Showing 81001 words to 84000 words out of 255288 words
Chapter 28 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
wani English wear buje da riga masu kamar son shagewa a jikin mutum,
Sam har ta manta da cewa akwai mutun a gidan nasu,
Don haka bata tsaya sa wani hijab ba kawai falon ta fado
Duk yadda taso ta tare jikinta hakan bai yi ba saboda kayan sunyi mata masifar kyau,
Shiko Yusuf kallo daya yai mata yakauda, kan shi gare ta
Abinda baka ra,ayi ko ya yake bazaka sahi arayuwa,ba,
Tunda bawai wani abune atsakanin su ba baiko dauki ganin ta haka dayayi dawata manufa ba, shi,
Itako sai kokarin kamay,kamay takeyi, don kada yakalli surar jikin ta,
Wayar shi ce ta sa kara alamar kira,,
Aisha ya furta a hankali, sai kuma alamar yar murshi dayayi alokacin
Hakan ya,tabbatar masu gabadayan su cewa da Aisha yake wayar,
Maryam ta juya bayan tace wa Anty ba ta jin yunwa,,
Tashige abinta batare da tatsaya jin kwam ba awayar da yake yi,
Bai wani dade ba yai ma anty dije sallama yace zai je ya shirya yazo tadauki Assalam su tafi, massalaci,
Shiga,sosai yayi na Muslims farar shadda ce dinkin ta,zarce
Wani hula yasa mai ruwan, siminti, sai takalma shige hular kan shi,
Kamshi agurin shi ba,a maganar, yana rike da wani bakin tasbaha kiran China,
Bai wani tsayawa ba don yana sauri, luckily ya samu an shirya Assalam ko, suka tafi,
Maryam wace ke tsaye daidai kofa ta sauke wani sanyayar ajiyar zuciya,
Ta waiga ida anty take tace cikin tabe baki yayi sa,a gaskiya da Allah yanufe shi yakarba kira,
Murmushi Anty Dije taimata tace abin ai daga Allah ne maryam,
Shiyasa mutum idan kasan farkon shi aibakasan karshen shi ba,
Sun isa massalaci anata zuba sahun a ko wani bangare,
Tareda Abdusamad sai jibrin da KB da suka uso da ranan nan, sai Ibrahim da yake acikin su,
Ido akan su caaaa wasu duk da a cikin massalacine harda leke sukeyi idan an nuna masu shi,
Hakan sai bai wa Yusuf dadi ba saboda irin yadda ake mai babu ko boyo, aciki,
A, cikin zuciyar shi yace, to komay kuma ya yi da ake mai haka,
Don shi ai tsan mani yayi za,ai farin ciki da kasancewar shi acikin wanan massallacin mai,albarka wanda yatara dinbi musulmai,
Duk da ana sallah amma wasu yan gulma idon su yana kan shi don suga yaya zaigi sallah shi,
Bayan an sallamay sai kawai sukaji ana, musuluntar nashi a she mahaifin jibrin ne yabada wanan sanar wan
Aiko mutane sai nunafarin cikin su sukeyi don dama andade ana rade radi,
Da kyat suka samu su kabar harabar massalacin don yawan jama,a masuyi mashi barka,
Labari ya iske Mr Ema cewa ga abinda yafaru a massalaci wanda wasu musulman mune suka kwarmatawa wasu daga cikin Ibon garin,
Mr Ema shida yan tawagar church har mada na wasu churches din sukayo kwamiti zuwa gidan Sarkin Sudan, cikin fada,
Don su azaton su, zadu ita shawo kanshi, jira sukeyi su gama aiwatar da shirin su,
Sai gashi anyi anoucement, a massalacin jumma,a cewa ya musulun ta,
Sarki yasa aka tare su, cikin dan mutunci,
Inda yasa sugabatar da abinda,ke tafe dasu
Rankashidade, muna karan wasu yaran musullumine gurinka cewa su ja yalon mu zuwa ciciin Muslims,
Batare da bakin mahaifinci ba,
Eheh, shine munzo mu fada ma,ka, shewa, muna son abamu yalonamu, afido dashi daga shikin isalama,wanda ya ciga,,,
Bayan mai martaba yagama jin korafin su ne, yadan magana da galadima,da waziri,
Galadima ya ari bakin mai sudan yai masu bayani kamar haka,
Muna son kuzo da yaron na ku nan don muji ta bakin shi, sanan, a kira wa,yanda suka maidashi ciki,
Fita sukayi daga wajen fadar maimartaba Sarki Sudan
Suna ta kus,kus ta yadda zasuyi su kawo Joseph gurin sarki,
Shi Mr Ema dakanshi, ya kira Joseph da wayar shi, kira daya ana biyu ya dauka,
Joseph come nd meet me in mai Sudan palace now,now
Yusuf wanda ke tare dasu KB suna wani estimate, din kaya,
Abin yabashi mamaki ya kalli su KB yace masu cikin bacin rai wai Dad dina ne fadar mai sudan,
Duk kan su cikin mamaki, sukace gurin mai Sudan fa,?
Sun so su bi shi sutafi tare amma yusuf din yace su bari kawai zai iya zuwa,
Mr, Ema tare dasu Ekewa, da su Barnabas Mr Ema wanda ke zaune cikin damuwa ya saye da wani rigar yadi mai hoton giwa, dajan colur, sai wani jar hula dayasa akan shi,
Yana rike da sanda a hannun shi,,maikama da kan gunki
Kallo guda zakai ai kane cewa yau rayuwar shi ba tada dadi sam,
Su na ganin shi sukayo kanshi caaa kamar zasu ciye shi danye acikin yare suke magana suna cemai, ya taimaki rayuwar shi kada ya bari wasu su rude shi,
Kowa daga cikin su da abinda yake fadi, don dai kawai ya amsa cewa bai musulunta ba,
Zazaune suke gaba dayan su a gaban,mai sudan, Inda mai Sudan yasa akara fadar abin da sukazo dashi
Yusuf na sauraren yai shiru saboda ladabi har lokacin da aka gama bayani akan komai,
Maimartaba ya kurawa Yusuf ido har nawani dan lokaci,
Sai yagano cewa Yusuf wayayye ne bazai ce Yes ba, yace No ba kuma
Don haka sai sarki yace mai samari kaji bayanin da iyayyen ka sukazo, dashi,
Zaman shi ya gyara cikin ladabi yakalli inda maimartaba yake, yace,
Assalamu Alaikum warahamatullah,
Sauran musulamai dake gurin suka karba mai kamar yafda sharia ta ce ayi,
Suko gaba dayan su suna jin wanan kalaman da ya fara magana da ita, suka dau da cewa
Emba, Juses crisis,
Oluwa, inji wani pastor yan olumba,olumba, yace cikin kada kai alamar takaici wai,,
Yusuf yace a gaskiya babu gaskita daga cikin zancen su,
Saboda ni yanzu nakai munzalin da ,zan daukar wa kaina duk abinda nake ra,ayi,
Heh Joseph come to your sense pls ?
Don't deceive your self
Magan ganu iri iri suka dan fara cikin, jin haushi da takai ci,
Nan da na fadawa suka daka masu tsawa dole suka natsu sukayi shiru
Yusuf yaci gaba dacewa,
Nazama musulmine ba tare da sda shawaran kowa ba,,
Ra,ayinane kawai yabani shawar gane hanya afificiya ta isalama,
Kai Na, lie, woo,
Wani bafade dake, kusa da mai maganar ya watsamai bulala tauuu,
Yace mai cikin daka tsawa behavi your self
Ganin haka yasa du natsuwa dole zuciyar su na suya
Yusuf yaci gaba da cewa, banzama musulumi ba saida nasamu kwararar hujjoji daga Alkur,ani maigirma,
Eyy,Eyyyy, he's finish wooo,
Abinda sukace gabadaya kusan lokaci guda ke nan,
Watau, Joseph ysi nisa har da Alkur,ani ya,yarda dashi,,
Yusuf yace saida na hada duk wani hujja wanda zanyi depending a kai sanan nida kaina nakai kaina wurin limamin central mosque na Abuja ya musuluntar da ni,
Saboda haka duk wani wanda ke zargin cewa wani ne yajani zuwa cikin islama ba gaskiya bane,
Ni YUSUF ban musulunta akan abin duniya ba ko mace ko aboki,
Na musuluntane saboda Alkur,ani maigirma,
Sai duk wanda ke cikin fadar musulumi suka dauka gaba daya dafadin Allahu Akbar,
Yace nakai lokacin da zan zabawa kaina abinda nake so daga addini, sana,a da kuma iyali,
Cheer, God wooo,
He, don go far,
A nan maimartaba yai masu warning akan cewa duk wani wanda ke son kawo mai fitina ko tashin hankali acikin kasa ashirye yake da yadauki mataki akan mai shi tunda har wanda suke magana yace ra,ayin shine shiga addinin da yakeso don yakai shekara talatin, yanzu,
Kuka sosai Mr Ema yadinga yi acikin fadar mai martaba yana fadin cewa a taimake shi amayar mai da danshi cikin Christianity,
Amma ba wanda ya bashi goyon baya haka suka tallabe shi zuwa bakin motar dasukazo dashi yana kuka, wi,wi,
Yana kiranan sunan joseph yana zuba gwalancin su,
Shiko yusuf dama yarigasu barin gurin don haka gidan Anty Dije yakoma,
Saboda yadan samu relief of mind, din shi sai,dai kana ganin yadda idon shi ya rine kamar garwashi zaka gane cewa, yana cikin tashin hankali,
Yadan dade yana waya da Alhaji sabo inda yake fada mai abinda yafaru dashi yau da mahaifin shi,
Maryam wace ke cikin bayi a lokacin tana jin abinda yake fadi har zuwa lokacin da yashigo ciki da rinanun idon shi,
Falo yazauna jagab saman kujera two siter dake cikin falo,
Maryam wace kafin yashigo,,tafito ko daga bayin
Tana cikin shigar atamfa, buje da riga masu ruwan multi, colour,
Dinkin yai mugun karban jikin ta kayan da tasane tai adon jin ma,a dasu, da rana,
Taso taje ziyara gidan su safiya amma sai taga yau Anty bata jin dadin jikin ta sai tafasa shine tashiga bayi ta gyara jikinta don tana fashin sallah,
Acan ne taji muryan Yusuf din yana waya dawani yana fada mai irin yadda yaji gamay da mahaifin shi,
Wani irin tausayin sa taji don tasan da zafi ace mahaifinka na kuka akan ka,
Inbadon addinin gaskiyabace kamar yadda Yusuf din yace da sai ya fasa yakoma gurin mahaifin shi
To amma ba,zai iyaba sam ya shiga isalama kenan har mutuwar shi acewar,
Bashiga bafita shiga sojan badakkare,
Tana bude labulen dakun tafitowa suka hada ido, ya sakar mata rinanun idanun shi da suka kada sukai ja ,
Kan ta, takawar gefe cike da jin tausayin shi alokacin,
Direct gurin fridge tanufa tabude tadauko kwalin madarar youghot mai sanyi mai hoton bafillata, na company Mrs Ghali, youghot,
Ta hado da cup din glass bata tsaya ba sai,gurin shi direct,
Ta, dan rage tsawonta ta fara zuba wa acikin cup din a hankali,
Sai a likacin yuduf ya bude idon shi dasuke lumshe yasauke su akanta,
Ta mika masa youghot din a hankali, batare da ce mata kala ba yakarba ,
Yakafa kai a hankali yana lumshe ido don sanyi da gardin youghot din,
Saida ya shanye glass guda a hankali ya cire cup din abakin shi murya kamar mai rada yace nagode Maryam,,,
Maryam ta mike daniyar barin gurin don jin ajiyar zuciyar da yayi,
Yace may ye sunan wanan madarar,
A, hankali tace Mrs Ghali, youghot,
Masha Allah yana da kyau,,,
ZEEEE MAKAWA
[3/11, 10:18 AM] +234 808 968 1079: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Garin duk yai mai zafi, gabadaya baya jin dadin rayuwar shi sam,
Don haka ya yanke shawarar ya koma gobe ,gobe tun bai dauki wani lokaci ba,a garin saboda bai ita jure ganin mahaifin shi a haka
A ranan bai kwana gidan su ba hotel ya kama,,
Da safe ya shigo gidan cikin shirin shi na tafiya, yaso yatafi batare da yayi sallama da Antysa ba,
Amma sai yaga cewa zai dade bai shigo ba don haka yakamata su,yi sallama, da Assalam din shi,
A bakin kofa sukayi kicibis da maryam wace ke kojaein fita siyo madu breads na break fasta,
Idon shi ya kade yayi ja, kamar mara lafiya,ya wani fada,
Dan Rabawa maryam tayi gefen shi ta wuce inda zata,
Saidai jikin ta ya,ba,ta, cewa yana kallon ta bayan ta wuce,
Maryam tashigo rungumay da breads har guda biyu, a gefen hannun ta,
Anty Dije tace kagani ai nace kabari,ta dawo ba nesa ta, tafi,ba,
Nan Maryam tagane cewa tafiya zai yi, acan cikin ziciyar ta sai taji tausayi shi yai dan mata yawa,
Don ta san cewa hakan nada nasaba ga maganar da taji yanayi jiya awaya
Bayan maryam tashiga a,gagauce ta hada mai ruwan shayi tafito dashi rike a cup, tanufo shi,
Idanu ya zaro don bai tsanmani hakan ba,daga wanan yariyar
May yasa yanzu take sasauta mai fiye da,da,?
Bakin,ta na dan rawa, tace, gashi na hada mai ai Anty,
Sai yau zata ce magana mai kama da ta mutunci tashiga tsakanin su,
Hararan ta ya yi ,yace, wanan ai yai min yawa, ga kuma zafi,
Kanta na kasa duke saboda bazata iya jure irin kallon hararan da yai, mata ba,
Muryan Anty ce ya katse su adaidai lokacin da yake shirin karban cup din tea din
Anty Dije wace je cewa gaskiya, Yusuf wanan tafiyar dai kamar ba shiri zakayi ta,
Nan da nan idon shi suka canza zuwa tsantar bacin rai,
Ba Anty Dije ba har maryam da ta dauko mai wani dan stol a falon su saida, taji wani iri,
Yace cikin dasasar murya, mahaifina ke son kawo min matsala Anty,
Yaki hakkuri da zancen musulunta na sai daga hankalishi yake yi,
Duk da nasan cewa zuga shi akeyi akaina, lokacin yadan fara kokari kurba shayin da maryam takawo mai,
Ammakin shi sai yaji baida mugun zafin da ya,zata zaiyi,
Idon shi yadago ya kalli inda maryam take tana kokarin aje mai wata yar kujera irin ta zaman mata, hannu ta na dauke da ruwan pure water leda,
Itama anty zaune takai saman farin kujerar roban da maryam ta aje mata dan nisa kadan da Yusuf din,
Nan yaci gaba da fadawa Anty Dije yadda duk suka kwashe da maihaifin shi tare da sauran yan kabilar su,
Yadago idon shi rinannu ya sauke su ga, maryam daniyar yace mata ta kwashe kayan tea din ya koshi, saboda bai faye cin abinci da safe ba haka,
Idon ta suna a rintse tana mai jin zafin labarin da yake fadawa Anty ta,
Muryan shi da taji yana cewa nagode zan tafi kada inyi rana ahanya, don gobe akwai inda zantafi indan Allah yakaini,lafiya yau,
Sai ji tayi bakin ta na furta,zancen da takeyi a zuciyar ta,
Kadaure da,duk wani, kalubalen da zaka samu daga gurin su saboda bara,zana ce kawai suke kokarin yima,
Ko zasu iya juya ka idan sunyi hakan don kawai suyi galaba akan ka,
Kawai ka bar su suyi tayi watarana zasu daina gaba daya don zasu saduda,dakan su,
A,cikin mamakin ya ware idon shi yana kallon ta, yau itace ke nuna concern din ta akan shi saboda yazama musullmi dan uwan ta,
Ashe dama saboda akidar addini take gwada mai wanan tsanar, tunda yaga suna dan hurda da Jibrin, sai KB ne ba su shiri har yanzu,
Saida takai aya tai shiru dan kanta daga haka tajuya da nufin tabar gurin,
Anty Dije ce tace mata maryam amma fa kinsan cewa mahaifin shi, ne taya zai yi mashi haka,
A ladabce tace to, anty baki ganin cewa suna iya jan ra,ayin shi yakoma masu,,
Murmushi yayi yana mikewa, tsaye yadan kalli inda take yace, kina ganin kamar zan iya komawa cikin su ko,?
Kanta ta sada kasa saboda kallon ido da idon da suke fuskanta a,tsakanin su,
Yace ai,ni na shiga ke nan insha Allah sai mutuwa kuma,
Ya juya gurin Anty Dije yana mai ce mata idan Assalam ya tashi sai ta, massa sallama,shi yatafi,
Kudi masu yawa yadebo daga cikin aljihun shi ya aje wa anty a gefen , yasa kai yafita,
Bayan fitar shi, wajen minti uku Anty takasa koda motsi balle magana, saboda yawan kudin da ya aje mata,
Maryam ce ta zo da zuciyar ta daya ta dauki kudin tafara kirgawa,
Abin a tagani, yasanyata saurin dago kai ta kalli yar nata, cikin mamaki tace dubu dari Anty,
Da sauri anty ta dago kai ido waje tace dari,fa Maryam,?
Dan tsuke fuska Maryam tayi, tana kokarin mikawa Antyn ta kudin,
Allah yakai idon yar uwar nata a fuskarta, cikin mamaki tace wa Maryam, may kuma akati,
Maryam wace dama ta cika fam, tace to shi ance masa kina kwadayin kudin shi ne kokuwa,
?
Cike da mamaki yar ta ke kallonta don maganar ya daure mata kai,
Ban fhince ki ba inji Anty Dije,
To may da,zai wani baki kudi haka, batare da wani, dalili, ba, ni wallahi ban son abinda mutum zai min gori akansa sam,
To ke Maryam may ye naki aciki da har zaki dinga wanan zance,
Dama tun jiya yake ce min, zai bar kudi wanda zan dinga mashi sadakar kosai da, sugar duk jumma,
Sai a lokacin Maryam ta danji dadi har cikin ranta don azaton ra yagan su mabukata ke nan, shi yasa yabasu kudi,
Kwana biyu bayan tafiyar shi sanan mahaifin shi yasan cewa yabar gari,
Don haka ya kara daukaka fushin shi, don yasan cewa da gaske Joseph keyi yabar Christianity ke nan har abada,
Ya jijiga kan shi shi kadai a zaune saman kujer da ke bakin gidan man shi, yace impossible,
Waya yadauka yakira wani aminin shi dake zaune a Lagos din
Yusuf wanda a lokacin yadawo agajiye daga inda suka tafi can kusan boarder,
Ya zube saman kujerar dake cikin falon nashi, yana mai da numfashi guda guda
Kokari yakeyi yadan sasauta aninin da ya ke saman wuyar rigar shi don yadan ji shahakat,
Ido biyu yayi da wasu murda murdan katai cikin bakaken kaya da wani bakin glass a idonun su,
Addu,an da