Showing 102001 words to 105000 words out of 270744 words

Chapter 35 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4614

da wannan family suke ciki a yau, sam baki ba zai iya furtata ba, ya wuce misali.

Haka Dr Salman ya rinƙa yin kuka yana faɗin kowa ya yafe mashi, ina Nawazuddeen ɗinsa? Dan Allah Nawazuddeen ya yafe mashi. Anyi anyi ya yi shiru yaki yi, ya ce har sai Nawazuddeen ya yafe mashi. Haka daddyn Rimsha ya rungume shi yana faɗin. "Daddy ni baka yi mani laifin komai ba, idan ma kayi, to ni na yafe maka, ban taɓa ji a ra'ina kamar ka taɓa yi mani laifi ba, kullum cikin yi maka addu'a da fatan alkhairi nake yi, dan Allah ka dai'na kukannan kada ka saka muma muyi kukan".

Sosai Dr Salman ɗin ya rubgume shi yana mai cigaba da matsar kwallah. Da kyar suka samu suka lallaɓa shi ya yi shiru, a tare suka rankaya izuwa cikin gida, kai tsaye bedroom na Lion suka nufa, while shi kuma Areef ya kai Ayla ɗakin gwaggo ya kwantar da ita a kusa da Rimsha, sannan shi ma ya fito izuwa bedroom ɗin na Lion ɗin.

Lion yana zama a bakin bed ɗin nasa yana ƙoƙarin fara duba hannunsa, sai ga family gabaɗaya sun shigo cikin ɗakin, duk sun biyoshi, gabaɗaya fuskokinsu ɗauke yake da tsantsan annuri da farinciki, yau Dr Salman ya dawo cikinsu, ga shi ba su rasa ko mutun ɗaya ba a cikin ƴaƴan nasu, abin ba karamar daɗi ta yi masu ba. Sun shigo ne dan su duba lafiyar Lion ɗin, dan kunga shi bai tsaya a wajen nasu ba, suna sauka ya wucu bedroom nasa kawai.

Kallo ɗaya Lion ɗin ya yi masu ya kawar da kallonsa gefe guda, ya cigaba da aikin da yake yi.

Ganin abin da yake ƙoƙarin yi na yiwa kansa magani ne yasa gwaggo da Areef suka kariso kusa da shi da sauri. A tare suka zauna a gefe da fefensa, suka sanya shi a tsakiya kenan.

Gwaggo ce ta fara karɓar A box ɗin tare da kama hannunsan tana dubawa, ba shakka ya ji ciwo sosai. A hankali ta ɗago da kallonta a kansa, hannu ta kai ta shafa lallausan kumatunsa kafin ta ce "Let me do something". Shiru ya yi bai yi mata magana ba, ya dai zuba mata idanu, shi ya mance da cewa ita ma babbar likita ce kamar daddynsu, sai da ta ce bari ta yi mashi wani abin ne yasa ya tuna ashe ita ma babbar likita ce sosai, dan haka sai ya miƙa mata hannun ya bita da idanu kawai.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara yi mashi aiki, duk wani magani da zata zuba mashi sai ta ɗago kai ta ce mashi sannu, dan tasan da akwai bala'in zafi ba kaɗan ba, bare kuma yanda hannun ta ɗauki lokaci, ta jiƙa sosai ciwon, dole zai sha zafi, sai dai kuma shi wayarsa ma ya ɗauko yana latsawa da hannu ɗaya, a cewarsa duk zafinta bata kai harbin bullet zafi ba, dan haka shi bai ga abin cewa da zafi a nan ba.

Haka gwaggo ta yi mashi treatment na wajen da kyau da kyau, sannan ta ce ya kwanta bari ta duba lafiyar jikinsa gabaɗaya. Sai sannu family suke yi mashi, sam bai ɗaga idanu ya kalli ko mutun ɗaya daga cikinsu ba, dan yana cikin wani irin yanayi wanda shi kaɗai yasan me yake ji bawan Allah, da yake shi kullum a siffa ɗaya yake ne yasa sam sam ba wanda ya gane cewa yana cikin tsananin damuwa, kullum face nasa a haɗe take, baka gane farincikinsa bare bakin ciki, harta TRIPLETS nasa ma basu iya rabe yana cikin farinciki ko bakin ciki, saboda kullum dai yanda yake a haka yake babu canji.

Bai yi wa gwaggo musu ba, ya miƙe ya kwanta a saman bed ɗin da kyau, dan a agajiye sosai yake. Duba lafiyar jikinsa ta fara yi ita da Areef, ya rufe idanuwansa yana tunanin duniya.

"Momma where is Meesha?". Kamar daga sama su gwaggo suka ji sanyayyar muryarsa ya gefo masu wannan tambayar, ya yita kuma idanuwansa a lumshe.

Kallon kallo jama'ar cikin bedroom ɗin suka fara yi, ita kanta gwaggon sai da gabanta ya faɗi na jin tambayar nan tasa. Ganin yanda suke kallon kallo a tsakaninsu ne yasa Aseef da Areef har suna haɗa baki wajen cewa "What is happening? Where is our Rimsha? Ya naga kuna ta kallon juna, is there any problem?". Kamar abin haɗin baki suka jera masu tambayoyin, Areef kam har da mikewa tsaye yana binsu da kallo, dan wlh idan wani abin ne ya sameta yau za'ayi yaki ba kaɗan ba, saboda ita ɗin tamkar bugawar zuciyar TRIPLETS ɗin take, dukkansu ukun suna tsananin sonta fiye da tunanin mai tunani, akwaita da mugu mugun shiga rai na wuce misali ne.

Kara datse idanuwansa gam Lion ɗin ya yi, kansa na yi mashi ciwo sosai, yana jin duk abin da suke faɗa, amma ya kasa buɗe idanuwansa, dan ƙwaƙwalwarsa ba zata iya ɗaukar wani abin ya sami Rimsha ba, shiyasa ma ba zai buɗe idanu ba bare ya ga fuskokin family su kara jefa shi cikin wani raɗaɗin.

"Areef nothing happened to her, just she is not feeling well, tana ma cikin bedroomna tana kwance, she is sleeping now". Cewar gwaggon kenan.

Kusan a tare Aseef da Areef ɗin suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da sauri Aseef ya ce bari ya je ya ganta ya tabbatar. A tare suka fita da Areef ɗin dan su je su dubata. Ita kuma gwaggo, sai ta cigaba da duba ɗan nata, Dr Salman ne ya ce su fita su bar Lion ɗin ya huta, dan ya gaji matuƙa. Haka kuwa aka yi, duk suka fita, ita ma gwaggon da ta gama yi mashi duk abin da ya dace, sai ta fita ta kyale shi, yana jin fitarta, amma bai ce mata komai ba, saboda yana da bukatar ya huta ɗin ne, ga salloli na la'asar da mangariba a kansa bai samu ya yi ba. Ransa cike da tunani barci ya yi awon gaba da shi, bawan Allah ya yi matuƙar gajiya na wuce misali, dole ne ma barci ta ɗauke shi.

A ɓangaren Aseef da Areef kuwa, da suka je suka tabbatar yes Rimsha tana nan tana zuba barci, sai suka ji wani irin sanyi da salama ya lulluɓesu. Hakan tasa suka zauna a bakin bed ɗin na gwaggon suna ɗan tattaunawa a tsakaninsu. A gabaɗaya cikin family an rasa wanda zai iya tambayar Aseef ya aka yi ya je shi Daular Mutuwa? Ga dai tambayar a cikin ran kowa, amma sun kasa fito da ita fili. To meye dalili? Alƙalamin PRINCESS TEEMA ce kawai zai iya rubuta maku dalilai, dan haka ku biyoni!!

A nan family suka shigo suka samesu. Da mamaki ɗauke a fuskar gwaggo take tambayar Areef ɗin me ya sami Ayla kuma?.

Kallon daddyn Jelly Areef ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, cike da tausayi ya ce "Sorry uncle, ta yi loosing pregnant nata ne, momma ki bata taimakon gaggawa, dan babu abin da muka yi mata, babu wani drugs or injection da yake a tare da mu, so tana cikin mawuyacin halin, help her". Ya kai karshen maganar tare da sa kai ya fice daga ɗakin, a lokacin ita ma Jehan ita da Anaya duk suna bedroom nasu suna barci, sun ci kuka ne sun ƙoshi, har barcin wahala ta yi awon gaba da su bayin Allah.

Haƙiƙa gwaggo ta tausayawa Aylar na ganin halin da take a ciki, dan haka sai ta ce Aseef ya kawo mata kayan aikinsu bari ta dubata, daga nan kuma ta yi wa daddyn Jelly ban hakuri. Kowa daga cikinsu Abba sai da ya bashi hakuri. Ba shakka ya ji zafin fitar cikin na Ayla, dan yana tsananin son yara, Jelly kaɗai gare shi, ita ma ta yi aure, so yana tsananin kaunar yaga ya sake samun yara, amma kuma farincikin dawowar Aylar ta fi yawa a cikin zuciyarsa sama da zubewar cikin, kuma shi dama mutun ne mai yarda da ƙaddara, dan haka ya yarda da ƙaddararsa, ya kuma rungumeta hannu bibbiyu, ya ce babu komai, haka Allah ya ƙaddara, dama ai ba su suka bawa kansu cikin ba, Allah ne ya basu, dan ya karɓi abinsa ba zasu ji babu dadi ba, shi ya godewa Allah ma da yasa ta dawo gida da ranta, iya wannan ma ya ishe shi murna, kuma dole ya godewa Allah da yadawo mashi da ita da ranta.

Da haka Brr Naurat ta ce kowa ya je ya yi sallar issha, tun ɗazun aka yi sallah su suna nan suna zaune. Haka suka watse kowa ya nufi bedroom nasa, dan su je su yi sallah, Dr Salman kuma suka tafi tare da Akil, ita kuma gwaggo Aseef ya kawo mata kayan aiki ta fara duba lafiyar Aylar, dan ta lura sai anyi mata wankin ciki ma.

Bayan ta gama sai ta yi mata alluran barci dan ta sami hutu. Daga nan ita ma ta mike ta fita izuwa bedroom nasu Jehan dan ta yi sallah, ta bar Brr Naurat tare da Aylar da Rimshar.

Tana shiga bedroom ɗin ta tarar da Areef zaune a saman bedside drawer kusa da Jehan, ya zuba mata idanu yana ta kallonta, ita kuma tana zuba barci, ya yi wanka ya canza kayan jikinsa izuwa na barci, da alama ya yi sallah ya ci abinci.

"In tasan maka ita ne Areef?." Cewar gwaggon, ta yi maganar tana nufar hanyar toilet dan ta yi alwala. "A'a momma ki barta, i want to see her ne ma kawai yasa na zo dubata, na yi missed nata over, yau ina gajiye sosai, ba zan iya da rigimarta ba, dan haka kyaleta sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa, ko kunyar gwaggon bai ji ba ya ɗan duka ya sumbaci Jehan ɗin a kumatu, sannan ya juya ya fice, ita ma gwaggon ko a jikinta ta shige cikin toilet abinta.

After some hours, gabaɗayansu sun yi barci, dan a tsananin gajiye suke, family kowa yana cikin bedroom nasa yana zuba barci, masu aikin dare suna yi, yau suma family za su yi barci a cikin salama, dan tun da TRIPLETS suka tafi basu samun barci mai kyau, a kaikaice suke yin barcin, to yau za su sami barci mai cike da daɗi.

Misalin karfe biyu yunwa ta farkar da Jehan, dan bata ci abincin dare ba ta yi barci, fitowa ta yi izuwa palon kasa, abinci ta ɗebo a plate, sam bata da labarin mijin nata ya dawo, komawa palon sama ta yi ta zauna a saman sofa, cikin nutsuwa ta fara cin abincinta tana yamutse fuska tamkar mai cin magani, ita kuwa Anaya sai zuba barci take yi, ita bata farka ba. Kamar daga sama ta ga Lion ya fito daga cikin bedroom nasa sanye da farar jallabiya a jikinsa, sai yanzu ya samu ya biya bashin sallolin dake a kansa, tun da ya yi barci sai karfe 1 ya farka, wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya zo ya fara biyan bashin sallolin dake a kansa, bayan ya kammala ne ya fito dan ya je ɗakin gwaggo wajen Meesha.

Ba karamar tsorata Jehan ɗin ta yi da ganinsa ba, da farko ma ta ɗauka aljani ne, saboda dare ne kuma ga shi da farar jallabiya, bugu da kari bata san sun dawo suna gidanba, sannan ya saki dark black cuirly hair nan nasa bai ɗaure ba, ga shi da tsawo sosai dama, ai dole ya bata tsoro.

A dubu ɗari ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin kurma ihu, sai gani ta yi ya shige ɗakin gwaggo bai ko kalli in da take bama, hakan yasa ta fahimci lallai sune suka dawo, dan haka sai ta ajiye plate ɗin abincin nata, da sauri ta sauka kasa izuwa bedroom na Areef.

Babu ko sallama ta faɗa cikin ɗakin, wani irin duhu ne a cikin ɗakin, kun san shi baya shiri da haske dama, idan zai yi barci a duhu yake yi, hakan tasa bata iya ganin komai, lallaɓawa ta yi a hankali ta nufi wajen switch, da kyar ta gano switch ɗin ta kunna wutar, nan take haske ya gauraye ko'ina a cikin bedroom ɗin.

Cike da tsohon abin da zata iya cin karo da shi a saman gadon ta ɗago kanta, a hankali ta kai kallonta wajen. Yana kwance cikin kyawawan kayan barcinsa yana zuba barci abinsa, ya rungumi pillow a kirjinsa, ya kuma ɗaura kafafunsa a saman pillow ɗaya. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, ta kasa motsawa daga wajen, ta zuba mashi idanu sai kallonsa take yi.

Saboda wannan haske da ta kunna mashi ne yasa ya ɗan fara motsawa yana son farkawa, ganin hakan yasa ta yi maza ta kashe wutar tare da juyawa ta fice daga ɗakin da sauri tana hamdala ga Allah.

Shi ma Aseef duk rigimarsa na son ya yi dis virgin ɗin Akila, to yau dai ya shafa mata lafiya, dan dukkansu a tsananin gajiye suke, sai barci suke zubawa babu kakkautawa, sun wahala ne over.

Jehan na fita ta koma palon saman, abincinta ta ɗauka ta cigaba da ci, tsabar murna na ganin mijin nata, sai ta ji abincin ma ya kara daɗi, haka yasa ta ci sosai ta ƙoshi, tun ranar da suka tafi rabonta da ta ci abinci dayawa haka, bayan ta ƙoshi ne ta ɗaura plate ɗin a saman dining table dake a cikin palon, sannan ta wuce cikin bedroom nasu, yau barcin nishaɗi zata yi, ranta fes mijinta ya dawo.

Shi kuma Lion bakinsa ɗauke da sallama ya shiga ɗakin gwaggon. Gwaggo na a saman dadduma tana sallah, Brr Naurat tana kwance saman bed tana barci, ga Rimshar a kusa da ita tana barci. Ɗakin nasu da akawai hasken wuta sky blue.

Saman bedside drawer ta ɓangaren da Rimshar ke kwance ya je ya zauna. Hannu ya kai ya ɗan janye bargon da Brr Naurat ta rufa mata. Da kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci bata da lafiya, dan ta yi muguwar rama sosai. Shiru ya zuba mata idanu yana tunanin to me yake damunta?.

A hankali ta fara motsawa, alamar tana son farkawa, hannu ya kai ya shafi face nata, hakan yasa ta farka mai gabaɗaya. Tana waro idanunta kai tsaye sai cikin nasa idanun. Turo baki ta yi tare da kawar da kallonta tana faɗin "Kai kuma waye? Daga ina da zaka zo ka tashe ni, kuma ka wani tsareni da wasu shegun idanu kamar na wancan mutumin da yake zama a palon kasan nan (Dr William)". Dama kunsan ciwon nata yasa tana ji da bala'in masifa, duk zafin Jehan sai da ta sarara mata, to yanzu ma tana tashi ta hau surfa masifa, ba gaira ba dalili.

Da farko Lion ɗin ya zaci magagin barci ne, sai daga baya ya fahimci babu magagin barci a tattare da ita, tana nan normal, hakan yasa ya fahimci wannan shi ne rashin lafiyar da take fama da shi kenan. Ko kaɗan bai ɗaga hankalinsa ba, dan shi ya fahimci menene matsalar tata, dama kuma already ya dawo da nufin ya yaki wancan matsalar, dan haka sai bai damu ba, godiya ga Allah ma ya yi da ya sanya ya dawo ya sameta ba'a dauketa ba, dan haka sai ya riko hannunta ɗaya, kasa kasa ya ce "Zo muje ki rakani to, sai na gaya mani wanene ni da kuma abin da yasa na tsareki da idona".

Kallon sama da kasa ta yi mashi kafin ta ce "Ni ka sake mani hannu hai, babu in da zanje, kuma ka bar mana ɗakinmu". Dama kunsan bata yarda kowa ya raɓeta sai Brr Naurat, duk wanda ya zo kusa da ita bala'i ne yake tashi ya tsaya gam, to shima surfa mashi bala'i ta rinƙa yi a kan ya bar masu ɗakinsu.

Nisawa ya yi tare da kai ɗan bakinsa ya sumbaci lallausan kumatunta, sannan ya miƙe ya nufi hanyar fita, yana jiyo muryarta tana faɗin "Mugu da zaka wani taɓani, ina ruwanka da ni?".

Bai kulata ba ya fice abinsa, duk abin da suke yi gwaggo dake saman dadduma tana jinsu, hakan yasa ta kara tsananta masu addu'a na samun lafiyar Rimshar. Shi kuma Lion yana fita ya koma bedroom nasa, ainahin wayarsa ya ɗauko, ba wanda ya saya a Ilorin ba, na ainahin ya ɗauko tare da kunnata. Duba time ya yi, karfe 2:40am dai'dai. Number his excellence ya kira, wayar ta yi ringin har ta kusa yanka sannan ya ɗaga.

A takaice Lion ɗin ya ce mashi "Zan shigo Usa gobe, ina da bukatar lokacinka at least 1 hour, so sai ka shirya". Yana gama faɗar hakan ya katse kiran, duk da ciwon dake a jikinsa, hakan bai hana shi ya tashi ta fara shirin tafiya ba, acewarsa, gara kawai ayita ta kare.

Duk wani abin da zai buƙata ya shirya a cikin trolleynsa, sannan ya fito ya nufi bedroom na gwaggo, ita kaɗai ya gayawa zai tafi yanzu ba sai anjuma da safe ba, ta so ta dakatar da shi, ta so ya bari ya huta, amma ya nuna mata yana sauri, dole ne ya isa Washington gobe goben nan, dan haka kawai ta bishi da addu'a.

Ko TRIPLETS nasa bai gayawa ba, a cikin wannan dare ya fita daga gidan tare da Donal, a hanyarsu ta zuwa airport ne ya sanar da Donal ɗin cewa zai turo likita dan a ɗaura kafar Mark, so ya kula da shi sosai, bawan Allah ya azabtu matuka, baki ma ba zata iya faɗar azabar da Mark yake a ciki ba, kowa dai yasan yanda karaya take, idan baka taɓa karyewa ba, to an taɓa yi a kusa da kai, tana da matuƙar raɗaɗi na azaba.

A takaice dai Lion da private jet nasa ya bar Nigeria, dama tun da su TGA suka zo jirgin tana airport babu wanda ya taɓata, to da yake yanzu tafiya ce ta ujila, sauri yake yi, sai bai tsaya yin booking na jirgin kasuwa sun ɓata mashi lokaci ba, kawai ya yi amfani da nasa. Ya bar Nigeria karfe 4:30 na asuba, sai addu'a gwaggo take zuba mashi sosai da sosai, su kuma TRIPLETS sai barci suke zubawa a tsananin gajiye, basu da labarin Lion ya bar kasar!.

Yana dira Washington Tga ya zo ya ɗaukesa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login