Showing 60001 words to 63000 words out of 270744 words
ta yi tana faɗin "No ina tsoro sosai gaskiya, ba zan iya zuwa kitchen ba". Shiru ya ɗan yi kafin daga bisani kuma ya sake cewa "Jeki cikin ɗaki, a cikin trolleyna da muka je Abuja dake ɗin nan, ki duba zaki ga wani littafin adduo'i, ki ɗauko ki kawo mani bari na koya maki wata addu'a dan ki rage tsoro".
Kasancewar a palon sama suke, sai ta ji tsoron ya ragun mata, dan daga palon suna iya hango cikin bedroom ɗin nasa, so tana jin motsin mutane, dan haka sai ta miƙe ta nufi cikin bedroom ɗin. Su kuma suka cigaba da tattaunawa, ana mai da yanda aka yi wasu abubuwa a baya.
Da shigarta ɗakin bai fi da minti uku ba, ta zunduma wani irin uban ihu mai tsananin rikita ƙwaƙwalwa. Mazan dake a cikin palon suna yunkurin mikewa su nufi cikin bedroom ɗin, sai gata ta fito a guje. Tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, kowa ya yi tunanin wani abin ne ya kamata, ko Queen ce ta ɓullo a gabanta, amma sai suka ga akasin haka, gata ta fito lafiya lou hannunta na rike da wasu hotuna tana zunduma ihun kuma again.
Bata zame ko'ina ba sai wajen daddynta, jikinsa ta faɗa tare da miƙa mashi hoton, tana kuka tana faɗin "Daddy wlh tallahi wannan ma ɗan uwan su Queen ɗin Daular Mutuwa ne, na gan shi a cikin Daular Mutuwar, sunansa baba, muna zama muyi hira da shi ni da su Ayla, Allah ban manta shi ba, wayyo nashiga uku, yanzu kenan har ɗakin yaya Saif akwai ƴan Daular Mutuwa a ciki, daddy Dan Allah mu koma gidanmu na Abuja kawai, ni dai wlh bana son Daular Mutuwar nan". Tun da ta fara surutan nan suka zuba mata idanu, baiwar Allah duk ta firgice yau.
Shi kuwa daddy karɓar hoton ya yi dan ya kalli wanene. Ai kuwa yana gani ya yi wani irin zabura, a hanzarce ya sauketa daga jikinsa tare da miƙewa tsaye yana faɗin "Daddy kuma a Daular Mutuwa?!!".
Da sauri shi ma Abba ya karɓi hoton yana kallo, zaro idanu shi ma ya yi ganin cewa hoton Dr Salman ne, to su a saninsu mutuwa Dr Salman ya yi, ya haka kuma, anya Rimsha shi ta gani kuwa? Wannan shi ne tambayoyin da suke yi wa kansu.
Masu karatu idan baku manta ba, time da Lion ya je Abuja, akwai wasu hotuna na familyn daddyn Rimsha daya kwasa daga ɗakin mum, kun tunasu? To a cikin waɗan nan hotunan ne da akwai hoton Dr Salman, shi ne yanzu da ta je ɗaukar littafin addu'ar, sai taga hoton, ita kuma kunga yanzu tunanin Daular Mutuwa kaf ya dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, ta san Dr Salman a can, tana tsaka da kallon hotunan ne, sai taga hotonsa a ciki, kunga kuwa dole ta birkice ai, tun da ita dai a Daular Mutuwa ta san shi, yanzu kawai taga hotonsa a cikin trolleyn Noorish nata, ai dole ta yi hauka, dole ta yi tunanin ko dai ƴan Daular Mutuwa sun fara biyota har nan ne kuma, to shi ne abin da ya faru.
Mamaki ya hana kowa magana, sun jima shiru kamar waɗan da ruwa ya cinyesu, sai al'ajabin wannan al'amari suke yi. Can Brr Naurat ta ce "Meesha kin tabbatar shi kika gani a can?".
Da sauri Lion ya ɗago idanu yana kallon Brr, saboda ya ji sunan da ta kira Rimsha da shi, shi dai yasan sunansa ne, shi kaɗai yasa mata wannan suna. (Brr Naurat ya da haka kuma? Ina ruwanki da sunan masoya?🧐)
Tamkar Brr tasan kallon me yake yi mata, sai ta ce "Ka yi mani kishi, na yi shiru bai yi magana ba, har da sake mata suna, to ba zai yiwu ba, nima dole ka sake mani suna, kuma nima da wannan suna zan kirata, dan ni ce uwar gida ai, duk ido zan saka maku".
Kawar da kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, wannan tsohuwa akwai sa ido, ya faɗa a cikin zuciyarsa, a cikin jirgin ruwa fa ta ji yana faɗin Meesha, shi ne har ta rike sunan, Brr kenan!.
Cikin kuka Rimshar ta ce "Brr wlh shi ne, shi ne baba na Daular Mutuwa, Allah ban manta shi ba, kullum yana zaune a ɗakinsa, ya tsufa, muna zuwa mu yi hira da shi".
Ammie ce ta karɓi zancen da cewa "Ba shakka tun da Rimsha ta faɗi haka, to wlh haka ne, ni dama na ce wannan accident ɗin shirya shi Queen ta yi, ai kunga ko gawar Dr dama ba'a kawo mana ba, sai dai aka ce babbar motar da ta bi ta kansu ta yi raga raga da su over, sai dai kasusuwansu, to wlh ba shakka Dr Salman yana raye, kuma yana cikin Daular Mutuwar kamar yanda Rimshar ta faɗa!".
Jin ance wannan baban kakanta ne yasa ta sake zunduma ihu tana faɗin "Wlh ba kakanmu bane, shifa yaron Queen ne, dan Allah ku dai'na cewa kakanmu ne, a Daular Mutuwa fa yake, wai daddy ka san Daular Mutuwa nan kuwa? Wlh ina gaya maka shi ma baban namar mutane yake ci, dan Allah ku dai'na cewa kakanmu ne, ni kam zan mutu yau".
Ganin suna neman su juyawa Meeshansa kwakwalwa, suna neman su sanyata ta birkice gabaɗaya, sai ya miƙe tsaye tare da nufar in da take, hannu yasa ya saɓeta a kafaɗarsa, sai kuka take yi, ya wuce da ita izuwa bedroom nasa.
Jama'ar palon ma babu wanda ya lura da su, sai jajanta wannan al'amari kawai suke yi a tsakaninsu. Yana shiga ya shinfiɗeta a saman bed nasa, sannan shi ma ya haye.
Rikota ya yi tare da fara yi mata raɗa a kunne, kan kace me, sai gata ta koma sakin murmushi, ga guntun hawaye a gefe, ga murmushi kuma a gefe, jim kaɗan ka fara dariya har da kyakyatawa, tamkar ba ita ce yanzu take zunduma ihu a palo ba, kome Noorish ɗin nata yake ta gaya mata a kunnen?.
Juyowa ta yi da kyau ta shige jikinsa tana faɗin "Amma Noorish ba'a jirgin ruwa zamu tafi ba ko?". Shiru ya yi yana kallon kyakkyawar face nata, duk hawaye ya bubbushe.
"Bakison tafiya a jirgin ruwa ne?". Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "Ina tsoron mu nutse kasa ne".
Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ce "Ba kina son shiga cikin ruwa ba? Idan mun nutse ai sai ki yi wanka ko?".
Turo baki ta yi tana faɗin "A'a ba irin wannan ruwa ba". Shiru ya yi yana ta kallonta.
"I like your lips". Ya faɗa a sanyaye. Ɗago idanunta da suke jajir saboda kuka ta yi, kai tsaye cikin idanunsa ta kai kallonta, ya tsareta da ido sosai.
"Noorish nima lips naka suna yi mani kyau over". Gyara kwanciyarsa ya yi, a in da ya rage tsawonsa, ya zama face nasu tana dai'dai da juna. Zubawa juna idanu kawai suka yi, suna zuba kallon tsantsar so da kaunar juna. Romeo and Juliet kenan!.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ita ta kawar da kallonta tare da shigewa cikin jikinsa tana dariya. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta yana shafawa tare da ɗan ciza laɓɓansa na kasa kaɗan.
A can palo kuwa, cigaba da maganar neman mafita ta yanda za'a ɗauko Dr Salman suka rinƙa yi. Sai can Areef ya ce masu dan Allah su bar mutane su huta haka nan, ai sun san cewa ko babu kowa nasu a cikin Daular Mutuwar nan, in dai Lion ya ji abin da ake aikatawa a ciki, to zai san yanda za'ayi a ruguje gidan, ballantana da akwai nasu har rayuka uku a ciki, bugu da kari kuma da akwai matar Aseef a cikinsu, ai dole ko ba zasu yi rai ba, dole su fito da su, dan haka shi dan Allah su dai'na damunsa da zancen wannan gida ta Mutuwa, idan suna magana, jikinsa har tsuma yake yi, ji yake yi ba zai iya hakuri ba, ji yake yi a yau zai tafi ya ɗaukowa Aseef matarsa, ya kuma kashe Queen ya ɗauko Dr Salman.
Gwaggo ce ta danne shi, dan ba shakka suna kara ɓata mashi rai idan suna maganar, ji yake yi tamkar ya tashi ya tafi a lokacin.
Miƙewa ya yi yana faɗin "Baby yunwa nake ji, na dawo baki bani abinci ba". Ya yi maganar yana kallon Jehan. Harara ta wurga mashi, zata yi magana idanunta suka sauka a kan mummynta, fasa yin maganar kawai ta yi.
Wucewa ya yi yana faɗin "Dan Allah kowa ya je ya ɗan huta, kunga lokacin yin sallar mangariba ta kusa, ku huta kafin lokacin ya cika, maganar nan ta isa haka, tun da mun gano matsalarmu, to In Sha Allah zamu yi maganinta cikin gaggawa". Ya kai karshen maganar tare da sauka izuwa bedroom nasa.
Gwaggo ce ta haɗa kan gabaɗaya matan, ta ce masu su je bedroom nata su huta, ina nufin su Ammie, Mummyn Rimsha, Aunty, da kuma mummy Anaya kenan, sune suka bi gwaggo, su kuma su Jelly, Anaya, Zaira, Umaisha, Jehan, suka wuce bedroom nasu Rimsha, Imran shi ya raka su Abba boys quarters na gidan, sannan ya wuce izuwa harabar gidan, dan ya sha iska abinsa, Aafia kuwa tana ɗakin gwaggon, dan dama tun shigowarsu aka kaita can, sai zuba barci take yi baiwar Allah, har wa yau, uncle Herry yana tare da Dr William a ɗakinsa, Dr William ɗin ya farfaɗo, amma ƴaƴan nasa sam sun ki zuwa wajensa, bare ma Lion, sam baya son haɗa hanya da su, ɗan gara Areef ma, time to time yana zuwa ya duba shi, wani likita Lion ya sanya aka kawo yana kula da shi, amma shi ko leƙawa yaki ya yi, daddyn kuma ba shi da burin da ya wuce ya ga yaran nasa, yana tsananin kaunar TRIPLETS nasa fiye da tunanin mai tunani, Aseef kam kowa ya sani, ɗan baruwana ne, yana can wajen gwaggo, dan haka shi yama mance da Dr William abinsa, yanzu ma da kyar suka lallaɓa shi ya wuce bedroom nasa, ban da haka ya ce shi wlh sai ya je Daular Mutuwa ya ɗauko matarsa.
Wanke Jehan ta je tayi, bayan ta fito ta duba time, karfe 6:10pm, mangariba ya kusa, ga shi Areef ya ce mata yana jin yunwa. Sauri sauri ta shirya cikin kananan kaya, sannan ta ɗaura after dress a samansu, sai binta da kallo su Jelly suke yi, ita kuwa, basu isheta kallo ba, ba wanda ya sami kallon arziki a cikinsu daga wajenta, tamkar ba ƴan uwanta bane, kun santa dama da iya tsare gida da jiji da kai, to ko sannu bata ce da su Umaisha ɗin ba, haka ta gama abin da zata yi, ta zuba perfume kamar ba gobe, sannan ta fito izuwa cikin kitchen, kafanta na sanye cikin flat shoe mai matuƙar kyau na Rimsha, dan ita bata da kaya a gidan har yanzu, kuma bata ce a saya mata ba, dana Rimsha kawai take amfani, duk da sun yi mata kaɗan, haka take sanyawa.
Abinci mai rai da lafiya ta shirya mashi a saman tray, sai dai dukka zaɓinta ta ɗebo, dan ita bata ma san irin abincin da yake so ba, shi ne yasa ta ɗauka mashi zaɓinta.
Ɗauka ta yi ta nufi waje, kai tsaye bedroom nasa ta nufa. Baki ɗauke da sallama ta shiga ɗakin, wayam babu kowa a ciki, bata yi mamaki ba, dan tasan halinsa da son ƴan uwansa, wata kila ya tafi wajensu ne.
A saman carpet ta ɗaura mashi abincin, sannan ta koma saman bed nasa ta bakin ta zauna, sai kallon ɗakin take yi, ko'ina tsab kamar sabo, sai tashin daddaɗar kamshi mai kwantar da hankali yake yi, ga sanyi Ac mai ratsa zuciya.
Ta ɗan yi nisa cikin tunanin irin kyawawan halayensa da kuma tsanar madarar kyau da Allah ya yi mashi, kamar daga sama ta gan shi a gaban mirror yana tsaye, ya bata baya, kugunsa na ɗaure da white towel mai matuƙar kyau, daga wanka ya fito, jikinsa duk danshin ruwa, ga gashin kansa yana ɗan zubar da ruwa.
Kallo ɗaya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kanta gefe guda, har cikin ranta ta tsorata da ganin kyakkyawar kuma kakkarfar surar jikinsa, suna da halitta mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali over.
Ganin kamar baya kallonta ne yasa ta mike a hankali dan ta bar ɗakin, saboda ta lura shi fa tsab zai iya yin komai a gabanta, dan ba kunya ne da su ba.
Tana tafiya tana tunanin irin yanayin jikinsa da ta gani, duk da kallo ɗaya ta yi mashi, amma ya tsaya mata a rai, jikin nasa kamar madara, soft skin nasa luwai luwai da shi. A dai'dai tsakiyar ɗakin, bata yi aune ba sai ji ta yi ya rungumeta ta baya tare da zuro hannayensa a saman shafaffen cikinta, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta.
Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali, ya sanya mata sanyin gashin kansa a wuya.
"Hyyy baby, ina zaki je kuma?". Ya yi mata maganar a cikin kunne.
"Zan fita ne na baka waje ka shirya". "Ni nace maki ina son ki bani waje ne?". Ya kai karshen maganar tare da sumbatar lallausan wuyarta.
Shiru ta yi bata bashi amsa ba. "Ina abin da kika ajiye mani? A waya kin ce kina kewata, na dawo kuma shi ne ba zaki zo ki ganni ba, sai da na roka ko? Na rokanma kin zo kuma zaki tafi tun ban ganki ba, kin san adadin kewarki da nake yi kuwa? Kin san me nake ji kuwa?".
Hannayenta ta ɗaura a saman nasa dake saman flat tummynta, kasa kasa ta ce "To ka bari sai ka gama shiryawa zan dawo, sai muga juna". "Why ba zaki zo ki tayani shiryawa ɗin ba? Yakamata ace kin saka mani kaya da kanki, please mana my baby".
Kasa jurewa ta yi, dan wlh tana tsananin kewarsa sosai, ga shi yanda yake yi mata magana a cikin kunne kasa kasa, duk sai ya kara tsumata, hakan yasa ta kasa jurewa, a wannan karon ta kasa dannewa sai da ta juyo ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa da kyau.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumeta da kyau da kyau, tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita. Da yake ita tana da tsawo sosai, Kamar gwaggo take, tafi Rimsha tsawo, sai tsayinta ya kai ta kwantar da kanta a saman ɓul ɓul ɗin breast nasa.
Hannu ya kai saman bayanta yana ɗan shafawa izuwa mazaunanta masu burge shi, kowa yasan matan turawa basu da halittar mazaunai sosai, shiyasa dirarren halittar su Rimsha yake ɗaukar hankulan TRIPLETS over, suna son mazaunan nasu sosai, barema Rimsha, Jehan, Akila, Umaisha, sun fi kowa diri a cikinsu, tamkar su suka yi wa kansu.......
"Baby". Ya ambata a hankali, kasa kasa ta amsa mashi da na'am. "Zaki tayani saka kayan?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce e zata taya shi........... JEHAN DUNIYA, BAFA ABIN DA YARINYAR NAN BATA IYA BA, KAWAI TSIYA CE IRIN NATA, SAI TA NUNA KAMAR MA BATA SAN KOMAI BA, SABODA SHEGEN JAN AJI DA TSARE GIDA.
Ɗaukarta ya yi cak, sai cikin dressing room ya sauketa, dressing room ɗin nasa sak irin na Lion.
"Ki zaɓa mani kaya to". Ya faɗa tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa.
"To ka rufe idanunka". Ta faɗa tare da wucewa izuwa wajen kayan nasa. Ba musu ya rufe idanuwan nasa, yau wani irin daɗi yake ji, saboda ta bashi kulawa, babu tsawa, babu tsiwa, babu haɗe fuska, bai san cewa ita ma sonsa yana neman yi mata illa bane yasa ta nema wa kanta mafita, yasa ta saduda ta fawwalawa Allah ta dawo ta fara kula da shi...... NI KO NA CE WAYE YA GAYA MAKI SOYAYYA WASA CE? DA KI CIGABA DA JAN AJI MANA, DA KIN MUTU A KAN SON SHI😂 KEBAKI GA AYA A KAN GWAGGO BANE? HAR YANZU SON DR WILLIAM NATA TAKE YI BAIWAR ALLAH, SO AI BA'A YI MASHI GARAJE! YANZU ZAI YI MAKA ILLAH, BA'A WASA DA ZUCIYA!.
Wandon jeans baka da T-shirt sky blue masu matukar kyau ta ɗauko mashi, kusa da shi ta dawo, yana tsaye ya datse idanunsa yana jiranta.
Kasa kasa ta ce "To ai ka fini tsawo, kuma ni ban san ta yaya zan sanya maka kayan bama".
Idanunwansa a rufe ruf ya bata amsa da cewa "To yanzu dai kin yarda na buɗe idanuna? Sai na nuna maki yanda zaki saka mani".
E ta amsa mashi da shi. Buɗe idanun nasa ya yi tare da matso da chair dake kusa da wajen watchs nasa, ya zauna a saman chair ɗin yana kare mata kallo. Ita kuma babu abin da take kallo a jikinsa saman da ɓul ɓul ɗin breast nasa, mamaki suka bata yanda suke ɓul ɓul kamar na mace. Jehan akwai dakiyar zuciya, ba irin Rimsha ba, da Rimsha ce ba zata iya tsayuwa tana ganinsa babu riga a jikinsa haka ba, tun da Rimsha take da Lion bata taɓa ganin surar jikinsa babu riga ba, ba zata iya ba, ita kuwa Jehan kun sani ba sai na sake faɗa ba, fin haka ma ta gani, ita da har video ta yi wa babban mutun tsirara a gidan Hjyr daɗi, ko kun manta ne? To na tuna maku,.....(Ita Jehan harta gogan nasu ma ta san ya yake abinta😂😂)
Ganin tana ta satar kallon kirjin nasa da mamaki a face nata ne yasa ya kai hannu ya jawota jikinsa. Zaunar da ita a saman cinyarsa ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Sun yi maki kyau ne kike ta kallonsu?".
Hannu ta kai tana shafa kyakkyawar bakin gashin dake kwance a kirjin nasa. "A'a sun ban mamaki ne". Ta bashi amsa.
Shi kuma jin saukar lallausan hannunta a kirjinsa ne yasa ya furta ash tare da datse idanunsa yana mai kara kankameta. (Da alama zancen Imran gaskiya ne, da ya ce wa Areef ɗin dan bai samu dama a wajen Jehan ɗin bace yasa yake cewa zai barta sai ta girma😂)
Jin abin da ya furta ne yasa ta yi saurin zame hannunta daga wajen tare da yin ƙoƙarin barin jikin nasa, kankameta ya yi tare da riko hannun nata ya ɗaura a saman breast ɗin nasa, kasa kasa ya