Showing 171001 words to 174000 words out of 255288 words

Chapter 58 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1375

saboda jin hukuncin da baba ya yanke a,kan ta,
Sai kuma ya sasauta harshen kadan yace ke maryam in banda abinki, wanan yaron ai abin tausayawa ne, a gare mu,
Dago kai tayi don jin abinda baba yace tadan kalleshi a cikin mamaki,
Taci gaba da cewa, kowa a garin nan yasan cewa baida gidan zuwa wanda yafi nan,
Yau ai abin kunya ne ace muna nan har ake mai gorin mace,
Wanan kawai bai isa mu wani ishara ba aiko da ace banda "ya ta cikina zan zagaya ko a cikin dangi in samo mai,
Balle gani da ku har ku hudu a gida ke ce kawai ko a gidan nawa zan iya bugun gaba da ke batare da raina ya baci ba,
Shiru yayi na dan tsowon lokaci, kadan sai kuma ya goge hawayen shi,
Abinda ya tayar wa maryam har Anty Dije da hankalo ke nan, suma kukan su ka fara yi,
Baba cikin muryan mai kuka yake cewa sam ban tsanmaci haka ba daga gare ki maryam
Sannin cewa da kikayi bazan iya cutar dake ba a matsayina na mahaifinki,
Idan har akwai wani da da nake so da tausayawa a cikin gida maryam bayan ki ne,
Badon komai ba sai kasancewar baki da uwa a cikin gidan Allah ya taimake mu ni da ke yaba mu Dije a matsayin uwar tayarwan ki,
Cikin muryan kuka maryam ta dago kanta tana mai cewa baba ni bance ba zan yi ma biyayya ba,
Amma wanda kake kokarin hada ni da shi shine duk yan uwan shi kafirai ne Arna
Wa yan da ba su sallah basu kuma da niyar yin ta ako da yau she,
Kafin ta kai karshen maganar ta baba yace kin ko ga idan ki shiga gidan shi kun zama ku biyu ke da shi,
Hakan zai sa ya rage kuncin rayuwar da yake ciki na yan uwa da rashi shakikin abokin shawara,
Anty Dije wace sai yanzu ta gane hikimar baba na wanan hadin da zai yi wa maryam da Yusuf,
Baba yace maryam kin san wanan yaron da dadewa kuma kina da masaniya daga wasu daga cikin halaiyar shi,
Kin ga ke nan abin zai zo maki da sauki don saboda sanin abubuwa da dama dakikayi a kan shi,
Yakare da cewa masu, kinga mu, wanan ne kadai gata da mutuncin da zamuyiwa Yusuf maryam, a irin yadda ya rike mu,
Maryam wace ta dago kai acikkn mamakin mahaifin ta wanda ke tausayawa wani bare bisa ga ita da take yar shi ta cikin shi,
Cikin kuka tace baba niko halin da zan shiga fa idan har an min haka,
Haushi ne ya kama baban don jin abin da yar nashi wace yake tinkaho da bugun gaba da ita,
Batare da ya bata ansa ba ya mike tsaye saboda takaici yana wa wanan shi hukuncin da na yan ke akai, bana son in kara jin komai,
Idan Allah ya kai mu lokacin mun dawo sai mu fara zan ce auren insha Allah,
Daga haka ya fita batare da ko ce madu mukwan lafiya ba kamar yadda ya saba ce masu a kullun,
A,zaune ya bar su kowa jikin shi a mace tun dai maryam wace ke ta sharban kuka alokacin,
Don jin cewa yau za,a raba ta da masoyin ta abin kaunar ta A,A,

Shigowar shi gida ke nan a gajiye daga office da kyat yake dan iya cira kafan shi saboda gajiyan da ya kwaso
Don yau su Alhaji sambo sun shigo garin tun da safe suke zaune a na wasu lissafi akan harkokin business din su,
Saman kujera guda ya samu yazube gaba daya maman Choima wace ke zaune daga gefen shi guda ta wani kalleshi a yatsune ta kauda kan ta gefe,
Saboda wani irin matsanacin haushin Yusuf din da takeji a yanzu,
Yamai da kan shi musulumi yakuma mai da diyar mutane dake zaune a karkashin shi,
Pipkin ne ya sheko da gudu daga dakin da ya fito,
Yazo ya fada mai ajiki yana mai oyoyo da dawo wan uncle din shi,
Rugumay yaron yayi tsam a jikin shi yana mai jin wani feeling akan yaron
Shi har kullun wanan yaron tausayi yake bashi a irin yadda zai tashi ya rayuwa babu mahaifi a tare dashi,
Kara rungumay yaron ajikin shi yayi ya dauke shi cak zuwa saman dining table, inda ya dire shi,
Sai,da suka kammala cin abincin su ya kira Nani din shi taje ta kwantar da shi saboda school da safe,
Shima a gajiye ya haura sama don yadan watsa ma jikin shi ruwa,
Wayar shi ce dake rike a hannun shi yaji tana ruri,
Bakuwar noba ce yagani don haka sai bai dauki kiran da wani muhinmanci ba,
Sai bayan fitone daure da alwala don ka,idan shi ce yin hakan,
A lokacin da yake sallah ya dinga jin wayar ta shi kira nata shiga,
Sai da ya idar yadauko wayan misscall goma sha daya yagani duk da noba guda,
Sai da ya zauna yakira mai wanan nobar da bai san ko waye ba,
Bakuwar murya ce yaji wanda bai san kowaye ba, ya karba mai sallamar shi,,
Tambaya yayi ko waye a layin tare da shi don bakuwar noba ce a gare shi,
Ansa aka bashi a dayan bangare da ce wa, hello don Allah da Joseph Emanuel nake magana,
Murmushi yayi kawai inda ya karba mai da cewa eh dashi kake magana,
Ok inji mai wayar yace kana magan da Aminu ne dan gidan, masuga dake a unguwar jankidi,
Look Joseph ina son sanin inda yaron da Ejoma ta taba haihuwa ne yake,?
Shin macce ce ta haifa ko namiji ina kuma yaron yake, ?
Tsuki Yusuf yayi baiko gama jin bayanin ba ya kashe wayan ,
Komawa yayi bakin gado yazauna ya mai harde hannayen shi a cikin juna,
Maganganun da,wanan guy din yayi a lokacin ne suke dawo mashi a rai,
Abubuwan da yace a gamay da Naimat din a wancan lokacin sune abinda ke mai yawo akai tankar yanzu akayi su,
Mikewa yayi zuwa downstairs dakin da Pipkin ke kwance ya turo a hankali,
Inda ya hango yaron a kwance cikin sleeping dress din shi fare masu dan adon pink colour,
Tsayawa ya yi daga kofan daki kafan shi a harde yana ma yaron wani kallon cikin tausayi,
Yasan dama something wrong zai faru da yaro din shi yasa duk kwanan na yake yawan tunanen al,amarin yaron,
Yadade gurin yana kallon dan yaron dake kwance dunkule a saman gadon shi yana barci,,,,,

Maryam wace ke jin cewa duk duniya ba mai son ta a wanan lokacin saboda babu mai kaunar farin cikin ta ashe,
Ba wanda yafi bata mamaki ga wanan al,amarin kamar Anty Dije wace, taki aiwatar da komai akan zancen,
Don a zaton ta Anty Dije zata iya shawo kan mahaifin ya yi hakkuri da zance hada ta da Yusuf da baba ke kokarin yi,
Idan har suna ganin cewa baba ya zai hada tane da Yusuf don wani ra,ayin kan shi to lalai sunyi kuskure sosai, da yin hakan,
Ita dai sam zuciyar ta yaki amincewa da zance Yusuf din akanta,
Mutumin da tun tsawon sanin shi da tayi babu wani zancen so ko makamanci soyayya a tsakanin su,
Shine yanzu za,a ce wai ta aura a matsayin mijin auren ta,
Yusuf din nada abubuwan da mata da yawa ke so a gurin namiji a rayuwar su,
Amma ita sam wa yan nan abubuwan basu burgeta haka kawai take jin tsanar sa,
Yanzune ma da suke dan sabawa a hankali tarage jin wanan tsanar da take mai,
Wanda tun farko ya samo asaline tun lokacin da yake dan mabiyi addinin Christian,
Tun alokacin take jin batason al,amarin shi a rayuwar ta,
Wasu hawayen ne masu zafi suka kara zo mata wanan karon, bata damu da wai ta goge su ba,daga fuskan ta ba,,
Jin alamar shigowar mutum a dakin baisa maryam wace ke kwance tana sharban kuka, dagowa ba,
Gefen gadon ta samu ta zauna takai wani lokaci ta kurawa kaunar nata ido sosai,
Tawani ramae acikin dan kankanin lokaci, tayi baki ga kukan da tasawa kanta duk ya wani kumbura mata ido,
Duk da farko tausayi take bata yanzun ganin da tai mata yasa ta jin tausayin ta sosai,,,,

SEENABU MAKAWA,
[4/7, 6:57 AM] ‪+234 703 981 8283‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

MA, LLIKI,YU,MMIDEEN,,,,,

BARKAN MU DA JUMMA,A YAN UWA MUSULMAI,,,ALLAH YA SADA MU ALHERIN DAKE A CIKIN WANAN RANAN
ALLAHUMA AMEEN👏


Hannun ta takai a hankali tadafa yar uwan nata dake a kwance tankar wace bata a cikin hankalin ta,
Sautin kukan na, ta ne tasake gaba daya a lokaci guda,,
Jawota Anty Dije tayi zuwa jikin ta itama hawaye takeyi saboda tausayin yar uwar ta,
Murya irin ta mai kuka Anty Dije tace, Maryam ki daina wanan kukan haka kada ki jawa kanki matsala,
Don dai kin san halin baba ko waye, mutun ne wanda bai magana biyu,
Kamar yadda ta fada maki cewa ke din tausayin ki ne yake ji har yasa kika samu fagen mai musu,
Ina son ki kwantar da hankalin ki kin sai dai cewa aure na Allah ne ai,
Kika sani cewa ko wani matsala yazo ya hana ayi auren,
Kamata yayi ki barwa Allah zabi akan al,amari ba wai ki kama butulce mashi ba, irin haka da kike yi,
Maryam sam banso tun farko har ki bari Yusuf yagane cewa ba kya son shi ba, haka,
Shima da ba wai baba ne ya haife shi ba ya daure ya nuna boyewar zuciyar shi,
Don may ke da baba ya haifa zaki kasa daurewa ki nuna biyayyan mahaifin ki,
Sai a lokacin ne maryam ta dago idon ta dake face face da hawaye ta kai kallon ta ga Anty nata,
Anty yakike son in yi da abin da raina baiso Anty ban taba jin cewa ina son uncle da soyayya ba arayuwata, tun farko,
Daukar shi nayi a cikin mu tankar wani dan uwar mu,
Amma Anty taya za, ace wai ni dangin mijina duk kafirai ne,
Da sauri Anty Dije ta dafe mata baki kafin ta karasa zancen ta,
Da cewa Assha maryam kin san abinda yasa Allah yai wanan hadin a tsakanin ku,
Kin sani ko shigar ki cikin su zai kawo sanadiyar musluntar wasun su,
Maryam Yusuf mutum ne wanda ke bukatar mace wace zata ba shi kulawa,
Saboda yana cikin maraicin rashin yan uwa na sahihi a tare da shi,
Yana son mace mai mutunci da sanin ya kama tane bawau irin wa ancan matan da suka laje mai don kwadayin dukiyar shi ba kawai,
Wani irin kallon tuhuma maryam ke aikawa Anty ta don jin wanan maganar da ta,jera a lokaci guda watau ke nan Anty ce ta ke son wanan hadin ko ?
Saboda son Yusuf din da takeyi tan,kar wani jinin ta can,
Wai may yasa Anty Dije take son al,amarin wanan bawan Allah haka ne,?
Muryan Anty ne ke cewa maryam kinfi kowa sanin cewa bawai don abin hannun Yusuf nake ra,ayin shi ba, ko ke da shi,
Tadan girgiza kanta cikin ban tausayi ta ce kawai don kyawawan halaiyan shi ne na alheri,
Wanda tun farko na hango su daga gareshi amma baida mataimaki,
Kanta takawar daga kallon yar nata, a lokacin da taji haka din,
Wani irin bakin ciki ne ya tokare mata zuciyar ta ta rasa yadda,zatayi da,shi,
Komawa tayi da kanta saman filo tana mai kallin silin din dakin a hankali ta lumshe idon ta saboda tuno wasu abubuwa da dama a zuciyar ta da tayi,,,,,

Kusan kwana nawa Yusuf bai kira yan dattijan da suka maye mai gurbin mahaifin shi ba gurin sa ma albarka da fatan gamawa da duniya lafiya,
Mahaifin jibrin ne ya fara kira inda suka gaisa a cikin ladabi da biyayya,
Sun dan kai wani lokaci yana mai bashi hakkuri da duniya, da mutanen cikin ta,
Sai kuma malam Abdulsamad da yakira shima kusan irin yadda sukayi da mahaifin jibrin ne sukayi da shi,
Sai kuma yai niyar kiran mahaifin Anty Dije wanda dattijon ke burge shi saboda irin halaiyar shi na sanin mutuncin mutane,
Da gaisuwa ne suka fara magana da mahaifin na su Anty Dije,
Inda yake mai magana kamar nasiha akoda yaushe,
Anan yake sheda mai cewa ya yi kokari ya shigo ya duba mahaifin shi,
Ya daina dadewa baizo gurin shi ba saboda hakkin mahaifa ya na a kan shi,
Sosai Yusuf yaji dadin wanan nasihan na baba shi yasa shi har kullun yake sun al,amarin wannan tsohon,
Ya kai wani lokaci, azaune gurin da su ka gama waya da mahaifin su anty dije din,
Hannun shi bibiyu ya tallabo haban shi da su yana mai tuna nen yadda zasu kwashe da mahaifin shi,
Murmushi yayi shi kadai don sanin cewa sai sun kwasa da mahaifin nashi,
Wanda har zuwa yanzu bawai ya hakkura da zancen shi bane,
Amma ya zai yi dole ne ya bi zancen dattijon nan don neman albarkan,mahaifa,

Ta gama shirya duk wani abin dazata bukata acikin yar jakar ta mai kama da handbag,
Kaya kala ukune tsab ta tura ciki sai yan abubuwan bukata kamar su, kayan shafawa, irin na mata da unders,
Wani katon hijab fari ta zunduma a jikin ta ta yadda ba mai iya gane cewa ta na dauke da wani abu a jikinta
Tafiyan ta a cikin natsuwa tare da dan jan aji kamar kullun,
Kokai waye ka ganta sai ka kara wai,gawa don ganin ta,
Can hanyar fita gari maimashin ya kai ta don ta tare motar da zai kai ta garin Bobi
Ana Sallah Azahar ta isa garin bobi inda ta samu jama,an gidan nasu mahaifiyar ta lafiya kamar kullun,
Duk sunyi farin cikin a ganin maryam din saboda jimawan da tayi bata zo garin ba,
Mahaifiyar dai kallon ta kawai take yi batare da tace mata komai ba,
Amma dai rayuwan ta ya bata cewa ba tafiyan lafiya yar diyar nata tayo ba,
Su biyune adakin yanzu tana zaune daga gefe ta na kallon yar diyar nata,
Daketa wasa da spoon a cikin abincin da kishiyar ta tasa asayo mata, abakin kasuwa,
Sunan ta, ta, takira har sai,da maryam din ta dan zabura sabboda nisan da tayi a cikn tunane,
Yar baba mai ke tafe dake ne haka a wanan lokacin,
Maimakon tai magana sai kawai tasa kuka kamar zata suke,
Bata cewa yar nata komai ba illa fita da tayi zuwa, dakin kishiyar ta,
Can sai gasu tare su biyu sun shigo dakin,hankali a tashe,sai kallon ta sukeyi,
Da kyat kishiyar ta tasamu Maryam ta tsakaita da kukan nata,,
Nan dai cikin hikima suka samu har maryam din ta dan labarta masu irin abinda ke tafe da ita da ,
Salati suka sa a lokaci guda suna mai, tafa hannyen su don mamaki,
Mahaifiyar ta ce ke cewa yar baba ina maki daukan yarinya mai hankali ashe ke ba haka kike ba sam,
Hankalin ki bai kai ba sam to yanzu mai kikazo gurina in maki,
In goya maki baya ki bijirewa mahaifin ki ko may,?
Kirufawa kan ki asiri tun muna mu biyu ki koma inda kika fito,
Kishiyar mahaifiyar ta ce ta dakatar da mahaifiyar na tada cewa ya isa haka ki bari abi a hankali,
Haba yaya zuwa tayi don ta ja min magana ga dangi, mu kawai ta barna min suna,
Kishiyar mama ce tace barin kira malam ina ga zaifi sauki,
A tare suka,shigo da malam mijin mama wanda fuskan shi kawai zai nuna ma cewa baiji dafin abin da tayi ba,
Maryam wace sai kuka takeyi a lokacin bata iya cewa komai don gaba daya yanzu tagane ba,a son ta kowa sai Yusuf,
Daga karshe dai shawara ya yanke akan cewa ta koma ita kadai batare da,wani ya rakata ba don kada agane cewa guduwa tayi,
Mijin mama yai mata nasiha sosai akan cewa tayi hakkuri da zabin mahaifin ta insha Allah bazata tabe ba,
Maryam tana share hawaye da gefen hannun ta ta mike jiki ba kwari don bin umurnin mahaifan ta,

Anty dije bayan tadawo ne ta laika ko ina bata ga maryam ba ,
Sai abin yabata mamaki saboda sanin cewa maryam dun ba ma,abociyar fita bane duk sanda taga dama,
Har gidan makwabciyar su ta leka da taji shiru amma sai matar tace aiba ta, shigo ba,
Hankali ta yakara tashi sosai amma sai bata kawo komai ba a ran ta,
Don haka tamike da, kan ta don yi masu girkin abin da za suci a ranan,
Har zuwa yamma ba maryam don haka hankalin ta ya kara tashi sosai,
Jin ana kiran sallah magarib ko ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login