Showing 48001 words to 51000 words out of 270744 words

Chapter 17 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2952

mun sami baby? Ai na shiga uku kawai, barmu dai mu cigaba da soyayya, zuwa gaba, idan ta kara girma, ta rage shagwaɓa, sai mu nemi baby, amma dai Areef kai mugun ɗan sa ido ne, waye wai ya gaya maka halin Jelly?".

Shiru ya yi bai bashi amsa ba, dan tun da yake, bai taɓa tsayawa ya yi hira mai tsawon haka da wani ba idan ba TRIPLETS nasa ba, ba shi da yawan magana, amma da TRIPLETS nasa yana magana, yau ɗin ma abin da yasa ya zage yake yin maganar, saboda yana so ne ya manta abin da take a zuciyarsa na tunanin gida, abin ya tsaya mashi a rai, so yana so ne ya ɗan rage damuwar, shi ne yasa ya biyewa Imran ɗin, ban da haka, ba zaka taɓa jin ya yi magana ta tsawon minti biyu mai kyau ba, zaka gan shi kamar bai san komai ba, amma wlh babu wani abin da bai sani ba, duk zaman da su Imran da Jelly suka yi a gidan, ya san komai, duk abin da suke yi, yana sane da komai, kawai dai baya shiga harkar kowa, kuma baya da yawan magana, shi ne yasa sam yake kamar bai san komai ba.

"Prof ka ji tsoron Allah, dama ni nasan abin da ya sa kayi aure kenan, amma kana musawa friend naka a kan ba auren kashe sha'awa ka yi ba". Cewar Areef.

A wannan gaɓar Irfan ne ya karɓi zancen da cewa "Kowa ya sani mana, auren rage zafi ya yi, amma yana musa mana, yanzu idan ba haka ba, me na hana Jelly ɗaukar ciki? Ai idan ta samu ciki ma dole zata rage shagwaɓa, kuma daga haka zata girma".

Ganin suna neman kure shi ne yasa ya ce "Ni ban hana Jelly ɗaukar ciki ba, ai ciki na Allah ne, idan Allah ya ƙaddara lokacin zuwansa, to kome zamu yi, sai ta ɗauke shi".

"Yanzu mu kenan zaka gwadawa Allah ba? To ai komai sai da sanadi, mun san Allah yake bada ciki, amma ta sanadin sex ko?" Cewar Areef....... Dama wannan magana ta rashin kunya ai sai Areef ɗin, shi da bai san kunya ba.🧐

"Ni ba zan biye maku ba, dan ni nasan gaskiyar tsananina da Jellyna, ni da yanzu gado ma daban daban muke kwana da ita".

Wani irin kallon Areef ɗin ya wurga mashi, irin kallon nan na bashakka haka ne, basu ma kwana ɗaki ɗaya ba iya gado daban daban ba, dakin ma daban daban suke, ɗan rainin wayo kawai.

Irfan ne ya ce "A'a karshe ma dai kana palo tana cikin ɗaki, shi ne karshe ba gado ɗaya kuke kwana ba".

Areef kuwa cewa ya yi "Ni prof sam ban san daga ina ka samu wannan jarabar tsiya ba, Allah dai ya bawa sister hakurin juriya".

Irfan ne ya ce "Kila dai ina ga mata huɗu zai aura, dan wannan mace ɗaya ta yi mashi kaɗan".

Allah sarki yau walaƙanci suke jin yiwa Imran, sun saka shi a gaba, bawan Allah.

Shi kuma Imran ɗin cewa ya yi "Yanzu kai Areef har kana da bakin cewa wani yana da jaraba? To aishekenan, Allah ya kwaci Jehan, dan da kake cewa sai ta girman nan ma, duk na san zance ne kawai, bari ka samu dama, hmmm na dai yi shiru".

"Irfan mata huɗu fa ka ce? A nan ku kuna auran mata huɗu kenan?". Cewar Areef ɗin. Jinjina mashi kai Irfan ɗin ya yi tare da tabbatar mashi.

Girgiza kai ya yi yana faɗin "No, we are marring only one girl, mu ko biyu ma bamu yi, Just 1 is okey, amma why zaku auri mata biyu ma? Ɗaya bata isa ba? Me zaku yi da har guda biyu? I can't share my heart to two girls, i can't share my love to two girls, is better for me to share the love and the heart with my childrens and 1 girl, so that we should get more happiness". Ya kai karshen maganar yana saukowa daga saman table ɗin, ya kammala kwance camerar.

Shi kuma baban Muneer baki sai kara kumbura yake yi, ya yi suntum, raɗaɗi da azaba sun hana shi ko motsawa.

Imran ne ya ce "Ni kai'na ba zan iya auran mata biyu ba, but most a time zaka samu masu auren mata biyu ɗin, jaraba ce ta yi masu yawa, and then suna ganin like matan ba za su iya kula da komai nasu ba, wasu kuma rashin samun soyayya daga wajen matan ne yake kaisu ga ƙara aure, wasu kuma rashin samun farinciki ne yake saka su yin wani auren".

Maimaita kalmar soyayya da farinciki Areef ɗin ya yi kafin ya ce "I think namiji shi ne yake bawa mace farinciki, i think shi ne ya kamata ya koya mata sanya shi farincikin, idan har kana sanya matarka farinciki, kana yi mata soyayya, to dole ita ma zata sanyaka farinciki, ga example a kan ni da my baby, before bata sona, amma yanzu ina mai tabbatar maka, wannan tafiya da nayi tana cikin damuwa, kuma ni na koya mata so na ɗin, ni na koya mata menene so, menene kuma farinciki, so duk abin da ka ɗaura mace a kai tun farko, a haka zata ɗaure, komai jarabar namiji, mace tana iya ɗaukarsa tsab, saboda halittarsu ce a hakan, duk yanda ka rukesu, to a haka zasu ɗaure maka har abada, idan baka bata farinciki ba, ta yaya zata baka ita ma? Idan baka kula da ita ba, ta yaya zata kula da kai? Ni ban ga wani dalili na kara aure a nan ba, is better na yi sharing love ɗina da yarana, na kuma sanyasu farinciki, seriously i love Jehan more than your expectations, then i can't share her love with other girls, she is special in my heart, bazan iya haɗata da kowa ba, dan ba zan yi adalci ba, daga kanta an gama". Ya kai karshen maganar yana ciro wayarsa dake ruri yana neman agaji.

My uncle, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cool murmushi ya saki kafin ya ce "My diramati, ba zata iya rabuwa da ni ba, and then kuma ba zata barni na zauna kusa da ita ba, amma for sure zan yi maganinki". Ya kai karshen maganar tare da ɗaukar kiran.

Kamar yanda ya yi tsammani cewa ita ce ba daddynta ba, haka kuwa ita ɗin ce.

Sallama ta yi mashi cikin nutsuwa, amsa mata ya yi yana mamakin ya aka yi ta nutsu muryarta akwai girmamawa a ciki haka? Bai san cewa mum ce ta yi mata faɗa sosai ba, lokacin da ta yi mashi tsawa a palo a gidansu da safe, bayan ya saketa ta koma sama, da mum ta haura saman, zuwa ta yi ta sameta, ta yi mata faɗa sosai tare da tunatar da ita cewa, Allah yana tsinewa mace mai ɗaga murya sama da na mijinta, sannan kuma yakamata ta sani miji ba abin wasa bane, dan ta samu yana sonta, yana biyemata a duk shirmen da zata yi mashi, to wlh gara ta yi amfani da damarta, idan ba haka ba, lokaci ya kure mata ta dawo tana danasani, Areef yana da hakuri sosai, ta sani mai hakuri fa bai iya fushi ba, fushinsa bashi da kyan gani, to wlh kada ta kuskura ta kure shi, zai yi mata ba daɗi, to shi ne nasihar ta shiga kunnan ta, dama kuma da ni da ku dukka mun san tana tsananin son shi, kawai iyashege ne irin nata, yanzu ma ba wai dan nasihar mum ɗin ce tasa ta kira shi ba, a'a tsananin kewarsa ne ya takura mata har ta ɗauki wayar daddynta ba tare da saninsa ba, ta ɓuya ta kira mijin nata............. Ni ko na ce ana so ana kaiwa kasuwa, ni idan ta yi mashi walakanci na janye shi daga gareta ato, dan samun irin Areef a zamanin nan da kamar wuya, abin sai an tona, ko ya kuka ce masu karatu? In yi wuff da abina, yo meyafi ra'ina? Miji na gari a zamanin nan wasa ne?.

Gaisuwa ta ɗaga mashi cikin girmamawa. Mamaki ce tasa har ya ɗago yana kallon su Imran, tare kuma da ɗan raba wayar da kunnansa, dan ya tabbatar ita ɗin ce, shi dai yasan wannan voice nata ne, dan ko muryar kowa zai ɓace mashi, to muryar TRIPLETS nasa, daddynsa, Rimsha da kuma ita Jehan ɗin, sai gwaggo a yanzu, muryoyinsu ba zai taɓa bace mashi ba.

Ya yi shiru ya kasa amsawa, sanyayyar muryarta ta sake dakan dodan kunnensa. "Yaushe zaku dawo?" Shi ne tambayar da ta sake yi mashi.

"Kina son na dawo ne?". Jinjina mashi kai ta yi tamkar tana a gabansa, sannan ta ce "E ina so". "Why kike son na dawo?". Shiru ta ɗan yi kafin daga bisani ta amsa da "I want to see you close..." Sai kuma ta kasa karisawa.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya yi kasa da murya sosai ya ce "Meyasa kika kasa karisa maganar? Kina kewata ne?". "E a'a ni dai kawai ka dawo"............ Ji wata amsa, wai e a'a kai Jehan duniya ce.

Murmushi kaɗan ya yi yana faɗin "Sai after one week zan dawo". Shiru ta yi, sai kuma ta katse kiran. Shiru shima ya ɗan yi yana ɗan murmushi, almost 2 mins, sannan ya sake kiranta.

Kira na farko bata ɗaga ba, sai a na biyun ne ta ɗaga. "Ya naji kin katse kiran kuma?" Ya tambaya yana kokarin ciro wata igiya da ya gani a wajen kusa da Ac.

Muryarta kamar na mai kuka, da alama kuka ta yi, ta fara magana kasa kasa. "Na ji kace sai after one week zaka dawo ne, shi ne na barka sai bayan one week ɗin". "To me kuma ya sanya ki kuka?". A takaice ta ce "Ni ba kukan da na yi!".

"Am so sorry my baby, wasa nake yi maki, naja kin zubar da hawaye a banza, idan na dawo dole zan biya hawayen nan, ai nima ba zan iya yin kwana ɗaya ba tare da na ganki ba, anjuma kaɗan zan dawo, me kika ajiye mani?".

Sam bata san time ɗin da murmushi ya subce mata ba, ga hawaye a face nata falala. "Duk abin da kake so". Ta bashi amsa tana goge hawayen nata. "Are you serious?". Jinjina kai ta yi tana faɗin yeah.

"Okey tom shikenan, idan na dawo zan gaya maki abin da nake so ɗin, amma yanzu Please give me a kiss". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai kama da na shagwaɓa.

Kafewa ta yi a kan ita bata iya kiss ba, jinjina kai ya yi yana faɗin "Ba zan yi maki dole ba, ki kula mani da kanki kin ji ko? Ko palo ma ni bana son ki fito, ba dan daddy da mummy ba, ai da ba zan barki ma a gidan ba, amma dai ki kula sosai kin ji my pleasure?".

Kamar daga sama ya ji ta sumbaci wayar, sannan ta katse kiran ba tare da ta amsa mashi ba. Murmushi ya saki yana mayar da wayar a cikin aljihunsa, sannan ya nufi baban Muneer da yake kwance shame shame a cikin jini.

Ɗaure shi ya fara yi, shi kuma Imran, mikewa ya yi tare da ciro wayarsa ya nufi waje yana faɗin "Nima dai bari na ji voice ɗin tawa pleasure ɗin, da dai bani da ita ne sai ka yi mani gori".

Ko sannu bai ce mashi ba, ya ɗaure baban Muneer, sannan ya mikar da shi tsaye yana faɗawa Irfan su tafi ko?.

Ko da suka fito, ma'aikatan dake companyn, sun yi ƙoƙarin hanasu tafiya da shi, amma sai Areef ya nuna masu tsab zai yi ball da su idan basu tashi mashi a kan hanyarsa ba. A hanzarce wasu daga ciki suka kira office ɗin ƴan'sanda, sai dai kafin ma ƴan'sandan su zo, sunbar company ma abinsu. Haka suka kamo hanyar Kaduna.

A ɓangaren Lion kuwa, sai da ya ɗauki good 3 hours a asibiti ba tare da ya motsa ba, sai zarya likitoci suke yi a kansa, Aseef kuwa, da shegen saurin kuka kamar daddyn Jelly, sai zuba kukansa yake yi, har idanuwansa sun kumbura suntum, yaki yarda ya matsa kusa da Lion ɗin, yana zaune a saman bed ɗin, gwaggo na zaune a gefensu, ga sojojinsa suna tsaye cirko cirko a kofar shiga ɗakin, Mark ne kawai ya shigo cikin ɗakin, sai Tga dake ta faman magana da likitoci.

Duk wanda ya doso ɗakin da Lion ɗin yake kwance, sai ya juya a dubu ya koma, dan waɗan nan zaratan sojojin da suke tsaye a bakin kofar, ganin su ba ƙaramin razana al'umma yake yi ba, ga su jajir da su, tamkar ka taɓa jini ya zuba, dukkansu babu wanda yake sanye da uniform a jikinsa, duk fararen kaya ne a jikkunansu, fuska kam ba'a magana, kamar na shanu! A ɗaure tamau!.

Har sai da Lion ya kara good 1 awa, sannan ne likitocin suka yi nasarar saita bugawar zuciyarsa, suka kuma yi sa'a ya farfaɗo.

Yana buɗe idanuwansa, da Aseef ya fara cin karo, ido huɗu suka yi da Aseef ɗin. Da sauri ya mayar da idanunsa ya lumshe, yana tariyo abubuwa da dama a cikin ƙwaƙwalwarsa. Tabbas jaririn da mutumin nan ya kawo, mai brown eyes ne, jaririn da Josephine ta miƙa mashi kuma mai blue eyes ne, shi ma ɗayan jaririn da yake kwance, blue eyes ke gare shi, wanda Dr William ya fita da shi kuma ash eyes ke gare shi, abu biyu ne suka sanya Lion zuciyarsa ta kusa bugawa a cikin wannan video da ya gani, kuma kunsan abin da zai sanya shi suma duk da irin taurin zuciyar nan tasa ba ƙaramin abu bane!!.

Abu na farko, jaririn da ya ga mutun ya kawo, tabbas mai brown eyes ne, idan hasashensa gaskiya ce, to Aseef ne kenan, dan wanda yake kwance a saman sofa dai, mai blue eyes ne, hakan na nufin shi ne kenan, babban abin da ya fi ɗaga mashi hankali shi ne, ya fi kaunar Aseef ɗin sama da kansa, ya fi son Aseef fiye da Areef, ya fi son Aseef fiye da kowa, sun fi shakuwa, shakuwar da take a tsakaninsu baki ba zai iya faɗarta ba! Gara ace mashi mutuwa ya yi, da ace mashi Aseef ba jininsa bane! Ba zai iya jurar hakan ba, ko na rana ɗaya ba zai iya rabuwa da shi ba! Yana kaunar shagwaɓatinsa! Yana son ɗan rigimammensa! Yana son pleasurensa! Shi ne bugun zuciyarsu! Ko daddynsu ya fi kaunarsa sama da kowa! Ya ilahi ya lillahi, ina zai saka ransa ya ji sanyi! Josephine ta cuce shi! Ta gama da rayuwarsu, sai da suka saba! Suka taso a tare! Komai tare, shakuwa tasa har suke jin juna a jikinsu, yanzu ya Areef zai ji? Anya zai iya yarda kuwa? Babbar tambayar da Lion ɗin yake yi wa kansa shi ne, to meyasa suka yi hakan? Meyasa aka canza masu ɗayasu? Me suka yi da wancan ɗayan da suka ɗauka? Ina suka kai shi? Yana raye ne ko ya mutu? Shin Aseef mutun ne ko aljani? Cikakken mutun ne kuwa? Ko shi ne yasa yake wasu abubuwa da bana cikakkan mutane ba? Dole dai akwai dalilinsu na yin waɗan nan abubuwa dukkan, haka kawai baza'a canzasu ba! Haka kawai baza'a kawo wani yaro daban a cikinsu ba!!

Ni kuma PRINCESS TEEMA abin da yake cikin ra'ina, yake kuma damuna shi ne ya Akila zata yi? Ya zata ji a ranta? Shin zata zauna da wanda ba mutun bane? Ko dai yaya? Anya zata iya rayuwa babu shi kuwa? Tana son heartbeat nata fiye da kanta, wai Meyasa Aseef ya cika mugu mugun shiga ran mutane dayawa har haka ne? Meyasa kowa ya fi son shi? Wannan ma ayar tambaya ce!!.

Abu na biyu da ya sanya Lion ɗin zuciyarsa ta kusa bugawa shi ne, wannan mutumin da ya kawo wannan jariri ba kowa bane face uncle Herry, ba shakka uncle Herry ne, dan da kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mashi, ya kalle shi da idanun basira, nan ya fahimci uncle Herry ne, duk da ya ɓoye komai na jikinsa, yana cikin shigar bakaken kaya, hakan bai hana kaifin ƙwaƙwalwa Lion ta gane cewa shi ɗin bane, saboda idanun uncle Herry, John, Jay, GTA, daddynsa, Aseef, Areef, ba za su taɓa canzawa ko su ɓoye mashi ya kasa gane su ba, ba zai taɓa kasa ganesu a ko wani irin yanayi ba, zaka gan shi wani lokaci kamar baya kallo abubuwa, amma yana sane da komai, tabbas uncle Herry ne ya kawo jaririn. Tambayar da Lion ɗin yake yi wa kansa, to ina uncle Herry ya baro daddynsu? Ina ya baro Dr? Bayan kuma a tare suka fita daga gidan a lokacin, ko dai ya yi wa Dr ma wani abin ne? Wai shin menene gaskiya? Me yake faruwa ne?!!!.

Waɗan nan sune abubuwan da suka hargitsa zuciyar Lion, ace kannen babansa dukka maciya amana, kuma su rasa amanar waye za su, sai na yayan nasu, kai duniya ina zaki damu, ɗan uwa ya ci amanar ɗan uwan sa, sun cutar da rayuwarsu, to wai me suka yi da jaririn da suka ɗauka? Kuma a ina suka samo jaririn da suka kawo ɗin? Ga dukkan alamu dai suma aiki suke yi a karkashin wata kungiya, ko kuma wani, dan ga dukkan alamu umarni suke karɓa, duba da yanda suka tsara abin, a lokacin shekarasun ya yi kankantar da za su iya tsara hakan, sun yi kananan wajen shirya wannan abin, dole akwai wanda ya fisu shekaru da yake shirya masu komai, wannan dalilin yasa Lion ɗin bai ji cewa yana bukatar ya zauna da su, dan su gaya mashi gaskiya ba, dan ya san irin wannan case ɗin, ko kashe su zai yi, wlh ba za su taɓa faɗar gaskiya ba, so is better for him ya nemo gaskiya da kansa, babbar magana, ta ina zaka fara kenan? Waye zaka fara tunkara?!!

Murya a dashe saboda kuka Aseef ɗin ya ce "My Lion, please ka tashi ka ji?". Kara datse idanuwansa sosai Lion ɗin ya yi, har cikin ransa yake jin muryar Aseef ɗin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login