Showing 132001 words to 135000 words out of 255288 words

Chapter 45 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1366

Kokarin wuce jibrin dake son jin abin dake faruwa ya yi,
Sai a lokacin maryam tace mugu kawai azzalu,,,,,,
Saboda yadda ya waigo ta rai a bace idon nan sun kada sun yi mai jajir
Matsowa yayi a hankali batare da yadamu da jibrin na gurin ba ya dan nuna ta da yar ya,tsar shi ya ce
Ki kiyayeni fa don bata maki tsari,
Bata son nuna kariya a gaban shi don haka sai ta dake acikin tsiwa itama tace mai
In dan ban ki yaye ka ba fa sai may?
Kai ya gyada mata yace ok haka kikace ko ?
Zaki san kin taba Yusuf maryam,
Ya wuce fuuu ciki yabar ta nan tsaye tana kara kallon yadda kafar ta yai wani jajir a lokaci guda,
Wani hawayen takai ci ya kara zubu mata a fuska ta sa gefen hannun ta takara sharewa,
Sai a lokacin ta sauke wata irin ajiyar zuciya wanda bata masan tayi ba,
Amma zuciyar cushe da mamaki da tambayar abinda taiwa yusuf yai mata wanan salon muguntar,

Da murna Anty Dije ta tare shi tana kuma yi mai korafi cikin harara,
A she saida kaga cewa zaka shigo gari shine ka kirani, ko,?
Yai yar dariya ya sosa kan shi da key din dake hannun shi,
Ai don kada in kara laifi nai ya sa na bugo maki lokacin muna bayan mariga kadan,
Kai Yusuf karage wanan gudun wallahi, mutun baya tausayin kan shi,
Shigowar jibrin ya sa tai shiru nan suka fara irin ba,an da akeyi a tsakanin matar wa da kanin miji,
Falo Yusuf yashiga ya zauna ya bar su nan suna ta shan matar juna a tsakanin su
Shigowar maryam yayi daidai da isowar ta da ruwa a cikin gora taba Jibrin
Batare da anty ta kalli fuskan maryam ba tace maryam ba Yusuf ruwa don Allah,
Jibrin yai sallama da su yana cewa zai tafi ya kai tsara ban da yayo gida don kada zafin buth ya lalata su,

Zaune yake saman kujera amma zaman balance yayi alamar yana tare da gajiya alokacin,
Tashigo falon batare da sallamar ba, duk kan shi na sama idon shi a lumshe bai hana yagane cewa ta gurin ba,
Saboda kamshin da ya daki hancin shi na turaren ta duk a ranan humrah kawai tadan shafa,
A hankalo ya bude idon shi ya sauke su gare ta, gutun hawayen dake makale a fuskan ta yai tozali dasu,
Subbahanallahi ya furta da sauri har saida maryam din tadan razana
Tana waigen bayanta ko wani abu yagani yake kiran suna Allah maigirma haka,
Cikin wata irin murya ya fara magana,
Dan Allah maryam kiyi hakkuri ki yafe min pls, ban san cewa zaki ji zafi haka ba har ki kuka,
Banza tayi da sai ta dangwar da tiren da takawo mai abin shan aรงiki gaban shi,
Tana kokarin mikewa yai yunkurin kai hannun shi da niyar ya rike ta,
Komay ya tuna kuma yai sauri ya jaye hannayen shi gare ta,
A,rau,nane yakara fadin don Allah dai maryam kiyi hakuri
Wallahi wasa nake maki saboda naga baki tare mu ba kina muna kallon mamaki, kawai, shine nataka maki kafa don ki san ba mafarki kikeyi ba,
Kala maryam batace mai ba sai mikewa da tayi tana kokarin barin gurin,
Haba maryam ina mun daina fada dake haka don may zan baki hakkuri ki kyale, ni,?
Ganin zai sa har anty taji ta dauka ko wani abin ne yasa maryam,
Tai saurin dagawa daidai lokacin da shima yadago sai jikin su ya gogi juna
Cikin sauri tabar falon batare da ta ko waiwayo inda yake tsaye ba,
Sai da yaga shigewar ta ya karkada kan shi yana murmushi don dariya ma ta bashi,
Sai gab da magrib ya bar gidan zuwa gidan shi don yaje ya watsa ruwa,

Washegari zaune suke saman wani benci a kofar gidan Abdulsamad din,
Cikin yaren su suke magana ,
Abdulsamad din ne bayan ya gama jin bayani Yusuf a kan zancen Ibrahim da Ejoma,
Yadan gyara yace wa Yusuf aiko don yariyar ta musulunta bazan hana Ibrahim auren ta ba sam ,
Ba don komai ba sai don jahadin da zai yi, ceto rayuwar yarinyar da ga kafurci,
Kai Yusuf ya kada don ya kasa ban,banta sakanin shi da Abdulsamad wanda ya rike musulunci gam gam gam tankar addinin da aka haife shi a ciki,
Abdulsamad din ne ke bashi shawaran cewa idan yazo yadinga zuwa yana gaisawa da mahaifin shi tunda yafara saukowa,
Yusuf wanda dama yana da niyar yin hakan amma kuma sai yaji dadi da shawaran da aka kara bashi akai,
Yaji dadi sosai na rashi samun matsala akan zancen Ibrahim din da Ejoma wanda dama bai tsamani haka din ba daga dattijon,
Sun shirya cewa azo da ita nan kwantagora a musuluntar da ita zai fi don mutane su sheda musuluntar nata,
Daya tashi wani katon shago ya shiga yai wa mahaifin shi sayayya a ciki sai daga ciki babu abin maye sam,
Direct gidan su ya wuce don yasan cewa yanzu suna gida basu fita ba tukun,
Taron da ya samu yau ba yabo ba fallasa a kai sai dai shi bawai yadamu bane da yadda ake wani daure mai
Tunda yasan cewa ba wai laifi yayi ga Allah ba akai,
Sun danyi hira da mahaifin saidai duk akan viwon shi ida Yusuf din yake cewa zai zo ya kai shi asibitin Turkish da ke abuja don adiba shi,
Ga mamakin shi sai yaji mahaifin nashi bai yi musu ba akai, sabanin yadda ya zata zai ce bazai tafi ba,
Karshe Mr Ema din yake cewa Yusuf yana son wanan Christmas din yazo gida ayi da shi,
YUSUF bai musa ba sai cew yayi in sha Allah zai zo a lokacin,
Dan dattijo ya bata fuska shi jin, dan ,nashi yace Insha Allah acikin maganar shi,
Daga gurin mahaifin shi ya juyo zuwa gidan Anty Dije don ya yi breakfast,
Duk da yake a gidan mahaifin nashi yasa may su, suna batun yin break,
Maryam bata gida yau tunda safe ta tafi gidan su SAFIYA,
Ba don komai tayi shawaran zuwa wanan uguwar ba don kawai gujewa haduwa da Yusuf din wanda ke gari,
Tun safe sai dare zuwa bayan isha,i ta dawo daga u,subu can uguwar su safiya din,
Da yar fara,ar ta ta dawo tunda tana zaton ya,tafi ko tunda da Jibrin suka zo garin don haka tana zaton suna tare
Amma sai fara,ar ta ya lake lokacin da taji wanda ya ansa mata sallamarta,
"Sannu da dawo"
Abinda ya furta mata ke na,
A cikin matse fuska ta ansa mai da "Yauwa"
Wani murmushi yayi kama da yake, duk da dare ne sai da maryam tagane na mugunta ne,
Yau kuma unguwa aka tafi har dare haka,?
Kafin ta san ansar bashi sai taji duk ta dabur ce,
Harara ta sakar ma sa ta gefen ido tace,
Ko a kwai wanda zan wa aiki ne idan nadawo da guri,
Maryam ta shige dakin ta tana kokarin cire hijab din ta, amma ta tuna nen ina Anty taje cikin daren nan,
Don bata ji motsin ta a gidan ba,
Falon tadawo don ta diba dakin Anty tagani ko lafiya,
A hankali ya tako, har zuwa inda take tsaye kofar anty
Yana saye da kananan kaya sun karbe shi sun mashi mugun kyau,
Duk da a cikin dare ne kyalin agogon hannun shi ya wadatar da maigani yasan cewa gold ne,
Ganin shi yanufo inda take yasa ta saurin dan ja da baya kadan,
Gurin fridge yanufa yadauko ruwa a gora tare da hadawa cup din dake saman fridge din,
Baki da gaskiya ne kila ko yace a hankali, sai dai fuskan shi daure tamau,
Batare da tai magana ba ta kara danna mai harara, tace,
I don't want to talks more with you,
B/couse of your wickedness,
So please excuse me ta fada cikin murguda baki, ganin yayo kanta gadan gadan yasa ta saurin shigewa ciki da sauri,
Muryan Anty Dije ne ke cewa wai har yanzu maryam bata dawo ba ne ?
Kai ma da kan ka kake service din kan ka yau, maryam tana ina,
Kamar ba shi ba yace ina ga kamar sallah takeyi,,
Maryan dakejin ya kare ta tai mamaki sosai a,cikin zuciyar ta,
Kamar ba shi bane Yusuf Joseph wanda ta sani a da,
Mai daurewa bai magana bai dariya bai shi ga harkan kowa,
Kodai shigar shi musulunci ce ta sauya mai rayuwan shi
Muryan Anty ce ke kiran maryam din ciki daga murya,
Take gabanta ya fadi don tana gudun tai mata fada gaban Yusuf,
Sannu Anty da dawo tace adan daburce kamar mara gaskiya,
Haba maryam ga Yusuf zaune kin ki fitowa kiyi serving din shi sai da ya tashi da kan shi,
Cikin kwantar da murya tace, Na zata ba yanzu zai ci ba ai shiya sa ban fito ba na tsaya yin sallah,
Ke dai kan halin ki sai ke maryam haba yaushe zakibar bawan Allah azaune yana jiran abinci,
Daga haka batakara cewa komai ba itama maryam din ciki ta koma abinta,
Sai da ya gama takira maryam tace tazo ta kwashe kayan,
Murya kasa kasa ta yadda ba kowane zai ji abin da yace ba
Next time zaki yi bayani ai ,


ZEEE. MAKAWA
[3/24, 2:21 PM] 0mmer Farouk: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
5โƒฃ6โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ya Allah ka kara muna imani da tsoron ka azukatan mu
Ya Allah kabu ikon bauta, maka bauta mai tsariki a cikin aiyu kan mu,
Allah ka karawa Annabi dara da daukaka,
Allah kataimaki musuluni karufa mai asiri duk inda musulmi yake a duniya๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘



Ejoma da Ibrahim sun iso kamar yadda Abdulsamad ya buka ta dacewa su zo,
A gidan ร€nty Dije aka sauke ta saboda babu halin zaman ta agidan su Ibrahim ko gidan Yusuf ,
Kasan cewar gidan Yusuf babu mace acikin shi
Can kuma gidan su Ibrahim din yazama kamar gidan sarakkan ta ne, yan zu,,
Maryam ta school ko da Ejoma ta,iso don haka dakin Maryam Anty ta kai Ejoma din,
So,sai taji dadin yadda Anty Dije ta tare tankar ta taba sanin, ta ada, can,,
Saboda haka bata samu wani matsala ba da take tunanen cewa za,a gwada mata kyama da farko,
Da yar sallamar ta tadawo gidan cikin gajiya kamar yadda ta saba shigowa gidan,,
A, zaune Ejoma take cikin shigar wata yar bakar buje daidai gwiwar kafar ta,
Sai wani riga mai dan gun,tun hannu, kanta yaci kitson attachment, mai ruwa biyu,
Kumbar hannun ta duk an fente shi da jakumba ja,
Wani irin kallon mamaki maryam ke mata tana wani dan ja gefe guda,
Kamar wace taga wani abin gudu ko kyama amms tans iya kokarin taboye,
Ejoma ce ke mata sannu da dawo wa saboda ta gane maryam ranan da suka je gai,she da Yusuf da yai accident,
Ejoma ta kara da cewa ya hanya, ya gajiya, sister, ?
A, daddare tace, ma Ejoma yauwa, sannu ko,
Dakin ta ta shiga bata zauna falon ba yadda ta saba yi idan tadawo,,
Turus tayi a,dakin don ganin kayan bakuwar mai dan gun,tun buje a dakin ta,
Wani wari hannci ya bugo mata dashi na man bleaching,
Hancin ta ta dafe da sauri ta nufi inda taje aje room fresh din ta, ta fesa ko ina,
Muryam Yusuf ne taji a falon yana magana da Ejoma cikin yare,
Wani irin bakin ciki ne ya ziyarya ci zuciyar ta a lokaci guda,
Anty ce ta shigo dakin don shakar kamshin room fresh din da maryam ta fesa tajiyo shi daga falo
Tasan halin maryam tana iya shuka masu tsiya yanzu,
Sunan maryam din takira wace ke tsaye tana mai da kwankon turen kamshin,
Maryam ta amsa da na,am anty ?
Anty Dije tace cikin tausa muryan ta,
Don Allah maryam kada ki nuna wa wanan bakuwar wani abin kyama ,
Kaunar Yusuf ne anzo da itane zata musulun ta zuwa jumma, ita ma,
Maryam zatai magana anty ce ta tare ta da cewa
Kin san dai Yusuf ya can,canci komai a gurin mu,
Saboda irin yadda yai wa iyayen mu mu,ma kin ga ko dole mu karbi nashi uzurin koba gaskiya ba,
Kai maryam ta daga a hankali alamar gaskiya ne maganar anty,
Sai a lokacin maryam ta tuna da irin halarcin da, Yusuf yai mata a kauyen bobi gurin mahaifiyar ta yar kauye,
Wani irin ajiyar, zuciya maryam ta sauke mai kama da ta wahala,
Fitar Anty Dije a dakin shine shigowar Ejoma dauke da wani ghana most go,
Kaya ne irin dinki na musulunci, zalla akayi mata saboda tasamu sauki ibada,
Cikin murna ta aje kayan a gaban maryam tana kokarin nunawa maryam cikin jin dadi,
Sister ki diba kigani wanan kayan zan dinga sawa yanzu, zan koma kamar ku ni ma,
Tafada tana yar dariya, zama tayi gefen maryam tana cewa sister na dade ina son inshiga cikin ku amma sai ban samu damar haka ba,sam,
Tun ina karama wanan ijab da kuke, saw a kai yana burgeni sose,
Har ma da saya nayi , ranan eh, nasha duka sosai a gidan mu,
Tausay taba maryam da take fadar haka dole maryam din ta maida hankalin ta gurin sauraren Ejoma din,
Ejoma tace ba karamin duka nasha ba fa har da kaini gurin wani malam Aminu yayi,
Malam din wanda yashe, wai in yarda da Aminu aka zai sa iyayyena su yarda da musulun,ta ta,
Aminu ya cuce ni sister sai yanzu ne nake gane mistake wanda nayi akai,
Takare fadin maganar cikin tsigar kariyan zuciya da nadama,
Tace Aminu har ciki yai min na aihu, da shi, infada maki daga karshe sai ya yi rejecting nawa,
Shine brother Yusuf yadauke ni zuwa gurin shi, har Allah ya kawo min Ibrahim,
Haweye ne suka dan biyu a idon Ejoma, wace ke kokari hade yuwun bakin ciki,
Duk da warin bleaching da maryam ke ji gurin Ejoma bai hana ta kokarin dan dafa hannun ta ba tana cewa tayi hakkuri akwai Allah,
Daya bayan daya suke fitar da kayan suna dibawa acikin yabawa, da irin kyau su,
Marym a za ton ta Yusuf ya wuce ko amma may ?
Sai ganin Yusuf tayi zaune a falo ya tasa computer shi a gaba yana aiki a ciki,
Kamar ta koma baya sai ta gane cewa ya gan ta sai ,yadai nuna cewa bai ganta bane,
Maryam taye fes da ita ta na saye cikin wasu siket da riga na lace,
Dinkin dinkin siket din mai dan fitar da sura ne, balle rigar da shima dinkin shi,
Irin fited din siket din ne ya wani dan matse ta dagwas,
Sai dan kwalin da ta daura tun safe amma yanzu da yake a gida take tadan turo shi gaba,
Ta daure bayan a can kasan gashin da ke daure da ribon
Sai fuskanta ya fito wani dan feyau da shi kamar wata, A, class lady,,,
Sai kamshin turen tana Madina da take yawan amfani da shi
Da ya gauraye falon sai kamshi take yi kamar kulun,
Takalman ta na gida plat shoes suke saye a kafar ta,
Anty Dije tana kitchen tana tuka tuwon dare da take yin
Maryam sanu da taron bakuwar ki fa,
Nagode kwarai da yadda naga kin kar be ta a matsayin ta wace bata sallah kamar yadda nasan sam bakya,son hurda da irin su,
A sanyaye ta ce mai ai bakon ka rahama ce, a gare ka don baka san alherin da yazo ma da ita ba,
Ya lumshe ido ya sa hannun shi guda ya rufe computer ta shi a hankali,
Kallon ta yake yi a cikin natsuwa na yadda ta jera mai magana a,lokaci guda,
Ita ko maryam daga haka ta wuce abin ga zuwa gurin da suke aje abinci, ta bude kulan don taga ko may Anty ta dafa masu da rana,
Shinkafa ce dafa duka, dai dai lokacin da anty ta shigo falon ke nan da goyon Abubakar a bayan ta,
Maryam sai yanzu na tuna cewa dafa duka nayi ina Allah Allah in dan dafa maki wani abu sai kuma na shafa sat, wallahi
Cikin sanyin jiki maryam ta ce yar ta ai ba komai zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login