Showing 261001 words to 264000 words out of 270744 words
dan ya bashi tsaro a wajen jirgin ruwan, ita kuma Rimsha su Mark suka cigaba da tsaron ɗakin da take.
Bayan ya yi wanka ya shirya a cikin three cuter, bai sanya riga a jikinsa ba, saboda yanayin weather wajen da akwai ɗan zafi zafi, kasar tasu akwai sanyi sosai, ga shi nan bakin ruwa suke, sai dai kuma wani ikon Allah wajen da ɗumi sosai kamar ba bakin ruwa ba.
A dai'dai bakin ruwan ya zo ya zauna bayan su Mark sun kawo mashi wata tsadaddiyar kujera daga cikin jirgin, Mark dai har yanzu mamakin zuwansu wannan waje yake yi, ya baro Anayarsa da baby's nasa, sai kewarsu yake yi Lion ya wani kawosu bakin ruwa ya ajiye, kamar ya yi kuka haka yake ji, to amma ya zasu yi? Dole ne su bi umarni.
Aikin latsa wayarsa ya fara yi yana tunanin yakamata ace Rimsha ta farka izuwa yanzu.
Bai kammala dawowa daga cikin duniyar tunanin da ya afka ba kamar daga sama ya ji ihunta.
A dubu ɗari su Mark ɗin suka juyar da kallonsu izuwa wajen ɗakin da take a ciki ɗin, shi ma Lion ɗin miƙewa ya yi tsaye cikin nutsuwa, dan yasan ba komai yasa ta yi ihu ba face farkawa da ta yi ta ganta a bakon wajen da bata taɓa tunanin zata ziyarci wannan waje ba, hakan yasa ta kurma wannan ihu.
Yana ƙoƙarin nufar ɗakin sai gata ta fito da gudu.
Dakatawa ya yi daga tafiyar da yake yi, zuba mata waɗan nan dara daran idanuwan nasa ya yi.
Ita ma dakatawa ta yi daga tunkarosa da gudun da take yi, ta tsaya cak tare da tsare shi da idanu babu ko kyaftawa.
Su kuwa su Mark, ai a dubu suka juya, dan kada su ganta, sai suka juya suka ba su baya tare da sunkuyar da kansu kasa.
Kasa karisowa in da yake ta yi, ta yi mutuwar tsaye ne a wajen.
Ganin bata da niyar karisowa gare shi ne yasa shi ya tako cikin nutsuwa, kafafunsa suna sanye cikin wasu shegun tsadaddun bedroom slippers, ga su farare tas masu kyan gaske.
Yana isa gabanta ya kai hannu ya kyafta mata yatsunsa a dai'dai wajen idanuwanta.
Ina ko kyaftawa bata iya yi ba, tamkar wadda ta yi samar tsaye.
"Meesha are you okey?".
Ya faɗa in a low voice sosai.
Kasa amsa mashi maganar ta yi, ta kafe idanuwanta a kansa kawai tana kallonsa.
Ba komai yasa ta yi wannan sumar tsaye ba face surar jikinsa, tun da suke bata taɓa ganinsa babu riga ba sai yau, bata taɓa kallon waɗan nan ɓul ɓul ɗin kyawawan breast ɗin nasa ba sai yau, hakan yasa ta yi sumar tsaye, taga abin da ya haura sheƙarunta.
Shi kuma bawan Allah sam bai ma san dalilin da yasa ta yi mashi sumar tsaye ba, yaga dai sai kallonshi take yi babu ko kyaftawa. Hakan yasa ya kai hannu ya ɗauketa cancak suka koma saman kujerar da yake zaune ɗin.
Ya zauna da ita a manne ajikinsa, sannan ya kai hannu ya ɗebo ruwa daga cikin tekun ya ɗan yarfa mata a fuska.
Dogon numfashi ta ja tare da sauke a hankali, sannan ta fara aikin kyafta idanuwanta domin ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi bada.
Kyakkyawar dogon hancinta ya ja kafin ya ce. "Lafiyarki kuwa my Meesha?".
Da sauri ta dawo da kallonta a saman face nasa, sai kuma ta fara sauko da idanuwanta izuwa saman Lion chest ɗin nasa domin ta tabbatar da abin da ta gani ɗazun gaskiya ce ko mafarki ne.
Ganin gaskiya ce yasa ta fara bin damatsan hannunsa da kallo, duk mamaki ya cika mata rai, anya yah Saif ɗinta ne kuwa? Ta tambayi kanta, dan taga kyakkyawar kakkarfar surar jikin nan nasa ya gigitata.
Shi kuwa mamaki ta bashi, ya rasa ma me zai ce mata, ga su Mark kuma can a kame sun juya masu baya, ba halin su juyo bayin Allah.
Ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta warware ta dawo dai'dai, sai kuma me? Ai sai ta hau yin murna na wuce misali, yau gata a wajen mafarkinta, bakin ruwa tare da mutumin da take mafarkinsa tun tana karama, mutumin da ta fi so sama da komai nata, kuma ya zo mata a sak irin mafarkin nata, ga shi babu riga, ita kuma da ƙananan kaya, abin ya yi mata daɗin da ba zai taɓa yiwuwa ta manta da shi ba.
Rungumarsa ta yi cikin tsananin farinciki tana mai manna mashi sumbata ta ko'ina a face nasa saboda jin daɗi da murna.
Shi kuwa ya yi shiru ya tsareta da idanun yana ta kallon kyakkyawar fuskar nan tata mai ɗauke da kayatatcen murmushi.
Sun ɗauki ɗan lokaci a wajen da a kallah ya kai awa biyu suna zuba love nasu, kafin ta ce
"Noorish ka kamo mun kifi, ina son in ci gasasshen kifi".
Ɗan zaro mata idanun ya yi. "Meesha me zaki yi da kifin cikin tekun nan? Idan kifi kike so ai sai Mark ya je ya kawo maki fresh ko?".
Kukan shagwaɓa ta saka mashi tana faɗin. "Ni bana son wani fresh, na cikin tekun nan nake so".
Shafa lallausan kumatunta ya yi kafin ya ce. "To ya isa haka rigimammiyata, yadda kikeso haka za'ayi, bari su Mark su kama maki".
Wani sabon kukan ta saka mashi tana faɗin. "Wai Noorish cikin Mark ne a jikina ko naka? Babyna ya ce shi wanda daddynsa ya kamo yake son ci, dan haka kai zaka kamo mun nikam, idan ba haka ba sai dai babynka ya hakura da ci, bana son nasu Mark".
Tana magana tana kuka, har da wani ɗan guntun hawaye na iyashege.
Ɗan dafe kansa ya yi yana faɗin. "Wannan baby da alama ya fi uwarsa rigima, to tashi mun a jikina bari na je na kamo maki".
Make mashi kafaɗa ta yi tana faɗin. "A'a ni dai sai dai ka goyani mu kama a tare".
"To tashi bari na miƙe sai ki hau bayan nawa ko?"
Ya bata amsa a takaice.
Da sauri ta miƙe daga jikin nasa, miƙewa tsaye ya yi tare da ɗan duƙa mata kaɗan ta yi tsalle ta haye bayansa tana dariya.
Cikin jirgin ruwansu ya koma da ita, dama kunsan a cikin jirgin ruwa da akwai abubuwan kama kifi, rigar ruwa, da dai sauran abubuwa, so shi abubuwan kamun kifi ya je ya ɗauko, sannan suka fito.
Ganin shi da abin kamun kifi a hannu yasa Mark ya ce. "Sir bari na kama maka".
Da yake ta gabansu Mark ɗin suka bi, shi ne yasa Mark ɗin ya gani.
Ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba ya ce. "No ka barshi kawai, baby ya ce kifin da daddynsa ya kama zai ci, so bari".
Yana magana yana tafiya, ita kuma ta wani kwanta mashi a saman bayansa tana aikin murɗa mashi dark black curly hairnsa ta bayan wuya.
Bakin ruwan ya koma ya fara aikin kamun kifi dan dole, idan ba haka ba babynsa dai ba zai ci komai ba.
(Wlh Rimsha ta san ta kan tsiya😂 yanzu His Excellence da kansa ta saka kamun kifi🤔 kai wannan yarinya tana yin son ranta, dole na zuga Lion ya kara aure, ya auro baturiya😒🥱)
Da kyar ya iya kama mata manya manyan kifi guda biyu, sannan ya ce ta sauka mashi a jiki ga shi ya kama mata bari ya kaiwa Mark ya je cikin jirgi ya gyara ya gasa mata.
Nan fa ta saka mashi kuka tana faɗin ita fa ba gashin su gas take so ba, da itace za'a hura wuta a gasa mata, haka babynta yake son ci.
"Meesha meyasa kike son saka mun ciwon kai ne? Itace kuma?".
Kuka ta sake saka mashi tana faɗin. "To ni Noorish laifi nane? Ba babynka bane yake son ci? Ni fa bana cin kifi, babynka ne nan yake son ci".
"To sauka bari su Mark su gasa maki da itacen".
Sake make mashi kafaɗa ta yi tana faɗin. "Baby gashin daddynsa yake son ci, ni dai kai nake so ka gasa mun, Allah idan ba kai ba na ƙoshi".
Tana magana tana kuka, har da hawayenta bibbiyu dan rigima.
Bashi da zaɓin da ya wuce ya gasa mata ɗin, domin kuwa yana tsananin son cikin nan nata, ga cikin watansa ɗaya kenan a duniya, amma sai rigima kala kala ta iya, kuma cikin yazo mata da laulayi tare da zaɓar abinci ne, yasan idan bai gasa mata ba to ba lallai ta ci abinci ba, abin da cikin yake so shi kawai take ci. Babbar magana.
Lion akwai shi da wani ra'ayi fa shi ma, ganin cewa dukka family suna ta burin Rimsha ta samu ciki, kowa so yake yaga ɗansa, shi ne fa sai ya ɓoye zancen ciki, yaki bari kowa ya sani, daga ita sai shi, ko gwaggo bai sanarwa ba, wai kada su sakawa matarsa ido, kada su damesu ita da babynsa, shi ne nan ya ɓoye menene yake damunta, ya ki bari gwaggon ta gwadata, ya ki bari kowa ya sani, kunga daga karshe ma ya ɗaukota sun bar gidan abinsa.
Ni kam PRINCESS FATEEMA TEEMA ina ganin ra'ayi kala kala a wajen Lion.
Sanya su Mark ya yi suka kawo mashi itacuwa busassu, sannan suka hura mashi wuta ta bakin ruwan, dan dole yau ya koyi gasa kifi, amma sai da Mark ya nuna mashi yadda zai haɗa kifin da kayan miya, da yake suna da komai a cikin jirgin
Kujera Mark ya kawo mashi ya zauna kusa da wutar yana gasawa. Ba dan tsananin tsoronsa da su Mark ɗin suke yi ba, da yau babu abin da zai hana basu yi mashi video ba, dan ko a mafarki basu taɓa tunanin zasu gansa a kusa da gas na girki bama bare kuma itace, sam basu taɓa yin gigin irin wannan tunani ba, sai ga shi yau saboda babynsa ya zauna a gaban itace mai ci da wuta yana gasa kifi, gaskiya mace duniya ce, duk wanda ya ce maka mace bata isa ba, to wlh bai shiga hannun macen da ta kai mace wadda ake cewa mace ba mun rako mata ba, kun san akwai mace wadda ta amsa sunan mace, sannan kuma akwai mun rako mata, sune zaku gansu sai a hankali, amma cikakkiyar hamshakiyar mace, ai ko namiji baya so sai ta juya shi son ranta.
A takaice dai yau ga His Excellence of United States yana aikin gasa kifi a bakin ruwa........😂
Kai mata duniya ne, dole haka ya yi wannan aiki ba dan ya so ba, sai dan yana son farincikin matar tasa da kuma abin da yake cikinta, a can gefe guda kuma Sir Safwan ya ɗake a saman kujerarsa cikin office nasa dake white house, ya haye kujera yana ta aiki tamkar Lion ɗin ne, babu wanda ya iya gane cewa ba Lion ɗin bane, kowa a matsayin Lion yake ɗaukarsa, ba su san ga shugaban kasarsu mai mulkarsu a nan bakin ruwa shi ma ana mulkarsa ba, ya mulki al'umma, ya juya su son ransa, shi ma kuma under 15 years girl ta mulkesa ta juyasa son ranta, wannan abin ni PRINCESS FATEEMA ZAHRA yana mugun yi mun daɗi..................😂(Team Lion kada wanda ta ji haushina kun ji na gaya maku😂 ato daɗi nake ji yadda Rimsha take murza kanbun mulkinta😂 ya gasa mana kifi muci😂 dama ni ina da Maltina mai sanyi 🥱)
Haka ya gasa wannan kifi tsab, sannan ya bar wajen tare da komawa ta gefe guda yana turɓune fuska. A saman laps nasa Rimshar ta zo ta zauna tana faɗin ya bata kifin a baki to.
Idan baku manta ba tun a book 1 Aseef baya cin namar kifi, hakan yasa dukka TRIPLETS basu damu da shi ba, ya zamana suma basu so, so har yanzu Lion wari kifi take yi mashi, bai iya ci ba, baya son karninta kuma. Amma a haka ya daure ya rinƙa bawa Rimshar a baki, dan ya samu ta ci abinci, yasan ba komai take ci ba sai abin da ta zaɓa.
Shi dai Mark izuwa yanzu ya gama sadaukarwa da cewa babu abin da mace ba zata sanya namiji ba, mace zata iya juya namiji son ranta idan ta san menene ciwon kanta.
A takaice sun ɗauki tsawon lokaci a wajen wannan bakin ruwan, sun sha soyayya ba karya, Rimsha ta zuba sarautarta son ranta, abin gwanin birgewa, sai da lokacin da zasu tafi Nigeria ya yi ne gwaggo ta kira shi a waya a kan ya dawo zasu je Nigeria.
Okey ya amsa mata da shi, amma sai ana gobe zasu tafi sannan ya dawo gidan.
Wani irin kyau Rimshar ta kara, jikinta ya samu sauki sosai, dan ta samu hutu, ga kayan marmari da take ci sosai, sai ta kara fresh over. Sai dai kuma har yanzu babu wanda ya iya gane cewa tana da ciki, sam basu gane ba, dan cikin bai fito ba, kwata kwata 3 months ne cikin, domin two months suka yi a bakin ruwan kafin su dawo.
Sun shirya zuwa Nigeria gagarumin shiri, dan sun tsara idan suka je zasu yi ziyara sosai. Sai dai fa ko da suka je Nigeriar basu sauka a gidan Lion na Kaduna ba, a villa suka sauka, a fadar shugaban kasa, saboda yanzu in dai ba tafiyar sirri zasu yi ba, to babu in da zasu je su zauna a karamin waje, sun wuce wannan level ɗin, ku kanku kunsan matsayi ta ci uban na da.
Daddyn Rimsha bai zo Nigeria ba shi, shi suka tarawa aikin a matsayinsa na vice president, suka tara mashi aiki suka tafi suka bar bawan Allah, mummy ta so zuwa, amma ina ba hali, haka ta hakura ya zauna tare da mijinta.
Sun sha yawo a Nigeria sosai da sosai, sun yi ziyara wajen ƴan uwa da abokan arziki, har Bauchi sai da suka je wajen ƴan uwan Dr Salman, sannan suka je Katsina wajen su Maman Sadiq. Jehan ce ta sanya Areef ya yi wa Maman Sadiq da Sadiq ɗin gagarumin kyauta, katafaren dankareriyar gida na alfarma ya saya masu a cikin gari, ya ce su bar kauyen nan, sannan ya biyawa Sadiq da Yusuf school fees na tsawon su kammala karatun a wani katafaren school na ƴaƴan manya, ya bawa Sadiq jari mai tsoka da zai iya isar sa ya rike ahali guda, shi ma baban Sadiq ɗin ya bashi jarin sosai, da farko Jehan ta so hana shi ya bawa baban Sadiq ɗin, ta ce ai munafikin uba ne mugu, sai da Rimsha ta roketa, sannan ne ta yi shiru ta hakura Areef ɗin ya bashi 5m.
Daɗi kamar baban Sadiq ba zai mutu ba, nan take ya hau zuba masu godiya tare da godewa Maman Sadiq da ta rike su Jehan mutanen kirki. Ni kuwa nace ɗan banza, sai yanzu kasan da cewa su mutanen kirki ne ba, da yake anji maiko, kai amma wannan hali naka dai tirr da shi.
Lion kuma Rimsha ta ce to ya biya masu kuɗi su je Makka su yi ibada, Okey ya amsa mata tare da cika mata abin da take so, su maman Sadiq za'a keta hazo zuwa ƙasa mai tsarki.
Bayan sun kammala zasu bar garin Katsina su koma Abuja ne Aafia ta ce da Uncle T zata je wajen Ummin Dr Nawid a gidan sarki kenan.
Ba musu suka ɗunguma zuwa can, dan ziyara suka zo, sai dai fa Lion da Rimsha basu bisu ba, sun kama hanyarsu sun bar garin, Rimsha ta tsayar mashi da rigimar sai dai ya kaita garin Ilorin, dan tana son ta je taga Kausar, dama kuma idan baku manta ba ya taɓa yi mata alkawarin zai kaita can, dan haka sai ya ɗauketa suka nufi can.
Su Aafia kuma sun je su duba Ummin Dr Nawid tana nan lafiya, a nan ne suka sami labarin Abbo ya dawo bai mutu ba, sai dai ya haukace yana yawo bola bola, ga ciwon kafa da yake fama da shi, kafar ta ruɓe har tana tsutsa, an nemi magani har an gaji babu sauƙi, hakan tasa aka raba auren Ummi da Abbon, da da farko ma an ɗaure shi ne, daga baya da aka ga wannan fa ba samun lafiya zai yi ba, sai aka sake shi ya shiga duniya ɗan banza.
Nasan zaku yi mamakin jin cewa Abbo yana raye, to dama bai mutu ba, da ginin tazo ruguzowa a kansa sai ya ɓace, hakan tasa yake raye, sai dai kuma aljanun tsafin nasa sun ce ba zasu yafe mashi ba, dan sun bashi arziki mai tarin yawa, da alkawarin zai basu mata, sau uku kenan yana yi masu alkawarin basu ƴan mata amma yana karyawa, ya yi alkawarin basu Jelly, Allah ya kuɓutar da ita, sanan ya yi alkawarin basu Aafia, nan ma Allah ya kuɓutar da ita, sai Adiva kuma, ita ma Allah ya kuɓutar da ita, hakan ne ya arzuƙa dodannin tsafin nasa suka haukatashi, sannan suka sanya mashi ciwon kafa mai azaban zafi har tana tsutsa.
Sosai Aafia ta ji daɗin hakan, amma bata nuna hakan a fili ba, sai ta ɓoye murnarta ta taya Ummin Alhini kawai.
Sun samu tarba ta karamci da girmamawa a wajen ƴan uwan Ummi, hakan ya yi masu daɗi sosai. Cikin dabara Aafiar ta tambayi Ummin ina Oummunsu wato hjy Hadiza, nan Ummin take sanar da ita ai ita ma Oummu ƙwaƙwalwarta ya taɓu an kaita gidan mahaukata an ɗaureta.
Cikin ruɗu Aafiar ta tambayi me ya sameta, nan fa Ummi ta bata labarin cewa Hjy Hadizar ta yi aure a kan aure ne da wani Balarabe har sun haifi yara biyu, to ashe balaraben kam mugu ne, duk ya lalata mata yara, ba wanda yasan me yake aikatawa har sai da ciwo ya kama yaran suka mutu, to Hjy Hadizar ta zo ta gane gaskiya shi ne kwakwalwa ya taɓu saboda son da take yi wa yaran.
Sosai Aafia ta yi kukan jin abin da oummunsu ta yi, abin ya yi mata ciwo sosai, amma ya zata yi? Haka Allah ya ƙaddaro masu nasu kaddarar, dole kuma su rungumeta.
Sosai Ummi ta rinƙa rarrashinta tana bata baki tare da nasiha a kan yarda da ƙaddara. Jiki a mace ta rinƙa zubawa Ummin godiya. Haka suka cigaba da yin hira har zuwa karfi 2 na rana, bayan sun yi sallar azahar sai suka ɗauki hanyar komawa Abuja. Amma fa kafin su koma sai da aka