Showing 45001 words to 48000 words out of 270744 words

Chapter 16 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2935

a goshinsa, nan take ya fashe wajen, jini ya fara tsastsafa. Salati Ummin ta fara yi, komai na cikin ɗakin Aafiar ta yi watsi da shi, har kayan jikinta ta cire, ya rage daga ita sa underwears, suma sai ƙoƙarin ciresu take yi.

Sam Akil bai damu da ji mashi ciwo da ta yi ba, karisawa cikin ɗakin ya yi tare da yin bismilah ya damkota da karfi, kokawa ta fara yi da shi da iya karfinta, shi ma saka karfi ya yi sosai ya murɗe hannayenta izuwa baya, sannan ya kaita kasa, dan ta kwanta, hakan zai taimaka mashi wajen danneta ya yi mata addu'a.

Ummi kam ban da kuka babu abin da take yi.

"Ummi jeki waje". Cewar Akil ɗin, dan ya lura idan bata bar wajen ba, ba zata dai'na kukan ba. Jiknta har kerma yake yi ta koma palo ta zauna. Shi kuma ya fara tofawa Aafia ɗin adduo'i har barci ya ɗauketa a wajen.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali na ganin ta yi barci, runtse idanuwansa ya yi yana tunanin meyake shirin faruwa da FAMILYNSU ne? Ayla ta ɓata, gwaggo ta kira waya cikin tsananin tashin hankali ta sanar masu Lion yana asibiti tamkar babu rai a tattare da shi, yanzu kuma ga Aafia ta haukace, anya kuwa ba wani gagarumin bala'in bane yake shirin afkuwa? Anya lafiya kuwa? Meyasa kuma dukka abubuwan a lokacin guda rana ɗaya?! Sannan a hankali abubuwan suna ta shafar kowa da yake a cikin familyn? Wai shin menene gaskiya? Waye zai warware mana wannan rikicin?........ Alkalami PRINCESS TEEMA ce kawai zai warware maku menene ainahin abin da yake shirin faruwa dama wanda yake faruwa a yanzu, ku dai ku kasance tare da ni!!.

Ganin ta yi barci ne yasa ya saketa tare da fitowa palo wajen Ummi, har lokacin sai kuka take yi, hakuri ya bata tare da tambayarta ina Dr Nawid yake bari ya duba jikinsa, sannan zai wuce gida da Aafiar dan a ragewa Ummin wahala.

To kawai ta ce mashi, sannan ta wuce gaba zuwa ɗakin Dr Nawid ɗin, bayanta ya bi cike da tausaya mata.

Baki ɗauke da sallama suka shiga, yana kwance tamkar yanda yake kullum, idanuwansa sun koma yanda suke, kamar basu taɓa canza launi ba, wannan hayaki da Aafia ta gani ta zauce, duk sun dai'na fita, komai ya ɓace, ya koma kamar yanda yake.

A gefen gadon Ummi ta zauna, shi kuma Akil ya matso kusa da shi da nufin ya tofa mashi adduo'i. Kallo ɗaya ya yi mashi ya san cewa rai ya yi halinsa, babu rai a tattare da shi. Zaro idanu ya yi, sannan ya kalli Ummi dake ta faman ruwan hawaye, nan take zuciyarsa ta karaya, ya ji ba zai iya gaya mata cewa Dr Nawid ya rasu ba, dan shi ne kaɗai gareta, idan ta ji zuciyarta zata iya bugawa wlh, Innallilahi wa Innallilahi ilaihir raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil.

Daurewa ya yi ya tofawa gawar addu'a, sannan ya ce mata yana zuwa, to kawai ta bishi da shi.

Fitowa waje ya yi ya kira Abbi a waya, ya sanar mashi wlh Dr Nawid Allah ya yi mashi rasuwa, Allah ya karɓi abinsa. Ba karamin girgiza Abbin ya yi da jin wannan bakin labarinba, dukkansu Ummin kawai suke tausaya, baiwar Allah, da ma ace tana da wasu yara ne, to da da sauki, amma shi kaɗai, ga shi Allah ya karɓi abinsa, innallilahi wa innallilahi ilaihir raji'un, yanzu ta yaya za su iya gaya mata wannan bakin labarin? Matar da kullum take zarya a kan rashin lafiyar nan tasa, ko abinci bata iya ci, ta rame fiye da tunanin mai tunani, duk ta fita a cikin hayyacinta, ta firgice kamar ba ita ba, ashe maganar da Dr ya yi wa Aafiar nan shi ne maganarsa ta karshe a duniya, ya ilahi ya lillahi.

Cewa Akil ɗin Abbin ya yi a kan suna zuwa yanzu, amma kada ya bari Ummin ta gane komai. Okey ya amsa tare da katse kiran ya dawo cikin palon.

After some minutes sai ga su Abbin sun iso, har da Abban Imran da daddyn jelly, shi dai Abbo shiru babu shi babu labarinsa, kuma babu wanda ya iya tunawa da shi.

Wayo suka yi wa Ummin, suka ce mata za su tafi da Dr wani asibiti ne mai kyau kafin komai na su ya kammala su wuce kasar India, dan haka ta bi Akil ya kaita gidan Abba ita da Aafia, dan kada a barta ita kaɗai a gidan. Ita dai ta amsa masu da to ne kawai, amma har cikin ranta tana jin ba lafiya ba, gabanta sai faɗuwa yake yi, sai dai bata musa masu ba, ta bi Akil bayan an saka Aafia a motar, haka ya wuce da su izuwa gidan Abba, su Imran kuma, sun ɗauki hanyar Kano dama already.

Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin musulunci, sannan aka shirya shi a cikin likkafani, dan su kai shi makwancinsa kuma gidansa na gaskiya......... To masu karatu zan dakata a nan wajen, sai Allah ya kai mu gobe.

*Yau na san kwakwalwarku zata shiga ruɗu sosai, to ina mai bada hakuri a kan hakan, labarin ne yake a haka, dole kuma zan rubuta abin da na tsara tun farko, ba zan iya canza komai na labarina ba, na san ba zaku so hakan ba, amma ina bada hakuri dai!!*

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E8




Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin musulunci, sannan aka shirya shi a cikin likkafani, dan su kai shi makwancinsa kuma gidansa na gaskiya.

A takaice su Abbi suka kai shi kabarinsa, ma'ana su suka yi jana'izarsa, sai dai duk cikinsu an rasa wanda zai iya gayawa Umminsa ga abin da yake faruwa, sai faman nuku nuku suke yi, dan suna tsananin tausayawa baiwar Allah'n nan.

A ɓangaren su Imran kuwa, sun isa Kano lafiya, kuma sun haɗu da baban Muneer a companynsa, a cikin office nasa, ya yi masu iso.

Ba tare da ɓata lokaci ba Areef ya fara jefa mashi tambayoyi, sai dai Areef ɗin da kallo ɗaya zaka yi mashi, kasan yana cikin tsananin tashin hankali, duk da bai san abin da yake faruwa da Lion ba, amma a jikinsa yana jin lallai ba shakka ɗaya daga cikinsu bashi da lafiya, dan bugawar zuciyarsa sauri take yi tamkar yanda na Lion ɗin take bugawa da sauri, duk ya firgice tamkar ba shi ba, har Imran ya iya ganewa, ya tambaye shi ko bashi da lafiya ne? Ko kuma tafiyar da suka yi a mota mai tsayin ne ya jijjiga shi?.

A'a ya amsa masu da shi, sannan ya ɗaura masu da cewa, shi ai idan ya je kasar da bai sani ba, yana yin tafiya mai tsawo a cikin mota, dan ya zagaye wasu daga cikin states na garin, dama dai Aseef ne ko Lion, sune za'a ce ba lallai su iya jure tafiya mai tsawo a mota ba, dan basu saba ba, ko'ina za su je, to wlh suna zaune a cikin gida, basu fita yawace garinma bare sauran states dake makwabtaka da garin, amma shi ai yana yawo sosai abinsa, su kwantar da hankulansu, kawai dai yana jin jikinsa ba daɗi ne.

Bawan Allah bai san cewa Lion yana kwance a gadon asibiti ba, kuma kamar yanda yake kwance bashi da lafiya, haka shi ma Areef ɗin yake tafiya da ciwo a jikinsa, da alama zuciyoyinsu a haɗe take over.

Kafe masu baban Muneer ya yi a kan shi bai ma san waye daddyn Jelly ba, kallon Imran Areef ɗin ya yi, sai ya yi mashi magana da larabci a kan, su kyale shi da mutumin bari ya gyara mashi zama!.

Da baban Muneer ɗin yaga za su matsa mashi, sai ya ɗauko wayarsa ya yi ƙoƙarin ɗaura videon daddyn Jelly da ya ɗauke shi a media kowa ya gani, ya yi ƙoƙarin cin zarafin familyn Dr Salman kenan. Ganin yana latsa wayar jikinsa har wani kerma yake yi, ga shi kuma sai musa masu yake yi a kan shi bai san wanenen ma daddyn Jelly ba, sai yasa Areef a cikin tunani.

Duk cikin office ɗin, cikin Imran da Irfan babu wanda ya lura da abin da baban Muneer ɗin yake yi, shi kuma Areef ya lura da lallai ba abin arziki yake yi da wannan wayar tasa ba, dan kuwa ga jikinsa sai kerma yake yi, hannunsa sai ɓari take yi, dama haka mara gaskiya yake, duk in da za'aje a zo, baya ɓuya.

Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya fusge wayar da karfi, har wani miƙewa baban Muneer ɗin ya yi tare da nufin ya kwaci wayar, wani irin wawan mari Areef ɗin ya ɗauke shi da shi, nan take hakwaransa biyu suke fita daga bakinsa. Tsawa ya daka mashi a kan ya koma ya zauna, idan ba haka ba, yanzun nan ya yabawa aya zaƙinta, an gaya mashi su sha'anin wasan sa ne?.

Ƙoƙarin gudu ya yi ya fita daga cikin office ɗin, Areef yana daga zaune yasa kafa ya kwashe kafafunsa, sai ga baban Muneer ya zube a kasa wanwar yana baza babbar riga, ya yi shiga ta mutunci tamkar mutumin kirki, ashe dai babbar rigar ce kawai.

"Prof ɗaure mani shi mu tafi da shi, dan jikina duk a mace, i can't do anything yanzu, ina son in je gida first, dan haka mu wuce da shi gidan kawai". Cewar Areef, yana maganar yana duba wayar baban Muneer ɗin. Ganin abin da yake cikin wayar na shirin yin posting na video a media da ya yi ne ya kara ɓatawa Areef ɗin rai, sannan ya kara mashi shakku da zargin baban Muneer ɗin a cikin zuciyarsa, idan ba rashin gaskiya ba, menene na yin yunkurin posting na video daga tambayarka ina Ayla? Da farko ma cewa ya yi shi bai san daddyn Jelly ba, to a ina ya samo wannan video kuma? Ga shi dai daddyn Jelly ne a cikin videon.

Ƙoƙarin kurma ihu baban Muneer ɗin ya yi, dan ma'aikatansa su kawo mashi agaji, sai dai ina, bakinsa ma ya yi muguwar kumbura, saboda hakwaransa guda biyu da suka fita, ga jini da yake malala kamar me, kun san hakori ba wasa ba, fitarta akwai azaba ga zubar da jini, bare ma shi da hakwaran suka fita ba shiri, dama gasu ba kyan gani, duk sun yi baki, saboda busar sigari, nan take bakin ta sunduma suntum, tamkar ruɓaɓɓen alala.

"Areef ni fa ba zai iya ɗaura mutumin nan ba, wannan aikin sai ku". Cewar Imran.

Harara Areef ɗin ya wurga mashi, da dara daran ldanun nan nasa, kafin ya ce "Prof ba zaka canza ba har gobe, ka yi auren ma baka gyaru ba?".

Shi ma hararar ya wurga mashi yana faɗin "Kai kam da ka yi auren ka gyaru ne? Ko dama akwai wanda ya ce maka aure yana gyara mutun ne? Kai ma ai gaka a yanda kake da shegen mugunta kamar Saif, yanzu kawai ka kama ka cirewa mutun hakwara da mari, dan tsabar zafin zuciya".

"Ka dai'na cewa kamar Saif, just call me Saif ɗin kawai kai tsaye, kuma ni ai ban san me auren bane shiyasa ban gyaru ba, amma kai fa? I think ma your wife has pregnant ma ko?". Cewar Areef ɗin.

"A'a Jelly bata da ciki, muna dai fatan samu, kai ba zaka dai'na saka mani ido ba ko? Wai waye ma ya gaya maka ni ma na san menene aure?".

Allah sarki shi dai Irfan, sai binsu da idanu kawai yake yi, yana ɗan murmushi, dan bashi da ta cewa, bai ma san me auren ba bawan Allah.

"Ka san aure mana, kai ne ma kasa na fara sha'awar yin auren".

"Ni kuma?". Ya faɗa yana zaro idanunsa irin na Jellyn nasa.

"Yeah kai mana, ko na tuna maka wen aka yi hakan ne?".

Ganin abin kamar wasa Imran ɗin yake yi, sai ya ce "Yeah tunan mani".

"Time da ka yi dis virgin na matar taka a gida, a time ɗin ka fara saka mani sha'awar yin aure, and then yan da kuke da matar taka, rigimammiya mara jin magana, tana baka wahala, abin yana yi mani daɗi, ina jin daɗin in ga tana wahalar da kai". Ya kai karshen maganar yana switch off na wayar baban Muneer ɗin.

"Wato Areef har gobe ba zaka canza ba ko Areef? Sai mutun ya kalli kamar baka san meyake faruwa ba, amma ka san komai, wato yanzu duk zaman da na yi da Jelly a gidan kasan komai ko?, Amma ban taɓa tunanin haka ba, sai mutun ya ganka kamar wani malamin islami, har ma jin daɗi kake yi idan Jelly tana wahalar da ni ko?".

Mikewa ya yi yana ɗan bincika cikin office ɗin ko zai samu igiyar da zai ɗaure baban Muneer ɗin, yana tafiya yana faɗin "Ni ai har abada ba zan canza ba, an gaya maka C.I.A wasa ce? Ai ni da ido ma idan naga mutun nasan ina ya dosa, just kawai kai ne ba zaka gane nasani ba, saboda already basaja a cikin jinina take, zan iya yi maka basaja kamar mace, kuma mu zauna da kai a haka".

"Da wannan murɗaɗɗen jikin naka ne zaka iya zama macen". Cewar Irfan, ya yi maganar da mamaki a kan face nasa, ya ga ne damatsan hannun Areef ɗin ma kawai abin kallo ne, sannan ga shi da tsawo da cikar halittar namiji, sannan ya ce mashi zai iya basaja a matsayin mace? Ai dole ya tambaya da mamaki a saman face nasa, dan ba gym na wasa shi ma Areef ɗin yake yi ba, jikinsa ta murɗe sosai.

"No Irfan, idan nace basaja a matsayin mace, ba ina nufin zan ɗauki kayan mata or something like that in yi amfani da su ba, you are not a C.I.A, that's why ba zaka gane ba, i mean zan iya zama da kai cikin raunin zuciya like mace, you will feel like bani da wayo, ina da raunin zuciya, and ina da ragonta, like yanda mace dai take, shi ne nufina". Jinjina kai Irfan ɗin ya yi, sai yanzu ya gane nufin Areef ɗin.

"Kai Prof waye ma ya ce ka ɗauka mani matata jiya ka tafi da ita? Na baka izini ne?". Ya yi maganar yana bubbuɗe drawers dake a cikin office ɗin na wajen ajiyar takardu.

"Waye ya ce maka ni na ɗauke ta?".

Harara ya sake wurga masu kafin ya ce "Ban samu peace of mind a daren jiya ba har sai da na bincika a motar waye ta biku, na san Lion ma ya bincika, kuma sai ka yi mashi bayanin dalilin da yasa ka kwashe mana bebs namu, ka hanamu jin daɗi".

Dariya sosai Imran ɗin ya yi, sannan ya ce "Ka ce jiya na ɓata maka harka? To ni nama san ta biyo ni ne".

"Ka dai ɓatawa Aseef harka, kuma wlh ba zai kyaleka ba, dan tun safe yake rigimar a bashi matarsa, kuma tun jiya da safe ya gaya mani ba zai kyaleta ba, idan suka dawo daga unguwa, sai ya yi dis virgin ɗinta, shi ne ka rusa mashi shirinsa ba? Zaku haɗu ne wlh, kasan halinsa, ni matata yarinya ce ai, sai ta girma, zan dai yi ta tsokanarta".

Wani irin dariyar iyashege Imran ɗin ya yi yana faɗin "Au dama haka aka yi? Kace Allah ya kuɓutar mani da sisterta, baiwar Allah, da yanzu tana can tana fama da azaba, da Aseef ya wahalar mani da ita".

"Au kai ba sister tamu ka azabtar ba kenan?". Cewar Areef

Shi dai Irfan tamkar babu shi a cikin office ɗin, shiru abinsa, sai binsu da idanu yake yi, sai da ya ji sun shigo da hirar Akila da Aseef ne ya ji zuciyarsa ta yi bakinkirin, sai ya ji dama bai biyosu ba, su kuma da alama Imran ya mance da cewa Irfan ɗin shi zai auri Akilar a baya, shi dama Areef bai san waye zata aura aka fasa auren ba!.

"A'a ni ban yi wa sisterku komai ba, ita ta ce mani tana son baby, ni kuma na bata, amma ina da tabbacin Akila bata cewa Aseef tana son baby ba, kawai zai azabtar da yarinya dan mugunta ba? To Allah ya kama shi, ta gudu ta koma gida". Cewar Imran.

Hawa sama table Areef ɗin ya yi yana ƙoƙarin kwance camerar dake a cikin office ɗin, ya ce "Jalilar ce ta ce maka tana son baby? Yarinyar da ita da kanta ma baby ce, wannan a ina zata iya renon yaro? Ita kanta yaushe ta gama kuka ana rarrashinta? Ai da ita da Rimsha ni ban san waye gwamma ba, kai dai prof ka ji tsoron Allah, ka dai'na azabtar da ƴar mutane, kada ka je ka bata ciki, wlh wahala kawai zaku sha".

"Ai jelila ba zata ɗauki ciki yanzu ba In Sha Allah, dan idan ta ɗauki ciki a yanzu, to na shiga uku, ta bakin naka ne, yanzu haka idan ta fara yi mani kuka, to sai na yi zaman rarrashi, ina ga kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login