Showing 63001 words to 66000 words out of 255288 words
Chapter 22 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
nazo na fadawa Anty,
Don alokacin ina ganin cewa ga yan mata nan wayayyu a cikin FCE amma zai buge da cewa, yana sona sai kawai nadauka yaudarata zaiyi kawai,
Ashe abin ba haka bane,,hadine daga Allah,
Marya tamike tsaye tana kokarin walwale kayan don su diba dinkin tace,
Tace don Allah safiya ki daure yau ku dan gana dashi, don muji ta bakin shi
Kinfa yace min ma wai shi zai tafi dake gurin hall din ajima,
Kinga ko inda bada gaske yakeyi ba da aibazai yi kokarin nuwa duniya ke ba,
Dan siririn ajiyar zuciya, safiya ta sake tace maryam bawai ban son hakan ya kasance bane,
Ina dai gudun abinda zai jawo min fitina ne kin san halin da mahaifiyata take ciki kada in dauko mata magana,
Amma ba komai tunda naga kin yarda dashi don nasan cewa bazaki kaini mugun wuri ba,
Wayar maryam ne yai kara,a,lokacini ko bata dauka ba tasan cewa A,A din tane akan layin,
Cikin kashe murya ta dauki wayan nan yake sheda mata cewa tajirashi zai zo ya kai su gurin bukin,
Duk da dai bata gaiyyace shi ba tun farko,
Maryam tadan kara kwantar da muryan ta tace malam nasan cewa baka wani hurda da sune shi yasa ban fada ma ba,
Yai yar dariya, yace wallahi jibrin ne ya fadamin dazu da muka hadu gidan mai dashi,
So ki bani nan da minti ashirin zan iso, insha Allah,
Kayan da su maryam suka sa yai bala,in fitar dasu sosai,
Saboda bawai samun irin materials din akeyi ba akon,ina don haka sai yazama wani abin kallo, ga jama,a,
Tsab suka fito gaba dayan su a lokacin, Safiya sai faman koda shigar maryam takeyi ita ma maryam din hakane,
Jibrin yazo har ciki da kan shi yana fadawa maryam cewa tafadawa safiya yana waje yana jiran ta,
A,Daidai lokacin A,A ya iso don tafiya dasu kamar yadda yace zaizo yakai su,
A,lokacin wani kanin mijin anty Dije ya zo don yakai su
Sai ya tar da za a kaisu amma Anty dije sai tace ya tsaya ya kai ta ita,
A hankali suka fito saida ga motoci nan gurin zakace ko a gidan ne ake bukin,
Har bakin motar jibrin Maryam ta raka sadiya tadawo,
Ta bude motar A,A, tashiga
A,A din yadan waiga yakalli inda maryam take yace,
Ina ita safiya din, kuma,?
Tana can a motar jibrin tare zasu,
Tafada a takaice,
Wani irin kallo A,A din yai ma ma maryam.
Yace kina da hankali kuwa, yarinya tazo maki buki sai ki bari tabi wani kato,
Maganar yaba Maryam mamaki, tace jibrin fa nace ma malam,
Yai yar tsuki Mtsss, maryam ban zaci har zaki amince da safiya ta bi wa yan nan da kowa yasan yan duniyar yarane, ne ba,
Yaran da duk gari ankasa gane sanar su har zuwa yanzu
Tunda yafara magana maryam kallon shi kawai, takeyi
Tace haba malam nafada ma cewa ba abin,in da zai samu safiyan,
Ya dan daga mata hannu yanu nna mata alamar ya isa hakanan,
Har suka kai gurin bai kara mata magana ba,
Gurin yacika fam da jama,a lokacin har, kujeru sundan kare daga ciki,
Wasu ne sukazo suka yiwa su maryam kwantace da wasu kujeru a can gaba,
A kusa dasu taga harda su anty dije suna nan gab dasu,
Basu wani dade ba akafara program din inda aka r da Amarya da ango,
Kujerun wasu yan mata dake dan nesa dasu kadan,
Taga ana dan nuno su a hankali bada wani jimawa ba taga A,A ya mike zuwa wajen yan matan,,,,
ZEEEE. MAKAWA,,,
[2/21, 9:15 AM] βͺ+234 806 595 8685β¬: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
2β£7β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Jinjina gare tare da fatan alheri ko yaushe Anty Nafisat, Aliyu Harzami, UmmuFadleeh safeenat Abuja, Mamam farida,Maman Walid, Maijidda Harzami, Mariya SB, Jamila Sifiyanu,Anty na hafsat Yusuf, da members din Zeee makawa novel, da members na takari novel Ina maku fatan alheri dacewa da Rahaman ubangijin mu, da kuma gamawa da duniya lafiya,
JUMM,AT, MUBBARAKππππππππ
Zaune take daga inda A,A yabar ta ko zataga dawo wan shi sai kawai taga tun yana yar kus,kus,da wanan matar da taga yaje gurin ta har sun kwasa sun fita,
Shigowan Joseph tare da,Aisha yasa ta dan daina kallon hanyar dataga A,A din ya bi, yafita,
Joseph da Aisha tare da Amina sun shigo cikin wani irin shiga ta alfarma,
Don dai ko makiyin su dole ya yaba ma shifagar su,
Aisha ba kunya tana make da Joseph gam saboda ta bushe fitilar ta bata kunya kowa agari,
Yan wasan gidan mai Jauje na kwantagora sun fito sun yi wasa,
Sai wani mawaki makwabcin garin kwantara daga KB state garin Yauri Sani Aiyu dan Dawo shima yafito yai nashi wasan
Nan masoyan Joseph da bakin su suka dinga barin kudi ga mawaka,
Daga karshe aka dan yi traditional show na yaren da ke cikin kwantagora,
Toran kawa, kambari, Dukkawa, Dakarkari, pure hausawa, da sauran su,
Wayan Maryam wace takai iya wuya, yai yar tsuwa, alamar sako ya shigo mata,
Budewa tayi sako tagani kamar hΓ ka Ki, yi hakkuri pls Maryam, bazan samu mayar, da ke, gida ba ,
Ku komatare da Anty pls,
Abinda aka rubuta ke nan a sakon , atake maryam ta fahinci, sakon daga, A,A masugane,
Wani iri maryam taji a ran ta, maganar da ya fado mata arai shine, muryan mahaifiyar A,A alokacin da suka je gaida ita,
Daga haka tamike tsaye daga inda take zaune,
Tafiya takama yi cikin tashin hankali take dan takawa,
Sai muryan Safiya taji a gaban ta tana cewa, banga motar A,A ba a waje maryam,
Dan ajiyar zuciya tayi don ta riga tayi nisa gurin tunane ,
Tafe suke a motar jibrin sai hiran wasan nin da akayi akeyi amma ita sam hankalin ta bai tare da ita,
Abinda zuciyar ta ke tambayar ta shine wacece wanan da A A yaje gurin ta,
Har tasa shi fita hall din taron yakuma iya wucewa ya bar maryam din, a gurin,,,
Har suka isa gida ,hankali maryam atashe yake gashi suna da aiki so sai don gobe daurin aure su zasuyi abincin reception,
Jiki ba kwari ba ku,zari haka ta, daure, tayi aikin cikin bacin rai tun bata walwala har ta dan sake jikin ta don taga amfara tambayar ta komay ya,samay ta,
Shiko A,A tun fitar su waje da kaunar maman, da suka hadu agurin bukin,
Sun kwashi lokaci da ina yana kokarin fahintar da ita akan maryam din,
Amma sam laminde taki fahintar shi sai ma kokarin kiran mahaifiyar shi takeyi ta sheda mata cewa bai rabu da yarinyar ba, ashe,
Hakan yasa yabar gurin cikin bacin rai batare da ya tsaya fada wa maryam zai wuce ba,
Safiya wace tun dawowan su jiya gurin friends day,
Ta fuskan kawar ta,na cikin damuwa, amma batason agane,
Itakuma bawai sun samu lokacin kebewa da ita ba ce,
Saboda haka yau da suka gama sa abinci a cikin take aways suka gyara inda sukayi aiki,
Sai sukayo wanka kafin a tafi daurin aure, don da andawo guri zai cikia ne, da jama,a,
Bayan sunan da shirya suna zaune su biyu a dakin maryam,
Safiya ta dan kali maryam wace tadan kurawa wani kwali ido kamar mai karatu,
Amma kallo daya zakai mata ka fahici ba wi kwalin take kallo ba a zahiri,
Tadan jima tana kallon maryam ahakanan tare da tunanen may ke faruwa da maryam din hakana wai,
Daga jiya zuwa yau ?
Ganin bazata daina wanan tunanen ba yasa safiya dan taba maryam, din wacce tai furgigit, cikin dan firgita,
Firgigit tayi alaman dawowa daga hayacin ta, sai yar ajiyar zuciya da take sakewa,
Wanda hakan yakara sa safiya kara kallon ta da kyau, ta ko hango tashin hankali a tare da maryam din,
Safiya tadan marairaice muryan ta tace maryam, wai make damun ki ne tun jiya fa na fanci kina cikin wani yanayi,
Kallon safiya maryam tayi kamar kartai magana saidai kuma tace,
Bari safiya ina cikin damuwa, tun jiya wallahi, jiya bayan zuwan mu gurin taron nan,
Sai A,A yaga table din wasu mata da alamar yan uwan shine safiya,
Yace min yana zuwa yatafi gurin su, sundade suna magana dashi sai suka batmr holl din gaba dayan su har shi,
Ban kara ganin shi ba,sai text da yayo min cewa wai in bi Anty zuwa gida bai,samun dawowa kaini gida,
Shine har zuwa yau din bai kirani ba baikuma yo min koda text bane,
Nan kuma ta kwashe yadda akayi lokacin da taje gidan su gaida mahaifiyar shi,
Safiya da ta gama sauraren maryam tai ajiyan zuciya,
Tadan riko hannun maryam tace gaskiya maryam kina cikin tsaka mai wuya,
Amma dai kiyi hakkuri pls kada ki sa wanan maganar a ranki,
Ita mahaifiyar shi da take fadin haka danta yafi ki ne,?
In,badon so ba may zakiyi da shi maryam,tuna duk inda aje son mace da tsari kin kai harkin zarta,
Maryam tace wallahi Safiya ina son A,A shima yana so na,
Matsalar mudai itace mahaifiyar shi yanzu, don ga yadda naji kalaman ta sam bata ra,ayina dashi,
Safiya tace wallahi maryam kamar yadda anty tace din,nan haka zaki dake dashi kiga gudun shi,
Yace yafasa mana yagani in baisha mamaki ba don dama ahi ya tare wa mutane guri,
Maryam tace nidai safiya kin san cewa bazan nuna mai cewa naji maganar da sukayi da mahaifiyar shi ba sai in shi ya gwada min wani alama daga haka,
Amma bari mu gani in har bai kiraki ba yau tau tabbas sunci karfin shi ke nan,
Idan har bamu ganshi ba yau tun da kince yau ce ranan zuwan shigurin ki da ma,
Yau wa safiya wallahi har naji dan sanyi daduk na rasa abinyi
Gaskiya naji dadin wanan shawarar da kika bani har wani dan sanyi ya ratsa zuciya na,
Safiya ta mike tajawo jakar kayanta da tazo dashi tana kokarin ciro kayan da zata sa,
Shiga ce ta dinkin shadda gezena fara kal, yayi
Saidaukar ido shaddan keyi irin dinkin yan Mali, akaiwa shaddan,
Agogon shi kawai zai fadama cewa akwai shegun agurin ,
Wata hulla da ta,shiga da kayan yasa mai kyau da ita sai kuma wasu takalma, yan company, BELLA, yasa a kafar shi
Kamshi dai ba,a maganar shi don yasa turare sunakai kala, biyar, alokaci guda,
Kudi ya dauko yan dubu, dubu da yan dari biyar biyar yasa a kowani aljihun rigar shi,
Motar da yashigo da ita tunda yazo bai shigeta ba tana aje,
Itace yashigo yau zuwa gidan su KB inda za,a dunguma zuwa daurin aure,
Jama,a sun ciki gurin makil, ana jiran motocin da za,a kwashe su,
Sauran motocin da yashigo dasu yasa aka kwaso, akadinga dibar jama,a zuwa gurin,
Duk wani abinda sharia ya tanadar gamay da daurin aure an gabatar a gurin a,lokacin,
Joseph da tunda yake baitaba zuwa daurin auren musulmai ba sai wanan karon sai abin tazama mai sabon al,amari,
Yaji duk abinda akeyi ya burge shi don komai a cikin tsari da kwanciyar hankali akeyin shi,
Tunanen farko da yafara yi a ran shi shine, may kesa musulumai suna kashe auren su dayawa haka
Dik da irin wanan, dokokin da akebi kafina mallakama mace,
Idan har zai iya tunawa yadda yaji KB nahiran abinda yakashe akan wanan bukn to bai kamata kalman saki ya shigo ga auren yaran musulmai ba,
Don yasan cewa musulunci batada banbancin al,ada,
Da mai kudi da tallaka duk abuguda za,ayi agurin auren su,
Hannu shi yadan daga ya shafi fuskan shi da yakeji kamar yawan jama,a yasa shi jin zufa agurin,
Sai alokacin yadaga kai yakalli irin yawan al,umman da aka tara agurin wai duk akan auren KB wanda yasani,
Jin ance fatiha yaga kowa na shafawa shima yadda yaga anyi yayi yashafa atare da kowa,
Tare da Jibrin da kb da sauran abokai,suka mike inda maroka suka biyo su caaaa nan suka fara zuba masu kudi,
Gidan Anty Dije akawuce don kwasan kayan abincin da za ai reception da shi awani katafare hotel mai suna NOMA FAMILY'S MOTTELS,,,,
Gurin yai mugun tsaruwa sosai anan suka kama guri, don haka duk kusan matasan da suka hakarci gurin sun isa Noma motels
Anci ansha komai yawadatar da jama,a sam,barka a gurin,
Sai shirin yin Dinners wanda za,a yi da karfe hudu na marancen ranan,
Maryam dake takure tun safe tana zullumin shawaran da sukayi ita da kawar ta,
Sai kawai taji kiran A,A yashigo mata alokacin cikin wata kasallaliyar murya yake mata magana cewa,
Bai samu kiran ta yadan yi tafiya ne zuwa mariga, shida wani kanin mahaifin shi,
Amma zai zo su tafi gurin dina tare zuwa anjima in ya shirya,
Bayan sunyi sallama, da shi takalli inda safiya take ta na mai yin ajiyar zuciya alokacin,
Don da dabai bugoba tadauka cewa tayi missing din A,A dinta ke nan
Wanan dinner ya hadu sosai don anyi abubuwan da yakamata agurin Maryam da A,A dinta sukan kebe a waje gurin wasu Flowers da aka shuka agurin
Yadan kalle ta cikin kulawa yana mai shafan kanshi,
Sai alokacin Maryam ta gano yayi wata yar rama akwanankin nan so sai don agaskiya ba haka yake ba da,
Gabanta yafadi damm tace a ranta kodai saboda fitinar magabar sune yasa shi ramay wa haka,
A,A ne yadan kauda shirun da cewa, maryam ina fatan bakiyi fushi ba jiya dana barki ko,
Wallahi wasu yan matsaloline sukadan sani nadan fita daniyar inje in dawo sai kuma ban gama da wuri ba,
Dan shiru sukayi alokaci daya shiko yana sauraren ta ne ko, akwai abinda zatace, da shi,
Amma sai kawai yaga tayi shiru, bata da alamun zatai magana,
Maryam shirun ki wani lokaci nasan maganace kawai,
Ki daure ki fada min may ke faruwa ne naga fuskan ki da akwai alamar damuwa acikin ta,
Shiru tayi kamar baza tai magana ba amma kuma sai ta yar nisa kadan, tace,
Malam shin akwai maganar mu kuwa ko dai da matsala aciki,
Ita kanta batasan lokacin da wanan maganar yafito mata abaki ba,
Shiko A,A saida yadan razana aran shi yace kodai wani yafadawa maryam abinda ake ciki ne shida mahaifiyar shi,
A hankali ya kira sunan maryam din ta dan dago kanta ta,kalle shi sai takawar da sauri,
Yace ma kika ga ni har zaki ce hakan,
Kai tadan girgiza mai alamar a,a ba komai,
Maryam ki daure ki fada min dan Allah may kika gani har ki ce haka,
Joseph wanda alokacin yadan fitowaje daga cikin hall din da ake taron,
Don yadan amsa call din wani yauron shi dake kiran shi can wani sabon depot da aka bude,
Waya yake yi da Chukuma, kamar ance yadaga indon shi sai hango A,A da maryam a tsaye gurin wa yan,nan furan,nin suna zuba hirar su ta soyayya,
Kallo guda yai masu ya kauda kai garesu yana mai ci gaba da wayan shi,
Saida yagama wayar da Chokuma ne har zai koma cikin holl din sai kuma idon shi ya kara sauka inda suke tsaye,
A cikin zuciyar shi yace wanan yarinyar itace har ta isa fira da saurayi haka,
Haba is too early ma,
Yai yar tsuki ya shige ciki abin,shi don bai iya ganin, takaici,
Yarinya kamar ustaziya amma ta iya abubuwan da bai kamata ba da dama,
Itace hawan mashin yau kuma harda hira,
Daidai lokacin da yake kokarin juyawa ne idon maryam ya sauka gareshi,
Inda takalla malam A,A yabi da kallo sai bayan Joseph din kawai yagani yana kokarin shigewa cikin hall din,
Maryam tsakanin mu ba dake yanzu yakamata mu fahinci junar mu sosai fiye da da,
Nayi alkawarin bazan taba auren macen da ba tsarina ba,
Ko kuma wace batada Qualities din abin danake so daga mace,
Ra,ayinane in auri mace, mai sirin,classic, atare da ita,
Wanda nasan cewa ta tara duk abin da nake muradi,
Bakowane zai iya hangowanan abin ba sai namiji mai irin ra,ayina,
So ki fada min ra,ayinki agamay dani pls, kada kuma kiji kunyar gayamin gaskiyar ki ,
Duk da nasan bazaki iya ki kalleni ki fada min kai tsaye komay ke acikin, zuciyar ki ba,
Magan ganun da A,A yai ta zuba ma gwaunatin shi don yaga yakarawa maryam karfin son shi komai wuya komai ritsi,
Maryam har mamaki yabata don jin yadda yatakarkare yana kokarin boye