Showing 180001 words to 183000 words out of 255288 words
Chapter 61 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
tare da kai yasan da hakan,
Don ruwa ba saa,n kwando ba ne ,
Dakata malam inji A, A yake cewa ina ruwanka da rayuwata da har zaka zo kana min irin wanan nasihar haka kamar wani malami,
Tubabbe irinka da bai ko iya karanta fatiha ba har zaka zo kace ni zakaiwa wa,azi,
Tun,da kai kagane cewa ina cin amanar tane ai in ka isa sai ka hana ta kulani,
Ko kafada mata cewa ga irin yadda nake ko ya kare yana wani shu,umin dariya, a karshe,
Azaton shi ya kashewa Yusuf baki ba zai iya cigaba da maganar shi ba,
Yusuf yai mai wani irin kallon na baka da mutumci yace ai ba sai na fada mata ba,
Don tagani da idon ta kuma tai kokarin confirming ko da gaske yaudarar ta kayi sai katabba tar mata,da hakan din,
So Wait and see what Will happen,
Ya juya kawai yabar gurin cikin kunar rai irin yadda musulmi dan uwar ka zai ma gorin addini ku,
Lumshe idon shi yayi yana mai jin kunar irin tozarcin da ake yawan yi mai akan zaman shi cikin musulmai hausawa,
Murmushi ya yi gami da,wani irin shu,umin murshi daya biyo bayan na farko,
Daga haka yamike zuwa bathroom don yai wanka yafita zuwa gidan Dad,
Anty Dije taimamaki acikin zuciyar ta jin maryam na cewa zata gidan su safiya tunda farar safiyan nan,
Murmushi tayi don tasan cewa, akwai dai saboda Safiya ce indan tazo kullun korafin ta shine maryam bata da zumunci,
Zaune take a dakin da aka warewa safiya da kannen ta acikin dangidan nasu mai gina irin na local people,
Hawaye wasu na bin wasu, ita ko,safiya wace ke zaune gefe acikin tashin hankali sai hakkuri take ba,
Duk da maryam din ta kasa magana balle ta fada mata abinda yafaru yasa ta wanan irin kukan haka,
Sai da ta,samu ta dan tsa,kaita kukan ne tafara tambayar ta ko may ke faruwa,
Sannu a hankali ta zayyanawa safiya yadda sukayi da A A din daren jiya,
Har saida takai karshe safiya tana sauraren ta bata ce komai ba alokacin,
Murmushi safiya din tayi da tagama jin may tace,
Ta ce gwada da Allah ya gwada maki kika gani da idon ki,
Ai yanzu zakiyar da da cewa dan iska ne macuci mayaudari,
Fuska a,daure maryam ke kallon ta tace ke nan ma ke kin dade dasanin kowaye shi ko,
Safiya tace tun yaushe maryam ai shima yasan nasani saboda acikin office din shi na kama,shi, red,handed,
Ido waje Maryam ke kallon Safiya don jin abin da tace, nan dai safiya ta bata labarin cewa taje gurin shi don tai mai magana akan takardun ta,
Shi ne ta samay shi tare da wata yarinyar yar IBO suna kiss,
Na shiga uku maryam tace tasake wani sabon kuka alokacin,
Safiya tace rokona yai tayi dan Allah in rufa mai asiri kada in bari ki sani ki, ki shi,
Harda alkawarin kudi yai mun nace mai ban so yadai daina abinda yakeyi,
Ni a lokacin maryam ke ce ke bani tausayi ina gudun kuyi aure ya dauko maki cutar kanjamau, a karshe,
Rinanun idanun ta da suka sha kuka sukayi jawur,da su, tadaga tana mai kallon safiya da su,
Tace cikin wani irin muryan kuka mai ban tausayi Safiya malam ya cuce ni wallahi,
Sai dai nagode ma Allah da daidai da rana daya bai taba nuna min true colour din shi ba,
Safiya tace ai kin san cewa yai min aike matar aure ce su ko wa yan nan na rayuwar waje ne kawai,
Safiya tadan dafa ta tace ki godewa Allah da bai sa yakai ga cuta maki rayuwa ba,
Kawai ki fita batun shi kiyi fatan Allah ya baki wanda yafi shi nan gaba,
Wani sabon kuka tasa ta shige jikin safiya saida tayi mai isar ta,
Ruwa safiya takawo mata ta wanke idon ta dashi sai faman ajiyar zuciya takeyi akai akai,
Duk yadda safiya taso su karya a tare maryam din taki don haka ta kyale ta kwanta sai barci mai nauyi ya kwashe ta abinka ga wanda baiyi barci ba adaren jiya,
Wayan ta yai kara safiya tadauka azaton ta ko A, A din ne tai mai tas sai taga ashe Anty ce,
Waje tafita don ta sheda mata tana barci hankali anty ya kwanta don jin lafiya maryam din take,,,,
Zaune suke a tangamaymayn falon su na gidan mahaifin shi dake dauke da jibga,jibgan kujerun da Yusuf ya sa masu da dadewa,
Mr Emanuel wanda ke zaune cikin shiga irin ta IBO, da,wani abu kamar zani ko buje daure ajikin shi,
Sai da yadan kurba ruwan Lipton din aka dafa mai as usual sanan ya kali inda Yusuf yake zaune yace mai,
Kada ka man ta da maganar da naima duk Christmas atare da mu zaka yi shi,
Yusuf yai yar murmushi kafin yace ai ba matsala saboda addini na ya yarda min da in shiga church don wasu yan dalilai,
Na ku daine sam ba a yarda ya,shiga muna gurin bautar mu ba saboda tsarkin sa,
Dad sai da naje Jerusalem na fara gane ce wa Muslim suna gaba da mu sosai saboda duk irin abinda sukeyi shine mutum zai yi acan,
Daga Alwala da kuma sa tufafi masu daraja sai cire, takalma don shiga cikin churches din,
Zaici gaba da bayani Mr Ema wanda tunda Dan nashi yafara bayanin abinda yagono a Jerusalem, yake ji tankar yana zuba mai ruwan zafi ne ajiki,
Duk da yasan gaskiyan maganar ke nan Yusuf ke fadi,
Yadaga mai hannu a lamar ya isa haka, bai son jin kareshen zancen,
Murmushi Yusuf yayi don yasan cewa gaskiya yake zaiyano mai baidai son jin zancen ne
Ga mamakin Mr Ema sai yaga Yusuf yadauko cup ya dan tsiyaya ruwan litop din yana kurba a hankali suna hiran business,
Inda mahaifin nashi ke fada mai cwa yanzu business din shi bai gane komai akai, saboda yaran dake gurin macutane,
Yusuf baiji dadin jin hakaba don haka yai alkawarin zai diba al,amarin company yai gyara akai,
Sai zuwa wani lokaci yai masu sallama ya nufi gidan uwar dakin shi, Anty Dije,
Bai wani dade ba a gidan don rashin ganin kowa yara,suna makaranta, maryam kuma bata gidan,
Don haka sai yaji gidan yai mai girma kamar bakowa a cikin shi,
Abubakar dan Anty Dije ya lake mai ya shuri yaron suka fita, tare,
Gidan man mahaifinshi yanufa inda yaje ya dan fara bincike akai,,,
Maryam wace yuwa yatayar badon taso tashin ba ta mike ba shiri a lokacin kusan karfe biyu saura,
Alwala ne taje ta dauro tazo tayi sallah,sai a lokacin aka shigo mata da wani kula green da plate guda biyu,
Danwake da mai da yaji ne da yankakken salad yasha kayan hadi,
Safita takaraso dakin bayan kaunar ta da tashigo da jug da cups a hannun ta,
Sosai tasamu taci dan waken ba kadan ba saboda tana,son shi dama,
Sai bayan sallah la,asar ta shirya tafiya zuwa gida
Zuwa dan a lokacin ta dan sake jikin ta, ba kamar yadda tazo ba,
Tafe suke da mai mashin din, da ya dauko ta daga, Usubu, uguwar su Safiya,
Suna tafe mai mashi na ta zuba mata surutu maryam wace sai addua, takeyi a bayan mashin Allah ya kai su lafiya don surutun yai yawa,
Yusuf wanda yake tafe daga gidan man mahaifin shi da ya ziyarta,
Kamar a mafarki yaga maryam a saman mashin,
Wani irin mugun mamaki ne yakama Yusuf din
Maryam akan mashin duk da ya ce mata baya so,
Sosai ya take motar ya cin masu, tana saye da wandon Jen's da wata yar riga karama pink sai katon hijabin da tasa, a sama, wanda baka gane irin kayan da ke a jikin ta,
Saboda mashin din da ta hau sai wandon Jen's din yafito don ta tattara hijab din kafatan saye da wasu plat shoes mai belts,
Horn yai masu amma sai mai mashin din yai zaton cewa ana masu ne don su kauce, a hanya,
Karo nabiyu da ya kara yi da karfi yasa su wai gawa har maryam din,
Fuskan shi daure tamau a cikin glass din motar da yake a ciki yana ja,
Kallon da tai mai kawai yasa ta fahinci mai yake nufi,
Cewa mai mashin din tayi ya sauketa inda a hankali Yusuf yazo gab da ida take ya Parker motar shi,
Shiko mai mashin sai kallon ikon Allah yakw yi kawai wanan irin tsaleliyar motar ga kuma mai tukin tankar bature,
Kudi tabude yar pos din ta daniyar ta bawa mai mashin din ,
Amma sai Yusuf yabashi dubu daya nan mutumin yai ta zabga godiya, har zuwa lokacin da ya bude gaban motar tashiga,
Sai a lokacin ta,ga Abubakar wanda ke barci a seat din baya,
A hankali yafara tafiya duk da gaban ta yana mugun faduwa bata yarda yagane hakan ba don ta wani dake afili,
Maryam yace acikin wani irin murya da ba,a,ta iya fassara shi ba,
May yasa bakya ji ne wai for Allah sake may kike ji ga hawa mashin kina hada jiki da mazan wasu,
Innalillahi ta iya furtawa don jin abinda yace
Wani iska ya fesar daga bakin shi saboda haushin da yake ji ko zai samu relief,
Yadan waigo inda take zaune a takure saboda sanyin A, C da ya fara ratsata,
Yakara cewa I hate dis wallahi mace a saman mashin macen kuma wai,,,,,,
Sai kuma yai shiru ya mai da hankalin shi ga titi,
Maryam wace tun tana jin haushi da takaici zuwa yanzu abin mamaki ya koma bata, kawai,
Sai ido ta samai yana ta masifa kamar wani mijin ta can
A,A wanda yake tsaye bakin titi wajen wasu kanikawa ya hango su tafe a haka,
Nan da nan wani irin gululun bakin ciki ya soke shi a zuciya,
May guy din ga dan IBO ke nufi da shi ne wai, akan maryam,
Don, dai ,something is fishing
Jibrin ne yashigo garin yakira noban Yusuf yaji ko yana inane a lokacin,
YUSUF ke cewa a cikin bacin rai gani zan shiga gidan sister, yanzu ok mu hadu a can Jibrin din yabashi ansa,
Yana kashe waya yadan juyo inda maryam take zaune ciki dakewar fuska ya ce cikin sasauta murya,
Maryam ke fa kikai min alkawarin bazaki kara hawa irin wanan mashin din ba, tsakani da Allah,
Maryam saboda rudewa da yanayin da yai magana
Tace Ya Yusuf dama kake son in fita da kafa tun daga gidan mu har Usubu gidan su Safiya,?
Shiru yayi dan a lokacin baida ansar bata da zai mai sanyi a rai don haka kawai sai ya share da ita,
A kofan gidan Anty suka samu su Jibrin din suna jiran shi,
Hannu ta mika da niyar dauko yaron inda akayi dai,dai da shima yamika nashi don daukan, yaron,
Kansu sne ya buge a lokaci guda ga kuma numfashin juna dasuke jin saukar shi tankar a hade suke sauke shi,
Maryam ce tai saurin jaye jikin ta tabar mai yaron don ya hi,
Yaron dake ta sharan barcin shi hankali akwance,
Ta dan tka kadan Yusuf din Yace dakata ki shiga dashi pls,
Cak tatsaya har zuwa lokacin da yakaraso zuwa inda take,
Mikamata yaron ya yi inda suka kara hada numfashinsu fiye da wanda sukayi adazu cikin mota,
Wani irin yarrrr taji wanda tunda take bata ta jin irin wanan yanayin ba,
Ga kamshi mouth fresh din shi tana ji kamar a hancin ta,
Sai kamshin turaen shi na THE da kaure ko ina ta juya agurin kamar yanzu ake fesa wa,
A hankali ya sauke mata yaron a hannunta da ya hade da nashi kamar bai sani ba,
Tajuya a hankali zuwa cikin gida da yaron rungumay a hannun ta kamar wace bata da lakka ajikin ta
Saida yaga shigewan su sanan ya juyo inda Jibrin da sama ila suke a tsaye bakin motar su suna kallo drama n secret lover's,
Gira Jibrin yadan daga mai cikin tsigar shakiyan ci
Daure fuska Yusuf din yayi tankar bai fahinci may suke nufi ba,
ZEEE. MAKAWA YELWA SEENABU
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
7โฃ3โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
A hankali maryam ta mika hannu don daukan Abubakar wanda ke barci a bayan mota,
Shima Yusuf a lokacin yakai hannun shi da niyar dauko yaron wanda ke ta barcin shi hankali kwance,
Hakan yakawo masu sanadin musayan numfashin su a lokaci guda,
Cikin sauri maryam tai yunkurin jayewa sai dai kuma ba bu filin da zata iya hakan,
Shi Yusuf din ne bayan ya lumshi idin shi cikin jin wani irin yanayi na daban,
Ya dauko yaron yafito dashi daga cikin motar mika mata yaron yai kokarin yi sai kuma hannun shi yadan kara,shigewa a na ta,
Yarrr, taji tai saurin kokarin saita numfashin ta dake barazanan tsayawa, don shock,
Nan ta dan wuce su jibrin dake kokarin fitowa daga cikin nasu motar shi da samaila,
Anty Dije wace ke kitchen a lokacin taji motsin shigowar maryam gidan a lokacin kuma ga Abubakar a hannun ta,
A nutse ta shimfide yaron wanda ke ta faman barcin shi hankali kwance kamar ko wani yaro,
Da mamaki Anty ke kallon ta na ina suka hadu da ita .
Ansa ta ba ta da cewa, a,saman hanya ina saman mashin muka hadu, dasu,
Daga haka ta juya zuwa ciki inda ta kwabe hijabin jikin ta saman kujeran dake kusa da inda take tsaye ta aje shi,
Wandon Jens din dake a jikin ta sai yar karamar rigar da tasa akai dai,dai iya kugun ta, ya tsaya mata ,
Shiyaba wandon ma,anan fito mata da surar jikin ta tsab waje,
Mazaunan ta da suka dan baje a baya suka sa Sharp din fitowa fili da kyau, sai kuma kirjin ta da,surar su ya baiyyana tsab waje,
Sam maryam ta shafa da cewa Yusuf yana a waje saboda hankalin ta na gurin da Anty ke girki,
Dai tsakiyar gidan ta dan bar kofan shiga ciki ita kuma bata karasa kitchen ba Yusuf da Jibrin sukai sallama a cikin gidan,
Sau guda yadan daga kan shi ya kallin wanan hallitan na maryam yai sauri kawar da kan shi yana mai cewa Barakallah masha Allah,
Ta wutsiyar idon shi yadan saci kallan jibrin ko ya ga irin abinda yagani,
Amma sai yaga shi jibrin hankalin shi na gurin Anty Dije wace suke ba,a da ita,
Mamakin wanan irin girma da kyau da maryam tayi a lokaci guda yakeyi,
Duk da ta ramay tadan yi wani faiyau da ita saboda yan maganganun dake ta tashi a kwanakin nan,
Gaskiya wanda duk yakawo sa hijab Allah ya saka mai da,alheri saboda ba karamin abu ya boye wa mata ba,
A hankali ya zauna yana mai lumshe idon shi tankar mai jin kasala,
Duk hiran da Anty da Jibrin keyi yana jinsu idon shi a lumshe suke,
Ya dan kai bayan shi a makarin kujerar da yake zaune akai,
Hannun shi yasa yadan shafo fuskan shi da su round ya furzar da,iskan da ya kumshe a bakin a fili,
Ismail ne ya kira jibrin din yana mai ce mai yazo mana su karasa gida ya shige ya manta da shi a waje kawai,
Jibrin ya ce mai idan ka gajine kawuce mana kawai kada ka takuramin fa,
Kasan ina tare da ogana ne,
Sai a lokacin Yusuf yadan bude idon shi da suke a rufe tankar mai barci a lokacin,
Yace kaje ka samay shi mana kada ya gaji da jiran ka, a waje,
Jibrin ya ce kai ina bai isa ya hanani abinda nake son yi ba, pa,
Katashi mu tafi 212 MOTOR, S ina son ina son in duba mota acan,
Da mamaki Jibrin ya ke kallon shi yace Man duk motocin sa ka bari a Abuja sai a kwantagora zaka sai mota,
Ansa Yusuf ya bashi a takaice da cewa basu da motocin kwaraine a gurin,
Jibrin yace su na dasu mana lates one masu kyau kuwa,
Sai bai kara cewa komai ba yai shiru kamar bashi yai magana yanzun ba,
รnty Dije ce tace kai amma ai maganar Jibrin gaskiya ne ko Yusuf kamar Abuja zai fi motoci manya ai,
Hannun shi ya dake a saman goshin shi yacire a hankali,
Saiga rinanun idanun shi sun fito waje jajir da su kamar mai ciwon kai,
Yace cikin wani murya mai rauni Anty ki duba fa ki gani for Allah sake ai maryam ce nagani asaman mashi, again,
Jibrin wanda ke kallon shi a cikin mamakin may zai sa ya nuna concern din shi haka akan wanan