Showing 75001 words to 78000 words out of 255288 words

Chapter 26 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1761

kallon mamaki sukai wa junan su, alokaci guda,
Cak Jibrin ya tsaya don a ganin shi ba gidan shi bane suka zo wata,kila sunyi batar kai ne,
KB nai yai kundun balar shiga cikin gidan kai saye,
Daidai lokacin da yake ruku,u, a cikin raka,a ta biyu,
Nunfashin su ne ya tsaya cak, kamar a mafarki suke ganin abin don sam basu taba tsan,manin haka ba,
A,lokaci guda suka, kali junan su tare da kara matsawa kusa da inda yakai goshin shi a kasa yana sujada,
Cikin mamaki suka karasa gab dashi suna mai wani irin kallo,
Yusuf din ne dai yai sallamay sallah shi yana mai daga hannu yana addu,a,
Har kasa inda yake zaune suka durkusa suna mai kallon shi a cikin mamaki,
Yana shafawa gabadayan su suka rungumo shi zuwa jikin su
Kowansu sai hawaye yake fitar wa don murna,
Shiko Yusuf ya rasa ko kukan may yakeyi, daga ciki,
Bayan sun samu natsuwane, suka bukaci dan, jin sanadin wanan abin,
Bai boye madu sanadin shigar shi ba da dalilai dayasa har yai sha,awan shiga wanan akidar ta isalama,
Shiru sukayi nadan lokaci gudu jin yadan dakatane gaba dayan su sukayi hamdallah,
Jibrin yace masha Allah irin musuluntar da ake so Allah yabaka, ,
Badon wani bukata ba,
Badon mace ba,
Sanan badon yin suna ko kwadayin wani abuba,
Gaskiya mun gode ma Allah daya baka dama da ikon shigowa cinkin musulunci,
Allah ubangiji yabaka, ikon bauta,madhi acikin tsarkakaken zuciya,
Suka amsa dafadin Ameen,gaba dayan su a lokaci guda,
Jibrin ne yace Old man yasani kuwa, acewan mahaifin Yusuf din,
Yusuf yadan gyara zaman shi yasa kan shi saman kujera mafi kusa da shi,
Saida yanisa sanan yace nasan zamu kwasa dashi sosai
Amma dai insha Allah ba matsala Allah zai kawo saukin abin,
Nan dsi sukai ta hiran su ,cikinjin dadi da a,nan shuwa,
Wanan zancen kamar an harba bindiga a kasuwa ne don nan a nan labari ya cika kwantagora cewa Joseph ya musulunta,,,
Wasu nacewa karyane wasu, nace ai hakan zai iya yuyuwa idan sunyi la,akari da irin halinshi
Abukamar yaki agidan su Joseph din don mahahaifin shi kamar mahaukaci ya koma, da yasamu labari
Sam bai yarda ba kiran Joseph din yayi a waya, Mr Ema tare da sauran abokanshi
Zaune ansa, waya a handfree anajira aji Joseph din abinda zai ce
Kamar bazai dauki wayan ba don yasan akan,maganar da za,ai masa,
Sai dai ya daure yadauka muryan dan nashi yaji ,,normal saida yadan girgizakadan,
Joseph yes Dad, ya karba,mai kamar yadda yasaba ansawa, idan ya,kirashi
I,want to know the true, of what, we hard here about your,
Baba what's going on there, now,?
Nan baban nashi ke fada mai cikin fada, cewa yarabashi yawo da yaran hausawa ga irin disgrace din da suka jamai
Fada sosai baban yakamayi sukima sauran mutanen dake gurin sai cewa sukeyi,
Ehhyya congurat, wooo,
Na,now we hear the true,
Wani iska mai zafi ya furzar tare da shafo kanshi har zuwa kasan wuyan shi,
Abubuwa da dama yake sakawa aran shi gamay da maganar mahaifin nashi,
Baikai ga mafita ba har tashi zuwa yin sallah, don lokaci da yaga yagabato mai,
Can wani unguwa mai nisa yake zuwa yin sallah, tare da mutane,
Tun lokacin da yaji cewa, yin sallah acikin jam,i yafi lada,

Anty Dije ranan da maigidanta yabugo mata yana fada mata,
Jin maganar tayi kamar a mafarki, alokacin,wani irin ihun murna tayi tana cewa Alhamdullaha, Alhamdullah,
Allah mun gode ma,
Joseph ya musulunta, maryam wace har takawo kofan falo alijacin taja tai tsaye,
Musuluntafa Anty, kikace,
Wanan kasurgumin Arne ai yayi nisa ko,
Subbahanallah Maryam bari mana, musulmi ne fa yanzu shima

Yau ba yawa kuyi hakkuri pls,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Abu, kamar wasa magana tafara zagaye gari, cewa Joseph ya musulunta,
Duk inda dan IBO yake cikin garin kwantagora da kewaye hankalin su ya tashi sosai,
Don su agare su wanan mugun labari don in, su na son mutuwar su to suna son jin irin wanan labarin,
Hakalin yan church din su Joseph yai matukar tashi sosai,,
Meeting suka hada duk wani elder dake a church din ya halarci wanan taron,
Batare da sanin Mr Ema ba wanda, sam baiyar da cewa dan shi na ita wanan abin ba,
Saboda su kaf tarahin su basu da yan uwa, musulmai, balle ace danshi ya shiga islama,
Sun wakilta wasu daga cikin su da zasu tafi har gurin Joseph din su samay shi face to face suji ta bakin shi,
Saidai sun sha bam,bam da Joseph din don yau yabar Abuja zuwa Lagos gurin kakar shi,
Sun yi kokarin bincike gurin maigadin shi amma basu gane komai ba don haka suka dawo da mamarai a ran su,
Shiko Yusuf ya isa Lagos lafiya da yake tafiyan jirgine,
Barci yayi sosai bayan isar shi sai musalin sha, biyu da rabi yafarka,
Inda yashiga bayi yai wanka tare da dauro alwala don sallah azuhur,
Key din motar shi ya dauka zuwa wani massalaci dake cikin unguwar na su,
Tare da shi aka gabatar da sallah azuhur, na wanan ranan,
Ibrahim wanda sai yamma yake dawo,wa daga gurin koyon computer da yake zuwa,
Yadawo cike da murnan ganin Joseph a yazo gari don yasan cewa ganin shi alheri ne babba,
Amma sai yaji Joseph cikkn yaren IBO yana ce mai yatashi su tafi masallaci kada su rasa jam,i,
Kamar a farki yaji zancen Joseph din don bai taba tsan manin haka ba daga gare shi,
Dashi akai jam,i Ibrahim wanda duk imani da,mamaki ya kashe,shi
Saida yakasa tambaya don bai san ta ina zai bullo mai ba,
Yusuf nagama addu,an da yadaga hannuwan shi biyu sama yana,roko tun bayan sallamay sallar ta,su,
Ya,shafa a fuskan shi da gangar jikin shi baki daya,
Sai a lokacin, yadan waigo inda Ibrahim yai mutuwar zaune,
Hannu ya mika mai tankar yadda sunna ta tanadar wa musullumi yai wa dan uwanshi musulmi,
A, lokacin ne ya mike tare da jawo hannun Ibrahim suka fito daga cikin massalacin,
Cikin wani irin murya maikama da wanda kasala takama ya fara magana,
Ibrahim katayani gode ma ubangiji na daya nufe ni da bani ikon gane gaskiya,
Ibrahim baisan lokacin da ya,rungumay Yusuf ba zuwa jikin shi sai she,shekar kuka yafara,
Bayan shi Yusuf yadan fara bubugawa shima, yana dan fidda kwalla masu zafi a idon shi,
Murna yakamata kai min Ibrahim ba kuka ba a wanan lokacin,
Ibrahim cikin dasashiyar murya irin ta mai kuka yace mai Dad yasani kuwa,
Murmushi mai daci Yusuf, yayi wanda baikai ciki ba yace bai sani ba tukun, yai yar ajiyar zuciya, yace,
Amma ,zai sani soon insha Allah,
Ibrahim zan tafi da kaina in tunkari mahaifina da zance,,
Duk da nasan hakan zai shafi rayuwar shi ta fan,ni daban,daban,
Amma hakan ba zaisa in daina abinda nai niyad yiba don kaina,
Musuluntata bata, jeka nayika bace, Ibrahim,
Nayita ne don ra,ayin kaina daganin dacewar hakan,
Yanzu ma na fara zurfafa acikin ta har sai ranan da naji cewa banda sauran numfashi a duniya,
Don haka na shirya tunkarar duk wani kalubalin da zan samu dayin hakan
Kara rungumay shi Ibrahim din yayi yana mai cewa masha Allah Allah mungode ma ubangiji Allah ka karawa Annabi daraja da daukaka,
Yusuf din yakarba da fadin Ameen, tare da hannun Ibrahim don su shiga gida,
Saidai yaiwa Ibrahim kashedin fada ma su mama yace sai ya fara fada wa, mahaifin shi tukun,
Ibrahim yace ina mai baka goyon baya brother har zuwa lokacin da zasu gane gaskiyan ka akan hakan
Ibrahim ya matse hawayen da ya cika mai ido,, yadan kalli Yusuf yace komai ukuba ko tsanani brother kada kabar addinin ka,
Babana yadade yana maka fatan kasancewa a hakan saiga shi yau Allah ya karba masu addu,an su a cikin sauki,
Kayi irin musuluntar da ake fatan yin shi domin Allah badon ra,ayin wani abuba,
Bayan sun shiga cikin gidane maman Choima da har yanzu bata kaunar ganin Ibrahim atare da su, tai mai wani irin kallo na kaidin wa,
Saboda lokacin da Yusuf baya gari sam baya shiga gidan saboda ita,
A, tare sukaci abinci shida Ibrahim ranan ibrahim wanda bai damu da yadda maman Ejoma ke mai ba.

Bayan kwana biyu Yusuf, Joseph, ya shirya masu tafiya gaba dayan su zuwa Niger, State,
Tun safe sai zuwa magrib suka isa, cikin garin a gagauce Joseph ya aje su mama yace masu zai kai Ibrahim gida yadawo,
A,lokacin Mr Ema yana kofar gidan shi kamar yadda dattijan arewa ke zama a kofar gidajen su,
Gani Joseph din yasa shi jin sanyi aran shi don yasan cewa zai wanke zargin da yan church din su ke mai,
A,masallavin uguwar jankidi, indagidan Abdullsamad yake nan sukayi sallah su atare da mutane
Murna gurin, Abdullsamad bai ko musaltuwa,
Yai ma Yusuf nasiha akan yadda zai tunkari mahaifin shi akan zancen,
Da murna sosai mahaifin nashi tare da yan uwan shi suka tare shi,
Sai murna sukeyi da zuwan shi fiye da yadda ma kullun da yake zuwa,sukeyi
Sun ci abinci kamar yadda aka saba sun dan fara,hira can, mahaifin shi ya jefo zancen,
Musuluntar da ake cewa yayi a,gari inda har mutanen, su sunfara yimai wani kallo,
Joseph yadan sunkuyar da kan shi kasa ahankali, sai yadago sukayi ido biyu da mahaifin nashi,
Yusuf yace a hankali is true Dad iam now Muslim,
Cike da mamaki mahsifin nashi da mama suna kojarin hada baki gurin tambayan, abinda su,ka ji kamar yace,
Yusuf yadan yi shiru can yace Iam Muslim now,
Cikin wani irin fushi mahaifin shi ke magana acikin harshen IBO
Mafarki kakeyi Joseph ko ko wasa,indan har haka kai ma,za kadaina don ban son irin,hakan,
Baba bawasa acikin zance na sam, gaskiya nafada bana cikin addinin ku yanzu
Wani irin ihu Mama choima ta sake wanda yai kama da ihun mutuwa,
Mr Ema wanda ya suma azaune bai masan ida yake ba alokacin, sai Yusuf din ne ya dan kula,
Yai kanshi ya na girgizawa a hankali yana mai kiran sunar shi, zuba mai ruwan sanyi yayi, yadan farfado,
Duk da acikin dare ne suke wanan abin bai hana wasu makwabta jin hayaniyar su ba,
Abokin Mr Ema ne yashigo lokacin don jin cewa Joseph ya shigo, gari, saboda shim a matse yake da yaji gaskiya don yai wa mutanen su, sheri,
John yayi matukar kidimay wa don ganin irin yadda abokin shi yake zaune jagwab, sai wani abu yakeyi kamar kaza tasha ruwa,
Mama Choima wace tsananin rudewa yasa ta faduwa kasa tana ta rusa ihu, da shure shure,
Tana ta zabga gwalanci cikin yaren su,na IBO duk a kidime take wanan sanbatun,
Yusuf wanda ahalin yan zu ya mike da ga tsugunin da yai a gaban mahaifin shi,
Y
Wanda shi da kanshi Mr Eman bayan yafarfado yai wa Yusuf din hannu alamar yajaye daga gurin shi
Ke nan baya son ganin shi agaban shi Yusuf wanda zuciyar shi tariga ta keykeshi bai jin ashhh,
Ya mike tsaye batare daya tsaya ko ban hakkuri ba, yakama hanyar zuwa dakin shi,
Hey stop, there mr man, don't enter my house, pls,
Yusuf yai tsaye kamar mai tunane nadan wani lokaci sai kuma ya juya kawai yai hanyar fita waje,
Cikin wani karaji maman choima, ta mike tsaye ta je tasha gaban shi tana mai tare shi da hannu,
Kada katafi my son idan katafi ,zasu kara rudin ka su cutar dakai da addinin su,
Mahaifin shi yace mata tabar shi ya tafi tunda yanaganin kamar cewa suna son shine don Allah badon kudin shi suke son suyi amfani da shi ba,
Yusuf Joseph yadan dago kai yakali mahaifin kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya fasa,
Ganin irin kukan da mama keyi yasa shi juyawa zuwa vikin gidan nasu,
Mr Ema wanda baikara yunkurin korar dan nashi ba wandda a shirye yake, da yabar gidan,
Tun shigan shi dakin shi sai yaji duk tausayin mahaifin nashi da kankashi,
Harma da yan uwanshi da,ke tafaman kuka cikin tashin hankali,
Amma saidai ina yai nisa ko acikin Isalama, baya jin kira,
Zima yana mazu fatan Allah yas su gane gaskiya sudawo hanyan gaskiya,
Sai cikin dare sosai barci yadauke shi, ko shi sama sama,
Don tabatar wa cewa yana cikin musulunci da shi aka tafi, sallah asuba wanda yai daidai da yadawo daga masallaci sukayi kicibis da maman chiloima
Wace tafito tin cikin dare takasa barci, suna yin ido biyu dashi sai ta hau wani irn gumza da ihu cikin kuka tana magana kamar mara hankali,
Kai kawai yakada yana mai murmushi abinda yaga tanayi wanda shi sam tama fara bashi dariya a,lokacin
Acikin takon shi maikama da kasaita, yafito,
Bakajin komai mai sai karan takon takalmin shi daya karade falon
Zazzaune suke kowanin su ya kurawa abincin dake saman table din ido,
Wanda sam yau duk kyau abincin bai,basu sha,awa,
Fita yai niyar yi a,lokacin, batare da yako kalli inda suke zaune ba,
Mama ce tai karfin halin yimasa magana da cewa son kazo kaci abinci kafin kafita,
Mahaifin shi wanda yai kicimkicim da fuska, ya zauna ya hade hanna yen shi guri guda yatokare habar shi da su,
Yusuf wanda alokacin yafara kyamar abincin su don ganin irin dan bujen dake ajikin su ga,wani gashi doki da suka jibga,akan su,
Inda take ya,dan taka cikin tako irin nashi ya dan rungumota tabaya yana cewa yanzu zai dawo ai bazai dade ba ai,
Cikin fushi Mr Ema yace ya sake ta tunda baidamu da damur su ba,
Sai yanzu yagane komay yasa tun farko ya ke bin diyan hausawa da musulmai
Mr Ema cikin daga murya yake fada da Yusuf yana cewa,
Tunda naga mahaifiyar ka ta haife ka lokacin watan da musulmai suke azumi,
Har suna zo muna murna wai na haifi, yaron lokaci mai kyau,,,,
Sai yadukar dakai kasa cikin bacin rai yakasa cigaba da bayanin dayakeyi,
A wanan lokacin members na church din su sun kai su goma sha, suka shigo,
Daya bayan daya Yusuf yakalle su basai an fada mai ba yasan komay ke tafe dasu daga shi har mahaifin nashi,
Kallo guda Yusuf yai masu ya kauda kai don dai kawai bazai ita masu rashin kunya bane da halin shi da yau yai masu,
Wani dan tsamurare daga vikin su maikamar shagada
Yace Joseph what's going on pls,?
A hakali yadago kai da idon shi da yai jawur yace,
Iam now Yusuf not Joseph
Mamaki karara a fuskan su wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wancan,
Maman Choimal wace sai hawaye takeyi cikin tashin hankali, ta na dan kada kafar ta cikin fitina,
Wani daga cikin mutanen wanda bai,karkare kai sauran shekaru ba ya ce Umm,ba,
Look mr let's have a serious talk pls,
Yafara magana acikin yaren su, kamar hakan ga,
Joseph may yasa kai wanan clash, din pls,
Mace, dukiya, ko suna, friendship?
Ido Yusuf ya kura mai don shi dai ma tausayi yake bashi shi mai maganar alokacin,
Don haka murmushin takaici yai mashi yana mai sauraren shi a natse,
Mai maganar yaci gaba da cewa idan har saboda soyayya ka koma ai muma muna da mata madu kyau daga cikin mu,
Idan kuma dukiya kake bukatan kari kafadi daga milliyan zuwa sama zamu hada maka
Haka kuma idan suna kake,,,,
Da hannu Yusuf ya dakatar dashi alamar ya isa hakanan
Baison karasa sauran shirmayn fon jin maganar yakeyi kamar may tatsuniya,
Sosai yabude idon shi yau gare su yafara da cewa,
Kudi mace, suna duk ni Alhamdullah, yana,mai pointing din kan shi,
Ra,ayi ne kawai bawai don wani abuba nashiga nadaiyi nazari naga cewa itace hanya mafificiya, dazata fissheni, arayuwata,
Daga haka yamike yana mai hada hannayen shi gurin daya yana cewa da kaga yai pls kada wanda ya kara maganarr,
Daga haka yasa kai fuu, yafita ya gidan batarecda yai ma kowa sallama ba,




ZEEE MAKAWA,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,


Bayan fitar shi daga falon Mr Ema wanda ke zaune cikin tashin hankali tunfarko yai wani irin dan ihu, sai kawai fashe da wani irin kuka mai tsuma rayuwa, duk wanda ya saurara,
Cikin sauri ,wa"yan da ke kusa dashi abokan shi suka dan riko shi cikin kulawa,
Mamsn Choima wace sai ye, Jesus come help me wooo,
Samuel dasu Ruth sai wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login