmmm akwai abubuwa da yawan gaske, wlh wasu cakwakiyar idan aka ɓallo maku sai kun ji kanku ta buga!!)

PRINCESS TEEMA..✍️❤️

Da kyar tare da addu'a da taimakon Josephine gwaggo ta dawo dai'dai, da farko da ta ji wahala na soyayyar Dr dake neman hallakata, sai ta ce wa Josephine ta yarda zata zubar da cikin kawai ta koma wajen mijinta, dan ba zata iya yin nisa da shi ba. Kasancewar Josephine tana bala'in son yaran yasa ta yi ta rarrashinta tare da yi mata dabara har ta yarda ta bar ciki.

After some weeks

A haka Cherish ta dawo hutu ta same su, abin kwata kwata bai yi mata daɗi ba, duk sai ta ji ta tsani Dr sosai, ta kuma tsani maza fiye da tunanin mai tunani.

Zaune ta isko Gwaggon a cikin bedroom saman bed, kusa da ita ta zauna tare da fara bata hakuri. A kule gwaggon ta ce. "Cherish kin san me kike faɗa kuwa? Hakuri fa kika ce nayi? Wlh ba zan hakura ba, sai na ɗauki fansan abin da Dr ya yi mini, wlh sai na kashe shi!".

Zaro kananan idanunta na ƴan China Cherish ɗin ta yi tare da dafe kirji, a ruɗe ta ce "A'isha kisa fa kika ce? Please ki dai'na batun kisa, kin san Allah ya hana hakan". "Cherish idan kika ga ban kashe William ba! To wlh ba Dr Salman ba ne ubana, William ya cuceni! Ya zalunce ni! Yanzu ki gaya mini me zan cewa ƴan uwana da iyayena? Wlh billahi ba zan zubar da wannan cikin ba, sai na haife shi! Kuma ba zan bar Washington DC ba har sai na kashe William! Wai da kike wannan magana ma Cherish kin san waye babana kuwa? Ba makawa kashe ni zai yi idan ya ji abin da ya faru da ni, dan haka kada ma ki sake kawo mini maganar na yi hakuri a nan wajen!!"................SU GWAGGO AN JI WUYA, AN TUNA DA DR SALMAN,😂 WAI SAI YANZU TAKE TUNANIN ME ZATA JE TA GAYWA DR SALMAN?🤔 SOYAYYA RUWAN ZUMA!

Shiru baiwar Allah Cherish ta yi bata sake yin magana ba har Josephine ta dawo ta samesu zaune a wajen, zama ta yi suka cigaba da jira. Ita dai Cherish haka ta wuni sukuku da ita har izuwa dare, sannan ta wuce gidanta.

A takaice dai haka suka cigaba da rayuwa, gwaggo tana zuwa school, sai dai bata bari su haɗu da Dr, har cikinta ya girma ya isa haihuwa, Dr bai sake nemanta ba, bai sake leƙota ba, da alama ya mance da ita, baiwar Allah, ita kuma tana ta faman dakon soyayyarsa, a kullum tana tunaninsa fiye da yanda take tunanin komai na rayuwarta.

A haka har Allah ya sauketa lafiya, tashin farko ta haifo ƴan ukunta tsala tsala da su, lafiyayyun yara masu jini a jika, kyawawan gaske, jinin Roshan. Ba abin da ya fi sakata cikin tashin hankali sama da yanda ɗanta na farkon ya yi mugun kama da Dr William, harta blue eyes nasu. Biyu daga cikin yaran nata sun kasance farare ne over, ma'ana sun fi ɗayan haske, haka zalika su biyun da suka fi hasken, sun kasance kwayar idanunsu iriɗaya ne, sak irin na Dr, shi kuma ɗayan haskensa kamar na Dr ne, sannan yana kama da Josephine sak babu maraba, kai kace ɗanta ne ma, saboda tsantsar kama.

Bayan ta dawo cikin hayyacinta ne ta zubawa ƴaƴan idanu, tana kallonsu, basu da maraba da familyn Dr, dukka babu wanda ya ɗaukota a cikinsu, duk su Josephine ne, jajir da su tamkar tsada, ga bala'in kyau tamkar su suka faɗi irin halittar da suke so ayi musu, abin ba'a cewa komai.

A lokacin ne kuma wani bakin shaiɗani ya shiga cikin tunanin gwaggon, nan ta fara tunanin to akan me zata rike yaran Dr? Ai kawai ta kai mashi kayansa, kada ta shayar da su, dan babansu ya cutar da ita, ya ci amanarta, ya ci amanar yarda da soyayya, tun da Allah yasa sun kammala karatu last month, kawai ta bashi yaransa, ita kuma ta koma Naija, idan har ta rike yaranma ai ya cuceta da yawa............. KUSKURE KU HUKUNTA WASU DA LAIFIN DA WASU SUKA YI MAKU,❌ DR SHI YA YI MAKI LAIFI BA TRIPLETS NAKI BA! KUSKURE KI CE BA ZAKI RUKE SU BA, DAN DR YA YI MAKI BA DAI'DAI BA!!

Wannan banzar tunanin ne yasa ta ɗaukesu tare da haɗa wasu kaya nata da kuma wani farar takarda da ta yi rubutu a kansa da yaren su na tatar, wato yaren Na'urat, ta haɗa da chains ɗin da Na'urat ta bata, dama chain ɗin guda shidda ne, ta bawa Josephine ɗaya, Cherish ɗaya, saura huɗu, sai ta zuba uku a cikin wani ɗan ƙaramin, bayan ta raba tambarin heart na ɗayar sarkar kenan. Sannan ta ɗebesu, sai hanata Josephine take yi tana bata hakuri, amma ina ta zuciya, shaiɗan ta buga mata ganga, kuma ta taka rawa, tukukin bakin ciki na abin da Dr ya yi mata ya dawo mata sabo, ji take yi tamkar ta kashe Dr kawai ma ta huta.

Haka ta ɗaukesu zuwa gidan Dr. Da sauri Josephine ta bi bayanta, dan kada su je su yi ɓatatciya da Dr, saboda ta san halinsa.

Ta kuwa yi sa'a yana gida zaune a palo, ya yi wani fresh da shi, ya yi ɓul ɓul abinsa.

Babu ko sallama ta shiga palon. A saman sofa ta ɗaura yara jariran da ko kwana uku a duniya basu yi ba, nono ma sau ɗaya ta gwada basu, da ta ji zafi ta ce ba zata iya ba, ta koma basu madara, daga karshe ta kwasosu zuwa wajensa.

Murje idanu Dr ya yi ya ce bai san da wannan zance ba, shi ba zai karɓi yaran ba, dan yaranta ne ba nasa ba, ta kwashesu ta fita ko kuma ya yi mata illa, ya sanyata ta yi dana sanin zuwanta duniya.

Kin kwashesu ta yi, ita ma sai ta hau dokin zuciya, a in da ta shiga gaya mashi bakaken maganganu over. Abin dai sam ya zamar musu babu daɗi. Daga karshe Dr ya ɗauko sandar buka horking nasu Uncle Herry, ya ce ko ta ɗauki yaran su fita, ko ya kasheta ita da yaran.

Ta dauka wasa yake yi, sai ta ce wlh ba zata ɗauke su ba, ya yi abin da zai yi!!.

Babu wani tunani, babu tsoron Allah ya ɗaga sandar zai buga mata. A guje ta miƙe daga samar sofar ta nufi waje, shi kuwa yana sauke sandar sai tsakiyar kan ɗaya daga cikin jariran nan nasa. Nan take yaro ya sandare musu, ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ya yi halinsa, amma ga jini yana malala daga kansa.

Ganin hanan yasa Dr ya yi wurgi da sandar ya yi kan yaran, dan ya tsorata sosai, yasan cewa idan wani abin ya samu yaron nan, to wlh gwamnati ba zata bar shi ba, duk da uncle nasa ne yake a kan mulki, tabbas sai an hukunta shi idan ya cutar da jariri, hukunci kuma mai tsaurin gaske.

Ita kuma gwaggon ta yi waje bata san me ya faru ba. Da gudu Josephine dake tsaye a bakin kofar palon tana ganin komai ta kariso cikin palon, dan ta duba jariran.

A matukar haukace Dr ya kwashesu zuwa asibiti dan a duba mashi yaron ya mutu ne ko yana raye, ba shi da kwanciyar hankali da zai iya dubasu!!.

Ita kuwa gwaggo, tun da ta bar palon bata sake waiwayo su ba, ta ce idan Dr ya ga dama ya kashe yaran ai nasa ne, dan haka sai ta wuce gida abinta.

Tana zuwa ta hau shirin komawa Nigeria, tun da sun kammala karatu. Sai dai fa, da kyar a daddafe ta yi kwana ɗaya na rashin yaran nan. Washegari ta wuni tamkar mara lafiya. A daddafe ta kai yamma. Zuwa dare ta ji ba zata iya rayuwa babu yaranta ba, dan haka sai ta shirya ta tafi gidan Dr.

Abin mamaki abin al'ajabi, ko da ta je sai Dr ya ce wlh ba zai bayar da yaran nan ba, yara dai yaransa ne! Kuma ta fita mashi a gida dama shi ba sonta yake yi ba, idan har bata fita ba, sai ya sanyata ta yi danasani mai girma.

Da farko ta ki fita, sai da ta ga zai yi mata kaca kaca ne ta kama kanta tana kuka tare da danasanin sanin Dr da ta yi a rayuwarta, tamkar ranta zai fita haka ta bar gidan.

A ranar Josephine ta zo har gidanta suka kwana a tare, dan ta ɗebe mata kewa. Kwana kuka Gwaggon ta yi tana danasani kai mashi ƴaƴanta da ta yi. Ita kuwa Josephine kwana rarrashinta ta yi. Abin gwanin ban tausayi, shaiɗan ya yi mummunar aika aika a tsakanin masoyan guda biyu.

A takaice a cikin satin Gwaggo ta shirya ta dawo Nigeria, dan ta zo ta gayawa Dr Salman abin da yake faruwa, saboda su je su karɓo mata yaranta, ba zata iya rayuwa babu su ba, zata mutu idan ba'a karɓo mata su ba.

Haka ta baro Washington ba tare da ta sake saka yaran nata a idanunta ba, bata san a wani hali suke ba, bata san ya suke a hannun Dr William ba, shin ya karɓesu a matsayin ƴaƴa ne ko yaya? Duk bata sani ba, bata sake sanin komai dan gane da su ba!!.

Tana dawowa gida Nigeria ta tarar da bakin labarin da ta gwammaci mutuwa a kansa. Wato ta tarar da labarin Dr Salman ya rasu da shi da Naurat da Amarya, a yanda aka ce accident suka yi dukkansu suka mutu. Abu kaɗan ya hana ƙwaƙwalwar gwaggo bai juye ba, ga rashin iyaye, ga rashin masoyi, ga kuma uwa uba rashin jariran ƴaƴanta, ga rashin ƴan uwa. Dole ta yi hauka data ga Dr William, dan ya cutar da rayuwarta, duk shi ne silar komai a rayuwarta. Da badan son shi ba, ai da ba zata mance da kowa ba har iyayenta su rasu bata sani ba!.

Tun tana kuka da hawaye, har hawayen nata suka dai'na fita. Cikin raɗaɗi da kunan rai ta nufi ɗaya daga cikin gidajen Dr Salman, in da aka ce mata nan Abba ya yi aure. Tana zuwa ta yi sa'a Abban yana gidan. Tana kuka tamkar zata mutu ta fara bashi labarin abubuwan da suka faru da ita, tun daga farko har karshe. Daga karshe ta rufe mashi da cewa, dan girman Allah ya taimaka ya karɓo mata ƴaƴanta a wajen Dr William, dan ba zata iya rayuwa babu su ba.

Nan fa taga bala'i a karo na uku, dan kuwa Abba a lokacin ma bai gama dawowa cikin hanyacinsa na abin da amarya ta yi mashi ba. Dan haka sai ya yi wa gwaggo tatas, ya koreta daga gidan, wai ta zubar masu da kimar gidansu, ta je wata ƙasa ta haifi yara, shi sam bai yarda da aure ta haifesu ba, dan haka ba zai karɓo ƴaƴan shegu ba, da ace ta zo da su ma, wlh karɓarsu zai yi ya mayarwa da ubansu su, dan babu ƴaƴan shegu a kaf zuri'ar Dr Salman. Haka dai ya yi ta surfa ruwan bala'i, ta in da yake shiga, ba ta nan yake fita ba. Daga karshe ya korata waje tare da rufo gate ɗin gidansa, ya ce ta je ya yafeta a matsayin kanwa!!.

A lokacin da yammane, wuraren karfe 6:30, bai yi wani tunani ba ya daketa ya koreta. Tana kuka tana rantse mashi da Allah wlh ba shegu bane ƴaƴanta, ƴaƴan sunna ne, dan Allah ya dai'na shaigantasu, amma ina haka ya sa kafa ya yi ball da ita. Ya ce bai san wannan ba.

Ganin zai yi mata illah ne yasa ta baro bakin gate ɗin gidan a guje kamar mahaukaciya, tana gudu tana kuka, Ammien su Imran ta yi ƙoƙarin dakatar da Abban, amma ina, sam abin ya ci tura, yaki sauraronta, ya hau dokin zuciya, dama idan baku manta ba, a baya na gaya maku, shi mutun ne mai bala'in zuciya da zafin rai!.

Bazama cikin gari gwaggo ta yi kamar mahaukaciya, da kamar zata je gidan Abbi, amma da ta tuna cewa, da Abbi da Abba halinsu iri ɗaya, sai ta gwammaci gara ta shiga duniya. Tamkar zautatciya haka ta zama. Tun tana iya gane hanyar da take tafiya a kai, har ta dai'na ganewa, ta fara ganin dishi dishi, da alama hankali ya gushe a tattare da ita. Daga karshe ma sai ta zube kasa a kasar wata bishiya ta bakin titi, kan ka ce me ta sume a wajen, saboda tukukin bakin ciki da yake cikin zuciyar baiwar Allah nan!!.

Nisawa ta yi tare da goge hawayen fuskarta, sannan ta ce "Tun daga wannan suma da na yi, ban sake sanin in da kai'na yake ba, sai da na shafi shekara kwance a gadon asibiti, lokacin da na farka kuma, da fuskar kanina Nawazuddeen na fara cin karo, shi ne yake gaya mani shakarata ɗaya a sume a gadon asibiti, tsabar bakin ciki ban ko tambaye shi daga ina ya tsintoni ba, kawai na bar maganar, shi ya cigaba da kula da ni, na bashi labarin komai na daga auren da na yi, har da yayana TRIPLETS, hakuri ya yi ta bani, ya kuma biya kuɗin jirgi muka je har Washington DC, sai dai bamu sami su Dr William ba, mun yi tambayar duniyar nan, basu ko ɗaya daga cikin gidajen iyayensu da suka bari, kowa sai ya ce bai san in da suke ba. Daga karshe dai muka hakura muka dawo, zuciyata cike da kaunar yarana, ina jin tamkar zan mutu. Kullum Nawazuddeen ajiye duk wani abin da zai yi yake yi, ya dawo gida ya zauna ya yi ta bani hakuri, yana kwantar mani da hankali, a lokacin ko aure bai yi ba, shi kaɗai yake rayuwarsa shi ma. Haka muka cigaba da rayuwa a tare, na zama tamkar mahaifiyarsa, yana yi mani biyayya over, ban taɓa yin magana ya saɓa ba, ya mayar dani islami, a nan na sami ilimin addini sosai da sosai, daga nan kuma nayi danasanin abubuwa da dama na rayuwar da muka yi da Dr, da na sami ilimin addini sosai, na fahimci wani abin, na fahimci da ni da Dr mun aikata saɓon Allah sosai a cikin soyayyarmu, kila shi ne yasa Allah ya jarrabeni da wannan kaddara, dama irin wannan saɓon da muka aikata ai ba zai taɓa yiwuwa aurenmu ta yi albaraka ba". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta.

Kowa da yake cikin palon sai da zuciyarsa ta raunata, ta kuma taɓu sosai, daddyn jelly kam kuka ya yi sosai, dan kun san shi dama, akwai shi da saurin kuka. Dayawa daga cikin jama'ar palon sun zub da hawaye.

Gyaran murya Brr Naurat ta yi, cikin dattaku da girma ta ce "Dr William ka ji bayanan A'isha ko? Me zaka ce kai kuma? Bayan A'isha ta baka yaran, ka gaya mana ya ka yi da su? Ina suke? Menene kuma ya faru bayan barin A'isha gidan? Ina yaron da ka illatar da sanda? Meyasame shi? Muna jiran bayananka kai ma!!". Nan fa gabaɗaya kallo ya koma kansa. Harta ƴaƴan nasa ma shi suke kallo.

Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci kafin ya ce "Ni duk abin da ta faɗa ban sani ba, ni ban santa ba! Kuma ban taɓa ganinta ba sai yau, wata kila da wani Dr William ɗin take yi ba ni ba!"........TASHIN SENSE

Brr Naurat tana ƙoƙarin sake yin magana Areef ya daka musu tsawa cikin tsananin ɓacin rai tare da tashin hankali. "Daddy kada ka mayar da mu mahaukata mana? How comes zata bada dukka wannan labari kuma ka ce karya ne? How comes ta san su kaka? How comes ta zayyano sunayen unguwar da gidajen kaka yake da sauransu?Kawai daddy ka gaya mana gaskiya!!". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye yana huci tamkar wani mayunwacin zaki. Tamkar ba Areef mai saukin kai da wasa da dariya ba.

Miƙewa shi ma daddyn ya yi yana faɗin "James a said a don't know her, what do you want me to tell you again?!". Ya yi maganar cikin tsawa shi ma.

Buɗe baki Areef ɗin ya yi da nufin ya yi magana. Bai kai ga yin maganar ba sai ganin Lion suka yi ya damki wuyar daddyn nasu da hannu ɗaya, ya maka shi da jikin bango tare da matse shi. Gabaɗaya ya canza lokacin guda, tamkar ba NooRin Meesha ba, idanuwansa sun yi jajir da su kamar wuta, har wasu jijiyoyi sirara ne suka fito mashi a damatsan hannunsa da kuma wuyarsa, sai wani irin numfashi yake yi mai kama da gurnanin zaki, jikinsa sai wani tsuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login