Showing 159001 words to 162000 words out of 270744 words

Chapter 54 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2947

maka, kuma dan kaga ina son kane yasa kake bani wahala ko? Dama ni nasan ni kaɗai nake sonka, kai baka so na". "Meesha why you said that? You know i really love you, amma kike cewa bana sonki?".

Mikewa zaune ta yi tare da ɗaukar wayar tana faɗin "Yah Saif baka sona, da kana sona ba zaka taɓa yarda ka tafi ba tare da munga juna ba, kasan kewarka da nake yi kuwa? Kasan......". Wani irin burki ta ja a maganar tata, kasa cigaba da yin magana ta yi, saboda wani irin tsawa da ya daka mata ta cikin wayar. "Do you know how many times i take together with you?! Meyasa kike son kureni ne Meesha? Kinsan da ya na iya danne zuciyata har nake iya sauraron maganarki na cewa bana sonki kuwa? Idan kika sake gaya mani irin haka sai na fasa maki baki, am i your mate?!".

Kuka mai sauti sosai ta kara rushe mashi da shi tana faɗin "Shikenan tom ka yi zamanka a in da kake, nima zan yi zama da iyayena, dama can da su nake zaune". Ta kai karshen maganar tare da yin wurgi da wayar a jikin bangon ɗakin, ji kake tarrr wayar ta tarwatse, ta zuciyane baiwar Allah, ta fusata, yau Lion ya kureta iya karshen kurewa, ba abin da ya fi bata haushi ma irin tsawar da ya daka mata, wannan shi ne a daki mutun a hana shi kuka, dama kun san idan mutun yana a irin wannan hali da take a ciki na ɓacin rai babu abin da ba zai iya faɗa ba, tana son shi kamar ta mutu ne yasa dukka hakan take faruwa.

Shi ma dai a nashi ɓangaren jin kalamanta na karshe yasa ya cire wayar daga kunnensa yana bin screenshot ɗin da kallo, nan take shaiɗan ya yi mashi raɗa da cewa yarinya under 15 years ce yau ta tsaya take yi mashi magana son ranta haka, kamar shi ɗin nan, shi da zaratan maza masu ji da jini a jika ma tsoron tinkararsa suke yi dan su yi magana da shi, amma yau under 15 years ce ta samu damar yi mashi irin wannan rashin kunya, lallai kuwa soyayya bata yi mashi adalci ba, kuma dole a yau soyayyarta ta fita mashi a cikin zuciya, dan bai ga wata ƴa mace da ta isa ta gaya mashi magana makamanciyar wanda Rimsha ta gaya mashi ba, wai ya yi zamansa a can, dama can ai ita da iyayenta suke zaune, kuma dama ba sonta yake yi ba, wannan abin ya kona mashi rai da har yasa shi ma ya yi wurgi da wayar tasa, ya kuma sanya a ransa daga yau ba ya cireta a ransa, dole ya rabu da ita tun da har abin ya zamana haka!!. Lallai akwai cakwakiya!.

Duk abin da suke yi Areef yana ganinsu, tausayin Lion ɗin ma kawai yake ji, dan yasan yariga da ya bawa Rimshar zuciyarsa, so ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma idan tana cikin damuwa shi ma Lion ɗin zuciyarsa ba zata taɓa samun sukuni ba, kawai wahalar da kansu zasu yi, dan ba zasu taɓa iya hakura da juna ba, zasu wahalar da kansu ne a banza, kuma zasu sha wahala in dai fushi da juna zasu yi.

(To mu dai bari mu gani, shin zasu iya yin fushi da junan ne ko dai zasu kasa🥲 namu ido😂)

Kwanciya ya yi tare da rumtse idanuwansa gam, tamkar zai fasasu, sai ka ce su ne suka yi mashi laifi, zuciyarsa wani irin zafi take yi mashi, tun ainahi kunsan su TRIPLETS basu son raini ko kaɗan, hakan yasa Lion ɗin yake ƙoƙarin kawar da Rimsha daga cikin zuciyarsa, saboda a cewarsa ta ra'ina shi. (Wani irin raini kuma ya rage tun da har ka iya kwanciya da ita, kana wasa da tula tulanta, ai daga nan ma kawai His Excellence Saif ka manta da batun ta rai'naka🥺😌 kun rigada kun zama ɗaya, kawai ka jawota ku rarrashi juna)

Kamar Areef zai yi mashi magana, sai kuma ya fasa, saboda ya lura ran Lion ɗin ya ɓaci sosai, idan ya kuskura ya yi mashi wata magana a yanzu, to suna iya dakuwa da juna, mafi a'ala kawai ya kyale shi sai ya yi barci ya farka, idan zuciyar ta sauka, sai ya gaya mashi ita fa Rimsha yarinya ce, kuma son shi da take yi ne yasa har ta damu da tana son ganinsa, idan bata son shi ba zata ko kula shi ba, a cikinsu dukka TRIPLETS ɗin waye ta kira ta ce sai dai ya dawo idan ba shi ɗin ba? Ai ko iya haka ya kamata ya san cewa ba wai dan rashin kunya ko raini yasa ta faɗa mashi magana haka ba, so ne ya jawo hakan, kuma su mata fa sai ya yi hakuri da su, dan annabi ya ce a karkace suke, ba zasu taɓa miƙewa ba, so dole ka bisu a yadda suke idan kana son zama da lafiyarka ba sai ka rinƙa ziyartar asibiti ba, bugu da kari kada ya manta da abin da ya yi mata kwanaki ashirin da tara da suka wuce, dan ma Allah ya taimake shi bata san me ya faru ba, ai ta cancanci ya ɗaga jirgi ne ma musamman ya je ya dubata ya dawo, ba wai ya kara ɓata mata rai ba, amma dukkansu zuciya da kuma shaiɗan sun ɗebesu, sun zuciya a banza, wanda hakan kuma sam ba shi ne solution a garesu ba, dan ba hanya mai ɓullewa suka bi ba, hanyar da zata jefasu cikin ukuba suka sake afkawa, zasu yi bayani ne dukkansu biyu! Dan dukkansu suna matuƙar kaunar juna na wuce misali!.

Miƙewa Areef ɗin ya yi ya diro kasa daga saman gadon, bedroom nasa ya nufa yana mai addu'ar Allah ya shirya mashi Lion ɗin nan, mutun sai bala'in zuciya, yana da tabbacin da'a gabansa Rimsha ta yi wannan magana, da ba abin da zai hana bai yi mata dukar mutuwa ba, dan duk cikinsu ma Lion ɗin ya fi tsanar kalmar raini, da sai ya yi mata ɗan banza duka, sai dai daga baya ya yi danasani, amma zata daku kam.

Lion a haka ya runtse idanuwansa yana mai jin zuciyarsa tana yi mashi zogi har barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi. Shi ma Areef ɗin bedroom nasa ya koma ya kwanta, dama shi Aseef already yana can bedroom nasa suna aikin da suka saba shi da Heartbeat a waya. Asuba ta gari.

KASAR CHINA.

Babban birnin Beijing, Capital Cityn kasar China kenan, birni ne mai matuƙar girma tare da cike da abubuwan more rayuwa da kawa, yana da matuƙar ɗaukar hankali, akwai guraren yawon buɗe idanu kala kala, kun san China da uban technology, akwaisu da iya ƙere ƙeren abubuwa, ga wajajen hutawa na more rayuwa, ko'ina a cikin birnin tsab yake babu datti, al'adunsu dayawa daga ciki gwanin birgewa, ga su da karrama bako, suna da son mutane, tsayawa zayyana maku yaɗuwar birnin Beijing ma ɓata lokaci ne, dan baki ya yi kaɗan wajen zayyano shi, dan fa kowa yasan China karshe ce, sun haɗu iya haɗawa, dan haka mu shige kai tsaye cikin storyn dan jin yadda zata kaya.

Ministry of defence, wato Ma'aikatar tsaro ta kasa bakiɗaya.

Wani tampatsetsen office ne a cikin Ministry of defence ɗin, a dukka ofisoshin dake a wajen wannan ya fisu girma da kawatuwa, ya tsaru iya tsaruwa na wuce misali, kai daga gani ko ba'a faɗa maka ba kasan cewa office ɗin Defence minister ne, wato Ministan tsaro, yanayin tsarin office ɗin nasa ma na daban ne, ya tsaru iya tsaruwa, gabaɗaya fentin office ɗin fari kal ne mai matuƙar kyau da tsada.

Daga cikin parlour na office ɗin, wato wajen meeting nasu kenan, wasu lumtsuma luntsumar tsadaddun Chinese sofas ne masu numfashi jere a wajen, set biyu ne dai'dai sofas ɗin, sun tsaru iya tsaruwa, gasu da laushi tamkar audiga, kana zama zasu lume da kai, launin ash color ne, lallausa kuma tsadadden Chinese carpet dake shumfuɗe a tsakiyarsu ma launin ash ɗin ne, daddaɗar kamshi tare da sanyin A.c mai ratsa zuciya tare da kwantar da hankali sai tashi yake yi a cikin parlour, kai kace parlourn wani hamshakin sarki mai ji da karfin mulki ne, amma kuma office na mutun ɗaya ne, common dustbin dake a cikin parlourn office ɗin nan abin kallo ne, dan ba kuɗin wasa aka zuba mashi wajen sayansa ba, na manyan kai ne, ko'ina tsab kamar yanzu aka zuba sabbin kayan cikin.

Akwai wani kyakkyawan table mai ɗauke da table chair da yake a gefe guda, wata farar tattabara ce, wato wata farar budurwa kyakkyawar gaske ce zaune a saman chair ɗin, da alama Secretariya ce, ƴar Chinance, tana cikin shiga irin na ma'aikata, mining sket black color and long sleeve fara, ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai, ta saki jelar har gadon bayanta, kunsan yanda gashin Chinawa yake ai? Ba sai na taya zuba maku dogon bayani ba.

Kana shigowa zaka yi ido huɗu da tampatsetsen frame na president, governor and Defence minister a manne a bango suna fuskantar kofar shigowa. Wani haɗaɗen Chinese door ne daga gefen dama, irin tsadaddun nan ne da suka amsa sunansu, cikin wannan door ɗin, nan ne ainahin cikin office ɗin, duk wanan kawatuwa da na zayyano maku a iya parlour ne kawai, cikin ya wuce tunaninku, idan ka shiga sai ka yi zaton kabar duniya, saboda wani irin ni'ima da zai ziyarceka lokaci guda, wani irin sanyin A.c mai bala'in daɗi ga kuma daddaɗar kamshi air freshener mai matukar kwantar da hankali, su kansu luntsuma luntsumar sofas dake a cikin office ɗin ya isa ya sanya mutun ya saki baki yana kallonsu, office chair ne mai bala'in kyan gaske a wajen wani katafaren table wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, wannan office chair ya wuce baki ya zayyano kyansa, shi kansa table ɗin ya wuci misali, tiles na kasar floor white color ne mai matuƙar kyau, ga shi fari kal, hakan zai tabbatar maka da cewa mamallakin wannan office ɗin tsabta tana yi mashi mubaya'a, tiles dake a jikin bango light ash ne, sai kyalli suke yi, alamar ko wace rana sai an gogesu tsab, tamkar hannu bai taɓa taɓasu ba, gabaɗaya Curtain dake a cikin office ɗin white color ne masu bala'in tsada.

Wasu tsadaddun desktop computers ne a ɗaure a saman wannan tsararriyar table ɗin, tulin files ne a gabansa kusa da computers ɗin.

Wani santalelen matashi mai jini a jikka ne zaune a saman wannan dankareriyar office chair ɗin nan, tsalelen matashi dogo da shi, daga kafafunsa dake sanye da wasu shegun black covers masu matuƙar kyau da tsada har izuwa kyakkywar dark black curly hairnsa dake kwance mashi har bayan wuya dukka tsadaddun kaya ne da suka amsa sunansu tsadaddun, komai na jikinsa kuɗi aka narka ba kaɗan ba, watch ɗin hannunsa kawai ma abin kallo, danƙareriyar diamond watch mai matuƙar ɗaukar idanu saboda kyalli ne, ɗayar hannunsa na sanye da wata ƴar siririyar diamond hand chain, akwai wani tsadadden diamond ring a ɗaya daga cikin kyawawan fararen ƴatsun hannunsa, baka iya ganin face nasa, saboda ya duƙar da kai ya kurawa wata hoto dake jikin jarida idanu. Black suit ce a jikinsa, ta yi matuƙar yi mashi tsantsar kyau, duba da yanayin fatar jikinsa kamar madara, hakan tasa ya yi wa suit ɗin matuƙar kyau sosai. Gashin kansa sai wani kyalli yake yi tamkar gashin kan Lion namu na Meesha.

Shiru ya zubawa wata hoto idanu yana kallo, idanuwansa na sanye da black glass mai matuƙar kyau wadda ta kara fito mashi da hasken face nasa, soft skin nasa tamkar madara, a kwance luwai luwai, ga wasu chains na zallar zinari masu bala'in kyau a wuyarsa wadda suka sauko mashi har saman chest nasa, fuskarsa a ɗaure tamau kamar hadari, alamar babu wasa a tattare da shi, tamkar yadda face ɗin Lion take a ɗaure kullum, haka nasa face ɗin ma take. Ba komai ya kurawa idanu ba face hoton Lion, bai taɓa sanin Lion ba sai a yanzu da Lion ɗin ya fito takarar neman shugaban kasa, a nan ne ya ga hotunansa a kafafen yaɗa labarai suna yawo, a news sai maganarsa suke yi tare da ɗaura ainahin hotonansa, ga postoci da aka yi mashi, kun san a da can baya ba kowa ya san ainahin face nasa ba, saboda da face mask yake yawo, so a yanzu babu face mask ake buga postocin siyasar tasa, ta hakan wannan matashi ya samu hotonsa na ainahi, abin ya yi matuƙar girgiza shi time da ya fara ɗaura idanunsa a kan hoton Lion ɗin, saboda babu wata banbanci dake a tsakanin face nasa tsawonsa komai nasa da ta Lion ɗin, time da abokinsa ya turo mashi hoton, lokacin da ya buɗe sakon abokin nasa, yana ɗaura idanunsa a kan hoton bai san time da ya miƙe tsaye a razane ba, da farko ya ɗauka hotonsa ne, sai daga baya da ya kalli na jikin hoton da kyau, sai ya lura Lion ya fishi murɗewar jiki, sannan ya fishi cika, kuma a jaridar an rubuta cewa ɗan takarar shugaban kasa na ƙasar America da ya lashe zaɓen primary election a halin yanzu, hakan tasa ya fahimci ba shi ne a jikin hoton ba, kama ce kawai da ta yi over, tun da gari ya waye ya zo office nasa ya fara aiki, tun da abokinsa ya turo mashi jaridar nan ya dakata da yin aikin komai, ya dakatar da kowa da samun damar ganinsa, ya zauna ya zubawa wannan hoto ido yana mamaki tare da al'ajabin irin wannan muguwar kamanni da take a tsakaninsu.

Abin ya yi matuƙar girgiza shi, ya aka suka yi irin wannan kama tamkar mutun guda haka? Abin ya yi mugu mugun tashin kansa ba kaɗan ba.

Tsadaddiyar wayarsa da take a gefensa ne ta fara ringing, har ta katse bai ɗaga ba, kira ta biyu ta sake shigowa, ita ma har ta katse bai ɗaga ba, sai a na uku ne ya ɗauki kiran. Kara wayar ya yi a kunnensa ba tare da ya ce uppan ba, sai a lokacin ne kuma ya ɗago kansa tare da ajiye jaridar hannun nasa mai ɗauke da hoton Lion, sannan ya koma ya jingina da jikin chair ɗin yana sauraron abin da ake faɗa mashi a cikin wayar. Haƙiƙa babu wata banbanci dake a tsakanin fuskarsa da ta Lion, duk da idanuwansa suna a cikin black glass, baka iya gane wani irin kalace da su, amma hakan ba zai hana ka ga tsantsar kamanninsa da Lion ba.

Ya ɗan jima yana sauraron abin da ake faɗa ta cikin wayar ba tare da ya amsa ba, sai ya ɗago hannu yana duba time a jikin dankareriyar watch dake a hannunsa. Calmly ya furta "Am coming". Da zazzaƙar muryarsa mai muguwar kama da ta Lion, Iya abin da ya furta kenan tare da katse kiran. Nisawa ya yi tare da ɗan ɗago da kansa da nufin ya miƙe tsaye. Turo kofar office ɗin Secretariyarsa ta yi tare da shigowa tana faɗin "Sir ARVIN you have some visitors from West Building, Zhongnanhai".

Shiru ya yi mata bai amsa ba, ganin haka yasa ta juya ta fita, da alama ta yi mashi farinsani, hakan yasa ta san fassarar shirunsa.

Wanene ARVIN. ARVIN dai shi ne Defence minister na kasar China bakiɗaya, wato ministar tsaro ta kasa, duk wani mai kaki a karkashinsa yake, idan ana maganar duk wani mai kaki kuma mai muƙami, to fa gaɓaɗaya ake magana, duk wasu jiga jigan Generals na sojoji, ƴan'sanda da dai duk wasu masu muƙami, harta General of the army's a karkashinsa yake, shi ne Minister tsaro gabaɗaya, mutun ne mai matuƙar girman kai, jiji da kai, isa, izza da kuma taƙama, mahaifinsa shi ne Senate president na ƙasar, yana da kanne biyu, namiji ɗaya sai mace ɗaya, namijin yana da shekaru 27 a halin yanzu, ita kuma macen tana da 13 to 14 years old, mutun ne miskili, ga kuma ɗan banzan farinjini kamar ba gobe, jama'a kowa son shi yake yi, yana tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, bashi da aure, ko budurwa bashi da ita, saboda shi gani yake yi ɓata lokaci ne ma ya tsaya sauraton mata, haka zalika kanin nasa ma bashi da mata. Wannan shi ne ɗan takaitaccen tarihin Sir ARVIN.

Miƙewa ya yi tsaye, dogo da shi tamkar Lion ne yake tsaye a wajen. Hannu ya kai ya rufe laptop dake a gabansa, kafin ya ɗauki tsadaddun wayoyinsa har biyu ya nufi waje cikin takun nuna isa, tsantsar lafiya da kuma izza.

Yana fitowa gabaɗaya kananan ma'aikatan dake wajen suka fara duƙawa suna yi mashi mubaya'a, kun san halin Chinawa da iya duƙawa kasa su gaishe da mutum, ko sannu zasu cewa mutun sai sun ɗan dukar da kansu kasa, so yana fitowa haka suka fara duka mashi cikin girma da girmamawa, ko kaɗan bai ɗago idanu ya kalli ko mutun ɗaya ba, dama na gaya maku yana da bala'in girman kai.

Sai da ya fito harabar wajen ne wasu jiga jigan bodyguards masu ji da lafiya da karfi, su goma sha biyu ciff suka take mashi baya har zuwa wajen wani haɗaɗɗen parking space dake a wajen, gabakiɗaya bodyguards ɗin Chinawa ne, jajir da su kamar tsada, ga su da faɗi, basu da tsawo sosai, kamar yanda kuka sani ne, bodyguards ɗin suna sanye cikin black suit kamar yanda kowasu bodyguards suke sanyawa.

A hanzarce wani ƙosasshe kuma lafiyayyen bodyguard ya kai hannu ya buɗe mashi wata dankareriyar mota kirar *ROLLS-ROYCE* Fara tas da ita tana wani ɗaukar ido, sai ka rantse da Allah yanzu aka fito da ita daga laida, wasu luntsuma luntsumar sofas ne a cikin wannan mota masu matuƙar laushi, kun san idan aka ce luntsuma luntsuma, ana nufin masu lumewa da mutun saboda laushi da tsantsar kyau, wani irin azababben daddaɗar kamshin car perfume ne yake tashi daga cikinta, ga wani irin sanyi A.c dake tasowa, kai tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan mota ma ɓata lokaci ne, dan ya wuce misali.

Cikin nutsuwa tamkar Lion haka ya shiga cikin motar ya zauna, zuciyarsa cike taf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login