Showing 222001 words to 225000 words out of 255288 words

Chapter 75 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1745

ta runtse idon ta, a hankali tare wani irin hade bacin rai,
Sai alokacin ne taji ajikin ta cewa bata da komai daga cikkn ta,
Cikin sauri takara jan bargon dake rufe ajikin ta tana mai kara shigewa ciki,
A lokacin ya idar da sallah ya dan shafa addu,a sama, sama,
Muryan shi taji yana cewa ki daure ki tashi ki dan gyara jikin ki yi sallah don lokaci ya ga ba to,
Ganin bata da niyar tashi Yusuf din yashafa addu,an dayakeyi a jikin shi, cikin tsanaki,
Mikewa yayi tsam zuwa bakin gadon ganin ya nufo ta yasa maryam ta runtse idon ta gaba cikin jin kunyan shi da nauyi,
Muryan shi taji gab da kunnuwan ta cikin rada yana cewa sorry barin tausaya maki,
Hannu ya mika da niyar kamota cikin wani irin ka murya mai ban tausayi take cewa,
Nooo, pls uncle, katafi kawai, kaje kaje pls kaje waje zan tafi,
Tsayawa yayi yana kallon ta cikin wani irin tausayawa,
Tambayar ta yayi da cewa zaki iya mikewa ke nan ko ?
Ganin da tayi cewa idan bata ansa mai, ba bazai barta ba ya sa ta ansa mai da kai ta cikin bargo tana cewa, tafi zan iya,
Fita Yusuf din yayi cikin jin tausayin ta saboda yasan cewa bai kyauta mata ba,
Saboda bai raga mata ba sam duk da yasan cewa shima ba laifin shi bane bai so hakan ba,
Kawai tsintar kanshi yayi da ganin shi dumo, duma tare da ita,
A hankali ta mike zaune tadan lalaba ta sauko da kafanta, kasa,
Da bin bango har ta isa bathroom din inda tasamu ya hada mata ruwa masu zafi,
Sosai maryam taji dadin wanan ruwan inda tadan dauki lokaci a cikin shi har sai da taji cewa tadan samu sa,ida,
Falo yake zaune amma tunane yakeyi ko wasu kaya maryam din zata yi sallah da shi, idan ta fito,
Sai da ya kwatanci cewa ta shiga bayin ya koma cikin dakin,
Wani jallabiyan shi baki yadauko mata inda ya aje mata a bakin gado tare da aje mata gyalenta a saman gadon
Sauran kayan gaba daya ya hada su guri guda yakai, gurin laundry,
Bayan fitowar tane taga wanan jallqbiyan tare da gyalen ta don haka tagane nufin shi,
Ba bata lokaci ta dauka tasa tare da daure gyalen a wuyan ta,
Tsab ta gabatar da sallah ta tare da daga hannayen ta sama tana kwararo addu,oi
Sai hawaye ke zubowa daga idon ta kamar anzubo ruwan sama,
A hankali ya iso gurin ta inda yadan dago ta fadawa tayi saman fadardar kirjin shi
Wani irin kuka takara sakewa cikin wani irin shagwaba, wanda ita kan ta batasan, ta na yi ba,,
Mai,da ita yayi saman gyararen gadon da ya gyara da hannun shi yau, batare da yajira mai gyara ba,
Kwantar da ita yayi a hankali saman gadon ba musu ta kara kwantawa saboda tana bukatan hutu a jikin ta don yasan bai sarara mata ba,sam
Don haka tausayi ta bashi saboda ko inba aure ba ya za,ayi wanan yariyar har ta dauke shi haka,
Ba bata wani lokaci takara komawa barci cikin gajiya da kasala,,

Falo ya koma cikin wani irin yanayi da yake jin kan shi yau wanda bazai iya mussalantawa ba,
Zaune yake yana tunanen shi may zai iya yi wanda zai sakawa wa yan nan mutane da wanan irin alherin da sukai mai,
Mahaifin jibrin gashi sam ya ki karban kudin da sukai mai sadaki da sauran dawainiya,
Ashe akwai mutane masu irin wanan a,kidar a duniya,
A gaskiya wanan halin saidai musulmai hausawa don dai yan kabilar su bazasu taba iya yin wanan halarcin ba,
Gaskiya shi bai ma san ya zai iya kwatanta halarcin wa yan nan mutanen,
Gashi yau dattijo yai mai wanan irin alherin da ba zai iya kwatantawa ba,
Saboda a duniya bai taba sanin cewa haka mace take ba, sai daren jiya,
Jiyan kwana yayi yana,sawa mahaifin maryam addu,a a cikin zuciyar shi,
Kofan gidan nasu yaji ana kwankwasawa, cikin mamakin kowaye ke mai sallama awanan safiyan,
Mikewa yayi zuwa kofan falon inda yake jin ana buga kofan,
Safiya ce tsaye hannun ta dauke da basket mai dauke da kuloli da kuma flask na ruwa,
Duk ta dan jike saboda dan yayafin da ake yi a garin,
Hanya shigowa falon yadan bata tare da kauce mata,
Sai alokacin yaga dan trolley din dake bayan ta na kayan maryam,
Taimaka mata yayi ta shigo da kayan inner room ya shiga da kayan inda ita safiya din ta wuce da basket din gurin dining,
A kwance ya samay ta ta dunkule guri guda alamar, tana cikin dan yanayi,
Batare da yatashe taba yabar dakin yakoma falo gurin safiya,
Zaine ya samay ta a saman kujera tana dan raraba ido ko zataga fitowan safiya,
Sai da ya zauna saman kujera da dan murmushin shi sanan yake ce mata maryam din na daga ciki tana barci,,
Yace don Allah ta taimakawa maryam din don tadan samu ta sake jikin ta,
Jiki ba kwari safiya ta mike zuwa cikin kuryan dakin,
Maryam dince tagani a kwance saman gado cikin wani irin yanayi na ban tausayi,
Tausayin aminiyar na,tane ya kamata, don tana ganin ta tagane cewa a kwai abinda ya wakana a tsakanin ta da Yusuf din,
Cikin barci maryam din taji nauyi kamar da mutum a kusa da ita a lokacin,
A hankali ta bude idon ta, ya sauke su ga safiya din wace ke zaune gefe tana karawa dakin kallo a cikin tsanaki,
A hankali maryam din ta furta sunan Safiya din wanda yasa safiyan juyowa da,sauri,
Maryam din ta yun,kura da niyar mikewa zaune amma sai taji wani irin ciwo daga kasan ta,
Hakan yasa ta komawa da sauri ta kara kwantawa,
Safiya tadan mike tsaye ta je gurin kanta ta dan gyara mata filon ta yadda zata ji dadin mikewa daga kwance
Da taimakon ta tasamu takai zaune amma kuma sai kuka ya kubce mata,
Safiya da kyat ta hade nata kukan tawayan ce da cewa haba maryam wanan kukan tun jiya kina ta abu guda ai yakamata ki ba kan ki lafiya hakana pls,
Hakana ta nuna wa aminiyar nata cewa bata fahinci komai ba akai,
Ki tashi ki shirya muje falo ki karya pls, ba musu maryam din ta daure cikin cijewa ta nufi bathroom inda tadan kara gasa jikin ta ,
Hakan yadan sata kara jin dan karfi a jikinta wanda yadan saita mata tafiyan ta,
A saman gado tasamu safiya ta fitar mata da wasu zani da riga na atamfa
Atamfar kore mai dan adon flowers ruwan kwai da fari, fari,
Dinkin fitted ya amshi jikin ta cikin kayan da yay iliya mijin anty ya dinka matane da sallah,
Ta gama sawa tana kokarin daura dan kwali a kanta ne,
Yusuf din ya shigo dakin kallon ta yayi yaga takoma mai wata sharrr da ita,
Har gurin da take tsaye bakin wani dan mirror ya karaso
Ta bayan ta ya tsaya suka hada ido daga cikin madubin ,
Cikin sauri maryam din ta dukar da kan ta a kasa saboda kunya da nauyin shi da take ji,
Murmushi yayi ya karaso gaban ta ya sa hannayen shi ya rungumota zuwa jikin shi ta bayam tare da shakan kamshin jikinta,
Sai da yawani ja numfashin shi ta yadda har tana iya jin shi sanan ya ce a hankali
I love you maryam with all my heart,
Thank you, for being, with me, yesterday night,
Idon ta ta rinstse tare da tarso wa wasu hawaye masu dumi acikin zuciyar rayuwan ta na ce mata yau ita maryam ce ta kwana da namiji,
Kara matse tayayi zuwa cikin jikin shi gam kamar wanda za a kwacewa ita, alokacin,
Zuwa wasu yan second's sake ta a hankali tare da wani jan numfashi, da ya sauke a hankali,
Cikin muryan tashi yai mata magana kamar da a kunnen ta yace Safiya na falo tana jiran ki da abinci,
Zarare jikin ta tayi a hankali daniyar wuce wa amma sai taji ya rike mata hannayen ta
Dago kai tayi tafan kalleshi cikin dan yanayin pls
Murmushi yasakar matata tare da sake mata hannun har tafara tafiya taji muryan shi yana cewa pls,
You should keep our secret ,
Kafin ya karasa tadago manya manya idanuwar ta taimai wanin kallo mai kama da harara,
Yana mai kallon ta har fice daga daki inda tafiyan ta yai bala,in bashi tausayi, sosai,
Safiyace ta samu a falon tana zuba mata pepper soup din kayan cikin rago a cikin wani plate mai dan zurfi,
A lokacin da maryam din ta dan ja kujera guda tadan zauna,
Ganin plate guda da cibi guda yasa maryam din dago kai takalli aminiyar nata tace,
May kike nufi da samin cibi guda aciki, muryan tama alokacin jin shi abin tausayi ne,
Safiya tace kedai ki karya don nasan haka kika kwana da yuwa jiya,
Idon ta ta lumshe saboda ambato jiya din da safiya tai mata,
Daren jiya karshen bakin cikin mai kunci, daren jiya ansha da wandake yin barci kar ku taba kaifin ta yafi na aska,
Safiya ta ce kisha mana maryam ga tea nan mai zafi a gaban ki,
Cikin daure fuska maryam din tace, idan bazaki sha ba malama ki fada min in tashi don saboda ke nake zaune a nan,
Safiya wace bata da wani zabi akai dole ta jawo kujera guda ta zauna tare suka shakomai da maryam din,
Sun kusa gamawa ne Yusuf din yafito cikin wasu Indian yard masu laushi da sulbi,
Sai kanshi ke tashi kamar wa a company turare,
Plate din yakai idon shi akai inda yaga ba wani abin kirki suka shaba,
Safiya ce tace mai uncle ga abinci a zubane yanzu saida yadan kalli maryam din sanan yace ,
I hope madam ta ci ita ko ?
M
Safiya tadan yamutsa fuska tace ba sosai ba dai
Maryam tadago idon ta takalli safiya din kamar wace zatai magana sai kuma tai shiru,
A hankali maryam tamike zuwa saman daya daga cikin kujerun dake a falon,
Inda itama,safiya ta kwashi kayan da,suka bata zuwa kitchen din gidan,
Yusuf ne ke cewa ta ahe da akwai wanda zai zo ya wanke su, anjima,
Amma sai safiya din tace bari kawai a wanke kada su bushe a hakan,
Zama yayi yadan zuba kadan ya fara sha amma sai yaji cewa bazai iya ba shima saboda cikin shi da ya kulle mai,
Amma yadan daure ya sha da dan yawa kadan gudun kar wani ciwo ya kama shi,
Mikewa yayi yana cewa a daidai lokacin da safiya din tadawo daga gurin wanke kayan,
Zan je ingaida su baba da gidan mahaifina,
Daga haka yadan kara gab da inda maryam din take kwance batare da jin nauyi ko shakkun safiya ba yakaiwa maryan din dan pick kiss a goshin ta,
Safiya tazo kusa da inda maryam take zaune nan tafara bata labarin bayan tagiyan ta jiya,
Da irin yadda Anty tai kuka sosai bayan tafiyan ta,
Dakuma shigowan da baba yayi gida,yau da safe
Inda yake ta sa masu albarka tare da fatan samun zuria masu albarka,
Maryam wace tadan kai kishin gide tadan lumshe idon ta saboda irin yadda take ji azuciyar ta,
Daga haka safiya tana mata hira barci mai nauyi ya kara kwashe ta,
Hakan yabawa safiya din dama tashi tagyara masu gidan tsab,

Yusuf ne zaune a gaban baba shida Jibrin da KB da Ismail,
Inda baba ke kara yiwa Yusuf din nasiha akan zama da iyali wanda hakan gaba dayan su sun ji dadin karin hasken da dattijon yai masu akan hakkin zama da iyali,
Wanda akasarin mazan yanzu suke subar da daman su saboda son zuciya,
Dagidan baba suka wuce gidan mahaifin jibrin din inda shima yai masu irin nashi gwargwadon fadan kamar yadda ya kamata,
Dafa can suka nufi gidan Abdulsamad shima yai ma Yusuf nasiha so sai akan sai yakai zuciyar shi nisa saboda yan uwan shi,
Da kuma matar shi don zasu dinga kawo mai fitina iri, iri,
Musalai kala kala dai yaba shi Yusuf din wanda sai da ya kara jin jikin shi ya mutu,
Sai bayan wani lokacine yakoma gida alokacin maryam tana falo kwance tana barci cikin gajiya,
Ginin tare da abokai yake yadan sa shi shafa mata fuska ahankali wanda hakan yasa ta bude ido sukayi arba, da junan su,,,,,,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI



Ya Allah kaja
kwanakin mu izuwa watan RAMADAN, kuma Ka Azurta mu da A dake cikin watan. Ameen Ya Allah, RAMADAN MUBARAK👏👏👏👏



ANTY NA, NAFEESAT HARZAMI TAREDA ANTY SAFEENAT wanan shafin nakune ku kadai fatan alheri gare ku akoda yaushe,




Sallama,sukaji daga kofan gidan azarin Yusuf su Jibrin ne amma kuma sai yaga ai matane,
Safiyace tai masu iso, da su karaso zuwa cikin gidan,
Dauke kowancen su take da robobin cincin da aka soya,
Har guda shidda ko wani roba da nau,in kalar abin da ke a cikin shi,
Tundaga dubbla guguru tsatsafa alkaki, dakuwa, da sai Donot, ,
Biyun wa yanda ba su kai shiddan girma ba naman kaji ne aciki soyayyaye,
Ba Yusuf ba har maryam din tana kallon wa yan nan kayan da mamaki,
Jibrin ne da KB suka karaso ciki tare da,sauran mata,
Matar mahaifin maryam kishiyar maman Anty Dije itace ke ce,wa Yusuf babane yace a kawo mai, shi da mahaifiyar maryam,
Yayi hakkuri da su saboda bai samu hadowa da kayan abinci ba abin yazo a girshi,
Kallon robobin yakeyi batare da yasan abinda ke a ciki ba,
Safiya ce tare da uwale, suka dinga bude robobin wani irin nauyi da kunya ne suka kama Yusuf a lokaci guda,
Maryam uwar kuka tana gefe idon ta ya wani ciciko da hawaye a lokacin,
Saboda tunanen da takeyi na cewa ina baba suka samu gidin yin wanan abin haka,
Tashi tayi tsam ta fada daki Yusuf wanda alokacin badon idon mutane ba ji yayi kamar ya rungumota,
Wanan matar mai magana na farko ke cewa sai zancen kayan gadon ta da sauran kaya zuwa gobe za,a kawo matasu gaba dayan su,
Cikin rashin fahintar zancen su Yusuf yafita inda su ma su KB da Jibrin suka bi bayan shi,
Fitar su yai daidai da mikewan uwale wace tabi bayan maryam din,
Zaune tasamu maryam abakin tamgamaymay gadon dakin,
Saida takarewa dakin kallo cikin kada kai ta zo gurin da maryam take zaune,
Jin shigowar ta yasa marya dan dago kanta idon ta taf da hawaye take kallon uwalen,
Tambayan da uwale tai mata yaba ta mamaki sosai,
Don ce mata tayi injin kin ta shiga ruwan zafi don tafiyan ki ya koma daidai,
Lokacin ne safiya ta shigo dakin ta wuce bathroom din nan ta kara hadawa maryam din ruwa masu dumi
Zaune suke suna hira har tafito daga bayin tare da dauro alwala,
Jikin ta yadan koma mata normal gefen safiya ta zauna, a,nan uwale ta shiga yiwa maryam din bayanan kissan zama da miji da yan uwan shi,
Tai mata bayani akan irin kayan matan da ya kamata ace maryam din tayi amfani da,su wanda zai kara mata haske a zuciyar mijin ta,
Uwale tace maryam nasan cewa ko a haka na barki bazaki taba wulakanta aidon mijin ki ba saboda Alhamdullahi kin samu duk wani horon da ya dace ki samu ga namiji,
Iyaka dai yadda zakiyi amfani da shine yanzu sai kin yi da gaske,

Yusuf yana fita waje tare da abokan shi yaja ya tsaya a bayan motar shi hannayen shi harde da juna,
Cikin marairaicewan murya yace wanan abinis too much for me,
Pls Jibrin ka gayawa baba cewa yadakatar da mahaifin su maryan hakana,
Matar da yaban kawai ya wadatar dani ga komai na duniyan nan,
Banda abinda zan saka mai dashi sai dai godiya saboda ya mai dani cikkaken mutum
Ya, bani macen da ban taba sanin cewa zan ita mallakan irin taba aruyawa na,
Da sauri su KB da Jibrin din suke kallon shi don jin abinda ya ce daga karshe,
Yadaga gira tare da kallon ido da ido yace mace kamila mai tarbiya ga mutunci da girmamana gaba wace ta rike darajan ta da martaban ta har zuwa ga mijin ta awanan zamanin ai tafi ko wace mace zama mafi daraja da kima,
Sun gane mai yake nufi da hakan gaba dayan su suka ansa da fadin hakane,
Don gaskiya Yusuf ya fadi irin wa yan nan matan matane na rufin asiri,
Don akasarin su da wuya ka samay su da wani matsala a rayuwan aure,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login