Showing 96001 words to 99000 words out of 255288 words

Chapter 33 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1381

โ€ช+234 803 381 3188โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
4โƒฃ1โƒฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Yusuf ya canza gaba daya ya wani murje yayi fari sosai da yar jiki daidai shi,
Wasa ya keyiwa Abubakar yana cewa wanan little friend din bai sanni ba , ama baka kai abokina kyau ba,,
Muryan ta na rawa ta iya furtawa Anty ta cewa zata dan fita,
Sai,dai kuma Yusuf din yadan tare hanya ta daidai inda zata dan wuce, zuwa waje,
Yaro nai yai sallama yace wai ana sallama da Maryam a waje,
Maryam da ke shirin fita hanya kawai take nema takumaji muryan Anty ta nacewa dan Allah maryam dan dauko wa Yusuf kujerar roba a waje,
Maryam wace dama a cike take don tasan cewa A,A yagajine har ya turo yaro,
Don yana zaton ko ta manta dashi a waje saboda motocin da yagani a kofar gidan su yasa,shi, zaton baki sun masu yawa ne,
Batare da tai magana ta juya tanufi inda kujeru suke aje a,dan wani kwanar da fridge din su na waje yake,
Kanta ta kawar gefe har ta isa gaban shi,ta ajiye mai kujerar, cike da jin haushi ta aje mai daidai inda yake tsaye,
Yana yawan dagula mata kwanciyar hankalin ta idan ya na a gari,
Ya zauna a hankali yana mai cewa bissimillahi, azu,bikalamatillah tammah
Kafin Anty ta takara sata yin wani abin da saurin ta tabar, gurin,
Tana shan kwana suka hada ido da Yusuf yasakar mata wani tsadadden murmushi wanda duk duniya ba mai mata irin shi, sai Yusuf amma ta kasa gane ko ta may ye,
Saidai da yake tasan cewa, murmushi wani part ne na rayuwar shi sai kawai ta share zancen
Kanta kawai takawar gefe cike da kara jin haushin shi,
Kafin ta karasa ficewa sai ga muryan Anty Dije na cewa,
Ki dauko mai ko ruwa mana maryam kinsan cewa, ba wuta falon da zafi,
Murmushi da yafitar wanan karon mai sauti ce don har Anty taji shi,
Komawa tayi cikin wani irn bata rai kamar bata taba dariya ba arayuwar ta,
A cikin tire ta jero, kayan shan har da da su cup,
A gaban shi ta ajiye kayan, shan tasan cewa idan bata zuba mai ba Anty zata kara kwafsa mata dole badon taso ba ta dan duka don ta zuba mai,
Kamshin turaren BUSSHIRAH da ta shafa ya gauraye ma hanci har saida ya yar ajiyar zuciya,
Muryan yaron dazu ne ya ratso kunnen su, yakara sallama yana cewa wai yace tazo don ba dadewa zai yi ba,
A lokacin Maryam tai yunkurin ta mikewa, sai ji tayi yana cewa ta karbi Abubakar daga hannun shi, pls
Sosai suka shaki numfashin juna tare da hada idon su a lokaci guda,
Maryam ce tai saurin kauda kanta gefe tana mai jin wani irin abinda bata taba jin shi ba arayuwar ta,,
Babu shiri tabar gurin da sauri daga haka tafita zuwa kiran da A,A ke mata,

Sai zuwa dare, ya shirya zuwa gurin mahaifin shi, saboda bazai iya kwana a garin batare da ya tafi ya gan shi ba,
Mr Emanuel yana zaune tare da abokan shi su biyu da suka zo mai hira,
Kasan,cewar shine mai hali acikin su dan sauran basu kai shi arziki ba ko kadan,
Duk idan an fara labaran NTA shiga yakeyi don kallo da sauraro,abinda kasa ke ciki,
Don haka sauran abokan hiran nashi suka mike zuwa gidajen su,
A kofar get din gidan suka ga shigar su Yusuf, tare da guards din shi,
Motocin suka bi da kallo inda hankalisu yabasu cewa shine yazo gari,
Sunji haushin barin gidan da sukayi batare da ya iske su a ciki ba,,
Yusuf din ne ya fara fita daga cikin motar da yake acikin ta, yadan dade tsaye da kofad motar rke a hannun shi kamar mai nazarin wani abu
Saidai a cikin zuciyar shi addu,a yake yi na neman rinjaye daga ko wani irn masifa da zai riska, agidan
Tunda motocin suka tsaya Samuel dake zaune a saman dining table ya mike tsaye,yadan leka tagar falon nasu don yaga kowaye,
Cikin murna ya ce "Ah, brother Joseph,, har ya mike kamar zai tafi sai sukayi ido biyu da mahaifin nasu wanda ya watsa mashi harara dole ya koma ya zauna,
A, cikin takon shi mai kama da ta kasaita, yashigo falon
Idon shi cak ya sauka ga na mahaifin shi wanda alama ta nuna cewa, ya cika fam, a ida yake jira kawai yake yi ua fashe,
Da harshen su na yaren, IBO ya gaida mahaifin nashi, wanda ke zaund daure da wani katon zani na atamfa da akayi shi kamar buje,
Kallo guda Mr Ema yai wa dan nashi yagane cewa har yanzu yana nan daram a cikin addinin Islama,
Mr Ema wanda tun dan nashi bai shigo ba ya nasa cewa zai falfale shi da masifa in har yana cikin Muslim har zuwa yanzu,,
Amma suna hadda ido sai yaga yaron nashi ya kara mashi wani irin kwarjini a fuska,
Har yaji cewa bazai iya ba amma dai karfin hali irin na kafiri, balle Mr Ema mai hali kamar na kafiran farko,,,,
Cikin kakausar murya, yafara wa dan nashi magana kamar haka,
Wai kai may kake nufi da zuwa gurin mu bayan kaba mu baya,
Yanzu mai kazo bida a gurin mu da har za ka,shigo min gida kai tsaye batare da izini na ba
Addinin naku bayace mutum bai da ikon shiga gidan wani batare da izini ba,
Joseph kabani mamaki kabani kunya a idon duniya,
Duk so da kaunar da na nuna maka acikin diyana sakkaiyan da zakai min ke nan,
Karasa addinin da zaka shiga sai addin musulunci addinin da yake na yan ta,addah,
Kafita kabar min gida na muddin kana cikin wanan addinin baza mu taba shiryawa da kai ba,
Duk da nasan cewa kana ganin kamar a yanzu kana da arzikin ka to ina son ka sani cewa gidan maina da kake harkoki dashi a Lagos na karbi abina,ko
Sai katafi gurin yan addinin ka suyi maka,contribution din sadaka subaka jari idan zasu iya,
Yakare maganar ko fadane yana huci kamar zai fashe,

Saida Yusuf yaji mahaifin nashi yadajatar da masifar da yakeyi ne,
Sai ya saki wani irin ajiyar zuciya lokaci guda yadago ida nun shi a hankali ya dubi uban,
Yace Daddy kayi hakkuri da abinda kagani that is my Destiny,
I can't change it,
Wasu kwalaye guda biyu masu kyau ya ciro daga cikin wani dan leda,
Ya taka har zuwa gaban Daddy din wani kwali dake daure da wani zare ja kamar na gift,
Ya fara aje wa a gaban daddy din ya dago kai a hankali cikin ladabi yace ma mahaifin shi wanan keys din gidan manka ne komai da yadangace shi yana a ciki,
Sai na biyu dake daure da wani blue din zare again, yafitar shima a gaban daddy din ya aje again,
Mr Ema wanda yake tsaye sororo yana ma dan nashi kallon mamaki da tsana,
Yaji muryan Yusuf din yana cewa wana wasu kudine da ya diba daga cikin kudin mai din a na sarrafa su a wani fanin to shi ne yahado kudin gaba daya har takardun business din, suna a ciki,
YUSUF yadan sunkuyar da kan shi yace babu saura komai nashi a hannun shi, yanzu,
Saboda addinin shi ya haram ta mashi cin dukiyar shi,
Aiko Mr Ema ina wuta yasaka Yusuf saboda wanan ce damar da yake hange da zai ja ra,ayin Yusuf din da shi,
Sai,gashi Yusuf din yana sanar dashi cewa wai addinin shi ya haramta mai cin ko kwandala daga dukiyar shi,
Jiki a sanyaye Yusuf ya juya dan barin falon cikin kunar rai yake tafiya saboda irin kalaman da Dad ke fadi,
Sa kai yayi yafita tare da yiwa falin wani kallon mai kama da ta karshe,, sai kuma ya waiga inda su Samuel da Ruth suke tsaye cirko cirko,
Kawai sai ya juya da karfi alamar shi kan ba,zai iya barin addinin shi ba komai zai faru ya faru
Amma yayi sallama da rayuwar kafirci da suke ciki har abada,,
Yusuf na daga labulen falon zai sa kai Ruth da Samuel suka sa wani irin kuka mai ban tausayi suna cewa
"Brother pls don't go,
Brother come back to us pls we don't want to loose u,
Tsawa Mr Ema yadaka masu saboda takaicin, da kukan su ke kara mai saboda yasan cewa yayi rashin dan shi na kwarai, da yake da shi,
Yana magana yana biyu bayan Yusuf din wanda ko waigawa baiyi ba tunda yasa kai,
Sai kuma ya koma ya zube a saman kujerar dake a bakin kofar yasa wani irin kuka mai sauti,
Shima dai Yusuf din yana shiga mota ya sa kyalen dake hannun shi ya goge hawayen da yadan gangaromai a fuska,
Drive yaja mota a hankali yabar harabar gidan,

A cikin dakin hotel din da suka sauka yake tsaye yana kallon titin da motoci ke zirga zirga akai tankar rana ce ba dare,
Muryan Dad ce ke mai yawo a kwakalwa yana cewa,
Saboda kai Joseph nasha kunya nasha takaici kasa banda mutunci acikin church din mu gabadaya,
Wasu ma ko gaisuwar arziki bamayi dasu sabo suna ganin cewa ban fi karfin family di na ba,,
Ka nemi kudin ka ka gina gidan ka barmin nawa,wanan ba naka bane,,,
Murmushi irin ta
takaici yayi yace watau dama Dad ta wanan hanyar yaso ya kamashi ke nan ko,?
Allah yasa ya samu Sheikh ya warware mashi wanan matsalar dake damun shi tun tuni,
Muryan yan kan,nen shi yaji suna kukan kiran shi yadawo kada ya tafi ya bar su pls,
Wa yan nan maganganun da ya ke tunawa sun sa shi ya shiga cikin damuwa da, wani tsananin tashin hankali sosai,
Nan da nan idon shi suka canza kala saboda damuwa,
Guri ya samu yakai zaune yana mai hada hannaye shi biyu guri guda,
Yadan tallabo habar shi da su yana dan bubuga kafar shi a kasa a hankali,
Tunanen da yazo mai gamay da yan uwan shi ya,sa,shi mikewa da sauri,

Sai washegari yasamu shiga cikin gari gaida mutane,
Gidan Abdulsamad yafara zuwa ida suka dan dauki lokaci mai tsawo suna tataunawa, a tsakanin su,
Yana tashi ya wuce sai gidan mahaifan Jibrin inda suka nuna mashi jindadin irin yarda yake girmama su
Yakawo Alheri mai yawa yai masu,
Wasu dattawa ne zaune a kofar gidan su jibrin idan rana yai zafi anan suke taruwa kagin ai sallah azuhur,
Kudi ya debo adadin da bai,san ko nawa bane ya basu don su raba,
Daya daga cikin su daya yake kwance yamike zaune yana tambaya dangidan waye ya basu kudi haka,
Sai cewa guda da ga cikin su yi, ai yaron nan tubabben nan ne,
Au to shine wanda ya tuba din nan, dan gidan katon Arnen nan maigidan mai hanyar Lagos,
Duk wanan maganar a kunnuwar Yusuf akayi su duk da yaji daci a zuciyar amma afili sai ya daure yana murmushi kawai,
A daidai zai shiga mota suka yi kicibis da Sadiya Mohammad joda
Karo na biyu kenan suna haduwa da ita,tun,da ta ganshi sai duk tashiga,,rudu saboda Allah yasa mata masifar son shi,
Itace tafa ra gaishe shi cikin rashi kulawa ya amsa mata,
Ya dan bar uguwar su Jibrin ke nan Kiran Aisha yashigo wayar shi
Sam yarasa may yasa bayason lamarinta yanzu tun bayan muzuluntar shi
Yake kokarin jabaya ga alamarin Aishan saboda sam baya son abinda zai sa sa a sabawa Allah ubangji
Ce mata yayi zai koma ne yau ko gobe kawai amma sai bai son ya fada mata gurin da yake don kada ta cin mashi,,,,,,,


ZEEE MAKAWA,,,,,,
[3/7, 1:15 PM] โ€ช+234 803 381 3188โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
4โƒฃ2โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Saye take da wani leshi mai ruwan kwai, (yellow), mai laushi, anyi mai yan ada da wasu duwatsu blue,
Dinkin buje da riga akai wa kayan sun dane jikin ta har surar jikin ta yafito fili,
A cikin sauri take shiri saboda, zata kamfanin Bobi ne yau don diba jikin mahaifiyar ta kamar yadda baba ya umurci Anty ta barta ta tafi,
Saidai ya umurta da kada ta tafi sai yazo tukun,
Ganin baba bai zo ba yasa Maryam din cire hijjab din ta don ta dai taimaka wa yar uwar nata da wasu ai yuka, kafin ta wuce,
Da sallamar shi ya shigo gidan kamar yadda ya saba yi tun bayan musuluntar shi,
Aguje su Assalam da Issalam suka dake wa Abubakar wasa saman kujerar falo
Suka rungu may shi yana murmushi yafara kokarin daga su sama kamar yadda ua saba yi masu,
A kunyace maryam ta gaishe shi saboda kayan da ke saye a jikin ta,
Yasha Voil mai kalar ruwan fari, kal, ajikin shi,wacce ke ta faman kyalli, da daukar ido,,
Kan,ta mayar kasa, cike da kunya don kallon da sukayi na hada ido a lokaci guda, don kada ya zata ko shi take kallo,
Saida ya shiga falo yazauna saman kujerar dake facing din kofar ta yadda duk wand ya gilma zaka iya ganin shi daga ci,
A hankali yakewa yaran yan tambayoyi gamay da school da kuma rashin zuwan su makaranta yau,
A tare suka hada baki suna,cewa ai yau weekend ne har da little mummy ma yau bata zuwa,
Shigowan Baba da yayi ne cikin yin sallama yana mai neman Anty Dije, wace ta dan shiga cikin babban gidan su maigidan ta,
Cikin damuwa Baba ya fara magana yana cewa, Maryama tun dazu ina can gurin bidan dan kudin da zakiyi kudin mota da kuma wanda zaki dan sai masu tsaraba,
Tunda ba,a zuwa gaida mara lafiya hannu sake amma ban samo wani abin kirki ba dan kudin da duk nake bi bashi tun jiya nake bi ko zan dan samu wani abu daga ci,,,,,,
Bai,kai ga karasawa ba Yusuf wanda ke zaune a falon yafito don su gaisa saboda Assalam ya fada mai cewa ga baba tsoho nan, ya shigo
Sai yakasance Baba din nata ma Maryam bayani a lokacin,
Maryam tace Lah baba dama kabar shi ai Anty ta bani kudin mota ko ,
Kai kawai dama nake jira don kace kada in tafi sai ka shigo
A,lokacin Anty Dije tadau dauke da wani bakin leda mai giwa a hannun ta,
Cikin yar fara,ar ta take gaida baba tana cewa yanzu ake ce min ga ka can ka shigo yanzu,
Dama na tafi ne, in dan samo mata abinda zata rika,
Allah yai maku albarka in ji Baba yake sawa yaran nashi,
Wani iri Yusuf yaji don jin yadda Dattijon ke ta sawa yaran shi albarka akan dan abu kadan,
Ina ma ace shine yasamu irin wanan mahaifin mai sawa diyan shi albarka haka,
Muryan Dadtijon ya katse mai yar tunanen shi yana cewa,
A ina , ta, shiga mota ne Dije, ?
Anty Dije tace dama cewa nayi ta tsaya a bakin hanya kamar zai fi,
A,a a,a inji Baba yace tashiga ta cikin gareji kawai yafi sauki don shiga mota bakin hanya ai hatsari ne Dije,
Baba yace idan kin tafi ki gayar muna da mahaifiyar taki Allah y bata lafiya
Duk suka amsa da Ameen,
Harda Yusuf wanda ke zaune a falon yana jin su,suna mai bashi sha,awa
Daga haka Baba ya fita suna, ta ce mai baba sai anjima inji su Assalam,
Maryam ce tafito daki acikin shirin ta tasa dan gyale blue,ta yane fuskanta,sai wasu yan takalma, suma blue daidai adon duwatsun Lecce din jikin ta,
Cikin dan siririn murya,kamar kulun taje sallamar yar nata,
Yusuf dake zaune tare da su Assalam suna hira yana jin su, amma hankalin shi yana gurin su,waje,
Muryan Anty Dije cikin tausayin yar kaunar nata wace take ji a lokacin kamar su tafi tare, saboda basu san halin da mahaifiyar nata ke ciki ba,
Duk da bawai sun saba da mahaifitar nata bane amma sai duk ta damu tun da baba ya fada mata cewa mahaifiyar ta bata da lafiya,
ร€nty Dije tace cikin murya mai rauni, maryam tsaya mana ga Yusuf ya kaiki tasha ko,
Maryam wace har takai kusan kwanar fita cikin gida alokacin,
Tace wa yar nata ai da ta barshi kawai sai in hau mashi a sauke ni,
Assalam da Issalam ya umurta da su tashi su raka little mummy,
Yaran na murna suka fito waje cikin dauki kowa na kokarin saka takalman shi a kafa,
Maryam, wacce a lokacin har taku sa isa kofar gida sai ji tayi yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login