Showing 111001 words to 114000 words out of 270744 words

Chapter 38 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2965

har dukkansu, to a lokacin Josephine ɗin sun kiɗime, sai suka bamu ɗan autanku a maimaƙon ɗan farin, har mun fara yin tsafi da shi, sai Uwargijiyarmu ta ce ai wannan iyayensa basu bada shi ba, ba shi ne aka bada ba, dan haka ba zai yi aiki ba, already kuma mun fara taɓa ƙwaƙwalwarsa, hakan yasa muka dawo da shi muka ɗauki babban yayanku wanda har lokacin yana ɗaure da white agogonsa na nuna cewa shi ne babba, yaro na farko da muka ɗauka Mahaifiyarku bata cikin hayyacinta, da zamu dawo da shi kuma tana a cikin hayyacinta, tun ɗaukarsa da kwana biyu muka so mu dawo da shi, amma ba dama, dan kullum tana a tare da ku, ganin hakan ne yasa muka ɗan hakura muna jiran wata dama da zata zo sai mu ɗauke shi. A lokacin da ta kaiwa William yaran, mune nan muka sanya William ɗin ya daki JAMES da sanda a kai, hakan ne ya bamu damar ɗaukar babban yayanku, muka dawo maku da ɗan autanku da muka ɗauka da farko wato Michael, so mu ba wani canza ku da muka yi, ita ma Josephine da wannan taɓa ƙwaƙwalwar Michael ɗin da muka fara yi ne ya bata damar samun hanyar baku kariya ai, so a takaice Michael shi ne wanda muka fara ɗauka, daga baya muka dawo da shi muka ɗauki yayanku, wannan dalilin yasa kaga Michael ƙwaƙwalwarsa ba'a dai'dai take ba, mun rigada mun birkita kwakwalwar mun fara yin tsafi da shi ne, kai baka yi mamakin idan kun tambayi William menene ainahin musabbabin ciwon Michael sai ya ce maku haka aka haife shi ba? Ai shi yasan komai, a gabansa aka yi komai, kawai yaki gaya maku ne, dan ma kada ku gane ba shi ne ainahin mahaifinku ba, William na ainahi yana kungiyarmu! Shiyasa ko wani asibiti da kuka je suka kasa gane me matsalar kwakwalwar ta Michael ɗin...........".

Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin yanda waɗan nan tsofaffi suka zauna suka shirya abu tiryan tiryan babu mistake a ciki, lallai sun cika shahararrun ƴan duniya, musamman shi Jacob Uban William ɗin da ya mutu, ya fi kowa iya tantiranci da haɗama, har da bada yaransa guda biyu, Allah mai iko, yanzu wani irin hukunci ne ma ya dace da waɗan nan azzaluman? A kan neman duniya kawai?.........Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, shi Lion yana nan, su gwaggo kuma suna gida Nigeria, kada kuma ku manta suna a tare da Uncle Herry da William na karya wanda kuma dukka sun kasance mambobine na kungiyar su His excellence ɗin, kuma ga Lion ya tirke kakansa a nan ya tonawa kungiyar tasu asiri, kuna ganin ƴan kungiyar za su barsu kuwa? Kuna ganin ba za su yi amfani da William da Uncle Herry su cutar da su gwaggo ɗin da suke gida ba kuwa? Kun dai ji Anderson ya yi umarnin a kashe Rimsha! Ga kuma garkuwanta Lion a nan ya taho ya barta, ga shi sun juya mata kwakwalwa ko sallah ma bata sani ba bare ace zata yo askar Allah ya kareta. My peoples PRINCESS TEEMA naku ta amana yau bana jin daɗi, saboda cakwakiyar TRIPLETS har wani zazzaɓi zazzaɓi nake ji! Na barku lafiya❤️

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E19


Date: 29/4/2024


Jinjina kai Lion ɗin ya yi, har cikin ransa ya ji tsananin farinciki na wuce misali, dama shi damuwarsa shi ne ace Aseef ba ɗan uwansa bane, ya fi kaunar Aseef fiye da kansa, Aseef ɗan lelensu ne, to yanzu tun da Aseef ya tabbata pleasure su ne jininsu ne Alhamdulillah, har ya ji ya kara samin karfin gwiwa sosai da sosai, ya kara samun nutsuwa.

A hankali ya ɗago da dara daran idanuwansa, kai tsaye sai kan face ɗin kakan nasa ya sauke kallonsa. Shiru ya zuba mashi idanuwa yana kallon yadda yake yi, tamkar wanda aka shake haka kakan nasa yake yin acting.

Ko sannu Lion ɗin bai ce mashi ba, ya bishi da kallo kawai yana ganin ikon Allah. Shakesa suka yi da karfin gaske, idanuwansa har suka firfito waje, suka yi jajir kamar jini, wasu jijiyoyi sirara a saman idanun nasa suka bayyana, sai fafutukan neman numfashi yake yi, ko da sunan wasa Lion bai yi yunkurin taimaka mashi ba, saboda ya ce dama duk kashe shegu zai yi, sai ya kashesu kamar dabbobi, shi ne yasa ko da sunan wasa bai yi ƙoƙarin taimaka mashi ba.

Da gurnanin kakan nasa ɗin ma ya isha shi, sai ya miƙe ya nufi waje abinsa, dan yana toshe mashi kunne da wani irin gurnani na mai fafutuka tsakanin mutuwa da rayuwa.

Lion ɗin yana fita bai fi da minti biyu ba suka kashe kakan nasa har lahira, sun kashe shi kuma kamar wanda aka bawa guba, bakinsa duk kumfa fari tas yake fitarwa, haka suka yi mashi.

Lion kuwa yana fita gida ya wuce abinsa. Yana komawa ba ɓata lokacin ya kira Areef a waya, wayar ta yi ringing na farko har ta katse bai ɗauka ba, yana can yana ta zuba barcin gajiya, almost karfe 12:30 yanzu, amma basu farka ba, sallar asuba ma da kyar suka iya tashi suka yi, dan fa ba karya sun wahala ne, kwanaki sosai suka ɗauka basu sami barci ba, shiyasa yanzu suke biya bayin Allah.

Sake kiransa a karo na biyu ya yi, cikin magagin barci ya kai hannu ya laluɓo wayar, ba tare da ya duba number wanene bane ya yi picking tare da kara wayar a kunnansa, yana mai kara jawo pillow ya matse a saman kirjinsa.

"Hello". Ya furta cikin murya irin na mai magagin barci.

"What is the time now?". Shi ne abin da Lion ɗin ya gaya mashi. Da sauri ya ɗan waro idanuwansa waje, sai kuma ya sake mayar da su ya rufe. A kasale ya furta "Why Lion? Why are you disturbing me ne? Me zan yi maka to idan na tashi?". Yana magana tamkar Aseef, kasancewar cikin kasale da kuma muryar barci, sai ya zamana kamar mai shagwaɓa.

"Go and kill William now". Shi ne abin da ya ce mashi.

A wani irin dubu ɗari ya mike zaune a saman bed ɗin, hannu ɗaya ya kai saman face nasa yana murje idanuwansa dan ya tabbatar a duniya yake ko dai a cikin mafarki, ya je ya kashe daddynsu kuma? Wannan wace iriyar lukutar bala'i ce da sassafen nan? Anya Lion yana cikin hayyacinsa kuwa? Ko ma dai ba Lion ɗin bane? Ko dai kunnensa bata ji da kyau bane? Sune tambayoyin da yake jerawa kansa, tuni ya nemi magagin barcin nasa ma ya rasa, cikin kiɗima ya ce "Lion is it you?".

Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya sake cewa "Areef i said go and kill William now, sannan Shaikh Sultan is coming, i think ma jirginsu ya kusa sauka, dan tun safe ya taso, zai zo ya yi wa Meesha abin da ya dace, so take care of all those things". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da yake kunna makekiyar Tv dake a palonsa.

Bayan ya kunna Tv ya koma saman luntsumemiyar sofarsa mai zaman mutun uku ya lume a cikinta, saboda laushi, suna mai cigaba da magana da Areef ɗin.

"Lion are you hard what you said kuwa? I should go and kill daddy?! For what reason? Are you out of your sense?". "Done talk! Go and do what i said". Ya kai karshen maganar tare da katse kiransa.

Shiru Areef ɗin ya yi, hankalinsa ya tashi matuƙa, ya za'ayi ace mashi ya je ya kashe daddynsu? Wannan ai ba magana ce da hankali zata ɗauka ba, shi dai a iya saninsa yasan Lion baya shan komai da ya danganci shaye shaye, ko lokacin da suke ji da zafin kansu, lokacin da suka taso jininsu na tafasa, Lion bai yi shaye shaye ba, ɗan gara shi ma ya sha sau ɗaya, yana farawa kuma ya ji ba zai iya ba ya dai'na, Aseef ne yake shan su wine a da can can ɗin ma, shi ma bai wani sha sosai ba ya dai'na, to yanzu ko Aseef zai ce a je a kashe daddynsu ne? Amma kuma da ya tuna cewa Lion baya yanke hukunci haka kawai, dole sai da wata ƙwaƙkwaran dalili, sai ya ji cewa zai iya kashe daddyn nasu.

Yunkurawa ya yi jikinsa duk a tsananin mace, sai zafi gaɓɓansa suke yi mashi. A hankali ya zuro da kyawawan fararen kafafunsa kasan bed ɗin, sai hamma yake yi yana yamutse fuska kamar wanda ya ga wani abin kyama, sam bai so tashi daga barcin nan a yanzu ba, kawai Lion ya zo ya wani tashesa ba gaira babu dalili.

Har zai mike sai kuma tunanin number da aka kirashi da shi ɗin ta faɗo mashi. A hanzarce ya jawo wayar tasa tare da sake dubawa, ba shakka ainahin number Lion ɗin ta Washington ne, da shi ya kira shi, sake waro idanu ya yi yana tunanin yaushe Lion kuma ya tafi Washington? Allah mai iko. Ƙoƙarin sake kiran number ya yi, sai dai babu network, wurgi da wayar gefe guda ya yi tare da miƙewa dan ya nufi toilet.

A hankali yake ɗaga kyawawan kafafunsa, haka ya shiga cikin toilet ɗin.

After some minutes ya fito ɗaure da farar towel a ƙugunsa mai shegen kyau, ga wani ɗan ƙaramin kyakkyawar towel ɗin nan a hannunsa yana goge gashin kansa.

A gaban mirror ya tsaya yana ƙoƙarin shafa lotions nasa, sai zuba hamma yake yi alamar yunwa yake ji. Yana ɗago ash eyes nasa ta cikin mirror suka yi ido huɗu da ita, tana tsaye a bakin kofar shigowa ɗakin, ta rungumo hannaye a kirjinta, jikinta na a sanye da wandon jeans baki da T-shirt fara kal, kayan sun zauna a jikinta da kyau da kyau, sun fito mata da ainahin kyakkyawar dirin da Allah ya yi mata, ta ɗan ɗaura ƙaramin veil a kanta, sai zuba kamshi take yi, kyawawan kafafunta na a sanye da flat shoe mai matuƙar kyau da tsada, face nata babu make up sam sam, ainahin natural beautynta ne ya bayyana, kyakkyawace ta gasken gaske, ita da Rimsha idan ma suka yi kwalliyar basu kyau, dan kwalliyar rage masu natural kyansu take yi.

A ɗari ya juyo da kyau, dan ya kalli shin ita ce da gaske?. Ba shakka ita ce, ta zuba mashi idanu tana ta kallon shi. Kasa magana ya yi, saboda wani irin abu da yake fusgarsa a kanta, ta tafi da imaninsa, sai ji ya yi gabaɗaya ya nemi gajiyar da kasalar dake a jikin nasa ma ya rasa, har wani sanyi ya ji a cikin zuciyarsa, tamkar wanda aka jefawa dutsen kankara a ciki.

"Yah Areef gwaggo tana kiranka". Shi ne abin da ta faɗa, ta yi maganar cikin sanyin murya, ta kai karshen maganar tare da juyawa da nufin ta fita daga ɗaki.

"Ji mana ƴan mata". Ya faɗa cikin harshen Hausa, sai dai kana ji kasan bai iya hausa ba, iya word ɗin kawai ya iya faɗa, ita ma ba dai'dai da kyau ya faɗeta ba, sai Allah ya san mashi daga ina ya jiyo wannan kalmar kuma.

A hanzarce ta juyo tana kallon shi, cike da mamaki ta ce "Dama ka iya hausa ne?". Shiru ya ɗan yi kafin daga bisani ya ce "What is the meaning of the word? I don't the meaning, and i didn't understand what you're saying".

(Kai amma Areef ɗan duniya ne!😂 Ashe ma bai san ma'anar abin da ya faɗa ɗin ba😂 yaran gwaggo nan sai dai Allah ya shirya😂)

Harara ta wurga mashi da waɗan nan dara daran fararen idanun nata, ashe ma ko manar kalmar bai sani ba, shi dai kawai ya faɗi abinsa, yanzu da zagi ne kuma fa? Kai Areef akwai neman magana, haka take faɗa a cikin zuciyarta.

Shi kuwa wannan harara da ta wurga mashi ɗin ba ƙaramar kara nutsar da shi cikin kogin kaunarta ya yi ba, alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Make mashi kafaɗa ta yi tana faɗin "Iya kiranka kawai gwaggo ta ce nayi, bata ce na zo na zauna ba". Ta kai karshen maganar tare da ɗan murguɗa mashi ɗan ƙaramin bakin nan nata.

Cool murmushi ya saki yana faɗin "Haba mana, wai baki missing nawa ne? Please come now, idan baki zo ba Allah zan zo har gaban momma ɗin na kamaki".

A takaice ta ce mashi "To sai ka zo kamani ɗin". Ta kai karshen maganar tare da juyawa abinta, har cikin ranta tana tsananin kewarsa, tana son ta je ta rungume shi, amma sai shegen jiji da kai da shegen jan aji, tun da ta shigo ɗakin kuma ta kasa kawar da kallonta a kansa, dan ya tafi da imaninta, dukkansu TRIPLETS suna da surar jiki mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali sosai, a duk lokacin da ta kalle shi, yana matuƙar tafiya da imaninta sosai, kawai dannewa take yi ta ja ajinta.

"Please my Jehan don't go, come to me my wife, ina kewarki sosai". Ya kai karshen maganar yana kama kunnuwansa da hannayensa dukka biyu, alamar ta yi hakuri ta zo gare shi.

Juyowa ta yi tana faɗin "Ni ba zanzo ba, dan baka yi kewata ba, idan da ka yi kewata ai da kana dawowa wajena zaka fara zuwa, amma baka je ba, ka zo kana ta barcinka kawai baka nemeni ba, dan haka mun ɓata".

Kara ruke kunnuwan nasa da kyau ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Sorry Queen of my heart, na fa je na dubaki kina barci, kema dai kinsan cewa i can't sleep without seeing your beautiful face my baby, please come now". Ya kai karshen maganar kamar zai yi mata kuka.

Harara ta wurga mashi kafin ta ce "To close your eyes". Ba musu ya rufe idanun nasa.

Cikin sanɗo ta lallaɓo ta kariso gabansa, daddaɗar kamshi perfume nata ne yasa ya fahimci ta iso wajen nasa, sai dai bai buɗe idanun nasa ba, yana jiran sai ta ce ya buɗe, saboda baya son ya ɓata mata rai, ya san halin kayassa sarai, sarkin rigimace number ɗaya, yanzu idan ya buɗe idanun ba tare da izininta bama, sai ya zama wata sabuwar rigima.

(Mata mu ɗin na daban ne, yanzu dai ku dubi shekarun Jehan da Areef, yana da 32 years, namiji cikakke mai jini a jika, ga kyau iya kyau, kuɗi iya kuɗi, mulki, isa da taƙama, taurarone shi mai tsananin haske a duniya, ita kuma tana da 17 years, amma take juya shi san ranta, ta sanya shi ya yi mata abu kamar karamin yaro, ji ta ce ya rufe idanu, kuma ya rufe yana ma jiran sai ta ce ya buɗe, Allah mai iko, waye ya taɓa tunanin TRIPLETS zasu biyewa mace har haka?🤔 Macen ma kananan yara, ji dai Rimsha, 14 years ke gareta fa, amma haka Lion yake biye mata, duk wata izzarsa yanzu a waje yake nunata, idan ya dawo cikin bedroom nasa, kamar baby haka yake biyewa Rimsha suna wasa!!! Abin mamaki abin al'ajabi)

Tana karisowa wajen ta faɗa saman kirjinsa tana ɓoye fuska na rashin kunya. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Cikin sanyin murya ya ce "Can i open my eyes now?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a kada ya buɗe.

Hannu ya sanya ya rikota da kyau a jikinsa, kasa kasa ya furta mata why. Ita ma kasa kasa ta ce bata son sa ido ne kawai, ya bari sai ta tafi sai ya buɗe idanun. Jinjina mata kai ya yi alamar okey ba damuwa, sannan ya fara shafa mazaunanta yana faɗin "I really missed over my baby".

Da murya kamar mai raɗa ita ma ta ce "I miss you too my husband". Wani irin sanyi ya ji tana ratsa shi, da kyar ya iya cewa "Please my Jehan ki barni na kalleki mana, please mana my baby".

Jinjina mashi kai kawai ta yi alamar to, ta yi hakan tana mai kai hannunta saman kyakkyawar gashinsa dake kwance a saman kirjin nasa. Da sauri ya buɗe idanun nasa, kai tsaye sai a kanta ya saukesu, ta lafe shiru a saman kirjin nasa.

Kara kankameta sosai ya yi tare da rankwafowa kanta, a hankali ya ambaci sunanta. Amsawa ta yi ba tare da ta ɗago kai ba. "Look at me". Ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan ɗago haɓarta.

Ajiyar zuciya suka sauke a tare kafin ya sake matso da face nasa kusa da ita sosai. Yana son ya yi missing nata, sai kuma maganar Lion ta faɗo mashi a cikin tunaninsa, ya ce ya kashe William. Tuna hakan yasa ya saki haɓar tata tare da rungumeta sosai a jikinsa yana faɗin "My baby zauna ki jirani a saman bed ɗin nan ina zuwa ko?". Okey ta amsa mashi tare da wucewa izuwa saman bed ɗin. Binta da kallo ya yi har ta haye ta kwanta, ta kwanta ta yadda suna fuskantar juna, kusan a tare suka sakarwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login