Showing 1 words to 3000 words out of 255288 words

Chapter 1 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1332

Compiled by Umar Dalha Funtua.


FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BY
1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA

🐎HUGUMA GROUP🐎
Bissimillahi Rahamanin Rahim
Allah ina rokon ka ka bani ikon gama wanan labarin lafiya da kuma nasara a cikin yin shi,
Ya Allah zunun da zan kwasa a cikin sa kayafe min
Ya Allah Alherin da ke cikin sa ka sadamu dashi ni da duk wani misullumi na duniya,,,,
Ina mai rokon masu karatu da idan lokacin ibada yayi dan girman Allah kada a shagala a dinga aje karatu a aiwatar da duk abin alhari,,,,, nagode,,,,,, taku har kulun,,,,, ZEEE MAKAWA,,,,,,

Sadaukar wa ga duk yan Family HARZAMI,,,,,,Tare da yan huguma group's


Churching, sith Domenic Church ne da kowa yasan babbace church ne, daga cikin manyan churching da muke da su a kasar Nigeria,
Church ce da akasari turawa ne ke zama father ko pastors din gurin,
Wanda daga karshe har suke daukan yaran bakaken fata zuwa kasashen su don karo ilimin addinin kirstanci,,,,
A kasarin mabiya wanan church din yan kabilar IBO,
Kusan duk wani babban gari nada wanan irin church din inda yan kabilar IBO ke yawan zuwa bauta,
Wana katon church din da ake taro yai a cikin garin kwantagora da da ke can cikin jahar Niger state,
Da, alamar buki sukeyi a gurin yau kuma bukin mai girma ne da ganin hakan,,,,,
Saboda yawan abin hawan da yau ya cika haraban churching, da kuma jama,a mabiya irin wanan churching da suka zo daga wurare daban daban acikin wqnan kasar,,,
Sai kida kawai, ke tashi kamar kunnuwa za su fashe wa mutum saboda karan, kida,
Matan church din sunyi anko har kusan kala uku kamar yadda mazan su, su kayi na su kallar anko din don kowa da tashi kalar shigar,
Wani matashine dan kimanin shekara ashirin da takwas,, ke tsaye a harabar church din da alamar shima wurin taron ya zo,,,
Dogo ne saurayin fari sol dashi, gashin kan shi sai sheke da walkiya sukeyi a cikin hasken rana,
Sajen fuskan shi yadan kwanta mai kamar shi yayi wa kan sa,
Kallo guda zakai mai kadau ka ko bafullatan,ce , shi,
Saboda duk zubin shi na fulani ne, sak
Tsaye yake, bakin wata bakar mota mai kirar landrove, jeep,,,
Farar shadda ce, kal a jikin shi dinkin rigar ce ,mai gajeren hannu, a jikin shi,,
Rigar an sa wasu manyan aninineya da akai ado dasu, a gaban rigar,
Hannun shi daure da agogon company Rolex, irin na maza, dagani kasan na gold ne, agogon,,
Sai wasu zubba da ya jera a yatsun hannun shi,,
Kafar shi na saye da bakaken cover,shoes, sai sheki sukeyi,
Sai, yar sarka da yasa a wuyar shi itama dai kallo guda zakai ma sarkan kagane cewa ta , gold ce,
Kusan duk wanda ya wuce shi ta inda yake, tsaye , alokacin yana waya sai mai shi,
yai mai hannu alamar gai suwa,, ta ban girma ko mutunci,,
Hakan ne, ya nuna cewa wanan matashin sanane ne sosai a gurin wanan taron, da akeyi,
Komawa yayi cikin church din ya zauna saidai kuma baifi minti ko biyar da zama ba wayar shi ta kara kara, kira ya shigo mai again,,,
Mikewa yayi yana ma shugaban nin su alamar daukan umurni a gurin su,
Baiwani dauki lokaci ba a waje wanan karon ya koma cikin church din ya zauna inda yatashi, da farko,
Daidai lokacin anfara yawo da turen ansan donations kamar yadda suka saba idan suna taro,
Yana jefa nashi envelope din ya mike batare da ko daga ido ba ya fara tafiya a daidai yar siririyar hanyar da aka tanada don bin masu fita da shige ciki,,
Sukuma church din duk sun mike maza da mata suna wakar yabo ga almasifu,,

Motar shi ya nufa direct, ya bude yai mata key yabar harabar church din
Daidai lokacin wani tsoho iyamuri yafito daga cikin church din yana kokarin tsaida dan matashi mutumin da hannu,,
Wanda shi a lokacin har ya fita daga cikin get din church din ko,,,
Yana fita yai dan yi ajiyar zuciya, daidai da, lokacin da kuma,wayar shi ta dauki kara ke nan ,
A hankali yadauko yana diba mai kiranshi again, sai ya ga sunar mahaifin shi a jikin wayar barobaro, (MY DAD,)
Barin kiran ya yi har ya katse tukun sanan ya kira mahaifin nashi , da kan shi,,,
Duk a lokacin yana tukin mota,abinshi, a ran shi yasan cewa kiran shi mahaifin shi zaiyi ya dawo,
Yadaga wayar yana mai fadin Alo,
A can dayan bangaren aka ansa mai da Alon ba,
Joseph where are u going now,
Sai kuma tsohon yaci gaba da magana cikin harshen IBO,
Yana cewa Baba ina da uzuri ne na fadama cewa yau nake son in koma portacourt,
No, no no Joseph it can b, possible,,,
I want us to pray for our successful, at home today night,,
Yace cikin IBO har na yi inviting din pastor yuhana ko,
Saida yadan diba agogon hannun shi tukun sannan yai yar tsaki cikin ran shi,
Saboda baya son wanan addu,an da mahaifin shi ke sa ana masu agida,
Don inda sabo ya saba ko da hakan,don tun suna yara ake wanan gaiyatar pastor a gidan su,
Muryan tsohon ya katse mai tunanen shi inda yake cewa Joseph kaji abin da nace ma ko,
Ya ansa mai da fadin Yes,, Dad,,,
Yana jin ajiyan zuciyar da tsohon yayi a cikin wayar,
Daidai lokacin da ya karya kwanan shiga uguwar kwanar kuka, ta inda zai sada shi da green,land, super market
A nan ya dan tsaya wani shago yace a bashi katin MTN,
Mai katin ya ce na ,nawa za a dauko mai sai yace na dubu goma, ai sai mai kati yaja yai tsaye,
Don shi a zaton shi, gatse ake mai,
Shiko a lokacin hankalin shi na can yana bidan wani takarda da yake son yaba mai shi,
Yana dago kai yaga ko mai shago ya kawo mai katin sai yagan shi tsaye gaban shi,
Hannu ya mika don yakarba sai mai shagon katin ya ce mai a nadauka bakar magana kai min, sir
Cikin mamaki yake kallon mai katin shiko ya koma da sauri don dauko katin,
Saidai mai shago ya tarar da katin bai kai na dubu goma ba don haka ya tsaya yi mai bayanin baikai ba ,
Hannu ya mika yakarbi wanda yasa mu yana mai mika mai kudin da yakirgo dubu goma,
Cikin mamaki mai shago yace ai na dubu bakwai kawai aka samu maigida
Cikin hausar shi kamar ba haihuwar IBO ba yace, kabar shi kawai daidai lokacin da yata da motar shi yabar gurin,
Mai shagon katin yai tsaye sororo ya bi shi da kallon ikon Allah,,,
It's been a long day without you my friend and,i will tell you all about it when i see you again ,we have come a long way from where we began,oh i will tell all about it when i see you again, (Wiz_Khalifa feat charlie puth)
SEE YOU AGAIN,
Baka jin komai a cikin motar sai wanan wakar ke tashi yana kokarin loading kudin da ya saya awayar shi, yana maming din wakan a hankali,,,
Phase 2 ya karkata motar shi zuwa, hanyar tudun wanda don yai saurin kai shi uguwar, phase 2,, din
Daidai, roundabout din da ya mike zuwa,Kwangwara, da Kan Wuri,
Ta, window motar ya ga ana mai hannu alamar ya tsaya, dan murmushi yayi dan ganin wanda ke kokarin tsaida shi a lokacin,,,,,
Wuri ya samu a gefen hanya, ya parker motar shi daidai lokacin da wanda ya tsaida shi ya iso gurin,,
Hannu suka mikawa junar su alamar gaisuwa a tsakanin su,
Cikin nuna jin dadi daganin junar su yasa suka rike junar su, suna ta dariya,
Kafin minti biyu sai ga gurin da suka tsaya yafara cika,
Duk wanda ya gansu cikin farin ciki yake tsayawa ya basu hannu,
Mutane da ke wuce wa sai kallon su sukeyi cikin mamaki,
Komay ke faruwa haka aka tsaya a gefen hanya,,,,,,



ZEEE MAKAWA,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎

Fatan alheri ga dukkan wayanda suka nuna min kaunar su da kuma kulawa,


Sai misalin karfe shidda da wani abu yadawo gida daidai lokacin da abokan shi ke shirin alwalal sallah magrib ,,
Tun fitar shi yana can phases 2 tare da abokan shi
Friendship din su ya dauko asaline tun a makarantar primary, daga nan kuma suka jona secondary,
Tun a lokaci baida wasu abokai sai yaran hausawa
Duk irin fadar da mahaifin shi da yan uwan shi ke yi mai bai sa ya daina bin diyan hausawa ba,
Kamar yadda akasan diyan IBO da rashin son dan bahaushe shi nashi halin na daban ne,
Don har abincin su yake ci ,idan yaje gidajen su, ziyara lokacin yana karami,
Bayan rasuwar mahaifiyar shi baban shi yaga cewa duk akidar shi kusan na hausawa ne yasa shi dauke shi zuwa kasan su don ya karasa karatun shi a can,
Yana gamawa sai kuma akatura shi, kasar Malaysia yin karatu can,
Acan Allah ya hada shi da dan wani millioner, dan yaren su na IBO
Amma shi bai,damu da karatun da sukaje yi ba,
Sai Allah yasa shi da ya maida hankali yana hadawa har da na Emzon yayi mai su test da sauran aiyuka,
Exam ne kawai, Emzon kezama yayi a haka har Allah ya taimake shi suka kare karatun su,
Bayan dawo wan su karatune Emzon ya jona Joseph, a business din harkan man petrol
Daga haka Allah ya taimake shi ya cigaba tun suna yi da kudin Emzon har suka daina hada kudi a tsakanin su,,
Wasa,wasa Joseph ya fara na shi harkan sai gashi ya canza wa uban shi sana,a daga saida manja, yakoma harkan petroleum, shima,,,,,,

A kofan gidan su ya iske baban shi zaune a saman wani benci, da wasu yan dattijawa kamar shi
Kwalaben giya ne suka tara birjik agaban su, sai shewa suke yi suna ta hayaniyar hiran irin bidirin dazun da akayi,,,
Yadan dade zaune cikin motar shi kafin ya fito ya fitowa sai yai kokarin bin ta kofar baya don ya shige cikin gida,
Muryan Mr Emanuel yaji cikin yar buguwa yana kiran shi yazo su gaisa da abokan shi,,
Bsdon yaso ba ya karaso har inda suke zaune,
Kwalban giya yake kokarin mika ma dan nashi yana wani irin dariya sama sama,
Kai kawai Joseph ya kada mai alamar a,a ya taka tabaya yadan juya zuwa cikin gida,
Yana shiga wanka ya wuce yi direct bayan fitone ya iske wayar shi na ringing,
KB aka rubuta barobaro a cikin harshen hausa yace KB ya,ya dai,?
KB ya ce mai yaga jibrin din da yake bida yadawo gari shiyasa ya kira shi don yafada, mai
Yace ka gane ne KB yanzu kabani a wa biyu pls, zan zo in samay ka muje gidan su,
Eneka sister shi ce tafado Dakin tana cewa brother muna jiran ka a,palour pa,
Saida yadan kara kamar minti goma yafito cikin wasu yan kananin kaya,
Yasamay duk a rusunne pastor yana tsaye sai addu,a yake zabgawa suko suna ta fadin Amen, Amen,
Bin sahun su yayi ya jona su a haka akai ta masu wana addu,an har zuwa wani lokaci,
Baban shi dama a buge yake tatil da giya tun a nan ya tuntsire ya fara nasari,
Joseph ya ciro kudi tare da dafa ma pastor baya har zuwa gurin motar shi, ya mika mai kudin yana nuna godiyan su da wanan ziyarar da pastorn yai masu,,,
Daga nan baikoma ciki ba, ya wuce zuwa inda KB, ke jiran shi su tafi,
Gidan su jibrin Bala suka tafi cikin daren nan,
Jibrin na cikin gida akace wai ana mai sallama,
Bai wani bata lokaci ba yafito , yayi mamaki kwarai ganin Joseph yasa shi yin wani dan ihu, har saida yajawo hakalin mutane,masu wucewa, gare su,
Yayi farin cik kwarai da,ganin Joseph yace Yusuf Joseph ke nan duk sai suka dariya a lokaci guda saboda, tuna wa da wani zamanin da yawuce a baya,
Inda Joseph ke cewa shima sunan shi Yusuf Joseph, ne, kama yadda Kabiru lawal Jibrin Bala,sai Musa Aliyu,
Shima Joseph sai ya cire Joseph Emanuel ,,
Yace ya koma Yusuf Joseph,
Dariya yayi yadankai wa jibrin din dan duka ga kafadar shi cikin dariya,
Suka kara lalewa, da junar su, nan fahira ya barke a tsakanin su na yau she rabo,
Sun dauki wani dan lokaci sanan sukabar uguwar yamman inda gidan su jibrin bala din yake,,
Kafin su rabu Joseph ya debo kudi masu yawa ya mika wa jibrin din yana mai bashi hakkuri,
Kan cewa bai san cewa zai kwana ba don bukin yazo na nada sabbin shugaban nin church din su da akayi, kuma duk ya kashe kudin shi ga jama,a
Tun da ya aje KB a uguwar tukura, yasa kai zuwa gida ziciyar shi fam da tunanen halin yadda ya ga abokan nashi ciki,
Duk da goma na dare ya wuce har da rabi hakan bai hana shi cin ma yan uwan shi zaune suna jiran shi ba,
Ya bude falon kusan lokaci guda bakin su ke cewa brother welcome,
Ya ansa masu da ce how you na dey,?
Saida yadan shiga daga ciki tukun sannan yafito cikin wasu yan kananin kayan barci,
Sai a lokacin ya tuna cewa bai co wani abinci ba don haka inda suke cin abinci ya wuce sakwara da miyar ego yaji egushi da naman shano,
Ya wanke hannuwar shi ya fara ci, sai da ya gama cin abincin sanan ya isa, inda yan uwan shi suke zaune yake tambayar su inda baban su yake,
Da hannu suka nuna mai hanyar kofar dakin shi,
Anan suka fara mai korafi kowa da abinda yake so amai da ga cikin su,,,
Wa yanda zaiba kudi yaba su, wa yanda kuma zai, sayo wa abu yai masu alkawari,

Tunda safe yai asubanci yabar gari yadauki hanyar lagos, saidai zuciyar shi fam yake da tunanen yadda ya yaga abokan shi suka koma cikin dan lokaci guda,,,
Bayan tafiyan Joseph abokan shi suka dinga rumors a gari cewa Joseph yazo wasu su ce yadawo,
Kafin wani lokaci sai maganganu ya karade gari wasu nacewa aiki yasamu mai tsoka,
Wasu nace harkan business din zamani yakeyi watau, dai smuggling, wasu kuma suka ce ai dan shan jini ne,
Inba haka ba ya zaiyi kudi haka cikin dan lokaci guda, kamar yafi su bida,

KB ne a saman babur din shi, yana tafiya zuwa gidan wani dan uwan su don ya kai sako,
Hadewa sukayi da jibrin a daidai junction, anan suka dan tsaya don su gaisa,
A haka suka sako hiran Joseph cikin zancen su, inda suke yaba alherin da yazo yai masu,
KB yace wai ko kasan cewa mutane da daukar wa kan su wahala da nauyi wai har sun fassara dukiyar Joseph da wata, ma,ana,,,
Cikin mamaki jibrin yace kai mutumina bari zancen nan pa,
Yace wallahi man ni ma su jamil suka tare ni hanya suke ce min wai ko da gaske ne zancen da sukaji game da Joseph ance wai yayi fitacen kudi,
Jibrin ya kada kanshi yace kai mutum mutum abin tsoro ne wlh,
Yanzun nan har sun fassara wanan guy din dawatq ma,ana ko,
Allah ya kyauta kawai suka iya cewa suka dan kara taba hira sukabar gurin cikin alkawarin kara haduwa nan gaba,
Daidai wanan lokacin Joseph yana zaune a cikin kayattacen falon shi da garin lagos zaune yake cikin shigar kananin kaya,
Kallo guda zakai mai ko ba,a fada maka ba zakasan cewa kaya ne, masu tsada a jikin shi,
TV yake kallo a zahiri saidai gaskiya ba wai abinda ke faruwa a cikin TV yake kallo ba,
Don dai zuciyar shi na can tana tunanen abokan shi na kurciya da yagani cikin halin taimako,,
A hankali ya furzar da yar iska daga bakin shi yana dan bugun hannun shi a hankali,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login