Showing 183001 words to 186000 words out of 255288 words
Chapter 62 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
yarinyar karama,
Anty ce ta tare shi da fadin ai indon hawan mashin ne duk shi muke hawa Yusuf,
Shima baban Assalam naji yana cewa idan ya samu kudi zai yi kokari ya siyo mota ya ahe muna,
Anty barin duba idan nasamu maikyau sai a saya ko anan din ne zai fi idan ma har zan aje maku driver ne kafin ku iya yadinga kai ku duk inda kuke so zaifi,
Yusuf inji anty dije tace kayi hakkuri har zuwa gaba pls don mutane zasui ma zancen mumunar fassara akai,
Kaga zasu ce ai don abin hannunka ne baba yake son baka mar,,,,,,,,,
Sai tai shiru don tunawa da tayi cewa Jibrin yana gurin kuma shine wanda ya hada connection tsakin Yusuf da Sadiya,
Tsab yamike tsaye yana cewa nifa anty ba ruwana da zancen mutane don ban zuwa gidan kowa tun farko sai nan,
Fita yayi daga cikin falin batare da yai masu sallama ba ko yace wa jibrin su tafi,
Anty taga kai takalli fafadan bayan shi har zuwa ficewar shi,
Jibrin ya tambaye ta da hannu cikin alamar may ke faruwa,
Ansa ta bahi da kafada ita ma batasani ba, gaskiya,
Tun wanan lokacin Yusuf ya canza gaba daya bai daina zuwa ba amma baya wani walwala a gidan kamar farko,
Don shi a ganin shi Anty bata sin abin hannun shi ne shi yasa ta doje wa zancen motan da koyaushe yake mata magana,
Maryam yau da wuri ta gama duk wani aiki da zatayi don tana son yin kallon wani series film a wani tasha,
Yaro ne mai zakin murya ya shigo gidan da sallama yana cewa wai ana sallama da maryam inji wani,
Maryam wace ke zaune a kasan falon su saman wani dan filo, taji gaban ta ya fadi dam,
Din tasancewa ba kowa bane A,A ne don shine mai wanan dabiar, kamar tace wa yaron bata nan sai dai ta daure ta ce kace tana tafe,
Maryam tafito cikin shigar wani bakin dogon riga har kasa yana da kwaliya na wani pink colour, sai gyale kayan da ta dan yane fuskan ta dshi,
Yana zaune cikin motarshi kafar shin guda ya daga waje,
Fitowar maryam tun daga nesa yake sakar mata, murmushi,
A zaton shi tunda har tafito wanan dan IBO barazanane kawai yai mashi,
Ya masan cewa koda da gaskiya ne maryam bazatai wani wuyan shawo kai ba zata huce tayi hakkuri,
Tun daga nesa yake kara kare mata kallon cikin so da kauna
Yarinyar na burge shi tana bashi sha,awa uwa uba ga hakkuri,
Irinta ce ya dace ya aje agida matsayin uwar ya, yan shi,
Don zatayi hakkuri da duk wani kwaran nashi, a rayuwa,
Barka da fitowa yace mata kalman da ya fara taron ta da,shi ke nan,
Sai dai yau ansar da yasamu sabanin na kulllum ne, yaji,
Lafiya dai ko malam tace mai cikin daure fuskan ta tankar bata san shi ba,
Cike da mamaki yake kallon ta don jin tambayan da tai mai,
Amma da yake dan duniya ne sai yai murmushi yace cikin kwarewa da zolaya,
Haba sahibata fune duk akan tafiya ba sallama, ko may ye haka nan, ?
Dan dakatawa yayi ya kalleta yayin da take a tsaye hannun a harde da juna saman kirjin ta,
Maryam don Allah dai ki fahince ni sai kuma yadan dakata ,
Can ya dan kalle ta yace wallahia office din mu ne aka turani wani course na sati, a Lagos,
Kuma zan makara idan nace sai nazo nan na fada maki ,
Zai ci gaba da tsarata maryam ta dakatar da shi da hannu cikin wani murya tace mai enough,
Malam is over now bawai wani ya fada min ba ni da kaina na ganka
Shima cikin murya makama da ta fada yace kina nfin karya zan maki ne ko may,
Maryam tace mai cikin dakiya kamayi ai bawai wani ne yafada min ba,
Kabani kunya wallahi duk yardan danayi dakai malam nake jin ka araina fiye da,duk wani da na miji,
Bata karasa taji yace o wo, ke nan wanan dan iskan iyamurin ya hure maki kune,ko,
Kin arda dashe sherin da ya kulla min ke nan akan ki,
Dariya tayi tare da yar shewar bakin ciki tace dakata kaji
Daga yau karka kara zuwa gurina kuma kayanka da ka kawo min ka aiko a karbar ma abinka,
Indai nice mai yin aure to na fasa kaje gaba kasamu daidai da irin ka acan,
Har zata tafi , sai kuma ta juyo tadan tako har inda yake, tace mai, kadaina, daukar alhakin kowa wallahi nida kaina ba na gan ka a gurin ba wani yafada min ba na ganka a kwanar kwangwara face to face da yariya a rungumay,
Ido yafitar yafara borin kunya maryam juyawa tayi abin ta batare da ta tsaya jin abinda yake cewa ba, tashige gida abin ta zuciyar ta na mata kuna da wanan baki rana da ta gani,
Kiris ya rage ta fashe a lokacin son irin yadda take ji a bin a ranta ,
Yakai wani wani lokaci gurin kamar wanda bai da kuzari bayan shegewar ta,
A hankali ta iya furta Innalillahi wa inna ilaihin raji,un ,
Sai ta rintse idon ta gam tana mai jin radadin da take ji yana ragewa a hankali,
Tagumi maryam tayi daga inda take zaune ta rasa, abinda yake mata dadi,
Don dai iyakar cuta A,A ya cuce ta sai dai kawai Allah ya isan mata,
Kai Allah ma ya isan mata din tunda bai kai ga nufin shi ba a gare ta,
Muryam anty dije taji a bayan ta tana cewa tashi ki shiga ki kwanta, dare ya soma,
Jiki a mace ta mike a hankali ta na dan dingisawa don kafarta yai mata nauyi ,
Saman katifa ta fa da faba dayan ta tare da sake wani irin kuka mai gumza,
A tsorace Anty Dije wace ke dafa falo ta kwasan yara,zuwa cikjn daki,
Karasowa tayi dakin da sauri inda take jin kukan kaunar na ta
Marayam so kike ki kashe kan ki akan wanan dan iskan mutumin ko yaya, ?
Jin kalaman Anty, ya sakata dakatar da kukan sai she,sheka takeyi,
A gaban maryam din anty dije ta dawo ta tsaya inda take iya ganin fuskan ta,
Abinka da dan uwa rabin jiki sai gashi ita ma Anty dijen kuka takeyi, cikin kukan take lalashin kaunar nata,
Cikin tausayawa da nuna kulawa, take ta cewa ai bai kamata ki kuka ba maryam
Wanda Allah ya hana ma A,A ya bashi Yusuf ai Alhamdullahi, ko ?
Dagowa maryam tayi suka hada ido da juna ita da yar na ta,
Sai kuma kawai tasa wani kuka, irin mai tsuma zuciya,
Anty Dije hannayen ta duka biyu takama sai ta kai zaune tana mai watsawa yar uwan nata ido,
Tace amma dai maryam kukan dadi kikeyi ko mai makon ki godewa Allah akan baiwar da yai maki da kuma wanda kike shirin riska,
Shine zaki din ga butulce mashi haka kina wana kukan,
A karshe dai bayan dogon nasihan da tasha sai ta sa hannun ta kamar karamar yarinya, cike da tausayawa tana cewa kiyi hakkuri haka kar kibari kowa yasan may kike ciki,
Maryam wace kan ta kawai ta kada a lokacin don baza ta iya magana ba irin yadda take ji, gaba daya tasa ta rasa A,A ke nan har Abada,
A haka anty ta samu maryam tai shiru, ta lafe tankar mai barci,
Kofan ta ta rufo mata a hankali, tafita zuciyar ta fam da tausayin maryam,din, wace ke bukatar kulawa saboda rabuwa da,wanda ka saba dashi akwai zafi,
Zaune su ke a falon gidan Yusuf din suna kallon wani plan din gina da akazana a wani farin takarda,
Zanen Gida ne mai kyau na gani na fada suke kallo a takardan,
Gaba dayan su, photo ginan ya burge su sosai duk sun mutu a kan shi,
KB ne yace kai Man irin wanan gidan kawai mutum ya samu lafiyyan mace ya saka ta aciki,
Kwashewa sukayi da dariya a lokaci guda gaba dayan su amma ban da Yusuf,
Wanda yace kai KB kai baka da zance sai na mata, ko ba mace ai a mutum zai iya zama ahi kadai,
Dariya suka kece mai dashi don jin abinda yace masu,
Sai,da KB ya dan gyara zaman shi sanan ya ce wa sauran abokan hiran nashi,
Wai ya zancen shi da Sadiya ce may ake ciki naji shiru mana,
Yusuf da,sauri ya ce mai tunda kaji shiru ba,sai ka tafi ka tambaye taba ko may yasa kaji shiru har yanzu,
Duk dariya suka kara sawa saboda irin yadda yayi mutum sam baya son ya zance mata,
Jibrin ne ya ce kai KB nifa zancen sadiya din nan yasa mun rudani wallahi,
Kamar ya ?
Inji KB wanda ke dan kurban drinks a hankali daga cikin cup,
Yusuf wanda yake a zaune idon shi na saman ties, kamar ba dashi a cikin hiran ba,
Ya ba Jibrin ansa a gajjarce da cewa kaso rudewa ne Jibrin,
Ni na fita cikin wanan zancen tun tuni ban ma son a tuna min akai,
Kallon kallon suke wa junan su, sai mamakin cewa may yake nufi da fadar haka,
Ya ce masu Yes now already ni har na samu wata wace, you all know her,
Da mamakin jin wai sun san ko wace ce ganin da yayi suna mamakin maganar shi,
Gyada masu kai yayi alamar eh tare da lumshe idon shi yana mai gyara zaman shin,
Jibrin yana shirin magana ke nan Yusuf yatare shi da cewa ba kowa bace maryam ce kaunar Sister,
Cikin mamaki wanan ya kalli wancan gaba dayan su sun rude da mamakin jin wai maryam,
Yace yes insha Allah da ita hankalina yafi kwantawa sauran duk ba suyi min ba,
Amma ita nasan tarbiyan ta da kuma halaiyar ta kaga abin zai zo min da sauki,
Daga haka bai kara cewa kala ba ya ma juya ya basu baya,
Ga magana a bakin su sai dai ba daman su yi ta saboda ba suga idon yin hakan ba,
KB yace ya zatayi da mr lecturer din ta, ne don naga ta mutu ga son shi,ban san ta da kowa ba sai shi,
Jibrin wanda ya ke kwance saman kujera yace kai wanan dama yan yan gidan su basu da mutunci
Brother din shi ne fa yaiwa yarinyar nan ciki wani lokaci har muka je gurin shi,
Yusuf yadan juyo gurin da jibrin yake zaune yace
Ok, ok family din su guda ko
Cikin tambaya,
Nan ya kwashe yadda sukayi da shi last zuwa da ya yi su kai ta dariya, suna mai Allah waddai da halin shi,
Da farko rayuwar jibrin yadan sosu da jin ansan da Yusuf ya bayar,
Akan maganar cousin sister din shi sadiya wace har gobe zancen ta akan Yusuf ne,,
Don haka jikin shi yaji duk ya mutu mai, tankar an aiko mai da mugun labari, sai kawai,
Bai wani dade ba yace masu zai tafi sai yadawo, Yusuf wanda a lokacin duk hankalin shi yana akan wayar shi dayake tura sako,
Fitan jibrin din gidan KB yace wa Yusuf mutumina fa bai ji dafin zancen ka ba,
Kamar Yusuf din bai ji zancen shi ba sai kawai ya share shi,,
Tafiya Jibrin ke yi a motar shi yana tunanen ya zasu kwashe da Sadiya idan har ta samu wanan labarin ,
Kodai ya kirata ne ya fada mata zai fi mai sauki
Sai kuma wata zuciya tace mai kada ka fara shi ya zama hadin fitina idan kai haka,
Kabarta kawai komin dadewa zata ji labari ai dole,
Duk kwana biyun nan a takure maryam tayi su kamar a kurkuku, take
Sam bata ko fitowa wahe tana daki a taure ba wani walwala a tare da ita,
Nobar safiya ce yanuna kira a wayan ta a hankali ta mika hannu ta dauko wayan cikin wani irin murya mai kama da ta mai jiya ta ansa mata,
Safiya din ce ta hauta da,sababi cewa yanzu ashe zaman su bana gaskiya bane tunda maganar ta ma sai dai taji shi gurin wasu,
Maryam bata gane may safiya din take nufi da zancen ta ba,
Sai take tambaya kamar ya wai, don ban fahince ki ba,
Safiya tace ai gata nan zuwa gidan da kan ta idan tazo za tai mata bayani,
Tana aje wayan takai kallon ta ga shimkafan dake acikin plate gaban ta kasa ci sai juya,shi takeyi da,spoon kawai,
Anty dije wace ko kallo bata ishe ta ba saboda duk yadda ya kamata tai mata tayi amma,still taki sake jikin ta,
Safiya ce ta shigo gidan tun daga nesa tagane cewa kawar nata na acikin yanayi don haka duk wani abin da ta nufi yi mata sai taji cewa bazata iya ba,,
Sun gaisa da Anty Dije a cikin nuna kulawa da kuma tambayar ta mutanen gidan su,
Safiya ta wuce zuwa dakin maryam don ganin maryam din ta tashi daga inda tske zaune zuwa ciki,
Ido ta kura wa maryam din duk da ta bata tausayi amma sai ta dake ta ce mata wai may ye haka maryam baki da lafiya ne, ?
Idon maryam da ya kawo hawaye take kokarin gogewa safiya din takai zaune tana mai kura mata ido,
Safiya tace ina fatan duk wanan abin bawai don A, A kikeyin shi ba maryam,
Shin maryam wai ke wace irin mutunce da bakya daukan kadara, ko shawara,
Ana fa son musulmi da tawakkali a ko da yaushe idan abu har ya faru da shi,
Sai a lokacin maryam ta dago idon ta da sukai lub, lub duk sun kumbure mata tankar ta yi jinya da dadewa,
Tadan kalli safiya din tana cewa cikin yar murya may kuma kikaga nayi da zaki ce min haka,
Baki safiya ta tabe tace idan har kina wanan haukar haka wallahi wata rana ke ce mai jin kunya ,
Shin maryam damay kikafi wanan bawan Allah ne wai,?
Wallahi ina mai shawartan ki da ki daina wanan halin tun dare bai maki ba,
Dubu naso ke Allah ya baki shine har kike butulce mashi,
Kallon SAFIYA maryam tayi don jin da tayi tace wai dubu na,so,
Suyi ta,so mana ni ina ruwa na kan su su ka,sani kaina na sani,
Manzan Allah fa ya ce muna kada mu aminta da kafirai don basu kaunar har a cikin zuciyae su,
Inna lillahi inji safiya
Maryam kanki daya ne kuwa ? take tambayar maryam din cikin budan baki kalar na mamaki,
Yusuf din ne kafiri kowa ye ?
A takace cikin bacin rai maryam tace yan uwan shi dai,
Wallahi safiya nayi ta ko,karin ganin na taushi zuciya na akan shi amma na kasa,
Duk lokacin da natuna cewa wai da su zanyi taraiyya amatsayin yan uwan miji sai inji raina yana baci,
Safiya yusuf furen kan juji ne,,,,,,
ZEE MAKAWA YALWA
[4/28, 5:33 PM] +234 902 951 1701: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
_*Hakika fadin jin dadin yadda kuke min bazai yiwa da bazarku nike rawa tabbas na yarda masoyi masoyine kullum godiya gareku bata yankewa hakan yasa na baku wannan shafin dungurum gum masoya*_
❤❤
**********************
❤❤
Shiru suka yi gaba daya dakin kowa da irin abin da, yake sakawa a,zuciyar shi,
Gama ga maryam wace ke sauke ajiyan zuciya akai akai
Safiya ta kau da shirun da cewa ki tashi ki gyara jikin ki ki sake rayuwan ki tankar bake ce a haka ba,
Sai a lokacin maryam tai dan murmushi jin abin da safiya tace ,
Abincin rana da Anty ta,gama ne ta aiko masu da shi a daki,
Maryam tafito da kan ta ta daukan masu ruwan sha, a cikin fridge,
Sun fara cin abinci ba da wani dadewa ba suka tsinkayo muryan Yusuf a falo,
Anty Dije wace yan kan nen nata duk sun dagular mata lissafinta,
Saboda sun tayar mata da hankali, shi Yusuf yana fushin a kan anty taki yarda,ya,sai masu mota,
Ita ko maryam taurin kai kamar mutanen farko da basu yarda da sakonin su ba,
Safiya ce taiwa maryam inkiya da cewa taje tai ma Yusuf sannu da zuwa,
Ruwa yake kokarin tsiyayawa a cup don yasha,
Maryam wace ta fito saye cikin dinkin buje da riga na wani material lace, ja colour mai yan fararen duwatsu, ajikin shi,
Dinkin shi kamar maternity ya karbi jikin ta so sai yai mata kyau,
Kusan kwanaki ke nan