Showing 66001 words to 69000 words out of 255288 words

Chapter 23 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1359

mata gaskiya,
Gashi ita kuma ta kasa fada mashi cewa taji maganar mahaiyar shi aranan
Yaya ma zata kalle shi, tace mai hakana don tasan zai ji mugun nauyin hakan,
Akarshe dai sai cewa tayi kasan aure nufin,Allah ne mallam, in Allah yakaddara hakan nafi kowa farin ciki da hakan,,,,,,,,,

Zaune yake tsakiyar saman gadon shi yayi dadaya da wasu takardu yana dibawa,
Abinda yafado mai alokacin sai irin yadda yaji, masu daura auren KB nayi wa juna alkawari,
Gyara zaman shi yayi yanamai tuna yadda yaga ana yawan cewa wai ai wani ya saki matar shi,
Ko kuma yadda yaji mutum na alkawarin cewa ya dauki nauyin ci da sha da suturan matar shi amma sa kaga matan gasunan a wahalce,suna wahala,
Kayan dake watse saman gadon ya dan har,hada saboda yagaji da aikin dayakeyi tun dazu,
Yana shirin shiga cikin bathroom don yadan watsa ruwa yana son zuwa club gurin wani mutum,
Wayan shi dake yashe a gefen filo, ce tai kara cewa, ana kiran shi
Dawowa yayi yadauki wayar nobar wanda yagani yana kiran shi, yasa shi saurin daga wayar shi,
Muryan Abdullsamada ce cikin wata irin sallama , yana cewa ya kake Joseph
Yana cewa baida kudi a,wayan shi da zai ishe shi yai maganar da yake son yi,
Amma ga Ibrahim nan Dan shi zuwa gurin shi daga haka wayar ta mutu dip,
Alamar kudin nashi sun kare,ke,nan, tausayin mutumin yakama shi sosai,
A ranshi yace,, may yasa wanan mutumin ke wanan wahalar haka, nan ya tuna da sanin da yai mai ada suna yara,
Manya,manyar shaguna gare shi guda biyu, tab da kaya yana bada sari da kuma sayarwa cikin fararshi mai sauki
Tunawa da yayi dattijon yace mai yaron shi ai zo gurin shi ,
Baisan ko yaushe bane zaizo don haka wayar ya dauka yakara kiran Abdulsamad din,
Nan dai ya sheda mai cewa, yaron wajen shi ne ya ce kan cewa zaizo gurin Joseph din,
Sai zuwa,safe yaron iso inda Joseph din ya tura azo mai dashi,
Ibrahim yaro matashi dan kimanin ashirin da haihuwa, kamili ne mai rikon addini,
Nan Joseph ya barshi har zuwa lokacin, da zai samu inda yasa shi cikin sana,ar shi,
In gari ya waye Ibrahim zai tafi wani massalaci mai nisa can kasan unguwar su,
Idan ya dawo kuma ,zai tsaya yadinga tillawa har zuwa wayewan gari,
Gashi da ladabi don har yan aiki yana basu girma sosai,,
Joseph a hankali yake kiwon halin Ibrahim don ya gwada shi yagani,
Idan kuma gurin abinci ne baida tsanda ko ra,ayi kamar wasu yara duk abin da aka bashi ,zai karba,
Sai wata rana Joseph yana daga ciki, sai ya dinga jin maman Choima tana fada tun yana sama yadan fara saukowa zuwa inda take.
Don jin komay ke faruwa,take fada haka sai ya iske da Ibrahim ne take masifa,
Wai,duk lokacin da sukayi abinci suka bashi sai bai cin nama yadawo masu dashi,
Joseph ya,dago kai a hankali, ya kalli Ibrahim, wanda ke tsaye gefe kan shi kasa,
Ibrahim may yasa kake haka inji Joseph, ?
Ibrahim wanda yadan gyara tsatin shi cikin ladabi yace ,
Brother bawai ina masu wulakanci bane, saboda addini na ya haramta min cin naman da ba musullumi dan uwana ya yanka ba,
Shiru Joseph yayi yana kallon Ibrahim yaro karami da,wanan akidar, acikin zuciyar shi,
Maman choima dake jiran taji Joseph yai mai cin mutunci don ita tana ganin rainin wayo yai masu,
Ji tayi Joseph yace idan abincin bai kwanta makaba arai zan dinga baka kudi kana zuwa gurin musulmai kana siya inaga zaifi,
Aiko nan tsohuwa tahau fada cewa ya daure mai gindin yai madu wulakanci,
Yakoma inda yafito mana waya kirashi da yazo zai ma mutane wulakanci,
Joseph yace cikin wata murya ta warning ma,ma stop dat pls,,,,
Maman ta wuce cikin kitchen, tana kallon naman,tana jujuya shi a, hankali,.tana masifa,,,,,,,,,,,


ZEEE MAKAWA
[2/21, 9:16 AM] β€ͺ+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Tafe yake cikin motar shi baka mai kama da siffan wani kifin ruwa, motar bakace wulk da ita,
Yana rataye da yar suit shi a gefen kafadar shi sai hannu yake sawa yana dan sa,sau,ta nicktie, din shi, dake makale a wuyar shi,
Air freshness yake son ya dauko ya, dan kara fesawa motar shi don shi al,a,dar shi ce sa kamshi duk inda yake,
Dan save din motar yajawo daniyar dauko dan kwalban dake dauke da ruwan, freshness din,
Wasu takardu suka fado daga gurin da yajo kwalban,
Takardun da ya manta tun shekaran jiya ne a motar shi,
Ibrahim yake son ya ba ya cika wani form, da yake son ya,je gurin computer training,
A gagauce yadan fesa kamshin, sanan yajawo takardun ya aje a gefen shi ta yadda zai iya tunawa,don kada ya manta,
Bayan ya Parker motar shi, yafito a,gajeyi don tun safe suke vurin wani taro da,akayi,
Da takardun a hannun shi ya wuce zuwa dakin Ibrahim,
Har yasa hannu zai tura kofar dakin, sai muryan yaron yani yana rera katun alkur,ani mai girma cikin wata irin murya maidadin sauraro,
Maimakon ya shiga sai yadan tsaya har nakamar minti biyar yana da yaron ke fidda,harufan ya da ya dace a cikin natsuwa,
Juyawa yayi yakoma hanyar cikin gida don ba zaiso ya katse mai karatun dhi
Tunda bai san lokacin da ya farawar ba, balle kuma ya katse shi,
A,hankali ya tura kofan falon ba kowa aciki a lokacin sai TV dake ta aiki, shi kadai
Tashan wasu Christos ne wai peace TV, rawa suke kwasa da i,ho,ce,i,hoce,
Wani iri yaji aran sa kawai sai yaji haushin su ,daukan remote din yayi ya kashe TV,
A hankali ya fara tafiya a saman steps din da zai sada shi da bangaren shi sama,
A kusan hawan karshe maman Choima tafito saye da wani dogon riga kanta daure da dankwali ta tsuke shi tam,
Tace wa Joseph, So, you, are back,?
You na welcome, wooo,
Thank u mama,
Your food don ready since,
Cikin wanan turancin may kama da yare ta dinga jefo mai magana tanayi tana hadawa da,harshen IBO din,
Ruwa ya watsa sai a lokacin yadan ji zuciyar shi tadan rage mai suyar da bai san dalilin yin ta ba,
Yaso ya koma gurin Ibrahim don yai mai bayani amma sai kuma ya kasa saboda gajiyar da ya kwaso,,
Don haka baima,sauko kasaba kamar yadda yasaba, indan yadawo yakan je gurin mama su dan yi hira,
Don kawar mata da zaman kadaici duk da yasan Ejoma tana iya kokarin ta da yar tsohuwar,
Washegari, musalin karfe takwas na safe, Joseph yasamu ya sauko tare da takardun Ibrahim na jiya a hannun shi,
Dakin nashi ya nufa don yakai mai yasamu ya cika idan zai fita yau sai ya tafi dasu ya mayar,
Tun daga yar hanyar da zata sadaka da dakin Ibrahim zaka ji muryan shi rarara, yana karanta suratul Maryam,
Jin maryam mu da yake ambata aciki yasa Joseph tsayawa guri guda cif,
Yace a hankali maryam in ,Qur'an, ?
Ji kawai yayi yai kundunbale fadawa dakin yaga may yaron keyi haka,
Ibrahim wanda ke zaune kamar a tsugune can wani dan sakon gado yana rike da Qur'an din shi yana mai karantawa,
Jin kamshin turaren Joseph dayayi a dakin yasa shi dan bude indon shi da suke a lumshe,
Don ya tabbatar da kamshin da hancin shi ya shako mai na Joseph din shine agaban shi ,ko,kuwa,?
In ko har shi din ne to ko jiya ma da,dare da ya jiwo wanan kamshi tabbas shi din ne a gurin duk da bai bude ido yatabatar da hakan ba,
Daidai ya kai A,ya" yadan dakata kadan yana mai cewa Sadakallahul,Azeen,
Ina kwana yai mai acikin yaren su na IBO, Joseph ya dan daga mai hannu yana mai cewa,sorry for disturb pls,
Takardun ya mika mai yace mai, ya cikia inda bai gane ba yasa may shi yai mai bayani,
Daga haka yajuya kawai yabar dakin yana jin wani irin abu kamar kasala tana lu,lube shi,
Sai zakakkan muryam Ibrahim ke mai yawo a kunuwa shi kamar a ciki yake wanan karatun,.
Lumshe idon shi yayi yabi bayan kujerar da yake zaune yadan kwanta,,

A hankali maryam ta ajiye, plate din da ta debo abinci, agaban Anty nata,
Wacce ke kwance saman dogon kujerar da ke cikin falon nasu,
Anty Dije tadan dago kai kadan ta kalli maryam wace ke kokarin juyawa don komawa dauko ma yar nata ruwan sha,,,
Cikin murya ta wanda je jin jiki Anty tace wa maryam ,
Maryam ba,zan iya cin wanan abincin ba don sam bakina bai min dadi wallahi,
Cikin dan marairaice murya Maryam tace anty dan Allah ko kadan ne kidaure ki danci, zaifi rashin cin da bakya, son yi,
Da taimakon maryam Anty Dije tadanci abincin kusan spoon, hudu, gana biyar ta mayar tana mai cewa ta koshi,
Bazata iya karawa ba haka don ji take tankar zata amaye dan wanda taci,
Gudun kada tai amai Maryam ta kyale yar nata tana mai tatara plate din zuwa kitchen,
Ido Anty tabi maryam dashi tana mai jin dadin irin kaunar da yar uwar nata ke yawan nuna mata ita da yaran ta,
Ringing Tone din wayar Anty Dije ne ya karade gidan nasu a lokacin,
Da sauri maryam ta isa inda,wayan take tana ruri, don ganin mai kiran yar uwar nata,
Yusuf Joseph tagani baro,baro a screen din wayar,
Kurawa wayar ido tayi har saida ya katse don kan shi,
A hankali Anty tadan dago kai daga inda take, kwance tana son tasan kowaye ke kiranta ya katse,
Don tana,son kaunar nata ta fada mata kowaye a layin,ke,kiranta,
Tana kokarin aje wayar ne wani kiran nashi yakara shigowa again
Dole ta nufi inda Anty take kwance, da hannu take mata tambayar waye akan layin,
Joseph tace tana kokarin kara mata wayan a kunen ta,
Da hannu taimata alamar, ta dauka kawai sai ta maida kanta saman hannun kujer a hankali,
Cikin muryan mai,kama da ta maijin kasala take magana,
Hello, ina wuni ?
Mai wayar batada lafiya ,
Juses crisis,
Dif maryam tayi tana mai cewa wa,iyazu,billlah,
Jitayi tankar ta aje wayan do haushi,
Sai jin shi tayi yana cewa may yasa may ta haka,
Zazzabine ke damun ta yau kwana biyu ke nan,
Jin wa,iyazu,billah da tafada dazu yadan sosai mai rai don yasan kalmace ta nuna wani tsari ga tsanar, abu,
Don haka yanzu sai yadan gyara harshen shi da cewa ayya sorry fa ina gaisheta pls anjima zan bugo mata,
Kagin ma ya kashe har maryam ta kashe wayar bin wayar yayi da kallo,
Sai mamaki kuma yake a ran shi cewa may yasa musulmai ba su iya boye felling din su in suka ji an ance Juses,a gaban su,
Maryam ko a hankali ta juyo gurin Anty tana fada mata abinda yace mata,
Yinin ranan duk a kwance anty ta ti shi saboda yanayin jikin ta duk ba dadi,
Ganin tana wahala da yawa yasa maryam bugawa yaya illiya waya tana sheda mai abinda ke faruwa xa yar uwar nata,
Wace duk kwanakin nan akwance take bata jin dadin jikin ta,
Ga wani amai dake zo mata yanzu duk abinda taci sai ta fitar dashi koda ruwa ne,
Hakalin Maryam ya tashi sosai cikin dare da Joseph yabugo muryan ta kamar na mai kuka take mai magana,
Tana sheda mai yadda ciwon ke matsawa yar uwan ta yanzu sosai,
Shiru yadan yi nawani lokaci har maryam din na,,zaton ko cewa ya kashe wayan ne,
Tace cikin siririyar murya, hello,,
Yace ina jinki kunje asibiti, ta girgiza kanta alokacin kamar yana ganin ta tace a,a
Saidai zuwa gobe insha Allah zamu tafi yaya yau ya bugo waya yake cewa mutafi goben,
Ok to barin yi magana da shi Illiya din tukun 'I will call you back,,,
Ok tau nagode tace tana mai kokarin aje wayar a lokacin shikuma yana mai ce mata ina Assalam yana lafiya ko?
Cikin kosawa da yin wayar tace mai yana lafiya sai anjima,
Itace kuma still dai ta,katse wayar kamar yadda ta yi dazu
Yai shiru yana dan mamakin irin halin Maryam na rashi son mutane
Yasaki ajiyar zuciya yana mai kara nazarin ta,
Tuna wa yayi da zancen kiran illiya don haka nobar shi ce ya kira,,
Bayan sun gaisane yai mai jajen ciwon matar shi sai, ya,kecewa
Dama ya bugo waya ne don ya tambaye shi ko yana iya tura mai doctor lawal yadiba matarshi
Don yadda akace mai tana jin jikin har ta kasa daukar waya daya kirata,
Ya, illiya yai murna kwarai da wanan taimakon da Joseph yai mai na turawa har gida a diba mai matar shi,
Saida Doctor Lawal ya iso gidan sanan Joseph yakira yake sheda masu cewa gashi nan shigowa,
Mamaki ne yakama maryam sosai don ganin cewa yasan yadda shari,ar musulunci yace ayi,
Am.a kuma da,tai tunane saitaga babu mamaki don yana tare da su jibrin yau da gobe dole yasan komai,
An mata allurai dakuma yan magunguna, sai fitsarin ta da akace akai gobe,
Bayan fitar doctor dakamar yan min tina sai,gashi ya kara kira yana tambayar ta
Ta girgiza kai tace ban san may doctor yace ba yadai mata allura,
Nan yai mata sada safe yana mai jaddada mata cewa ta tabbatar da cewa Anty tana shan maganin ta,
Joseph yaso ya shivo saidai yana tsoron irin masifar da tsohon shi ya za,zaga mai,
Inda ya bashi umurni da cewa indan har bashi yace yana son yazo ba kada ya fara yashigo garin kwantagora,
Tunda badon su ya haife shi ba da zai dinga kashe masu kudin shi abanza hakana,
Fada sosai yaiwa Dan nashi lokacin bukin KB da sukayi inda labarin komi yazo kunen Mr Ema din a lokacin ne yai kamar zai daki Joseph din don haushi,
Jikin Joseph a sanyaye don badamar zuwa yadiba halin da Anty nashi ke ciki, don gudun masifar mahaifin shi wanda sam bai son hurdan shi da yaran varin da yake amfana dasu,
Hannu yasa yadan shafo sanjen fuskan shi da ya kwanta mai lub a fuskan,
Ya furzar da yar iska mai dan dumi daga bakin shi,
Ibrahim ne yafado mai arai don haka yatadashi inda yai mai shatar mota zuwa kwantagora da kayan dubiya irin ta marasa lafiya,
Anty Dije tayi mamaki kwarai da irin kayan da Joseph ya bayar ,akawo mata tundaga Lagos har KG,
Lemo, Abarba, Ayyaba, Apple, kwakwa, carrot, water millow, pears, da,sauran su bar manja da garin can saida ya siya mata,
Waya anty tasa aka bugawa Joseph tana son tsi mai godiya na taimakon da yai mata, ga likita ga kayan marmari, da yayo mata,

Likita ya tabbatar da cewa Anty Dije tana dauke da shigar ciki na wata biyu da da kwanaki,
Maryam tafi kowa murna da wanan labarin cikin, wanda har uwar mijin ta tafara zance wai ya karo mata tunda anty tabar haihuwa,
Da sun dan samu matsala dasu yanzu zasu fara mata gorin taki haihuwa kuma ta hana auri wata,,,,


ZEEE MAKAWA
[2/21, 9:16 AM] β€ͺ+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


Yan uwa musulumai ina mika gaisuwa gare ku ,akan wa yan nan yaran makaranta yan garin misau da ke cikin jahar Bauchi da suka samu harin mota ta hanyar su zuwa kano ziyarar Arewa 24,wanan satin da yagabata suka mutu su ashirin ta re da malaman su,,
Masoya TAKARI novel da FUREN JUJI ina fatan za muyi masu adduan fatan samun Rahamar ubangiji, tare da mika ta,aziyar mu ga yan,uwa, da, iyayyen wa,yan nan yara, Allah ubangiji kasa Aljannan Fiddausi tazama makomar su,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

Mahaifin , Ibrahim Abdulsamad, yaji dadin yada yaga dan shi ya koma cikin dan kankanin lokaci,
Bakamar yadda suke zube a cikin gari ba da babu mataimaki,
Babu wanda ma yasan cewa suna cikin wani halin bukata na rashin yan uwa da galihu,
Yana ji yana gani matar shi ta gudu mai da yan shi mata, zuwa kasan su,
Wanda bakomai yasa shi kyaleta dasu ba sai tsabar yawan talauci dake cin shi,
Ki abinda zasu ci tunda yai gobara shagunar shi suka kone kurmus,
Amma sai yara,daya daga cikin musulmai wanda zai taimaka mai da wani abin,
Gashi har zuwa yanzu yan uwan shi na da suna kawo mai tayi akan ya koma akidar shi tafarko,
Babu komai acikin wanan sabuwar akudar da yadauko, illa wahala,
Dariya kawai yakan masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login